Showing 9001 words to 12000 words out of 38923 words

Chapter 4 - Deejama Book Compelet

16 Sep 2026

163

sannan aka Kira mal shafi'u,Nan
kuwa ta zayyane duk abinda yafaru.
Cikin bacin Rai Abba yace katanan ku zaneta,ko Kuma ni nazaneta da kaina,kukan munafurci
na saka Ina fadin wallahi shegemaster ba haka akayi ba(Wai headmaster ne shegemaster)

gabadaya saura rena akayi nayi nawa bayanin,nafara da cewa"tunda nashigo islamiyar yake
mun maganar 'yan iska Yana cewa yasan mu talakawa ne nazo yayi iskanci Dani zai bani
kudi,kullum-kullum haka yake fada da yaga naki yarda ne shine ya tsaneni yayi ta zanana,abin
duka da bana duka ba yadau jibgata,shine ranan yatareni a lungun oske Wai zaiyyi iska*ci Dani
nikuma na masa haka.
Gabadaya Office din salati Akasa,shikuwa mal shafi'u Banda zufa Babu abinda yake alamun
rashin gaskiya, shegemaster yace Ashe Mal shafi'u baka bar wannan banzar halin naka ba?to
ni bazan iya ba wallahi wannan Karan Dole kabar islamiyar nan kada ka lalata yara azo ana
kuka dani. Malamai kowa yace gaskiya kam kada wani Abu yafaru ayi kuka da makarantarmu,hakuri Mal
shafi'u ke badawa,Ina nan kuwa akabashi red card,Ni kaina sai da yabani tausayi,but a zahiri
hakinsa kenan sai dai ni baimun ba,kawai nema ma kaina mafita nayi.

Nan naciga da zuwa islamiya, Aunty Saudah ma tadawo,yanzu tadena zuwa talla ni ke zuwa Ni
kadai,wata Rana nayi sha'awar shiga kasuwan tudun Wada don Kai tallah,wata matace na
hango tsohuwa da ita tana tafe tana dingisa kafa daka ganta bata cikin wahala sai dai daga gani
rigimammiya ce,wani ne ya taho da Sauri ya bangaje ta,Aiko tsohuwar nan ta baje a kasa,babu
Wanda yamasa magana nan kuwa yafara magana Yana karkata mouth alamu dai Dan daba ne
ku tsofaffin nan 'yan iska ne taya Zaki shigo kasuwar mu wallahi kinci darajar ke tsohuwa ce da
nayi Miki bakin aiki,cikin tsiwa na taho na dagata ina cewa sannu kaka,amsawa tayi tanamun
godiya.
Zagina yafara Yana cewa Ni ajawon inace don uwata?banza na masa ganin hakan yasa yajiyo
gabana ya dauke ni da mari dafe kunci na nayi Cike da azaba don naji zafi sosai kada kumanta
a lokacin 12years gareni bansan sanda nayi kukan kura na dauki bucket din pure water Dina ba
na buga masa, dai-dai lokacin wani Dan sanda yazo wucewa Aiko ya kariso Yana tambayar
neje faruwa?Nan kuwa tsohuwan nan ta zayyane mai komai tana kuka,albarka yasamun sosai
sannan yace nakai tsohuwar gida,tab nida bansanta ba daga haduwa taya zansan gidanta,a
gaskiya tacema Dan adai-dai tan da ya daukemu take,tayimai kwantancen layin Aiko nan aka
kaimu.

Wani dankareren gida mukaje Wanda tunda nake bantaba ganin gida mai kyau da haduwa irin
gidan ba don haka nema cikin zumudi nabita gidan,gani nayi ma'aikata kowa na ya duke a kasa
Yana kwasan gaisuwa tsoro ne yakamani bansan sanda na diddilo idanuwa waje ba Fadi nake "
_innahu min sulaimanu wa innahu bismillahir-rahmanir-raheem_ yau nakawo kaina mahallaka
garin temako,wani falo muka isa babba mai cike da Kayan alatu wallahi kamar ba gidan mutane
ba Zama tayi a wani kujeran one sitter tare da dannna wani kararrawa,can sai ga masu aiki sun
Kai goma suka taho ajere,kirari suka fara mata tare da zubewa suna kwasan gaisuwa,Murmushi
tayi ta dubi daya daga cikinsu tace"Jakadiya!wacce akakira da jakadiyar na kalla babban
macece sanna tafi sauran shekaru kayanta daban ne Kuma duk cikansu suna jinsu neat.
Murmushi tayi jakadiyar tare da karisowa tana fadin"gaisuwa nake uwar dakina uwar gida
sarautar mata gani gareki fulani.
Murmushi tsohuwan nan takuma tace"Uhm kuntashi hala baku ganni ba? Eah wallahi fulani
tunda banganki ba nace yanzu haka kinje zaga gari ne kamar yanda Kika Saba.

Murmushi tayi tace"Aikam nan take Basu labarina tanuna ni sannar ta sanar masu da duk
abinda yafaru,duk cikansu kallo na suke Cike da mamaki da yanda nayi fada da Dan
daba,Jakadiya tace"Amma fulani meyasa baki Kira waya ba anzo ankoya Masa hankali?
Fulani Tace kada kidamu ko yanzu wannan yarinyar ai tayi gaba Koda zaiyi zai tuna da abinda
yafaru,Jakadiya tace haka ne.
Duba na fulani tayi tace 'yammata yaya sunanki? Bata amsa nayi da Maryam Amma anfi
kirana da Shakeerah,wow Masha Allah tafada,Cike da mamaki na dago ina kallonta,ba komai
yabani mamaki ba illa wow dinda tace nikam da bansan meaning dinshi ba.
Tambayata tayi nabata labarina,nan kuwa na zayya ne mata komai,abubuwa da dama dariya
take nan tadubi Jakadiya tace taje tacema Sarkin gida a shirye motoci uku xataje unguwa.
Ba'a dauki lokaci ba muka shirya nidai Ina rungume da bucket din pure water da farantin
bread.
Shiga motocin mukayi Wanda najini tamkar nashiga cikin jirgin sama tsaban dadin danaji,a
haka nadinga musu kwantace har muka Kai kofar gidan mu,ya wanci 'yan layinmu duk sunfito
ganin motoci da manya manya a hankali suka tsaya aka budema fulani murfin motan,nima aka
budemun. Tunda akaga amfito Dani daga cikin motar 'yan unguwar mu sukafara gulma kala-kala.

Fulani ta dubeni tana tambayata gidan mu,nuna mata gidan nayi,jakadiyar ta da kuyangi uku
muka shiga sauran kunyangin da dogarai suka tsaya a waje.
Tafe suke da carpet dinsu da Sauri Ammi tatashi ganin antaso keyata gashi daga gani masu
kudi ne.
Murmushi ne a fuskan fulani,sannu da zuwa Ammi tafara mata sannan tashiga dasu daki don
wajen babu wajen fakewa Rana.
Dakinmu ta kaita,Wanda yake shimfide da wani tsohon dadduma sai dai tsafta yasa yanajinshi
fesss.
Carpet Jakadiya tayi kokarin shimfidawa sai fulani ta hanata Zama tayi akasa suka fara
gaisawa da Ammi cike da fargaba.
Fulani ta dubeta tace"kece mahaifiyar wannan yarinyar Koh?Ammi cike da fargaba Ammi
tace"Eah nice! Da fatan dai bawani lefi tayi ba?
Girgiza Kai Ammi tayi Nan tasanar da ita duk abinda yafaru sannan tace idan Babu damuwa
tana son ganin Abba.
Nan Ammi tafita tasamu Dan makota yaje kiransa a wajen bread.

Basu dau wani time ba suka shigo shima da kaganshi kasan Cike da mamaki yake a tsakar
gida Ammi ta tareshi tace Abban su yau Shakeerah ta nemo Mana magana.

Shiru Abba yayi tare da sallama ya Shiga,su Jakadiya fulani ta kalla alamun su bamu waje,fita
sukayi tsakar gida,nan suka gaisa cikin mutumci da Abba.
Tambayar shi tayi sana'arshi yace mata bread ne,tace to yau yarinyar ku ta temakeni da
alamu daga gidan tarbiya tafito tunda har tasan darajar tsoho,ganin haka yasa na biyota don
ganin iyayen ta.
A tare suka sauke nannauyan ajiyar zuciya.

Fulani ta cigaba da cewa idan Babu damuwa,zanso in temaka muku da muhalli sannan Kai
nabaka jari mai karfi.
Jin kalaman fulani mukayi kamar a mafarki,cikin rawar baki Abba yace Ni...n...I...diin..? Daga
Masa kai fulani tayi ai a take anan suka fara godiya saboda tsananin murna.
Nan takira ma'ajinta Mai kula da harkan komai tace masa tanaso a dubo mata gida mai kyau
Mai 3 bedrooms,Kuma yazama dakwai komai da komai da ake bukata na muhalli.
Amsa mata yayi da toh,Aiko cikin awa biyu yakirata yace ansamu,tambayar shi tayi a Ina?yace
a kwangila.
A lokacin Ammi tagama alqlen gwangwani rai-rai da dakaken yaji tafarnuwa,nan akazuba ma
fulani da da kuyanginta da fadawa gaba daya,mukuma ko oho,tsabar yunwa tasa mun manta
da yunwa,sosai sukaji dadin alalen.

Shakeerah ta dubi su Fauzi tace"In takaice muku fulani itace dalilin arzikinmu.

Munje munga sabon gidanmu,gaskiya yayi kyau sosai nida Aunty Saudah a daki guda,daki
daya na Ammi dake kallon namu sai daya na Abba da yake da kofa ta waje,duka dakuna biyu
Italian bed ne,Daya Kuma Royal shine na dakin Abba,dakuna ne manya² Wanda da safayan
1-1 sitter sai na Abba ne da 1-2 sitter da bangaren dining Falon Kuma kujeru ne hadaddu
golden saikace glass Sunyi kyau sosai.

Jali tabawa Abba na miliyan Daya sannan ta hadAshi da direban ta suka fara sana'ar sai da
motoci.
Nan kuwa 'yan uwan Abba suka sake tsanar sa suna yawon cewa yankan Kai yafara,watarana
muna zaune da Ammi shi Abba bayanan sun fita da direban fulani sunje kano dauko wata mota.
Wani yaro ne yayi sallama ya shigo,amsawa nayi na fita tambayata yayi Wai ance Nan ne
gidan wai malam muhammadu? Na'amsa da Eah nan ne wake nemanshi? yaron yacemin
wasu maza ne su biyu a waje,cema yaron nayi muje nagansu tare muka fita na bude gate din
gidan,Cike da mamaki nake dubansu baba Ayuba ne da baba sani,duk yayyen baban mu ne. Ganina yasasu sakin murmushi gaba dayansu,Nima murmushin naayar musu Ina cewa lahh
kune?ku shigo,da to suka amsa ko wanne yana kokarin fara shigowa ganin zasu bangaje ni
yasani matsawa suka Shiga,gaba daya bin gidan suke da kallo,wani kolulun bakin ciki baba
Ayuba ya hadiye har muka shiga falon,daburcewa sukayi ganin kujerun,Cike da fara'a Ammi ta
tarbesu Zama sukayi akan kujerun duk da sunsa ba gani a gidan chairmomin local
government,gwanda ma baba sani idan yaso kirki yanayi Zama sukayi,Nikuma nashiga kitchen
da kyar na iya bude firij saboda kauyan cina yayi yawa lemu na dauko musu da ruwa na Basu.

Nan baba Ayuba ke tambayar Ammi Abba Tace Aiko bayanan,sun tafi kano,wani takaicine ya
lullubesu baba sani kuwa har Yana kwarewa yace kano Kuma?
Baba Ayuba yace oh rayuwa yanzu muhammadu ne da wannan gidan?harda zuwa kano? Idan
natuna sanda yake kwasan masai da bola abin mamaki yake bani.
Magana suka gasama Ammi itama Kuma tagani,Murmushi nayi nace wallahi kuwa baba gashi
yanzu a dalilin katsalan dan dina muka shiga daukar nan,yaran da ake tsine musu idan ba
iyayensu ke tsine musu ba ai abin sai kaga Yana tafiya yanda akeso,yau da hjy 'yar mai goro

nanan nasan da zatayi alfahari(wato mahaifiyar Abba) harara baba Ayuba yasakin min yace Mai
Hali dai Sam baya canza Hali to yanzu dake nayi magana?Nima hararar na wurga mai nace
maganar mahaifina fa kakeyi shiyasa nasa baki.
Kwafa baba sani yayi yace ai yanzu Dole muhammadu yayi aure tunda arziki yasamu kaga ni
saina samo Mai bazawara.
Daka tsalle nayi kamar nice za'ama kishiya nace wallahi bazai yuwuba Kuma Abba bazai
dauki shawarar na ba,galala suka saki mouth suna kallo na,Ammi tace Shakeerah tashi kiwuce
ciki,da toh na amsa mata na mike Suma mikewar sukayi daganan suka fara Dora ashar,inaso in
rama saboda jikina har tsuma yake sai dai Ammi ta hanani. _I need ur comment and sharhi_



Xahratty ce�🏽
Lallai Alqalami🖋�Yafi takobi 🗡�
💕💕
��
[7/18, 2:05 PM] Xahratty🥰😘: �✨ *DIAMOND LADIES* �✨
( Daukar Fansa )




Story& writing
By
PATEEMA ZAHRA LAWAL
______�🏽______




*TAMBARI WRITER'S ASSOCIATION*
🔱(( Home of Expert and talented writers,da tambarin mu muke tafe domin kawo gyara da
cigaban Al'ummah))

*_T.W.A_*
_________________________
https://www.facebook.com/Tambari-writers-Association-106058867819812/
_________________________


Marubuciyar⬇�

_ _A DALILIN 'YAR TSUNTUWA_


*DA*

_ _MIJIN ZAHRA_


*Littafin diamond ladies (Daukar Fansa) na kudi ne duk maiso ya turo katin Naira dari#100 katin
waya ta wannan number 08060710719,sai nayi adding din mutum a group din.*



Bismillahir-rahmanir-raheem.

*Da sunan Allah Mai rahama Mai jin Kai...*


Page:1�⃣1�⃣--1�⃣2�⃣🖊�




_________Tunda suka shigo cikin school din kallonsu ake daga student din har lecturer's
din,bawai kwalliyar su kadai ke burge mutane ba,hadda salon tafiyar su day kyansu da iya
magana ke burge mutane,uwa uba Kuma ga kwanya suna jinsu kamar gifted.

Shigar larabawa sukayi gaba daya,Wanda yasake haskasu.
Shiga hall sukayi domin gabatar da Exam nan sukayi suka gama batare da sun kula kowa ba.

Bayan sun fito suka wuce gida Cike da gajiya,da yake yau khadee ce da girki,cake kawai
sukasha da lemu ta Shiga kitchen don dora girki.

Sai da aka yi sallar magrib sannan khadee ta sauke shinkafa da miyar souce Wanda yaji
attarugu,basuci abincin ba sai da suka gabatar da Isha tukuna sannan sukaci abinci sunayi
suna shewa da hira.
Sun kammala cin abinci ,Fauzi ta dubi Shakeerah tace"babee muna jinki.
Murmushi Shakeerah tayi tace"dama nasan kina Nan kina kwakwa da kokarin son Jin labari.
Dariya suka sa gabadaya,khadee tace wallahi nima haka shi naketa kwa-kwan son ji.

Shiru tayi ta dauki tsawon minti 3 zuwa can tafara magana kamar haka.
"Da fari dai ni Sunana Maryam Muhammad Adali, Ni haifaffiyar Zaria ce anan na girma anan
nataso,gaskiya tun tasowar mu muka taso masu rufin asiri azahiri bamu dashi domin kuwa mu

ba 'yayan masu kudi bane,ba musan wani Abu karatun boko ba sai dai na Allo wannan fa akwai
shi Wanda mahaifin mu yatsaya Kai da fata yabamu nida Aunty ta.
Mu biyu ne Abba ya haifemu Dani da yayata mafi soyuwa a gareni ta nuna mun so fiye da
komai,kun ganni hatta talla nayi tallan biredi saboda tsaban rashi,tun Ina karama ake daurawa
Aunty Saudah tallah,macace mai hakuri tare da kawaici irin Ammi,kada kuyi tunanin Wai a son
ran iyayen mu muke talla a'ah Babu CE takawo haka,tun farko Abba shagon Saida agoguna
yake Rana Daya Bari suka tsiyatar dashi.

Aunty Saudah haka zata dauki tallah batare da ta karya ba,Kai hatta ni mutan gidan,da yawa
idan takai ba siya ake ba sai dai a lallatsa a tafi a bar mata,wani ma a kwance aci,ace baza'a
siya ba.

'Yan uwan baban mu suna da Hali dai dai gwar-gwado sai dai temako ne baza suyi ba.
Aunty Saudah kuwa duk abinda ke faruwa bashi yake hanata gobe fita da bread ba,ana cikin
haka na girma Wanda na taso da shegen rashin ji da fitsari,ba anuna mun yatsa a maida lafiya
ba'amun na kyale,tun Ina gida,dalilin haka yasa Ammi ba kasa fai take Bari na fita ba.

Koda nakai 9years tsiyata kuwa ta karu,domin kuwa rigima nasa akan abarni Nima nadinga fita
talla kamar yanda Aunty Saudah ke fita,munada kyau daga mu har iyayen mu,Amma tsabar
wahala tasa mun kode,kafafuwa na kuwa duk Sunyi faso tsabar gantali yamun yawa da yawo
Babu takalmi. Kullum nasihar Ammi da Abba shine mu natso,nikuwa Shiga takeyi tanan tafita ta can.

Tallah nafara bin Aunty Saudah ita a lokacin tana da 14years, Nikuma Ina Daukar pure water.
Wata rana muka dauki tallah da ita gashi garin da Rana sosai,wani gareji mukazo wucewa
kunsan dai garejin masu gyaran motoci to nan.

Alamu sukayi mana da baki kamar fito, Aunty Saudah ce ta juyo da Sauri ta nufi wajen su,domin
ita burin ta a kullum da tafito a siye tanajin nauyin komawa gida ba ayi ciniki ba.

Zugwi-zugwi nabi bayanta kamar tsohuwar munafuka,wasu maza ne suka kariso tare da
Daukar bread din,Daya ya bude ya dauki na hamsin ya ciye tassss tare da Daukar pure water
na yasha,gyatsa yayi irin na 'yan iskan Nan,shikuwa dayan da ya dauki bread din rabi yawafce
sannan ya aje ragowan.
Daure face Wanda yacinye ledan bread Daya yayi,sannan ya dubi Aunty Saudah yace"wareee
anan wajen,Cike da tsoro Aunty Saudah ta sungumi farantin bread dinta domin gudu.
Dubana yayi yace"kema dauki wannan ajawon ruwan naki ki wuce,yayi maganar Yana wurgi
da bucket din ruwana.
Nan kuwa ruwa ya fadi wasu Kuma suka farfashe,cikin bacin Rai na dago na dubeshi sannan
na dube bucket dina.
Daya a cikinsu yace"ba magana ake Miki ba don uwarkiiiiii?
Itakuwa Aunty Saudah fara jana tayi Cike da tsoro tana cewa"Shakeerah zo mune gida mu

barsu da Allah .
Fusge hannuna nayi na nufi inda bucket Dina yake,da yake irin na karfen nan ne Mai
murfi,dauka nayi ba nufo su,sukuma a lokacin sun juya sai dariya suke tikawa ba suyi aune ba
sukaji saukar bucket akan daya a cikinsu,ihu yasaka,a firgice dayan shima yajuyo Aiko na sakin
mai bucket din a gushi,duk cikansu ihu sukasa domin wajen ya fashe bucket din datsan su yayi. Cikin Sauri ragowar mutanen dake garejin suka kariso ana tambayar meke faruwa?a ciki kuwa
harda ogan wajen.
Cikin bacin rai nafara magana"Saboda zalunci irin naku da mugunta akan me zakuci bread
kuce mutafi sannan kuyimun fatali da bucket din ruwa,oho dayake tasaba zuwa ita kadai dama
kume masu Mata haka Koh?to idan ita ta dauka Ni bazan dauka ba eheeee,na karishe maganar
Ina murguda baki. Ogan su ya tambayi ba'asi Nan kuwa na zauna na zayyane komai harda karawa da
gishiri,Cike da bacin rai yake dubansu yace"lallai abinda yarinyar nan tayi tamun dai-dai gaba
kwasake......cikin Sauri nace"wallahi gobe ma kuka sake sai nayimuku mafiyin wannan,kudena
ganina 'yar karama akan ahalina babu abinda bazanyi ba,kowa Cike da mamaki take dubana
sukuwa samarin tsoro na ne yashigesu.
Tambaya na shugaban garejin yayi ruwan nawane?nace jakar leda uku CE.
Nan kuwa yaciro dari biyar ya bani,sannan yace bread na nawa sukaci?bashi amsa nayi da
cewa da bread din hamsin da rabi sannan ai ba yau sukafara mata haka.
Karshe dai Sai da mukabar gareji da Naira dubu Daya da dari uku,sannan nace"Babu Wanda
ya Isa yahanamu kawo talla garejin.
Daukar bucket Dina nayi muka tafi,a ranar dai nayi dambe Yafi a kirga,Kuma duk akan bread
da ruwa,masu yima Aunty Saudah rainin wayo sai da na Rama Mata.

Abin mamaki mun siye bread din nan tass Babu ko lankare, murna sosai Aunty Saudah tayi.
Haka kuwa muka nufi hanyar gida muna Cike da farin ciki,a hanya muka hadu da wani wan
baban mu akan mashin dinsa Sabo

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login
google.com, pub-9213700357025247, DIRECT, f08c47fec0942fa0