Showing 69001 words to 72000 words out of 73076 words
Ni gaskiya bazan boye
miki ba, ina ganin laifinki acikin wannan lamarin"
"Mene ne Laifin nawa Nur?"
Aunty karkiga kamar na miki rashin kunya dan Allah ki gaya min, Yaya Abdallah mu bashi bane
Baban Ummi?, idan kuma bashi bane to waye Aunty?
CIWON 'YA MACE
BY
Fadila Lamido
ADABI WRITER'S ASSOCIATION
Page 50
Zamewa Aunty Bilkisu tayi daga kan gadon zuwa kasa, tare da fashewa da kuka, saida tayi
kuka ma'ishi sannan tace, "Nur bantaba soyayya da wani namiji ba sai shi, ni nama kaina cikin?
Shine saurayina na farko kuma shi na aura, acikin kwana shidda da mukayi a tare be kusance
ni ba tabbas, amman akwai wani srirri tsakanina dashi" Cikin rashin fahimta Nur tace "Har
yanzu baki bani amsa ba Aunty" Hawaye ne suka zobowa Bilkisu alokacin da take cewa "A
zahiri bashi bane babanta, amman a badili bata da uban da ya wuce shi." Mikewa Nur ta yi tare
da cewa, "Yaya Abdallah yasan da hakan?"
"Hmmm, be sani ba kamar yadda ya nuna"
To mai yasa kikayi shiru tun abaya Aunty?
"Nur! Nayi shirune sabo da bani da hujja da kuma yanayin yadda ya bijiro da maganar ya fini
gaskiya, babu wadda zai fahimce ni"
Shiru Nur ta yi tsawon lokaci zuwa can tace, "Tunanin ki kenan babu wadda zai fahimceki
amma akwai, Aunty na shirya taimaka miki ki fita daga cikin wannan zargin"
"A'a, Karki fara Nur, zaki tayarmin da fininane kawai na samu abin ya fara kwanciya, bazaki iya
ba Nur, kinyi kankanta, iyayenshine kawai zasu iya tursashishi, saidai su dinma babu hanyar da
zasu fahimce ni."
"Aunty idan anyi shiru zancen ya kwanta mai zakicewa yariyar nan alokacin da ta bukaci son
ganin Ubanta? Ni dai ki bani hadinkai kawai."
"A'a Nur, ki bari kawai, Kinga akwai zumunci a tsakanin ku, wannan maganar tana iya lalata
muku zumunci, kuma daga karshe baza'a fahimce ki ba, nagode Nur bazaki iya ba."
"Zan iya Aunty, bazan yi maganar nan da kowa a gida ba, na yi wayau yanzu ba yadda kike
tunani bane, karar shi zaki yi a kotu, ni kuma zan tattara hujjoji in tsaya miki, abun mai sauki ne
indai kin bani hadin kai, dole zai amsa yariyar nan." Shiru Bilkisu tayi tare da cewa "Su Mamy
ma ai bazasu yarda ba Nur, da sunji zaki shiga maganar komai na iya faruwa." "Babu ma wadda zai sani Aunty, shi ya Abdallah takardan kawai za'a kai mishi sai in yaje koto"
Nutsuwa ne ya fara shigar Bilkisu, domin bata tabayim irin wannan tunanin ba, ajiyan zuciya
Bilkisu taitayi, yayin da take karajin nutsuwa na shiganta, saidai tana ta tunanin zumuncin Nur
da Abdallah karya samu tankarda, dan haka Nur ta nuna mata ko ba itaba akwai kawayenta da
zasu iya taimakawa, jin haka Bilkisu ta gamsu, har suka yanke karahen watan za'a shigar da
karan kotu. Wannan ranar cike da farin ciki Nur ta koma gida, haka ma Bilkisu wani irin nishadi
taji yana shigarta domin kuwa idan har akwai yadda za'ayi kowa ya gane ita ba yar isa bace
zarafi kowa farin ciki da hakan. Nur kuwa aharabar gidan ta samu Abdallah da Yaya Bashir
zaune, sun shinfida babban darduma, wucesu tayi bayan tawa Yaya Bashir sannu, daker ya
amsa tare da hararan bayanta, Abdallah ne ya kalli Bashir yace "Wai Bashir mai ya hadaka da
yariyar nan ne wai? Abin mamaki yake bani, yadda kake mata yanzun"
"Hmmm, Abdallah na kule sosai da ita, kaima ai kaban haushi shiyasa ban gaya maka ba, tun
kafin abin yayi nisa na kawo maka zancen kaki saurarona, har ankai matakin da yanzun Nur ta
tage wai wannan Poul din zata aura"
Wanni irin kallon Abdallah yayi wa Bashir tare da cewa "Da gaske ko wasa?"
"Wanni irin wasa kuma, dan Allah waike duk gurmin da akayi agidan baka sani ba?"
"To ni inama nake zuwa gidan, ko nazo ma ni aba'amin maganarta, yanzu ita da gaske take
zata aura wadda ba musulmiba?"
"Ai ya musulunta, tun shekara 6 baya, kuma wallahi sabo da ita ya musulunta, sun dade tare
wannan abun Yana Kona min rai, yama raina mutane, abin ma da yake kara kuna min rai, wai
Abba cewa yayi idan ta dage bashi ita zaiyi, dan bazai mata auren dole ba, narasa mai yasa
Abba ke lallabata, duk abin da take so shi yake mata, wai yasa a mishi bincike akan halayyar
yaron a yanzun tunda shi take so"
"Wanni irin kallo Abdallah yayiwa Bashir, tare da cewa, "Aiko bazata aure shiba, ka bari zanyi
maganin abin, ai naga ta girma yanzu, har wani kwambu takewa mutane, ni tama wuce da ajina
ko kallona bata yi bare da kaisheni, ni banso Abba ya barta ta yi karatunbama, amman zanyi
maganinta idan bata gaidani dan Allah ba zata gaidani dan dole" Mikewa Bashir yayi cike da
haushi yana cewa "Narasa wanni iri so Abba yakewa yariyar nan, sam baya son bacin ranta,
nasan tun da yace haka babu wadda ya isa ya hanashi yayi mata abin da ranta yake so cikin
mu.
Bayan Bashir Abdallah yabi da kallo, har ya fice acikin gida, sai fada yake kasa-kasa, da alama
sosai abin yake sosa ranshi, mikewa Abdallah yayi shima ya nufi cikin gidan, adakin Mamy ya
samu Nur zaune kusa da Mamyn, sallamar da yayi Mamy ta amsa itako Nur dagowa ta yi ta
kalle kofar ganin Abdallah ne ta kauda idonta tare da mikewa tsaye ta dauki wayarta da kwanon
cincin din dake gabanta ta fice batare data kalli Inda yake ba, Binta da kallo Abdallah yayi har ta
jawo kofar sannan ya kalli Mamy alokacin da take cewa Bashir fa?
"Ajiyan zuciya yayi tare da cewa ya wuce ai, amma kila zai dawo anjima"
"Be min sallama ba, naso na ganshi kafin ya wuce"
"Lafiya?" Abdallah ya fada bayan ya tsare Mamy da ido"
"A'a be shafekaba maganar Nur ne, kuma aikai ba shiga lamarinta keke ba" Mikewa Abdallah
yayi tare da cewa "Kai Mamy, wai be shafeni ba" Juyawa yayi yana kokarin fita adakin tare da
cigaba da cewa "Shikenan dai" Bin bayanshi ta yi da kallo har ya fice sannan ta tabe baki tare
da cewa "Aure dai ya gagari Abdallah idan ma wani abin yake har yanzun Allah ya shiryeshi ya
dawo dashi kan haya kan madaidaiciya. Lokacin da Abdallah ya fito Nur na zaune afalo, can
gefe ta juyar da kanta, shiko ta gefen idon sa yake kallonta har ya fice afalon. Adaren ranar
Bilkisu ta kira Nur a waya bayan ta mata bangajiya tace, Nur hankalina yana ta kara nutsuwa
akan maganar shigar da karan Abdallah, sai dai ina tunanin karya rofe ido ya min rashin
mutuncin da yayi min abaya.
"Hmmm, Aunty Bilki shari'a sabanin hankali ce, nasan halin Yaya Abdallah fiye da yunwar
cikina, idan baki mantaba bama shiri ni dashi, nasanshi farin sani makirine, nasan ta yadda zan
bollo mishi"
Amman Nur sai nake ganin idan na sakaki agaba amatsayin wadda zata karenj a kotu rikicin
ku da Abdallah zai kara gaba kuma ban miki karaba"
"Kara? Har kike maganar kara Bilkisu ai wannan abin kamar taimakonshi ne za'ayi idan ya
yaga laifina nasan daga karshe iyayenmu zasu fahimta, yanzun da baya magana dani din kare
ki nayi, ai ki cire wannan tunanin, kisa a zuciyarki cewa baki sannan alakarmu dashi ba, ni
Kuma na miki alkawarin in sha Allah Abdallah saiya karbi Ummi, Ina da tarin hojjojin da zaisa
Alkali yabawa Abdallah Ummi amman sai da hadin kanki, wai to mai ya hana Abdallah ya
kusanceki tsayon kwana shidan?"
Wallahi Nur haka kawai bayan ya gama wasa Dani yace wai mukulla.
Lumshe Ido Nur tayi, ganin hakarta ta fara cimma ruwa, cikin dibara Bilkisu zata fada mata
yadda akayi Abdallah yayi mata wayau, afili kuwa cewa ta yi, "Ai tun barko naso da aka tambayi
ki ya kusanceki kice eh kawai, tunda ya kwana dake adaki daya akuma kan shinfida daya kuma
saida kika cika wata goma da auransa kika haihu dan haka aure ya bashi, matsalar kawai ke da
kika ce be kusanceki, to amman nasan yanzun zaki fada min komai ai"
"Ai ni Nur yanzun mafita kawai nake nema abin yaki ci yaki cinyewa"
"To kije ki shirgar da karanshi koto da zaran an kawo mishi sammaci zanzo muyi magana"
Sallama sukayi bayan Bilkisu tawa Nur godiya.
Bayan sun gama waya falo ta fito ta zauna cike da tausayin Bilkisu a yammacin ranar gaba
dayan su suna falon Mamy Aunty sai Nur, hira suke sama-sama sukaji sallamar Mamma, cikin
sauri Nur ta juya ta kalleta sannan tai saurin rufe idonta kamar mai bacci, dan a yanzun yar
kunya suke shiyasa sai su jima basu hadu da Zainab da ita ba domin yanzun ba shiga cikin
gidan take ba, hakama Zainab bata zuwa tunda ta gaya mata abin da Yaya Bashir yace akanta ,
su Mamy ne suka amsa sallamar bayan ta shigo suka nuna mata wurin zama, Ganin haka Nur
ta tashi zaune tare da gaida Mamma cike da jin nauyinta, itako Mamma cike da nuna kauna ta
amsa, mikewa Nur ta yi ta nufa daki alokacin ta taji Mamma na cewa "Mammy wurin ki nazo"
dan haka ta kasa shigewa dakin ta makale jikin bango, muryan Mamy taji tana cewa "To gani
Mamman Zainab" Cikin nutsuwa Mamma tace "Mammy Nur na zo akan maganar Nur da Aliyu
na, naji cewa yanzu kunsan suna son junansu, dan Aliyu ya gaya min abin da ke faruwa, Aliyu
na son Nur sosai, ta dalilinta rayuwarshi ta canza, ta dalilinta yana kula dani da kanwarshi,
Kuma har gobe kullum hallayyarshi dada gyaruwa take, na fahimci a yanzun da rayuwar Nur
yake koyi, Duk irin tsaron da ya kula ana bawa Nur a gida irinshi yake bawa Zainab, duk abin da
ya kula inaso kafin ma in fada yana mini, tunda Aliyu ya musulunta bansake zubar da hawayen
damuwarshi ba, domin kullum nunawa yake yafi jiya kirki, a yanzun nasan samun shi nasan
rashinshi, haka kuma dazaran ya shiga damuwa gabana yake kawo damuwarshi, bazan boye
muku ba Ina jin dadin wannan yanayin da muke ciki, Kuma na tabbatar da cewa Nur ce ta kawo
haske acikin rayuwarmu, ya jima da rabuwa da matarshi yanzu ko sunanta baya son a ambata,
Mamyn Nur, Dan Allah ku taimakeni bana son ya rasata, sun dade tare, sun saba da juna,
tunda yaji abin da Babanta yace ya shiga damuwa walwalarshi ta ragu, zamowa Mamma ta yi
kasa ta Isa gaban Mamma ta rike kafarta tare da cewa, "Dan Allah ki taimakeni kuyi hakuri
karku nuna kyama a garemu"
Yadda Mamy taji ta rukurkume kafarta yasata dafa kafadar Mamma tare da cewa tashi
Mamman Zainab, ai matar mutum kabarinsa ce, duk yadda wani yaki ta da Aliyu, idan Allah ya
nufa matarsa ce babu wadda ya Isa ya hana, haka Kuma duk iri son da danginta sukewa Aliyu
idan Allah ya nufa ba mijinta bane ko ranar auren ne baza a daurashi ba, abin da nake son ki
gane shine, wani baya taba auren matar wani, tun da naji wannan labarin addu'a nake idan
Alheri ne Allah ya tabbatar, idan Kuma babu alheri Allah ya canza musu da mafi Alheri, shi
kanshi Abbata gabanta ne ya tsaurara abin, amman a bayan idonta addu'a yake Allah ya zaba
abin da yafi alheri" Nur dake labe ajiyan zuciya tayi tare da murmushi, acikin zuciyarta take
cewa "Ai nasan Abba bazai matsa min ba, kuma nasan idan na dage Aliyu nake so zai aura
minshi, domin shine ma alheri, saboda shi nake so, Kuma na dage da addu'ar Allah yasa ya
zamo mijina" Muryan Aunty ta jiyo tana cewa "Mamman Zainab ki kwantar da hankalin ki, kema
ki nemi zabin Allah, amman ko kadan ba yadda kike tunani bane" Mikewa Mamma ta yi sannan
tai godiya, tana kokarin fita Mamy tace "Kuma idan Abbanta ya dawo zan sanar dashi zuwanki
dan ya kara daukan abin da mahimcin" Sosai Mamma taji Dadi ta fita tana godiya bayan Mamy
da Aunty sun Dan taka mata. Daki Nur ta koma cike da farin ciki, tshinta kanta ta yi dayin dariya
ita kadai a dakin. Adaren ranar taji Baffah yazo, Mamy da Aunty falon Abba suka tafi, Dan haka
ta fito falo ta zauna, tun tana jinta cikin nishadi har ta fara gajiya da zama, domin gani ta yi har
goma ta buga batare da sun dawo ba, mikewa ta yi da Nufin wucewa daki taga su Mamy sun
shigo, Aunty ce ta dubeta tace "Ina zaki? Bacci nake ji, zanje in kwanta" Nur ta fada tana
kokarin famintan fuskarsu, Mamy ce tace "Ki yi sauri ga Baffanku can kije ku gaisa" Aunty ce
tace "Anya kuwa taje?" Ji tayi Mamy tace "Gara taje tun da Abban su ya yanke magana bazaice
komaiba Kuma" Ganin sunyi shiru Nur ta juya ta fita, hangosu ta yi a harabar gidan suna
kokarin fita shida Bashir, dan haka ta daga daga Murya tace "Baffah!" Waigowa yayi ya kalleta,
sannan ya juya yaci gaba da tafiya, Bashir ma Waigowa yayi ya Dan kalleta sannan ya bode
motar ya shiga, shima Baffah cikin motar ya shiga ya zauna, Adaidai lokacin da Nur ta tsaya
bakin get din tace "Baffah Ina wuni" Daker ya iya Bude baki yace "Lafiya lau" kafin ta sake cewa
wani abu taga Yaya Bashir ya ja motar sun wuce, da sanyin jiki ta koma cikin gida, tana kokarin
shiga falon taji su Mamy na cewa "Ai dole aji ra'ayin Ummynta, ba a yanke hukunci ba" Jin haka
yasa tana shigowa ta masu sammala ta shige dakinta cike da damuwa, bayan ta gama tunanin
yadda Abba ya amsa gaisuwarta, ta koma tunanin Ummy da taji su Aunty na maganar za'a
nemi shawaranta, tsaki taja fali, tare da cewa "Wai dama haka ake shiga damuwa lokacin aure?
Kowa sai an nemi shawaranshi? Yanzu nasan ana tambayan Ummy sai ta yi shawara da
yaranta, duk su gama zugeta tunda ba sona suke ba" wayarta ta jawo ta Kira Ummy, cikin
yanayi irin na wadda ya fara bacci tace, "Nur lafiya bakiyi Bacci ba har yanzun?"Eh Ummy, cikin
nutsuwa ta fara bawa Ummy labarin Aliyu daga karshe tace "Ummy idan an tambaye ki kice kin
yarda karkiyi shawara dasu Yaya Jamal" Jimmm Ummy ta yi bayan tsawon wani lokaci tace "Ke
ce ma zaki gaya min abin da ya dace in yi?" Kina hauka ne Nur tubabben zaki aura sabo da
idonki ya rufe ko?" Can kasan makoshi Nur tace "Ummy mun dade tare, dan Allah karkice
komai, yadda tai maganar Kamar ta ce wayyo Allah yasa Ummy cewa "To ni gaskiya Nur idan
zan gaya miki kiji banaso, maganar iyayenki Kuma idan sunkirani bazance komaiba tunda
ubanki na raye, duk abin da ya yanke shikenan, amman ke ina son ki canza tunani" "Ummy shi
nake so, shakaranmu shidda tare, dan Allah ki mana addu'a kawai, kuma karki bari su Yaya
Jamil su sani" Sabo da kin dauke su makiyanki ko? "A'a Ummy, ba haka bane, ni kiyi hakuri
dan Allah"
Can kasan makoshi Ummy tace "Shikenan, naji, Saida safe, kashe wayar ta yi batare da ta bari
Nur ta yi magana ba, dan haka Nur ta kalli wayar ta yi murmushi kadan. Washari Misalin karfe
bakwai na safe, Abdallah ne yayi sallama falon Baffah, Baffah da Bashir ya samu aciki, dan
haka ya Isa daf da Bashir ya zauna, tare da gaida Baffah, bayan Baffah ya amsa ya bawa
Bashir hannu suka gaisa, Baffah ne yace "Jiya da daddare ai na dauka zanzo in sameka anan?"
Murmushi Abdallah yayi, tare da cewa, "Na dan jira ai Baffah da naga shiru na wuce nace da
safe na dawo" Baffah ne yace "Toh hakan ma babu lalifi, Ina can gidan nakune ai, Babanku ne
ya kirani, Jinjina kai Abdallah yayi alokacin da Bashir ke bin Baffah da Abdallah da kallo, ganin
haka Baffah ya kalli Bashir yace, "Jiya lokacin munacen gidan Abdallah ya kirani awaya gashi
yazo wurina bana gida." Murmushi Bashir yayi sannan ya kalli Abdallah dake kokarin saka
wayarshi a aljihun gaban rigarshi, a daidai lokacin da Baffah ke cewa "Abdallah to ya wajen
kasuwancin ku?"
"Alhamdulillah Baffah"
"Ma sha Allah, Baffah ya fada yayin da ya sake cewa to lafiya dai ko keke nemana?" Wannan
karon sunkuyar da kai Abdallah yayi tare da shafo keyarshi yace, "Lafiya lau Baffah, dama akan
maganar Nur ne" Cike da Mamaki Bashir yabi Abdallah da kallo, kosawa yayi yaji wata dibarar
zai billo dashi domin hana auran Nur da Aliyu, gani yayi Abdallah nata fama shafa keya, har
Saida Baffah ya sake cewa "Inajin ka Abdallah?" Kanshi akasa ya ce, "Baffah dama ina santa
ne, abani auranta"
Wanni irin kallo Bashir yawa Abdallah yayin da Baffah ke cewa "Ikon Allah, kai kanka ko kuwa
abokinka ka ke nemanmawa?"
Batare da ya dago kansaba yace "A'a, ni ne Abba."Shiru Baffah yayi yana kallon Abdallah da
har yanzu kanshi na kasa, haka shima Bashir har yanzun ya kasa cire idonshi akan Abdallah,
mamaki yasashi rasa a inda yake, daker ya iya juyar da kanshi ya kalli Baffah dake dannan
waya fuskarshi daure, kosawa yayi yaga mai Baffah ke shirin yi Kuma, bayan ya gama dannawa
a kunnensa ya daura tare da cewa "Barka da safiya" Shiru yayi zuwa can yace "Abdallah ne
yazo yanxun ya sameni akan cewa yana son Nur, zai aureta" Shiru Baffa yayi sannan yace
"Nace nabashi" saurare ya