Showing 6001 words to 9000 words out of 38923 words

Chapter 3 - Deejama Book Compelet

16 Sep 2026

182

hannu a wannan annobar hatta munafikin likitan Daddyn ki.

Fauzi tace"Tabbas wannan yacika azzalumi Allah yasaka muku,insha allahu sai yayi
mummmunar karshe,ki yahakuri mahaifinki ne,Amma meyasa kikace mun ke 'yar bauchi ce?

Khadee ta share tears din da suka zubo Mata tace"Eah Mana ni bauchi nasani garinmu,bakiji
labarin bNe?

Fauzi tace"ok naganae sorry kinji kada kidamu kinji?
Khadee tace"kada kidamu am ok.
Shakeerah tace"to ya maganar sajida ita tana wane skul ne yanzu?
Khadee tace"tana A.B.U teaching hospital ne yanzu tana karantar dental.

Shakeerah tace"Allah sarki ummi taga iftila'i,to maganar Aunty Nana fah?
Khadee tace"tayi aure yanzu haka tana kasar Argentina ta auri wani dan jarida.

Shakeerah tace"Allah sarki rayuwar duniya duk babu dadi,idan kana ganin damuwar ka idan
kaga na wani sai jikin ka yayi sanyi.
Fauzi tace"Allah sarki ni kuwa sai na dunga ganin kamar tawa damuwar tafi ta kowa.

Shakeerah ta buga tagumi tace"Fauzi muna sauraranki.

Fauzi ta cigaba dafari dai,
"Sunana Fauziyya Aleeyu ni haifaffiyar garin gombe ce,mahaifina mutum ne mai rufin asiri
dai-dai gwargwado gaskiya mu ba masu kudi bane,mahaifiyata wacce nike cema Inna mu uku
ta haifa nice babba Sai kannena su biyu duka Mata,sana'ar mahaifiyata sai da manja da man
gyada Kuma Alhamdulillah Yana rufa Mana asiri,shikuwa mahaifina icce yake siyarwa,a haka
Allah ya rufa musu asiri suka samu a makaranta.

Kishiyar Inna ta muna kiranta da baba ladi tanada yara hudu duka mata,tunda muka taso muka
cidda baba ladi itace ke mulkar gidan mu sai abinda tace ayi akeyi,da yake Inna macece mai
hakuri Sam magana ba yadameta bane,a hankali nataso da bakin jini a gidanmu har a wajen
Inna ta wanda narasa dalili,ana cewa babu Wanda yakai mahaifiya son 'yayanta,Amma Banda
tawa mahaifiyar domin kuwa a cikin wahala na taso,mutum Daya ne zuwa biyu nake raba naji
dadi,mahaifina da yayata 'yar-'yan baba ladi itace babbar 'yarta.
Sune kawai kesani bakin ciki abubuwa da dama idan Inna ta tayimun Zama nake na
tambayeta anya ita ta haifeni?

Tunda nataso bantaba Jin dadin uwa ba,itace kyara hantara,lokuta da dama nasha kwana
bansa abinci a bakina ba,inda Allah yake temako na wajen kanne na nake kwata nace wallahi
Muddin bazanci ba Suma ba zasu ciba,saboda inada bakina to abubuwa da dama su suke
temakona,a cikin kannena akwai khadeeja wacce muke cema dijee,yarinya ce mai natsuwa
jinimmu ya hadu sosai,hadasiyya itace ke bina sai dai ko kadan bamu ga maciji,itace 'ya mafi
soyuwa a zuciyar Inna saboda ita ta amince da talla,muko nida hadasiyya da babbar yayarmu
munason karatu ,sai dai ita Kuma baba ladi duk cikin yaranta babbu wacce takeso kamar Yaya
kaltume babbar yayarmu,kujifa wayau,eah Mana wayo saboda ita baba ladi tana zuga Inna ta
mana tijara Amma ita Sam Bata ma yaranta,yaranta tamkar kawayenta,zata zauna taji duwarsu
Amma Banda tamu uwar.

Kullum idan na zauna Ina tunanin anya hakanan baba ladi tabar Inna?sai dai ance zato zunubi
don haka cikin Sauri nake goge wannan zaton a Raina.
Har yazo takai mahaifinmu yakwanta jinya,duk tausayi irin na Inna sai da ta canza hali,daga ita
har baba ladi Babu Wanda yadamu da rashin lafiyar baba,nida dijee da Yaya kaltume ke jinyar
sa wannan dalilin yasa Inna tace Muddin bamu rabu da jinyar baba ba zata tsine mana nida
dijee. Nikam cewa nayi bazan bar jinyar mahaifina mai tausayamun ba,sai dai duk abinda zatayi mun
tayimun.

Inna bata tsine mana ba,sai dai ta koremu a dakinta,sannan ta dena bamu abinci nida dijee da
mahaifinmu,duk wannan abun baba ladi ta bata shawar tace itama bata bashi.
Abinda Inna bata sani ba shine baba ladi na Aiko Yaya kaltume da abinci,Kuma duk dare tana
zuwa gaishe shi.

Maganar kanwata hadasiyya da sauran 'yan uwana yaran baba ladi su uku
hassana,usaina,hauwa,su hudun nan sai suka fara harkan karuwanci,domin kuwa maza har
cikin gida suke kawowa,suyi iskancin da zasuyi sufita,wannan dalilin yakara haddasa jikin baba
yayi zafi. Ya Zama na unguwar mu babu gidan da akewa Allah wadai da tirrr Kaman gidan mal Ali mai
icce wato gidanmu.
Kunsan Allah daimond ladies sam bamuyi dace iyaye na kwarai ba,domin baba ladi da Inna su
suke nuna ma su hadasiyya yanda zasuyima maza suyi iskanci dasu.
A kwana a tashi baba ladi ta ragewa Yaya kaltume sanwa,Wanda ake samu taba baba shima
ta dena,mu dama tuntuni Inna ta yayemu.
Ita burin baba ladi Yaya kaltume ta gujemu tace sam bata yimmu.

A hankali muka fara shiga wahala da tagayyarar rayuwa hatta tufafinmu Basu da kyan gani
saboda bamu da maraba da almajirai,shawarar Yaya kaltume na nema akan zamu je neman
aiki gidajen masu kudi,da kyar ta amince shima sai da taja mana kunne sannan ta amince,ita da
kanta ta samammana aiki a gidan wani hamshakin attajiri babban Dan siyasa senator Ahmad
shehu tabako.
Gidan mutane masu karamci da sanin darajar Dan Adam,Basu da matsalar komai da tawuce ta

matan uba,Sam matar shi a maryan Bata da hali.
Koda Yaya kaltume taje muka musu bayani ni kadai suka dauka aiki Banda kanwata
dijee,munyi kokarin su dauketa Amma abin ya gagara domin sunce tayi karama da yawa a
lokacin tana 8years.
Haka muka hakura,mub rabu sun daukeni aiki gobe zanfara zuwa wajen bakwai na safe.
Bamuyi kasa a gwiwa muka cigaba da bin gidajen masu hannu da shuni don nemawa dijee
aiki,cikin yardan Allah muka samu a gidan wani dan siyayasa shima.
Alhamdulillah sun dauki dijee,matarshi tana da kirki da fara'a ga son mutane,ta dauki dijee
bayan tace itama gone zata fara zuwa,kafin mutafi sai da tayima na ihsanin kudi dubu biyar tace
dijee tasai sabulu tayi wanki,sannan ta bamu kayan abinci, taliyace guda biyu da doya hudu.
Cike da farin ciki muka dawo gida,duk inda muka wuce zunde a ke Mana da baki,a dalilin 'yan
uwan mu da suka fada harkan karuwanci.
Bayan munshiga gida Yaya kaltume ta amsa abincin da kudin ta adana mana,makota tashiga
gidan wata kawarta ta dafo Mana taliya ta kawo mana mukaci saboda Babu halin girkawa a
gidanmu.

Wata ranar alhamis da safe usaina ta shigo da kwarton ta sun gama shedan cinsu da masha'a
Aiko daganan tsiya ta barke ita dashi,dambe suke sosai tana zazzaginshi.
Mari ya kifa mata Yana cewa wallahi kome zakiyi sai dai kiyi bazan aureki ba mezanyi da anawo
irinki 'yar titi wacce rijiya ma tafi halittarki daraja.
Kukan kura usaina tayi ta cakumo mashi kwalar Riga,gaba daya gida ya hargitse da hayaniya
hadda makota sunzo suna saka baki Amma sunki denawa,usaina kuwa anyi anyi ta saki
kwarton ta taki.
Sake tsinka mata mari yayi Wanda yasata sakin ihu ta kaimasa cizo a kunne,Aiko zafin da yaji
ne yasa ya fusgota ya hade kanta da garo.
Wani Kara ta saki tare da sulalewa kasa,ko kafin kace me kanta ya fashe sannan ko motsi
batayi,da aka dubata aka bincika Allah yamata rasuwa.
Domin ko numfashi batayi innalillahi wa inna ilaihirrajiun ranar munga tashin hankali wacce ba'a
samata Rana munga iftila'i,kafin kace kwabo 'yan sanda sun zagaye gidammu.




Xahratty ce�🏽
Lallai Alqalami 🖋� Yafi takobi 🗡�
💕💕
��
[7/18, 2:05 PM] Xahratty🥰😘: �✨ *DIAMOND LADIES* �✨
( Daukar Fansa )

Story& writing
By
PATEEMA ZAHRA LAWAL
______�🏽______




*TAMBARI WRITER'S ASSOCIATION*
🔱(( Home of Expert and talented writers,da tambarin mu muke tafe domin kawo gyara da
cigaban Al'ummah))

*_T.W.A_*
_________________________
https://www.facebook.com/Tambari-writers-Association-106058867819812/
_________________________


Marubuciyar⬇�

_ _A DALILIN 'YAR TSUNTUWA_


*DA*

_ _MIJIN ZAHRA_


💎💎💎
_Jirgin diamond ladies (Daukar Fansa) tana maraba daku,naji korafe korafen ku Akan littafin
Nan,masu yabawa nagode,kamar yanda masoya na suka roka na Kuma amince albarkacinsu
na maida book din diamond ladies (Daukar Fansa) Naira #100 only Babu damuwa Allah yabar
zumunci_💎💎💎


Bismillahir-rahmanir-raheem.

*Da sunan Allah Mai rahama Mai jin Kai*....


Page:9�⃣-1�⃣0�⃣🖊�

__________Bayan komai ya lafa na hargitsin gidanmu abinda yafaru da usaina bazamewa
iyayenmu darasi ba,dominko a lokacin nema lakafa ya cigaba domin iskancin su hadasiyya
gaba yayi,idan kazo gombe kaje unguwarmu duk Wanda kacema gidan mal.Ali mai icce babu
Wanda baisan badalar da akeba,ana cikin wannan yanayin na annobar masifa a gidan mu Allah
yayiwa baba rasuwa.

Innalillahi wa Inna ilaihirraji'un kunsan iftila'i da muka gani?
Girgiza Kai su shakeera sukayi.
Fauzi tace sallar gawa an rasa Wanda zaiwa baban mu,haka nida Yaya kaltume muke bin
gidaje Kiran makota don yimasa sallah,Amma abin yagagara.
Da yake ranar juma'ah baba ya rasu,ganin haka yasa nanufi masallacin juma'ar nayuwa
limamin masallacin bayanin abinda ke faruwa.
Ana kuwa idar da sallah ya sanar cewa zasuje want sallar gawa,don Allah Mutane su taho a
tafi.
Haka kuwa akayi manya manyan Mutane masu ilimi da kudi suka dungumo gidanmu don yiwa
baba sallar gawa.

Ganin haka yasa makota Suma suka fito,akayi Masa wanka a ka tada sallah......hmmmm
bansan ranar da abin kunya zai gogu a tarihin rayuwa ta ba,domin ana cikin yima baba sallah
hauwa tazo wucewa Tasha giya tayi tatillll a cikin maye, ta karisa bakin gawar ta fincike
likkafanin da aka rufe baba. Gaba daya sallame sallar Liman yayi,tuni hayaniya ya kaure a wajen dubban jama'ah Fadi
suke subhanallah.
Wani yaron Liman ne yakariso inda hauwa take ya Dalla mata wani gigitaccen Mari.

Tsalle hauwa tayi gefe guda cikin muryan maye tafara duramai wasu arnan zagi,sake kifa mata
Mari yayi Wanda yasata kundin bala ta baje a qasa.
Janta yayi da karfi ya Shiga da ita zauren gidanmu,sannan aka cigaba da yiwa baba
sallah,cikin yardan Allah aka kaishi gidanshi na gaskiya.
Bayan sunkai baba suka jiyo gidanmu,Liman da kanshi yafara yiwa su hauwa da hassana da
hadasiyya nasiha akan suji tsoron Allah su shiryu tun kafin duniya ta shiryar dasu,su lallabawa
rayuwansu su fito da miji suyi aure.....
Wani uban tsaki hadasiyya taja Wanda yasa Liman yin Shiru,Cike da mamaki kowa ke
kallonta,hassana itakuma ta dauka"kaga malam dakata! Tayi maganar tana daga Masa
hannu,idan wa'azi kakejin yi ga masallaci can kuje kuhau munbari kayi,mu yaranka ne da
zakazo kana mana wani nasiha na munafurci?
Cikin da bacin Rai samarin dake wajen suka Mike sukayi kan hassana.
Dakatar dasu Liman yayi,Wanda koni akaran kaina banso haka ba,naso yabari aci uwar
kowacce a cikinsu.

"Haba shamsu bai kamata ku biye musu na ni domin Allah nake musu nasiha,duniya CE ta
ishesu Riga da wando duk Wanda ya dauki duniya don Jin Dadi ya sauke,sannan yajuyo
wajen su Inna yace"ko ba'a fada ba nasan kune matan marigayi inaso ku kula da tarbiyyar
'yayanku kada ku manta 'yaya Mata Allah yabaku,meyasa bazaku gyara rayuwarsu ba?
Baba ladi tace"kaga malam Liman don Allah katashi katafi mungode da nasiha,dama ba'asan
asalin balbela bace sai Tace daga Sudan take,don kawai yanzu an shiryu shine za'ace ga zance
ga magana.?
Shiru gabadaya wajen akayi,a hankali Liman da tawagarsa suka Mike batare da kowa ya sake
magana ba.
Suma matan makota da suka shigo ko wacce mikewa tayi ta fita,baba ladi tace"Eah
MUNAFUKAI a gayas shegu.
Inna tace"Ai a sararru ne masu kwana da Ido daya.

Da nida Yaya kaltume da dijee kuka muke sosai,Ina nadama da danasanin wannan rayuwar na
ahalinmu.
Washegari da safe muka shirya nida qanwata muka nufi gidajen aikinmu,domin bamuga
amfanin Zama da matsiyata irin ahalinmu ba,baba ne Kuma ya rasu Babu abinda yake bukata
sai addu'ah.

Dijee nafara rakawa gidan aikinta,daganan Sai na na wuce nawa.

Tabbas bazance muku banyi dace da gidan aiki ba,sai dai Sam matar da nakewa aiki batasan
darajar Dan Adam ba ita da yaranta,idan Ina aiki bana fuskantar komai sai wulakanci da kyara.
Inda Allah ya temakeni akwai mahaifiyar Hon Ahmad itace take taka musu burki.
Abinci kuwa sai anci an rage ake bani,ban damuwa nakeci saboda a gidanmu ko kwantan
kwatan shi bazan gani ba,wata Rana na ragewa khadeeja wata Rana Kuma Yaya kaltume.

A daddafe nayi wata Daya a gidannan,albashina aka bani dubu goma,nayi farin ciki sosai,ji
nake kaman anbani wan manyan kudi.
Dijee itama dubu goma aka Bata a gidan da take aiki sai kwancen Kaya kala biyar.
Duk da cewa girman mu Daya da karamar kanwar tawa sai tabani kala biyu a cikin
Kayan,muka gyara dakin baba muka koma.
Dama abinci nace muku andade da ciremu a cikin 'yan gida.

Rayuwa muke mai cike da nishadi,Ina manta Ina da damuwa sai na je gidan aikina,mahaifiyar
mu Bata damu dajin matsalolinmu ba,a haka nafara al'ada Wanda da temakon Yaya kaltume
nasan komai,ita takasance mana tamkar uwa,ita ke mana nasiha danuna mana tsoron Allah,
barimma ni Dana fara wannan Jan motar,tafi jamun kunne saboda gidan danike aiki suma
'yayan Allah shirya ne,mazan duk suna neman mata.

A kwana a tashi muka dauki shekara da fara aiki Babu karatun Arabic ta bangarena balle na

boko,itako dijeee gabadaya tana xuwa makarantun,ta cika tazama big girl Bata da matsala
wajen uwar daki da mijinta,sun dauketa tamkar 'ya! Da yake Basu taba haihuwa ba.

A hankali tafara koyamun karatu daga bokon har islamiyar.
Hmmmmm da mahaifiyar mu a raye gwanda Babu ita,domin mun koma kamar abokan
gabarta,gashi bamusan dangin mahaifiyar mu,ita kanta tsintar ta akayi,mahaifiyar babam mu.

Wata rana haka na tashi da ciwon ciki Wanda yahanani zuwa wajen aiki,Kuma idan banje ba
Koro na za'ayi Bayan Ina samu Ina rufawa kaina asiri nida kanwata.

Dijee na roka Wanda takoma amfani da khadeeja Aliyu,Akan tajemun gidan aiki a makofin ni

A take anan Fauzi da fashe da kuka Wanda yasa Shakeerah da khadee Suma kukan,ta cigaba
da cewa"da nasan abinda zai faru da khadee kenan wallahi da ban turata gidan aiki ba.
Domin kuwa Daya daga cikin yaran Hon Ahmad yayimata fyade na wulakanci da
tozarci,Wanda tunda ya haike mata sai da Allah yayi mata rasuwa.


Dalilin haka Inna ta tasake tsanata sannan Tace nabar gidan ta.
Kada kumanta a kasar nan mai hali shine Mai gaskiya,don haka kirir-kiri akaki hukunta yaron
Hon Ahmad,sannan sukace karyane take tsintar ta sukayi,Bayan masu aikin gidan da masu
gadi sun sheda haka.

Inna kuwa korar cin Kare tayimun Wanda zaka rantse ba ita ta tsuguna ta haifeni ba,Yaya
kaltume na kuka Ina kuka mukarabu,sai dai takara jadadda mun duk inda zanje a fadin duniyar
Nan nakula da kaina da rayuwata sannan kada na manta da mahaifata,nayimata alkawarin
haka mukarabu.
Rasa inda xan nufa nayi,daga karshe nayanke hukuncin nufar inda khadeeja ke aiki,matar Cike
da mutumci ta tarbeni tana tambayar Ina khadeeja?

Anan nake sanarda ita da mijinta abinda yafaru.
Tayi kuka sosai,saboda sunji mutuwar khadeeja.

Daganan rayuwata ta koma hannun Daddy Alhj Kamal da mama hjy rahama,tunda ga wannan
ranar ban sake komawa takan gidammu ba,daga karshema garin fantami muka koma da maza.
Sai dai na dauki alkawarin daukar fansan abinda akayiwa dijee Ina Mata addu'ah ita da baba.

To wannan shine labarina.


Gaba daya ajiyan zuciya suka sauke,itako khadee Banda kuka Babu abinda takeyi.
Shakeerah cikin bacin rai da kunar zuciya tace"tabbas dole mu dauki fansa a rayuwar

mu,Amma meyasa Kika CE kinada matsalar matar uba?
Fauzi tace"gud question daimond lady dama nasan a halinki sai kimmun tambayar Nan,to
abinda yasa da naso boye Miki asalina ne,Amma Dana fahimci mu din hadin Alla NE sai na
bayyana Miki komai.

Shakeerah tace"Kai duniya Ina Zaki damu?wannan kalubale da muke fuskanta a
rayuwarmu,diamond ladies so nake mu dauki fansa Wanda tunda ake ko a tarihi ba'a taba jinsa
sai dai dole ya Zama na da temakon wani namiji.

Shiru sukayi gabadaya ko wacce tana thinking...... Shakeerah tace"yauwa khadee kince brother
naki barrister ne,ya kamata ace mun fara hada kai dashi tunda babban lawyer ne ko ya kuka
ganin babe's?

Cikin Sauri sukace gsky ne hakane.
Shiru sukayi gaba dayan su ko wacce da abinda ke damunta.
Shakeerah tace"ya kamata mu kwanta saboda school gobe da wuri zamu Shiga idan
mundawo munci abinci sai na Baku nawa labarin.

Amsawa sukayi da to kowacce ta shige bedroom dinta don bacci.

Asuba tagari diamond ladies.


Xahratty ce�🏽
Lallai Alqalami 🖋� Yafi takobi 🗡�
💕💕
��
[7/18, 2:05 PM] Xahratty🥰😘: �✨ *DIAMOND LADIES* �✨
( Daukar Fansa )




Story& writing
By
PATEEMA ZAHRA LAWAL
______�🏽______




*TAMBARI WRITER'S ASSOCIATION*
🔱(( Home of Expert and talented writers,da tambarin mu muke tafe domin kawo gyara da

cigaban Al'ummah))

*_T.W.A_*
_________________________
https://www.facebook.com/Tambari-writers-Association-106058867819812/
_________________________


Marubuciyar⬇�

_ _A DALILIN 'YAR TSUNTUWA_


*DA*

_ _MIJIN ZAHRA_


*Littafin diamond ladies (Daukar Fansa) na kudi ne duk maiso ya turo katin Naira dari#100 katin
waya ta wannan number 08060710719,sai nayi adding din mutum a group din.*



Bismillahir-rahmanir-raheem.


*Da sunan Allah Mai rahama Mai jin Kai....*


Page:1�⃣3�⃣--1�⃣4�⃣🖊�




_________Kijina ne yaketa aikin lugude da faduwa tashin hankali ya bayyana a fuskata
nace"A'ah Abba karabu dasu Sunaso ayi kure ne Kuma ni banaso na fallasa abin kunyar da
yayi namai haka.
Abba yace"koma menene sai anje islamiyar.

La'asar nayi Abba yatasa keyata har office din headmaster

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login
google.com, pub-9213700357025247, DIRECT, f08c47fec0942fa0