Showing 72001 words to 73076 words out of 73076 words

Chapter 25 - Ciwon Ya Mace Book Compelet Lamido

18 Aug 2026

645

tsaya yi daga cikin wayar sannan ya cigaba da cewa, " 'Yarkace
amman ai danane yake so, a'a dakata mana, ni ban maka katsalandanba, yariyar yar kace ni
kuma na sanar maka d'ana naso, nasan baza'ka iya ce min a'a ba, ko ka tsallake ni kabawa dan
wasu" Shiru Baffah ya sake yi zuwa can yace "Ba biye mata za'ayi ba ai" sauke wayar yayi
sannan ya kalli Abdallah dake sukuye dakai har yanzun yace, "Shikenan ka je karka damu"

Godiya Abdallah yayiwa Baffah, sannan ya mike ya fita, Bashir kuwa bin Abdallah yayi da kallo
har ya fice, Daker ya iya mikewa yabi bayanshi, acikin motar ya samu Abdallah jiki a sanyaye,
cikin kureshi da Ido yace "Abdallah lafiyarka kalau kuwa?"
"Hmmmm, Mai ka gani Bashir?"
"Nasan tsakanin ka da Nur ba shiri kuke ba, kasha cemin ba ruwanka da ita, amman kaje kana
cewa Baffah kana sonta zaka aureta, wai kana nufin bayan ka kore Aliyu zaka dawo kace wasa
kake ne?"
"Hmmmm, Ba wannan maganar Bashir, da gaske nake zan aureta.
Kallon cikin Ido Bashir ya sake yiwa Abdallah tare da cewa "Ta yaya zaman ku zai yiyu ahaka
alhalin ba son juna kuke ba?"
"Ni ina sonta Abdallah, kuma itama nasan nan badadewaba zata soni."
"Tab lallai, dan Allah Abdallah karka lalata mana zumunci."
"Bashir ka kwantar da hankalinka, tunda nace ina sonta Ina sonta ne. Ban damu da tasoni a
yanzun ba, da zaran an daura auren anyi me wuyar, sati daya yayi yawa zata saki jikinta, in dai
nine, kuma da bakinta zakaji tana yabon halina, cikin awanni zan iya canza tunaninta, domin ni
kamar wahainiya haka nake, a duk lokacin da naso ina canza launi." "Kafada Abdallah ya daga, tare da cewa shikenan Allah ya tabbatar da alheri" Motar ya bude
ya fita yayin da Abdallah ke cewa "Bazakaje can gidan ba" batare da Abdallah ya juyoba yace
"A'a" Motar ya tada yabar wajen, shiko Bashir dakinshi ya koma ya zauna, duk yadda ya so ya
samu nutsuwa ya rasata, ganinsa yayi yanata zarga-zarga bashi zaune bashi tsaye, zuwa can
yasa hannun sa ya shafi kumatusa ruwa yaji, dan haka ya kalli Hannun tare da cewa "Hawaye?,
Mai yasa zanyi hawaye dan d'an uwana yace yana son Nur, Mai yasa lokacin da naga an
amince mata da Auren Aliyu banyi hawaye ba?" Tsaki yaja afili, sannan yaci gaba da cewa
"Ashe ni ma dai wawane, wani tsaki ya sake ja, sannan yayi murmushi ya nufi bayin dake cikin
dakinshi ya wanko fuskarshi.
*******
Ku tayani Jin wani al'amari mai ban mamaki, Wai Abdallah ne yaje wajen Baffah su wai yana
son Nur zai aureta"
Tukunyar dake hannun Nur ce ta subece ta fadi, Karan fafuwarta yasa su Mamy waigawa
gaba daya, "Abbane yace waye yayi Bari?" Cikin sauri Mamy tace "Nur ce"
"Au tana gidan ne? Agogon dake daure a hannunshi ya kalla tare da cewa "Bata wuce
makaranta ba?" Cike da damuwa Mamy ta Isa bakin kitchen din kokarin shiga take taga an turo
kofar, hannu tasa ta tura amman ko motsi kofar bataiba, hakan ya tabbatar mata da kulle kofar
ta yi, Aunty dake bin bayan Mamy ne ta ce "Taji abin da Abban su ke fada ne fah" Shiko Abba
kofar ya fara bugawa tare da cewa "Nur to mene ne na rofe kofar kuma? Ki fito mana kiji."
Nur kuwa komawa ta yi ta jingina da jikin bango bayan abincin ya bare a kasa, Ahankali ta
zame ta zauna akasa, tare da kai hannunta duk biyun ta daura a ka, saidai babu ko digon
hawaye a fuskarta, bakinta ta motsa tace "Na shiga uku na lalace, wannce irin masiface? Ya
Allah na rokeka karka kaddaro min auran Yaya Abdallah, mugu ne, azzalumi macuci, wadda
besan darajan mace ba" Kasa ta karayi da murya tace "Mazanicine ya Rabbi karka hadani aure
dashi, Fasikine masharraci, idan akwai sunan da yafi na zalinci muni Yaya Abdallah ya
cancanshi" Murya Mamy taji cikin rawa sosai tana cewa, "Nur daga Jin ana magana sai ki rufe
kanki aciki, kina haukane? Ki bude ki fito ai ba dole ba" Shura kafa Nur ta fara kamar mai shirin

yin birgima, kasa-kasa taci gaba da cewa, Mamy bazan iya kallon idan ku keda Abba ince
bason Abdallah ba, idan kuma bance banson Abdallah ba, yaya zanyi da Aliyu, ina tsananin
sonshi, shine irin namijin da nake son aure, yaya rayuwar shi zata kasance bayan ya rasa ni"
Sai wannan lokacin hawaye ya zobo mata, yayin da taci gaba da cewa "Zaice naci amanarshi
bayan Kuma ni shi nake so, zaice na yaudareshi tsawon shekara shidda, wallahi bazan iya
rayuwa batare da Aliyu ba, ina tsananin tausayin shi, Kuma Yaya Abdallah wurin Baffah yaje"
haura kafa ta sake yi tare da cewa "Idan ma wurin Abba ya tsaya ya zanyi ince bana son
d'ansu? Bayan sune suka raineni har nazama cikakkiyar mutum, na shiga uku, zai yi wuya in
tsallake auren Abdallah, ni gaskiya bazan aureshi ba, saidai idan mace tana auren maza biyu" a
daidai wannan lokacin wayar Nur da ta fadi akasa tai kara, kallon wayar ta yi tare da rarrafawa
ta isa gabanta ta dauka, ganin sunan Bilkisu yasa gaban Nur faduwa tare da tuna alkawarin su,
cike da jarumta ta dauka, muryan Bilkisu taci cike da zaki tana cewa "Nur na je na shigar da
kara har an taho kawo mishi takardan sammacin" Kasa cewa komai Nur tayi domin gudun karsu
Mamy dake bakin kofar su jiyota.
Abba kuwa tuni hankalinshi ya tashi domin ko motsin Nur din basaji, dan haka yanzun da yaji
wayarta tayi kara ya cigaba da kiran sunanta cikin tsayawa tare da bata Umarni ta bude kofar....

Alhamdulillah anan nakawa karshen Littafi na daya free ne, Littafi na biyu za'a daurashi ne
akan manhajar Arewabooks, ku biyoni domin jin yadda zata kasance acikin Littafin na biyun
kuma na karshe da yardan Allah, yanzu za'a fara wasan, wannan labarin salonshi daban ne,
wadda baya anfani da Arewabooks yayi kokari ya sauke ayi Following dina @fadilalamido ko ta
link din da ke kasa.

WhatsApp no: 07014197556
https://arewabooks.com/book?id=63ea17c2c189e841487b66f2

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login
google.com, pub-9213700357025247, DIRECT, f08c47fec0942fa0