Showing 1 words to 3000 words out of 30377 words
Chapter 1 - CANJIN RAYUWA BOOK 1 HAUSAWA NOVELS BY HALIMA ABDULLAHI K MASHI
CANJIN RAYUWA
Littafi na Farko
Rubuta Labari
Halima Abdullahi k Mashi.
arewanovels.com.ng
Hajiya saudat tana zaune kan sallayarta ta idar da sallar azahar tana istigfari, 'yar kimanin
shekaru arba'in da bakwai zuwa da takwas,amma ba ta yi kama da shekarunta ba saboda kyan
jikinta da kuma hutu.in an ce ka fadi shekarunta za ka iya cewa talatin da doriya,kyakyawa ce
mai cikar mutunci. wayarta da ke gefe samfurin nokia tayi ruri, cikin natsuwa ta kai hannu ta
dauka tare da kallon fuskar wayar. kamar yadda ta za ta, maigidan ne domin duk yinin
yau ba ta samu kiransa ba.sallama ya yi,ta amsa cikin ladabi, sunanta ya kira ya ce,hajiya ki
karbi bakuncin mu anjima. cikin taushin murya tace,shine ba ka fada mini ba tun safe? cikin
lallashi ya ce,na yi ta neman layin ki bai samu ba, ta ce,da ka nemi ta su usaina,kila network ne
domin waya ta kunne ta ke,ya dan murmusa,ba mamaki zan iso da yunwa fa,don haka a tarbe
ni,ta yi 'yar dariya,wace irin yunwa?shi ma yayi 'yar dariyarsu ta manya,duk wata yunwa ta,da
ita zan zo,ta ce, kar ka damu allah ya kawo ka lafiya,ya ce,amin. ki sa a yi
wa uwata farfesun kifi tare za mu zo,take ta hade fuska, tamkar yana kallon ta,ta ce alhaji don
allah kar ka zo min da mimi.ya ce,saboda me?ta ce,ka san komai, alhaji MIMI in ta zo gidan
ba,ba maaikatan gidan ba.ta sani,na fada mata kar in sake ganinta a gidana matsawar ba ta
canza halin ta ba,ba na bukatar ta.yayi shiru domin ranshi ya baci,kusan minti daya duk sun yi
shiru. sannan ya ce,sauda, ba zan gaji da fada miki cewa ban jin dadin abinda
kike yi wa MIMI ba gaskiya, zai fi kyau ki fito fili ki zage ni sai ya fi min sauki maimakon aibanta
MIMI. allah! in ji hajiya saudatu,ta sake tausasa muryarta,ban san lokacin da za ka fahimce ni
ba alhaji,amma kayi hakuri.in dai don mu zaka zo,to ka zo kai daya zan fi so haka.cikin dan zafi
ya ce,sauda muna hanya kar ki manta da abincin ta na yau da kullum,ki fada ma duk 'yan gidan
wanda bai son ganin ta zai iya barin gida har sai ta tafi,
[01/10 12:45 pm] Abdul: STEP (2) sannan ya kashe wayarsa. ta dan ciji lebe tare da lumshe
ido cikin takaici,ba ta da zabin da ya wuce yin abinda mijin ta ke so.a fili ta ce ni kan bana son
zaman MIMI garin nan,na tsani halin ta,a ce yarinya karama a bar ta tana yin yadda ta ke so.ta
mike tana nunke sallaya. Abdulkarim ya yi sallama, ta amsa fuskar ta daure,sannan ta yi
tsaki, abdulkarim ya ce,lafiya hajiya?alhaji ne ya kira ni wai suna tafe shi da MIMI. abdulkarim
ya ja tsaki,don jin ambaci sunan MIMI, sannan yace,ashe yanzu zan juya a kan sawuna mu
gaisa kawai hajiya in sabi jaka ta,ai a wannan sati bani da darasi kamar yau,sai na sake dawo
wa. hajiya sauda ta yi yar dariya tare da fadin haba abdul,ka taho tun daga zariya har katsina
sannan ka ce mu gaisa kawai ka wuce saboda MIMI?ta ci gaba da fadin ba zai yiwu ba.dauki
jakarka kawai ka wuce sashin ku,ka watsa ruwa.barin in sa mutuniyarka tabawa ta kawo maka
abinci na san yanzu sun gama na rana.ya ce,ai ni bana son rainin wayonta ne hajiya,a ce
yarinya karama kanwar bayanka ta zo tana kawo maka rainin wayo,ba dama ka yi magana.ni
kuma kin sanni da zuciya sai in doke ta. hajiya tace,aa kar ka soma,ka san halin alhaji.ina fatan
baka manta da yadda yayanka abbas suka kwashe ba,in ka tuna zungure mata kai kurum
yayi,amma ta inda alhaji yake shiga bata nan yake fita ba.tsawon wata shida yaki ams gaisuwar
abbas.sai da biki shi sannan alhaji ya sauko,shima sai da abokan abbas suka taro abokan
alhajin aka hadu ana taba shi baki, sannan ya hakura da kyar da dokoki a kan 'yarsa.
Abdulkarim yayi ajiyar zuciya cikin takaici,sannan ya ce,ban manta ba.hajiya shi yasa nace, zan
koma,tace ka hakura da harkanta.yace, gaskiya alhaji ba yayi mana adalci,a ce cikin 'ya'yansa
mu ishirin da biyu,amma ya zabi daya rak yace,ita ce star don kawai tana da sunan
mahaifiyarsa.allah hajiya abin yana damu na, kanwarmu ce fa,amma ko shawara da ita sai
abinda ta ce a family. hajiya sauda ta ce,ku yi ta hakuri,
[01/10 12:45 pm] Abdul: STEP (3) Dadin abin ita dai ta mace ce,duk abinta ai dole ta yi aure
ko? abdulkarim ya ce, tabdi, wannan 'yar jin kan?ya zauna a kujera, sannan ya ce,allah ya sa ta
saurari wani.hajiya ta ce, ayya abdulkarim dole tayi aure. ba dai mace ba ce?shi kanshi zai so a
bar masa ita a gabansa?abdul' ya yi 'yar dariya,sannan yace,kila ya ce mijin ya dinga biyo ta
nan gidansa.hajiya ta ce, oho mishi su dai suka sani, suka yi 'yar dariya,ta ce ba su lokaci
kawai.ni dai ina ta fada ma allah,ku da ma na haifa ciki daya kuna jin takaici da haushinta,bare
wadanda ba ni ce na haife su ba.abdul ya mike tare da saba jakarsa,bari ni kan na isa
dakinmu,hajiya ta ce, to ni ma bari in je babban kicin. hajiya sauda ta tafi gefen babban
kicin,ka san cewar gidan babban gida ne mai tsari,tun daga waje za ka san cewa mamallakin
gidan ya tara abin duniya ba kadan ba.ta isa babban kicin din,mata uku ta samu a ciki suna ta
aiki,suka maido da hankalinsu gurinta tare da yin mata sannu da shigowa,ta amsa da sannunku
da aiki cikin girmamawa,ta kalli tsohuwar cikinsu ta ce,baba tabawa me aka yi da
rana?tsohuwar tace,taliya ce ke kan layi da rana,da dare kuma zamu yi tuwon masara da miyar
danye kubewa,ga taliyar nan ma yanzu na sauke. hajiya tace to,a canza na dare a yi mana
dan waken gari dawa sannan ayi shi da wuri.baba tabawa tace,maigida yana nan shigowa
kenan?hajiya tace eh,suna tafe,suka hada baki guri cewa,allah ya kawo su lafiya.hajiya tace
amin.sannan ta kalli jummai muna da kifin ruwa ko?jummai ta ce eh,hajiya ta ce yawwa ki dafa
kadan kar ki cika yaji kuma kar ki sa tafannuwa. sannan ki kula kar ya dagargaje na
MIMI ne. dukkan su suka hada baki gurin tambayar har da MIMI ne za a zo?jummai ta ce, allah
ya fishe ni yin kuskure. hajiya tace kar ki damu, sannan abinda kawai zan fada maku in tazo,ku
kawar da kai duk abinda za tayi kun ji ko?cikin karyayyar murya suka ce to shikenan,tabawa ta
kalli jummai kar ki sa mata tafannuwa,
[01/10 12:45 pm] Abdul: STEP (4) Wancan zuwan da ta yi maman sani daga sa tafannuwa
shikenan ya zama sanadin korarta. jummai tace,zan kula insha allah. hajiya ta kalli ramma
tace,da safe me muke da shi?ramma ta ce, shayi ne,hajiya tace,to a canza zuwa kosai da
kunun gyada,ta ce to hajiya. tabawa tace akwai kafar safa ko wannan karon ba zaayi ma alhaji
ba?hajiya tace,a dora zan dinga zuwa ina dubawa,na zata babu ne,tabawa mutumin ki fa yazo
abdul,a kai masa abinci,ina magajiya?tabawa ta ce allah sarki abdul ne yazo zan kai masa ma
da kaina maigida sukutum.hajiya ta juya tana dariya tare da fadin kowa ya duba abinda babu
sai yazo ya fada min. Da kanta ta nufi wajen me wankinsu yana ta gugar kayan yara,ta ce
masa ka je ka fadawa mai gadi da mai kula da fulawa cewa MIMI za tazo anjima,sannan yau
direba ya same ni a falo.ta sake cewa,danladi na fada maku ne don ku kiyaye bana son ana
korar min ku,danladi yace,zan fada masu.ya nufi gurin mai gadi,ya turo mata direba ya sanar da
su zuwan MIMI nan suka dinga tattauna rashin mutuncin MIMI,ya same ta tana duba nono a
cikin firiji.domin tasan aladan shi ta sha furan dare. Direba yayi sallama cikin
girmamawa,hajiya ta amsa,ya gaida ta sannan yace,ga ni tace,malam yau da ma ina son sanar
da kai ne,yau MIMI zata zo na san ba ka santa ba.amma ka samu labarinta?cikin in'ina yace eh
naji gurin su danladi.tace to ka tafi filin jirgi tun misalin hudu da rabi,gara ka jira su,domin da
jiran da suka yine wancan direban namu shine sanadiyyar korar shi da MIMI ta sa alhaji yayi.ya
ce zan kiyaye insha allah. Tun hudu yau ya nufi filin jirgin,jiran zai fi masa sauki da haduwa
da fushin MIMI. biyar da minti talatin suka iso,Alhaji bashir aliyu masari ya fito daga cikin
jirgi,MIMI tana biye da shi, sanye cikin riga da wando masu kalar pink sun dame ta tsam.sai
after diress baka mai sheki,sannan ta gaba an ratsa pink hakanan rigar ba ta kai kasa ba.don
haka ana ganin wandonta, dan siririn mayafinta ba shi da girma,
[01/10 12:45 pm] Abdul: STEP (5) Shima pink bai rufe dogon gashinta ba. Kafarta sanye
cikin takalmi shima pink dinne,da ratsin baki marar tudu mai igiyoyi,purse din hannunta da
wayoyin ta kirar nakia duk kalar pink ne.can sama goshinta zaka iya kallon wani katon gilashi
irin wanda wayayyun 'yan mata masu jin kansu suke sakawa.da gudu yau ya nufe su domin duk
da bai san MIMI ba ya san maigida na su.cikin ladabi ya yi masu sannu da zuwa,ya amshi jakar
hannun alhaji, alhaji ne kawai ya amsa, MIMI kan ko kallon shi ba ta yi ba. ya bude kofofin
motar sannan ya sa jakar alhaji a kujerar gaba,bayan sun fito daga filin yana hawa titi zai raraka
da gudu,alhaji ya ce tafi a natsuwa MIMI bata son gudu,yau yace,to ranka ya dade. shi kanshi
mai gadi a waje ya tsaya yana jiran zuwan su,yana hangosu da gudu ya nufi ciki ya wangale get
din,kamar yanda MIMI ke so,don bata son jira.ko da direba ya tsaya ya bude masu sannan ya
cire jakar ya bi bayan su MIMI ta kalli gidan sannan tace,Dad gidan nan yana son fenti yayi
datti,ya yi 'yan kalle-kalle,yace,na lura da haka za a sabun ta shi da fenti.direban ya ajiye jakar a
kujera sannan ya kalli alhaji Alhaji, na barku lafiya ya fita.Alhaji yaso ma kiran
hajiyata-hajiyata,ta fito,dankwali a hannun ta,domin lokacin ta gama saka kayan,ta yi adonta
cikin super kalar blue da ratsin yellow sai kamshin turare take yi. Ta kalli mijinta, sannu da
zuwa alhaji,ya ce,yawwa sauda ta dubi MIMI wadda tunda suka shigo falo ta natsu saboda duk
iya-shegenta tana tsoron uwarta,ta san hajiya sam bata daukar reni.ta dago ido cikin fargaba ta
kalli mahaifiyarta sauda tace, sannu hajiya,ta amsa yawwa,ya mominku nafisa da kuma sauran
kannenku?ta ce kowa lafiya,hajiya ta ce,masha allah,ta dauki hular alhaji da jakarsa da kuma
malun-malun dinsa ta nufi dakinsa tana fadin za a hada ruwan wanka ko? aa rabona da abinci
tun safe shima ba wani abinci na ci mai nauyi ba coffee ne,ta karasa dakin ta aje kayan
hannunta ta fito tana fadin mu je Dining.
[01/10 12:45 pm] Abdul: STEP (6) Hajiya ce ta janyo masa kujera ya zauna,ya kalli MIMI zauna
mana uwata.ya mayar da kallon shi ga hajiya sauda, an yi mata farfesun kifin? hajiya ta kalli
MIMI cikin daurewan fuska,sannan ta ce,an yi,MIMI ta turo baki tare da hada rai. hajiya
tana zuba masu dan waken cikin plate tare da colslow,ta janyo wani plate din tana zuba masa
farfesun kafar sa,ta tura gabansa tana fadin alhaji ba ka tambayi yaran gidan ba?ya kalle ta
cikin 'yar zolaya yace,duk ganin ki ne ya mantar dani.ko da dai na san zuwa yanzu suna
lslamiyya ko?ta ce eh,yau kam ma da murna suka fita,don na gaya masu cewa kana tafe,ya ce
ga shi ban riko masu tsaraba ba.amma bari in sa direba ya sayo masu,ta ce aa zai fi kyau ka
fita dasu don yaran nan basa samun kulawarka,kamar fa sam basu shaku da kai ba. Ya
kalli MIMI wacce ta jibga tagumi,ya ce zan gani ko da lokacin,kin san fako a can ba samu zama
nake yi ba.shiru tayi don ta san kome za tace ba fahimtar ta zai yi ba,ta jima tana yi mishi nacin
cewa,ya dinga baiwa yaran ko da awa daya ne a cikin lokacinsa, amma sam ya ki.ko su da
suke matansa basa ganin shi a kan lokaci,sai yayi wata ko sati uku in kuma yazo kwana biyu
yake yi, nan guri ta ya kwana daya ya je malumfashi wajen hajiya binta ya kwana daya
tunaninta ya katse lokacin da ta ji yana tambayar MIMI menene uwata?na ga duk kin bata
ranki?ki ci kifinki mamana. ya kalli hajiya sauda ina kifinta?hajiya ta nuna kular da cokali,ga
kular kifin nan gabanta?ta dauka mana ko a baki zan bata?MIMI ta sake tura baki tare da kallon
mahaifiyarta,ni na koshi,hajiya sauda ta ce, karyarki dubu wallahi kin yi kadan ki ce a dafa miki
abin, yanzu ki ce baza ki ci ba,saboda bakin raini ai na lura da ke tunda ku ka shigo gidan nan
na san baki so zuwa ba, ko katsinar ce baki so zuwa ba oho miki, amma bakin ranki ya kare
miki can. Sauda!alhaji ya katse ta tare da daga hannu, gaskiya ni bana son
abinda ki keyi,a ce ke da 'yarki ta cikinki amma ba ki kaunarta?....
[01/10 12:46 pm] Abdul: STEP (7) Hajiya tace, ba kaunarta bane bana yi, halinta ne bana
so.kuma in har ta ga mun zauna inuwa daya da ita to ta tabbatar ta canza halinta,in ko ba ta
canza ba to sai dai ta nemi wata uwar ko da yake tana da ita ma. ya tausasa murya
ai ba maganar fada bane, amma gaskiya ba zan iya kallo kina mata irin kalaman ba, kullum
tana yi mini korafin ba ki sonta,ita in fada mata gaskiya ko dai bake ce ki ka haife ta ba?ya aje
cokalin hannunshi,na rasa me take miki,ita dai ba ma a kasan nan take karatun ta ba.sai ta zo
hutu irin haka,amma sam ba kya ko yin kewar ta. hajiya ta tsiyaya masa lemun abarba,wanda ta
hada masa,a cikin kofi sannan ta tabe baki ta ce,halin ta kawai zata canza,in dai tana son
soyayyata.yanzu baka kalli shigar da tayi ba? tun daga abuja ka sako ta gaba har katsina, kana
mahaifinta ga shi kanta a waje,kayar jikinta duk sun dame ta,wai ita dole ta waye.
ya kalli MIMI sannan ya kalli sauda, da dan murmushi,ina laifin kwalliyarta,ni ban ga aibun ta
ba,haka 'yan mata matasa irin ta ke yi.ya kalli MIMI,ci kifin ki uwata kar ki damu kin ji?tsaki
hajiya ta yi ta nufi dakinta.sai lokacin MIMI ta samu damar yin mita,kaga ko dad,sai da nace ka
barni can in gama hutu na,ka ce aa sai na zo, ni daman na san hajiya ba za ta taba so na ba.
Ta mike tsaye tare da kallon jikinta,shiga tafa, mene ne aibunta?ya kalle ta cikin sigar lallashi
yace, ban ga laifi ba.ita hajiya wai sai tace,sai na saka hijabi da atamfa,ni kuma ba zan iya sa iri
wannan kayan zafin ba.na yi karatu na waye ni ba irin su usaina ba ce kauyawa.yayi
murmushi,shgwabarta tana burge shi.kallon ta ya ke yi tamkar 'yar shekara biyu. ya mike ya
zagayo wajen ta ya dafa kafadarta,kar ki damu uwata.mamanki tana sonki,na san ta ga nafi
damuwa da kene cikin 'ya'ya na,kin san don ita ce ta haife ki,shi ya sa fa.in da a ce kamar hajiya
binta ce ko nafisa da tuni na sallame su,kin manta na taba kora hajiya binta saboda ke?ta ce na
tuna Dad,
[01/10 12:46 pm] Abdul: STEP (8)Ya ce to kar ki damu ina son mahaifiyarki ko da bata haifamin
ke ba, bare ta haife ki. kina son a ce mahaifanki biyu ba su tare?ta ce ba zan so ba dad.amma
ka yi mata magana ta daina matsa min,ya ce zan yi mata, amma ke ma ina son cikin kwana
biyun nan ki canza kaya sawarki,ki rinka saka irin wadanda take so.ta ce zanyi in dai za ta bar
ni in yi abinda na ke so,ya ce za ta barki mana kin ji,ki dai na kuka.ya yi ta lallashinta har ta
daina kuka. suna cikin cin abinci hajiya ta sake fitowa daidai lokacin yara suka
dawo daga lslamiyya da sallama suka shigo, ita ce ta amsa