Showing 18001 words to 21000 words out of 73076 words

Chapter 7 - Ciwon Ya Mace Book Compelet Lamido

18 Aug 2026

652

wayar da ta ga yayi cikin dare, kenan baya
bacci koma ya na yi to bana kirki bane, sannan ganin shi cikin yan fim yasa ta fara tunanin
domin dama batasan aikinsa ba tasan dai ya na zuwa Office amman bata San me ya ke acan
ba, wata zuciyar ce ta ce kila dai yana zuwa gurin yan matanshi ko abokanshi amman Abba
nasan bazai barshi yayi wasan Hausa ba.
Tsakanin gidan su dana su Auwal babu nisa, dan haka nan danan ta isa, ta na tura get din
gidan ta hangi takalman maza da yawa a bakin kofar wannan ya tabbatar mata da suna da
yawa acikin dakin.
Bakin kofar ta tsaya ta rangada sallama cikin zazzakar muryanta, da ga cikin dakin ta ji an
amsa ganin babu wadda ya fito Kuma babu motsin tafiya ya sata sake yin Sallama yayin da aka
sake amsawa daga ciki tare da cewa shigo mana.
Yamutsa murya Nur ta yi sannan ta tura kofar tare da shiga cikin dakin, suman tsaye ta yi
ganin Sumayya zaune Yaya Abdallah ya daura kansa akan cinyanta, idon shi rufe yayin da
Sumayya ke wasa da kasunbarsa, kasa cire idonta ta yi a kansu, ta na mamakin wannan
lamarin bakinta sake. Ita ko Sumayya tun da suka hada ido da Nur tai saurin cire hannunta a
jikinshi tare da rasa abin yi.
Da ga bayanta ta ji ance, "Abdallah ga kanwarka." Da saurinshi ya bude idonsa tare da
waigowa ya kalli Nur sannan ya fara kokarin tashi zaune yana me cije lebenshi na kasa, bayan
ya tashi zaune ma saida ya damki sumarshi sannan ya ce, "da ga ina? Me ya faru?" Kawar da
kai Nur ta yi sannan ta fito da hannunta da ga cikin hijjabin ta mika mishi wayar tare da cewa
"Inji Aunty" Hannu ya mika ya amsa dan haka Nur ta juya da nufin ficewa a dakin, sai a wannan
lokacin ta kula da wasu matan dake gefe su biyu tare da Auwal da wasu abokan nasu guda
biyu. Cikin sanyin jiki sosai ta fice a falon a daidai lokacin da Abdallah ke cewa, "Inazuwa karki
wuce, ki jira ni anan kinji" A harabar gidan ta tsaya nesa da dakin kadan, fitowan Sumayya ta
gani dan haka ta bita da kallo, babu abin da ke daure mata kai kamar wannan al'amarin,
wannan lamarin shine mafarin gigicewarta domin kuwa Sumayya tana da aure da yaranta biyu,
"ina ta baro mijinta ta taho nan gurin? Anan ta kwana? Ko kuwa da safe tazo? Mijinta baya gari
ne? Ko kuma yana garin amman ta tsallakeshi ta fito ta na dakunnan gemon katon kawai?
Yaranta fa? Shiryasu ta yi suka tafi makaranta ko kuwa?" Nur ke tambayan kanta, ganin babu
me bata waddan nan amsoshin ya sa ta sakin ajiyan zuciya tare da dauke idonta akan get din
gidan.
Adaidai wannan lokacin Yaya Abdallah ya fito har ya kawo inda take bata motsa ba, cikin
daure fuska ya ce, "Mu je" Gabanshi ta shiga ta fara ta fiya da sauri, ganin haka Abdallah yai
saurin cewa "Ke tsaya" Nan take ta tsaya tare da kallon shi, kawar da kanshi yayi tare da cewa,
"Me kike son nasiya miki?" Kawar da kai ta yi sannan ta ce, "Babu komai" Yawo ya hadiye
sannan ya ce, "A'a mu je na siya miki wani abu mana" Shiru ta mai har suka isa kofar gidan,
cikin bada Umarni ya ce, "Tsaya a nan na dauko mota mu je ki zabi abin da ranki keso ko nawa
ne zan biya" Turo bakinta ta yi gaba tare da cewa "Yunwa nake ji bari naje naci abinci tukuna"

"Ki tsayani nace ko" Abdallah ya sake fada cikin yar tsayawa.
Dole ta tsaya, domin ba yadda ta iya dashi, cikin gidan ya shiga ya fito da mota duk tana tsaya
kawai tana binshi da kallo, "Shiga" Abdallah ya fada cikin bada Umarni, wannan karon ma shiga
ta yi batare da tace komaiba,. sannan ya daga waya ya kira Mamy ya sanar mata da in da za su
sannan ya sauke wayar yana satan kallon Nur. Koda suka isa dankareren kantin da kanshi ya zabar mata kayan shafa da turaroka, sannan ya
ce, idan akwai abin da take so ta dauka. Kallon shi kawai ta yi ta kauda kai bayan sun fito a
gurin suka dauki hanyar komawa, ganin sun kusa gida ya waigo ya kalli Nur tare da fadin "Na
miki siyayya bakice min kin gode ba? Can kasa-kasa Nur ta ce, "Na gode" Murmushi ya yi
kadan sannan ya ce, "Ko ke fa? Kanshi ya shafa sannan ya ce "Nasan kiga Sumayya ko?" Kai
Nur ta da ga alamar eh, Abdallah ne ya cigaba da cewa "Ta yiwa su Mama kara ne tazo duba
jikin Auwal, kinsan ya kwana biyu babu lafiya" Sanyi jikin Nur ya kara; daker ta iya da ga kanta
ta kalleshi. Ganin haka Abdallah ya yi ajiyan zuciya sannan ya ce, "Amma dai duk da haka karki
fada ma Mamy, kinsan har yanzu ba dadinta nake ji ba, tun akan wancen batun da aka gaya
miki karya ki ka hau kai kika zauna, ki ka kasa yiwa yi min adalci alhali hakan ba gaskiya ba ne,
kuma kinfi kowa sanin ba halina bane, dan haka ina rokon ki dan Allah kada ki gayawa kowa.
Ta gefen ido Nur ta sata kallon shi sannan ta ce, "To" Numfashi Abdallah ya fesar sannan ya
ce "Kin min alkawari?" Wannan karon kai Nur ta daga a dai-dai lokacin da suka shiga gida,
kokarin Bude motar ta fara Abdallah yayi saurin cewa, "Nur nasan halinki ke din kina da sirri,
kuma bakyacin amana" Wannan karon ma dai Kai Nur ta daga sannan ta fice acikin motar. Lokacin da Nur ta shiga gida kallon mamaki Mamy ta yi mata, ganin ta rike da ledoji ga kuma
Abdallah da ke binta abaya. Wani shashin na zuciyarta ne ya tuna mata baya kadan, dan haka
ta kawar da tunanin komai. Abdallah ko bebar falon ba Saida ya ga Nur ta gama cin abinci ta
kwashe ledojin siyayyar da yai mata ta shige dakinta. Washegari ta kama Moday dan haka Nur da wuri ta wuce makaranta.
***
"Abdallah wai yau lafiya kuwa? Yanayin ka kamar mara lafiya" Mikewa yayi tare da fadin,
"Bacci ne be isheni ba Mamy Sam ban rutsa ba" Da kallo Mamy ta bi shi sannan tace, "Kuma
kace lafiya lau kake?" Yana Shirin barin dakin ya ce, "Eh banajin ciwo sam." Bayan ya fito kofar
gida wani ajiyan zuciya ya sauke sannan ya ce afili, Tun da har ta fita bata gayaba nasha in sha
Allah, hannunshi ya mika ya shafa suman shi sannan ya sake cewa dole tabar gidan nan,
akullum kara tsanarta nake yi ta takura ni da yawa" Saman motarshi ya zauna tare da neman
hanyar dazai yi maganin matsalar da take Shirin fin karfinshi
****
Nur da Helen akan hanyar su ta dawowa daga makaranta, da kafa suke tafiya yayin da Nur ke
cewa "Helen ki dago kafa mana, yau naga kina nafiya ne lakakai-lakakai.
"Wlh yunwa nake ji Nur, kwana na uku basa wani kwakwaran abinci a cikina ba" Da sauri Nur
ta kalleta tace "Sai me to?" Cikin halin ko in kula ta ce, "Ya ce bashi da kudi me gidan, kudin
dake hannun Mamma kuma duk sun kare" Lumshe ido Nur ta yi sannan ta ce "Matar shi fa?"
Hmm suna yin abincin su suci..." Tun kafin ta rufe baki Nur tace, "Wannan ba daidai ba ne,
shiwai bejin tsoron Allah ne, kato dashi ya na yiwa Maman shi horon yunwa? Na ga baya jin
tsoro ko shakkar mama, shiyasa ada bana yadda idan akace itace mahaifiyarshi, ya kamata
asamu wani yayi mai wa'azi.wai ku baku da wani Malami ne da zai nuna mishi mahimcin

iyaye?"
"Hmmm, Mamma ta hakura da zama tare dashi, ta ce kudin mota kawai take nema mu koma
Kauyen su, Nur kila karatu na zai tsaya kwanan nan"
Sosai maganar ta doki zuciyar Nur cike da tausayawa tace "Karki yi wasa da karatunki, gara
kuci gaba da hakuri, ko Kuma ku dawo gidanmu ku zauna idan har kun gaji da zama anan"
"Mamma ta gaji Nur, kullum ta na kuka bata baccin kirki, idan ya ga tabar kusa dashi za'a iya
samun saukinshi"
"Ni dai karku tafi Helen, yanzun kizo muje gidanmu kici abinci kafin kije gida"
"Da sauri Helen ta kalli Nur ta ce, bazan iya zuwa ba bayan nasan mama bataci ba, bama ta
da lafiya tun shekaran jiya"
Adaidai lokacin da suka kawo kofar gidan su Helen din Nur ta ce "Mu je to idan kika ce saiki
kamai Mama nata"
Jin haka yasa Helen tabi Nur sai dai Koda sukaje bata tsaya ci ba zuba mata a ka yi ta tafi
dashi.
Bayan tafiyan Helen ne Nur ta bawa su Mamy labari halin da su Helen suke ciki, sosai suka
tausaya ma su, saidai mama na tsoron taimakonsu saboda Poul ba kirki gareshiba
***
Washegari misalin karfe 04:12pm Abdallah ne zaune a gaban Abba, tun da Abba ya kirashi a
waya ya zufa taki tsayawa har yanzun da yake zaune a gaban Abba, zallar bacin rai da
damuwa kawai ya ke hanga a fuskar Abba, dan haka hankalin shi ya tashi sosai, kosawa yayi
yaji dalilin kiran, sai dai Abba yaki kallonsa sai aikin Bude takardu yake kuma fuskarshi babu
wasa ko kadan acikinta, rabon da yaga fuskar Abba haka har ya manta saidai wata zuciyar na
ce mishi kila zato ne kawai yake yi, yayin da wata zuciyar ke tuna masa da matsayin Nur a gurin
Abba, Sunanshi da yaji Abba ya kira shi ya katse mishi tunanin azabure ya dago ya kalleshi..
CIWON 'YA MACE
By
Fadila Lamido

ADABI WRITER'S ASSOCIATION



Page 15-16

Dagowa Abdallah ya yi da sauri ya kalli Abba, saidai gani yayi kamar bashine ya kira sunan
nashi ba, dan haka gabanshi ya cigaba da faduwa, zuwa can ya dake cikin sunkuyar da kai ya
ce, "Abba lafiya kuwa?" Fuskar Abba daure tamau ya dago ya kalli Abdullah sannan ya ce, "Na
ji wani mummunan al'amari da ga gareka Abdallah, banso ace na yi maka magana yanzubaz
saidai hankalina yaki kwanciya, nakasa zuba ido koda na kwana biyu ne, idan abin da naji
gaskene zan gwammaci matuwa da ganin irin wannan al'amarin"
"Ni Kuma Abba?" Abdallah ya fada tare da tattara hankalin sa akan Abba gabanshi na faduwa
sosai.
"Kai fa Abdallah, ina son in san menene alakanka da Sumayya? bana son zagaye-zagaye,

abu daya na tambaye ka, dan haka amsan na ke bukata, ina son in san ta in da ka kulla alaka
da matar aure dahar, karkamin karya" Zufa ne ke kara yanko wa Abdallah, tare da nemo
kalmomin da zai kare kansa da su wurin Abba, gefe guda na zuwaciyarshi kuwa na kara zuzuta
mishi kiyayyar Nur, tare da rayawa azuciyarshi dole ne ya kirkiro sanadin da zatabar gidan. "Da kai nake magana" Abba ya sake fada wannan karon a hasale ya ke.
Cikin tashin hankali Abdallah ya sunkuyar da kanshi batare da ya shirya ba, jin sunan
Sumayya a bakin Abba, daker ya iya daurewa ya ce, "Abba waye ya fada maka?"
"Abdallah amsan kawai nake son ka bani, aina naji ko waye ya gaya min wannan ba matsalarka
bace"
"Abba bani da wani alaka da ita" Cikin Ido Abba ya ke kallon Abdallah gani yayi zufa sai
gangaro masa ya ke dan haka ya ce, "Hakika zan ji mamaki kwarai idan na tabbatar da ka na
aikata irin wannan abubuwan, domin ko kadan be yi kama da ɗabi'un ka dana sani ba, kana da
ilimin ka daidai gwargwado, sannan ka mallaki hankalin kanka, kasan cewa kebewan da macen
da ba muharamarka ba haramun ne, bare Kuma matar aure, Babana me ya kaika wannan
danyen aikin?"
"Abba ni ban aikata hakanba Sam, yadda dani da kuke yi yasa ake son a bata ni a gurin ku,
kuma nasan cewa ba kowa bane zai yi irin wannan maganar sai Nur, dan yariyar nan yanzu..."
Katseshi Abba yayi da cewa, "Me yasa zaka ce Nur ce ta fada?"
"Abba baka sani bane, yariyar nan ta dade tana son taga bayana, kwanaki Nur ta hadani
Mamy akan maganar Sumayya, bansan da ga Ina aka turota ta batani a wurin ku ba, taje ta ce
ma Mamy wai ina neman Sumayya, haka ran Mamy ya faci kiris ya rage ta tsine min, na yi
kokarin wanke kaina awurin amma Mamy taki bani dama, kuma har yanzu ta na akan haka,
sabo da kawai Nur ta fada mata, kenan ita Nur bata karya nine makaryaci, aranar raina ya baci
har na daki Nur, ganin haka ciwon Mamy ya tashi, bansan me na tarewa Nur ba acikin gidan
nan Abba, idan baka manta ba kwanaki a gabanka ta jefeni da babban kufin kwalba batare da
na mata wani abu ba, ko na mata wani abu ma ai be dace tamin haka ba, yanzun kuma wurinka
take son batani, me na tare mata Abba" Karake maganar yayi kamar zai fashi da kuka; dan
haka Abba ya ce' "Babu abin da ka tare mata, wata kila gaya mata ake waje, amman akwai
wadda taci min adakin Auwal ta ganku tare da idonta ba gaya mata aka yi ba"
"Abba to ta kawo wadda ya fada mata, idan ma ita ta ganni ta kawo shaida, ni zan iya kiran su
Auwal su zamar min shaida, waya yake kokarin dagawa Abba ya ce "Dakata Babana, duk ba
wannan bane mafita, ko ka aikata ko baka aikata ba Ina baka sharawa kaji tsoron Allah a
dukkan lamuranka, sannan abu na gaba shi ne, maganar aure. Ina son ka yi aure nan kusa,
dan banga abin da kake jira ba."
Jikin Abdallah da sanyi sosai ya ce, "Abba ka manta da mgnr karutu da zan tafi nan da wata
biyu masu zuwa, kuma zai iya daukana tsayon shekara daya kafin na dawo"
Kara daure fuska Abba ya yi tare da fadin, "Toh yanzun Yaya ka ke nufi?"
"Idan na kammala zan yi Abba."
"Babana bani da wani buri ayanxun illa inga ka yi aure, Kuma nan kusa nake so, idan tafiyan ta
tashi saika wuce da matar ka.
Shiru Abdallah yayi tsayon lokaci, zuwa can ya ce "Shikenan Abba, zan yi in sha Allah"
Yauwa zan yi tsananin farin ciki da hakan, nasan a kodayaushe kai me bin umarnina ne, ina
son akan auren ka burgeni kazo min da labarin nan kusa"

Godiya yawa Abba, sannan ya tashi ya fice jikin sa a sanyaye. Kai tsaye dakin sa ya wuce
cike da haushin Nur dankare a zuciyar shi, tunanin ya shiga mai zurfi akan shakkun da Nur tasa
azuciyar Abba da Mamy game dashi, mafita ya shiga nema idonsa jawur akarshi hankalinsa ya
tsaya akan cewa yayi auren kawai domin shine zaisa Nur ta fita hanyarsa. Bayan sati daya Nur ce kwance tsakiyar gado bayan ta dawo Islamiyya, har yanzun tunanin
Abdallah da tagani tare da Sumayya take, sosai abin ke daure kanta, tana cikin wannan Yana
yin ta ji muryan Helen dan haka ta tashi zaune a daidai lokacin da Helen din ta shigo dakin,
yadda taga fuskan Helen ya sa hankalita tashi sosai tare da fadin lafiya? Nur ni da Mamma ne, na zo in gaya miki ne zamu tafi, idan mama ta ji sauki kila mu dawo...
Katse Nur ta yi tare da cewa "Karatun ki fa?"
"Ban sani ba Nur, ni dai kawai nasan Mama bata da lafiya shine abin da ya dame ni yanzu,
nina ce mata ta zo muje mu nemi lafiyarta"
"Babu Inda zakuje Helen, ki shigo da Mamma nan gidan barin je inyiwa Abbanmu magana.
Jimmm Helen ta yi tana kallon Nur tare da mamakin Kaunar da take nunawa a garesu batare
da ta damu da banbancin addinin dake tsakanin su ba, bayan Nur ta fita dakin tabi da kallo
komai tsaf, duk da cewa gidan Poul keraren gidane amma sai ya fiye mata can ban sha'awa,
haka nan taji kaunar gidan na ratsa sassan jikinta, dan haka ta saki ajiyan zuciya mai cike da
kwanciyar hankali.
****
Nur zaune gaban Abba, bayan ya sallami wani dake zaune daf dashi ya ce, "Nur! Cikin wasa da
hannun Nur ta dago kanta, Cike da fara'a Abban ya ce, har yanzun baki bar damuwan bane? "
"Na bari Abba"
"Yauwa ki kwantar da hankalin ki, komai zaizo karshe, na yi magana dashi sosai, a yanzun haka
maganar da nake miki aure

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login
google.com, pub-9213700357025247, DIRECT, f08c47fec0942fa0