Showing 24001 words to 27000 words out of 38923 words

Chapter 9 - Deejama Book Compelet

16 Sep 2026

187

*Saudat(ummu farhana*)
*Precious*
*Khadija tijjani*
*Ayusha*
*Fatima mansur*

Bismillahir-rahmanir-raheem.

*Da sunan Allah mai rahama mai jin kai....*



_FREE PAGE_


Page:2�⃣8�⃣--2�⃣9�⃣🖊�



___________Sosai su Shakeerah suka mai da hankali wajen karatun sa, a gefe daya Kuma
Daddy ya turo magabatan sa wajen fake magabatan Shakeerah an tsayar da magana nan da
two weeks za'a daura Aure.
Daddy yaso ayi event sai dai Shakeerah tace ita Sam bataso bada itaba,kudi yaturomata
10million akan tayi siyayya kuma ta hada ma kanta lefe.

Komai shiya siya hatta da kayan daki,domin a dangin Shakeerah bb Wanda yasan da maganar
daga Ammi sai fulani Shiyasa bb wani shirye-shirye da ake gudanar wa ta bangaren ta sai dai a
gidan hjy harirah.
Ana saura sati guda biki 'yan uwan Daddy suka kawo kayan lefe ciki kuwa harda car key,abun
ya birge kowa akwati dozin uku gaskiya Daddy yatara dukiyan haram Allah ya kiyashe mu.


Ranar wata laraba da daddare Daddy na bacci yaji zoben hannun sa yafara rawa,alamun
anason mgn dashi,bude ido yayi, nan kuwa zoben yayi haske sosai sai ga wani mutumi ya
bayya na a gaban sa da jajayen kaya,mummuna sosai sai wani baki gashi bb alamun imani a
fuskan sa, cikin tsawa yace"Lallai Sani kana nan kana bacci muko muna cikin matsala babba.
A firgice Daddy yace"Oga Patrick tuba nakeyi........tsawa ya dakama Daddy"kayimun shiru kaje
zaka auro Mana masifa da bala'i a binciken da mukayi wannan yarinyar annoba ce a cikin mu
meyasa zaka Aure ta?
Cikin Daddy na shaking yace"A'ah oga Shakeerah Bata da matsala kafin na Aure ta sai da nayi
bincike kuma an tabbatar mun da Babu abinda zai faru kamar yanda sauran suka faru.
"Alhj Sani kanaja da magana nane?da binciken da akamaka da Wanda mukayi wannene
gaskiya?
Shiru Daddy yayi.

Mr Patrick yace"Oh nagane ka Saboda kaga nabaka karamin shugaban kungiya shine kakeso
kayi abinda kaga dama?to Bari kaji Muddin ka Aure yarinyar nan aka samu matsala to kayi kuka
da kanka badamu ba.

Yana gama fadar haka yabace battt,tsaki Daddy yaja yace"kilama kunyi bincike ne kunka da
alkhairi shine kukeson rabani da ita,aini da Shakeerah sai dai mutuwa,Yana gama fadar haka ya
juya ya cigaba da baccin sa.

Shakeerah dasu khadee Suma ta bangaren su sun dage da addu'ah sosai akan Allah yabasu
nasara akan Daddy,haka ta bangaren Ammi,fulani da Ummi ma ba'a barsu a Baya ba,a kwana
a tashi biki ya kasance saura kwana hudu,Babu wani gyara da Shakeerah taje yi domin ita ba
Aure zataje yiba.
Hjy sameera hankalinta yatashi Jin Daddy zai Kara Aure tunda ake mata kishiyoyi bata taba Jin
irin wani mugun kishi ba sai akan wannan da za'akawo mata,gaban ta na tsanan ta faduwa
matuka ta rasa dalilin hakan.
Kwatsam su Shakeerah na school chairman din department dinsu yakira su Kan cewa antafi
yajin aiki,ba karamin Jin dadi sukayi ba shikenan faduwa tazo dai-dai da zama,Ranar Asabar
kuwa aka daura Auren Shakeerah da Daddy duk da Babu taro Amma Sai da Daddy ya turo
abokan sa,unguwan du hjy harirah yayi makil da manyan Mutane,ana gama daurin Aure Daddy
ya dauki Amaryan shi,dama tunkafin yazo Shakeerah taje sunyi sallama da su Ammi da
fulani,sosai suka sake bata shawarwari da ja mata kunne Akan kada ta kuskura ta yarda da
Daddy.
Irin kukan rabuwar nan da'akeyi Sam Shakeerah batayi ba sukuwa su khadee da fauzy Sunyi
kuka kamar ransu zai fita,a dalilin kewar Shakeerah ita kuwa cemusu take suyi hakuri tana nan
dawowa soon.


Sosai 'yan uwan Daddy suka tarbeta d farin ciki da kauna tunda family house dinsu suka
kaita,Bayan sallar isha'i suka dauketa suka kaita gidanta,direct part din hjy Sameera suka nufa
da ita,domin Amarya ma tana can.
Sun samu hjy Sameera akan kujera tayi daurin kirji ture kaga tsiya Sai karkada kafafuwa take
tana taunar chwengum.
Sun aje Shakeerah 'yan uwan Daddy zasu gabatar da ita hjy Sameera ta dakatar dasu,kunga
kutashi kutafi wannan abun da zaku fada ba yau nasaba jinsa ba don haka nariga na haddace
ku ajeta ku tafi,duk da cewa 'yan uwan tane suma,mikewa sukayi suka fita batare dasun tanka
ba,don sun San halinta ba kirki tacika ba.
Tsaki Hjy sameera taja tace"kekuma munafuka Sai ki bude mana face din naki domin kuwa
muba siyan sa zamuyi ba.
Daddy ne yayi gyaran murya tare da shigowa,sannu da zuwa Aunty Amarya tamai,batare da ya
kalleta ba ya amsa.

Bude taro yayi da addu'ah sannan yafara magana kamar haka"Amarya Ina Miki maraba da
shigowa gidan ki,Allah yasa kin shigo da kafar dama,pls inaso ki bude face din ki don 'yan uwan
ki su ganki kigansu,toh Shakeerah tafada tare da yaye mayafin da ke kanta a hankali.
Duk cikan su suka mike tare da tsalle, Hjy sameera tace"haba haba no wonder,dama nasan

za'a rina tunda naga tazo gidan nan nasan tuggu aka shirya maka,Yaya tarasu shine aka baka
kanwa ka Aura?lallai ne.ita kuwa Aunty Amarya nuna ta take tayi tace"Amma ke maciyiyar
Amana ce,daga zuwan ki rannan shine har kintafi da zuciyar shi wajen malaman garin ku?lallai.
Ture Aunty Amarya Hjy sameera tayi gefe ta matso har gaban Shakeerah tace"lallai yaro baisan
wuta ba sai ya taka,yayarki ma bataci galaba akaina ba wajen kishi balle ke 'yar tatsitsiyar ki
dake,wallahi tundaga gobe kifara irgawa cewa kinkawo kanki gidan wahala,domin Babu ke
babu samun farin ciki a gidan nan. Tana gama fadar haka ta fice,shidai Daddy shiru yayi Yana tunanin yanda zai yi ya shawo kan
matsalar,tsaki Aunty Amarya tayi ta dube Shakeerah tace"munafuka........ Daddy ne yadaga
hannu zai mari Aunty Amarya cikin Sauri Shakeerah tarike hannunn shi tace"haba papi na kada
kaga lefinta kishi ne yakawo haka,kishin na naka,sannan akan me zaka dake?ita mai danyar jini
ma tayi kishi Ina ga wacce tsufa yazomata ta Fadi maganganu na rashin da'a baka hukunta
taba sai wannan.
Shiru Daddy yayi tare da wucewa fuuuuu ya nufi wani part daban da alamu shine na
Shakeerah,duban juna Shakeerah da Aunty Amarya sukayi suka kece da dariya, Aunty Amarya
tace"gaskiya Shakeerah plan dinki yana kyau,yanzu mutashi a part din nan kafin tsohuwar nan
tadawo tamana rashin M. Tabe baki Shakeerah tayi suka nufi part dinta,zage-zage Aunty Amarya take cikin pretend ta
wuce part dinta.tsayawa Shakeerah tayi a kofar Falon batare da tashiga ba, Saboda talura Hjy
sameera na leken ta ta window,don haka sai tayi kamar batasan inda zatashiga ba.Wayar ta ne
yafara ringing cikin sauri tadauka ganin Daddy ne,hade rai tayi kamar yana gabanta batare da
tayi magana ba,a hankali yace"Amarya ta kina Ina?
A zafafe tace"gani a waje cikin tantagar yan sanyi Babu Wanda yabani muhalli.


Wat? Daddy yafada tare da mikewa,fitowa yayi yasamu Shakeerah duke ta hada Kai da
gwiwa,kwalkwal tayi da Ido cikin Sauri Daddy yakariso yadaga ta yace"Ayya Darling afwan,aina
zata kina biye dani dazu dana fita shiyasa.

Turo baki Shakeerah tayi tace"Bakaine kana fushi damu ba?Shiyasa ban biyo ka ba,rungume ta
yayi yace"Sorry Darling kinji zo muje nakaiki part dina.
"A'ah ni kawai ka nuna mun part dina na shiga nibazani naka ba,no kizo muje nawa yanzu ina
wani Abu ne a cikin nan.

Wani irin kallo Shakeerah tamai tace" ban Isa inga abun bane papi?

Daddy rudewa yayi yace"Haba Darling kin Isa har kin wuce zo muje part dina inyaso mayi
maganar da zamuyi,hannunta yakama itama Kuma Sai waigen part din nata takeyi,part din
tabbas yatsaru iya tsaruwa ya hadu iya haduwa, bedroom din shi yawuce da ita sannan yace
gashinan zuwa tashiga toilet ta watsa ruwa kafin yazo.
Dubanshi tayi cikin Sauri tace"papi Ina akwatinan kaya na?Dafe kai Daddy yayi yace"nabarshi
acan but mezaki dauka?

Zansa pad ne da Kayan bacci,diddilo idanuwa yayi yace"kina al'adah ne?
Shakeerah tace"Eah,shiru Daddy yayi sai zuwa can yayi murmushin gefen baki,Wanda bakowa
xai fahimci yayi ba, Amma dayake Shakeerah Shakeerah ce Sai da tagano manufar smile din
nashi ko na menene I don't know.

"Darling bari naje give me 10 mnt.
Kada Masa kai Shakeerah tayi kamar kadangaru wa,cikin Sauri yafita,mikewa tayi tafara lekasa
ta window,cikin Sauri yqshiga part din ta,yamai da kofar ya rufe,sam Bata tatashi daga window
din ba, minti goma kamar yanda yace mata sai gashi yafito da wasu manyan Mutane kamar sa
su biyu sai saurayi daya,duk kansu sai gyara mazagin wando suke.

Sakin labulen Shakeerah tayi cikin Sauri ta fada toilet tare dasa key,wanka tafara,tanajin
shigowar shi,shima Kayan ya tube sannan yasamu gefen gado ya kwanta dagashi sai boxes da
singlet.

Fitowa Shakeerah tayi sanye da towel a kirjinta Wanda yatsaya mata dai-dai kan
manya-manyan cinyoyin ta,sam Shakeerah bata zata yana dakin ba,don takashe glob din mai
haske tabara mai duhu na barci.

Jitayi kaman ana mata numfashi a dai-dai kunnun ta, tsorata tayi cikin Sauri ta juyo.


_manage pls my guy's_
I NEED UR COMNENT.



Xahratty ce�🏽
Lallai Alqalami 🖋� Yafi takobi 🗡�
💕💕
��
[7/18, 2:05 PM] Xahratty🥰😘: �✨ *DIAMOND LADIES* �✨
(Daukar Fansa)




Story&writing
By
PATEEMA ZAHRA LAWAL
_______�🏽_______

*TAMBARI WRITER'S ASSOCIATION*
🔱(( Home of Expert and talented writers,da tamvarin mu muke tafe domin kawo gyara da
cigaban Al'ummah))

*T.W.A*
_________________________
https://www.facebook.com/Tambari-writers-Association-106058867819812/
_________________________


Marubuciya:-
_ *A DALILIN 'YAR TSUNTUWA*

_ *MIJIN ZAHRA*

*ND*
*NOW*
*DIAMOND LADIES*
(Daukar Fansa)


*Littafin diamond ladies (Daukar Fansa)na kudi ne duk maiso ya turo katin Naira dari 100 na
waya ta wannan number 08060719719,sai nayi adding dinsa a group din*


Bismillahir-rahmanir-raheem.

*Da sunan Allah mai rahama mai jin kai....*



_FREE PAGE_


Page:2�⃣4�⃣--2�⃣5�⃣🖊�



___________Cikin mamaki Shakeerah ta dago tana dubanshi tace"Aure kuma Daddy? nice
zaka Aura? Face din tausayi yayi yace"wallahi da gaske nake Shakeerah zanbaki irin kulawar
da kikeso zanji dake Allah.

A jiyan zuciya Shakeerah tayi tace"Ok naji but kabani time inje inyi thinking,sake marairai face
yayi yace"har tsawon wani lokaci kikeso nabaki Shakeerah ta? Dariya ne yaso kubuce ma
Shakeerah a dalilin Shakeerah ta da yace,daure wa tayi tare da yatsine face tace"Anyway sai
na koma gida duk yanda mukayi da mom zakaji. "Ok babu da muwa,Daddy ya fada yana washe hakora,fita Shakeerah tayi a motan ta nufi cikin
gida.
Ta mirror din jikin motan shi yake ganin yanda take tafiya,ga buttocks din ta suna wani
juyawa,miyau ya hade da Sauri tare da lashe harshe a fili ya furta"zan kasance dake har
abada,kuma bazan taba bari ki haihu ba shakeey beb.

Shakeerah kuwa Koda ta shiga ta cidda fauzy ita da matan Daddy suna hira suna cin kaza guda
daya,sallama tayi ta shiga dakin duk cikan su suka amsa.
Amaryan Daddy tace"hmm albarkacin ku wai yau ni nake cin kaza a gidan nan da
nama,wanda rabon da nagansu ankusa 1year.
Daga Shakeerah har fauzy dagowa sukayi suna duban ta, Shakeerah tace"kina irin wannan
tankamemen gidan kike cewa rabon da kiga nama kin manta?murmushin yake tayi tare da
nooding head nata kasa tace"bazaku taba ganewa bane Shiyasa na kagu Alhj Sani ya sakeni
but yaki ya zanyi?gashi sai aikin shekemun yara akeyi a Kan wane dalilin? Zama su Shakeerah suka bata,cike da bariki Shakeerah tace"Aunty Amarya wani irin magana
ne wannan?dama yaranki duk kashesu akeyi?

Shiru Amarya tayi taba share hawaye tace"kwarai ma kuwa,domin duk Ina da hujjuji na,shi din
azzalumi ne,mugu ne kuma matsafi.
Cike da furgici su Shakeerah suke duban ta,ta cigaba da cewa"wallahi tallahi Alhj Sani Mai
Iyali har jinin Mutane yanasha a ciki kuwa duk na 'yayan sa ne,yanzu haka akwai tsohuwar
matan sa da diyoyinsa uku mata da suka gudu har yau ba'a gansu ba,sannan shugaban tsafin
su ya sanar Masa da cewa muddin wannan khadee tana raye to zata hadu da hatsabibiyar
kawa wacce ita zatayi sanadiyar rugushewar farin cikin sa.
Dalilin da yasa yake nemansu ruwa ya jallo kenan Amma Bai gansu ba,babban danta dayake
karatu a Spain ma yanzu ya bace babu shi babu labarin sa,Yana so na cigaba da haihuwa yana
kashemun 'yaya Shiyasa naje aka daure mahaifata,dashi da uwar gidansa suke wannan halin
sai dai inaso na tona masa asiri yace"Muddin na tona sai yasa an tsotse mun jini da duk
dangina.

Gabadaya tagumi Shakeerah da fauzy suka sanya,tabbas Daddy azzalumi ne,shine a haka
yake Abu sumumi sumumi dama ance ka kalli mutum grassnes.


Kwanan su Shakeerah biyu,a kwana biyun nan sunga abubuwan al'ajabi kala-kaka a ciki kuwa
harda Hjy sameera inda tafito yin tsafi farfajiyar gidan tsiraran Allah haihuwar uwanta da uban
ta.
A bangaren Daddy ma ya matsama Shakeerah lamba da maganar soyayya,ke a karshe dai

Sai da Shakeerah ta bashi number wayar ta sukayi sukuni,sosai kafin su tafi suka sissiyoma
Amaryan Daddy Kayan kwalam,su busashshen kifi,soyayyan kaji, cake's, doughnuts da dai
sauransu,sannan suka mata ihsani sosai.

Hannun fauzy jaye da Dan madaidaicin trolley bag din su, Amaryan Daddy ta rakosu,sun cidda
Daddy da wata mata sai Hjy sameera a farfajiyan gidan,da alamu magana suke sosai.
Gabadaya Mai da hankalinsu sukayi kansu Shakeerah cikin Sauri Daddy yakariso Cike da
mamaki yace"Ah Shakeerah yau ne zaku tafi gida,wani shu'umin kallo tayi masa mai tare da
fassarori da dama ciki kuwa harda kara rikita zuciyan Daddy ai ko tuni ya rufta tace"Eah zamu
tafi yanzu Saboda muna da Exam gobe a school,dafe kai yayi yace"Oh Kai nima na sha'afa
wane school kike ne? Sake watsa manyan eyes dinta tayi tace"A.B.U nake, Daddy yace"Ok
then wani department kenan?
Yatsine face Shakeerah tayi tace"bangaren Medical lab am bari muyi sauri Koh?
Murmushi yayi yace"Babu damuwa ku jirani na fito koh?juyawa yayi zuwa part dinsa.

Hjy sameera kuwa ganin rawan kafar dayake akan su Shakeerah yasata karisowa dai-dai
gaban Shakeerah ta tsaya ido cikin ido take kallon Shakeerah tun daga head to toe,yanda take
mata itama Shakeerah shi takeyi mata, Hjy sameera tace"Kukuma daga ina kuke har kukayi
kwanaki bansan da zaman ki gidan nan ba sannan kunfito bangaren wannan munafukar?tayi
maganar tana dungure kan Amaryan Daddy,duban ta Shakeerah tayi itama ido cikin ido
tace"kijira idan mijinki yafito sai ki tamvayeshi ko mu din suwaye kingane?

Daddy ne yafito hannunshi rike da bandir din dolas har guda biyu ya bawa Shakeerah tare da
cewa ayi siyayyan school, godiya suka Masa fauzy Kuma ta'amsa kudin, Daddy da janshi ya
dauki trolley bag din su yasaka musu a but,ita dai Hjy sameera tana kallon ikon Allah,figar motar
tayi a sukwane ta fita Mai gadi na daga mata hannu,domin 'yan kwanakin nan da sukayi tare
yaga gidan ya dan gyaru kadan.

Bakuwar su Daddy itama sallama ta musu ta tafi sai yarage daga Daddy sai Hjy sameera sai
Amarya,tsawa hjy sameera ta daka mata tace"munafuka to tsayuwar me kike mana Kuma
anan?da gudu Amarya ta shige part din ta,juyowa tayi kan Daddy tace"Kai kuma wannan rawar
kafar da kake a Kan wannan 'yan matan na menene?dariya Daddy yayi yace"kannen
marigayiya saddiqa ce koko kinaso nadinga nuna shariya a garesu ne har a gano wani abu a
gareni,Murmushi Hjy sameera tayi tace"Shiyasa nake sonka Alhj na Saboda wayanka.
Shima dariya yayi,Nan suka shiga cikin gidan.

Alhamdulillah su Shakeerah sun Isa gida lpy sosai suke farin cikin ganin juna,murna khadee
take sosai,lafiyayyan waina da miyan da tayi ta zobo musu.
Zama sukayi gaba dayansu,fauzy tadubi khadee tace"khadee me aka girka Mana ne?Murmushi
khadee tayi tace"waina ne gashi nan kuyi manage don kunsan vazai taba kaiwa dadin na
Shakeerah ba bari na dauko muku man shanun Kila ya soyu.

Sosai sukaci wainar gabadayansu daganan aka dasa hirar yaushe rabo,bawa khadee labarin

komai sukayi,fauzy tace"gaskiyanki khadee mahaifin ki hatsabibin mutum ne,mgnr zargin Hjy
sameera da ake babu karya domin kungiyar su daya,Cike da damuwa khadee ke duban su
tace"Dama Daddy baiyi nadama ba,hasalima neman mu yake yakashemu,duk soyayyar dake
tsakani na da Daddy?sosai suka fara lallashinta,khadee tace"munsamu dama ta farko Wanda
shine mafita Shakeerah da Daddy na yace"Yana sonki mekika ce?Murmushi Shakeerah tayi
tace"nace masa yabani lokaci nayi shawara.
Khadee tace"Toh shikenan Allah yakara dauramu bisa kan kowa.


______*SAUDI ARABIA*_____


Tas! tas!! tas!!! Karar cover shoe dinsa ne kawai ke tashi,duk da alamu yana da tsayi ko ba'a
fada ba Saboda tsayin kafar sa, Wow Masha Allah kirarren namiji Mai jikin Kira ko da ganin jikin
sa kasan cewa ana motsawa Saboda yanda yake da Kira,da yawan mutanen asibitin sai
gaisuwa suke aika masa dashi,face dinsa babu yabo babu fallasa da alamu dai kaman shi irin
mutanen nannne marasa son hayaniya ko wace iri ce,face dinsa zagaye yake da saje Wanda
ya kwanta yayi lufff dashi gashi bakin Kirin,mutum ne shi mai manyan idanu ba su cika manya
ba,hancinshi har baka sai mouth dinshi dan dai-dai a tsakiyar sajenshi,fari ne shi irin farin
larabawan nan. Shirt ne ajikinsa da

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login
google.com, pub-9213700357025247, DIRECT, f08c47fec0942fa0