Showing 9001 words to 12000 words out of 30377 words

Chapter 4 - CANJIN RAYUWA BOOK 1 HAUSAWA NOVELS BY HALIMA ABDULLAHI K MASHI

fili ta
ce,ka ji hajiya wai da talaka da mai kudi wai duk daya ne,ta ina suka hadu?ai bambamcin ma a
bayyane yake.ai talaka wahalalle ne bayin mu ne,ita hajiya dai kawai bata waye ba ne,take irin
maganar. shi kuma wawa sakaran malamin allah yasa ya yarda ya bini zuwa abuja, sai
na taka shi,na ja shi,na tozarta shi,sai ya gane ya taba MIMI.lta kuwa hajiya da dadin rai ta fita
dakin,na ta a zaton ta 'yarta ta soma hawa hanya,
[01/10 12:46 pm] Abdul: STEP (25)Tunda har ta soma ba da hakuri,abinda bata taba yi ba a
tsawon rayuwarta.watau tayi laifi ta bayar da hakur,gani ta ke yi ta kaskanta. da
sallama hajiya ta shiga dakin yana zaune kan kujera,yana duba jaridar leadership.ta zauna a
hannun kujerar ga ni alhaji. ya kalle ta,kin san dai tafiya zan yiki ka koma dakin kika share ni
ko?ya ci gaba,ni gaskiya wannan zuwa ba samu wa maraba sosai ba kamar baya.ta yi yar
dariya,sai dana ce,kar kazo da MIMI,ai amma ka ki,duk ita ce ta yi ta dama min lissafi.ya ce,to
naji shikenan,ai tunda nima nayi mata fada wasa da sallah,ta daina in sha allahu, don haka ma
nike so ki taimaka kiba mu aron malamin nan na yaranki tunda naji kina yabon shi gurin kwazo
da jaruntar koyar da yara,in ya so sai ki samo masu wani. hajiya ta ce,tabdi,ai ba zai
yiwu ba,sai dai in a samo maku wani,ya ce.saboda me?bafa da koyarwan gidan nan kadai ya
dogara ba.malami ne a makarantaru,ina zaton akwai gidajen da yake koyarwa.ka bar ta kawai
ta karasa hutu a nan,na san kafin ta koma nan da wata biyu ta samu abinda ta samu.ya kama
hannunta ina son ki kira shi fiye da abinda yake samu.ta ce,in har ya amince kana ganin zata yi

karatun a can? ya dan matse hannunta, kar ki damu sauda zata yi,ta ce,shikenan zan kira
shi,sai dai ban so ba zai bar yara na,ni dai suna karatu sosai a gurin shi. hajiya sauda ta
kira malam lsmail ta ce masa don allah in yana da lokaci yazo maigida yana son ganin shi.ko
yarinyar nan ce ta kai karar shi,kuma yasan halin masu kudin nan da jarabar son yaran tsiya.
ta katse mishi tunani da cewa,kar ka damu alheri ne,bari ma dai in fada maka,a takaice so yake
ya dauke ka zuwa abuja saboda yarinyar nan,ka dinga koya mata karatu da kannen ta na
can.don allah zan roke ka kar ka ce aa, saboda nasan zai biya ka da kyau.kuma nima zaka
taimake ni.ya ce,hajiya gaskiya yarinyar nan da kyar in zata bayar da hadin kai a kan karatu,ga
ayyuka na a nan.ta ce,ka dai zo din a yi magana a zaune ko?
[01/10 12:46 pm] Abdul: STEP (26)Ya ce,to shikenan in na yi wanka yanzu zan taho.
sai da ya bita gidan su mahamuda abokin shi,ya isa yayi sallama mahamud ya amsa tare da
cewa,dan halak!sauri nake in zo gidanku yanzu,ashe kana tafe,ya ce,lafiya dai zaka
zo?mahamuda ya ce,lafiya lau,takardun nan ne na manta,wanda headmaster ya baka kayi
makin na dalibai. ya ce,shaf! na manta,ko dana zo gida fa ban tuna ba.suka fito tare ya ce,in
bazaka fita ba mahamud mashin dinka zan ara,zan je gidan bashir masari.mahamud ya ce,to ka
sauke ni bakin kasuwa?ya ce,to ka san me zai kaini?ya ce,aa lsmail ya ce,hajiya ce ta kira ni,
wai tana son in koma abuja in koyar da wannan mara kunyar da nake baka labari jiya.wai tasan
zan sami kudi.mahamud ya ce, kawai kaje,kar ka manta da tarin bukatun ka wadanda kudi
kawai suke so.lsmail ya ce,ina sane, matsalar kawai bana jin zan dauki rainin yarinyar ko da
suna taka kudi.mahamud ya ce,ka dai je kaji in abin zai yiwu,amma dari bisa dari na baka
goyon baya. A falon baki abdulkarim yayi wa lsmail jagora,ya shiga ya sanar da hajiya
cewa ga malamin yaran nan tare da alhaji.suka jera zuwa falon bakin ya gaida su cikin mutumci
da sanin ya kamata,hajiya ce ta gabatar ma malam lsmail bukatar,yayi shiru.alhaji ya ce,kar ka
damu nasa kana koyarwa a gurare dabam-dabam ba da gidan na kadai ka dogara ba.ina son
ka hada abinda kake samu a kowane wata ka fada min.in har zaka amince ni kuma zan ninka
maka kudi abu daya dai da zan roke ka shine ka tabbatar yarinyar nan ta iya karatu. hajiya ta
ce,ka dinga yi mata nasiha ka tsoratar da ita.alhaji ya daga mata hannu,wata irin tsoratarwa
kuma?karatu dai ta ce, shikenan karatu ai ya hada komai.lsmail dai yan jinsu kanshi a sunkuye
lissafi yake tsakanin amincewa ko akasinta,can alhaji ya katse mishi tunani da cewa, me ka
ce?ya dago ya dube shi da nufin cewa aa,sai mutuncin hajiya da kwarji ninsu ya hana shi fadin
haka,sai ya bige da cewa,a bani lokaci domin sai na sanar da gidajen dani ke koyar da
'yayansu.
[01/10 12:46 pm] Abdul: STEP (27)Na rubuta takardan barin aiki a lslamiyyar dani ke koyarwa.
alhaji ya ce,yanzu dai a takaice ka yarda kenan?lsmail ya ce,na yarda,sai dai in fara watan
gobe.alhaji ya ce, shikenan,nawa kake samu duk wata?hajiya ta ce,ai sai ya je yayi lissafi ko
malam lsmail?ya ce,eh! haka ne.alhaji ya ce,kana da mata ne?ya girgiza kai tare da cewa
aa,ina dai nema.alhaji ya ce,to shikenan,hajiya gaki nan,za ji komai gare ki.amma kafin haka
zan so in san wanene lsmail?ya dago ya kalli alhaji,hajiya ta ce,wannan kaidar shi ce in dai zai
dauki mutum aiki a karkashin sa,sai ya san wani abu daga tarihinsa,ko da kadan ne.
lsmail ya ce,haka ne. lsmail bin abdulrahaman shine suna da aka fi kira na.mahaifina malam
abdulrahaman ya rasu tun ina jss2,haifaffen nan katsina ne,dan kauyen 'yargoje.amma shi yayi
gidansa a nan kofar soro.hakanan mahaifiyata ta rasu wata shida bayan rasuwar mahaifina,mu
biyu ne 'ya'yanta.kasancewar tana da ciwon sikila tana shan wahala a guri haihuwa ta hakura

tun daga kaina,sai aka tsaida mata,ciwon shine yayi sanadiyyar mutuwarta. kafin haka
dama bata jin dadin zama da abokiyar zamanta lnna,wacce ita ce uwargida.lrin mata nan ne
masu kishin tsiya,yaranta goma sha daya,kuma duk su ne manya damu,bakwai duk maza
ne,sai mata hudu,kuma duk suna raye,daga cikin yaran nata, manya guda uku suna zaune a
gidan yanzu haka da matansu da 'ya'yansu. dama an raba mana gado, ni na samu daki a
soro,ita kuma yata dake aure a kofar soro sai aka bata wani dan fili karami dake jikin dakina ta
kofar gida. lsmail ya dago ya kalli su hajiya,ku yi hakuri ina fada maku ba.nima ban san
dalilin da zuciyata amince in sanar daku abinda bana son ina tunawa bama.hajiya ta ce,kar ka
damu ci gaba.tunda na rasa iyayena haka na taso bana jin dadin kowa a gidamu,tun daga
yayyina har ya zuwa mahaifiyarsu, babu mai biya min kudin makaranta.yaya amina kuwa,ita ma
ba mai karfi take aure ba.ga yara tana dasu har biyar.don tsakani na da ita akwai tazara ta,
[01/10 12:46 pm] Abdul: STEP (28)Don tsakani na da ita akwai tazara ta gurin haihuwa,mijinta
ne ya kai ni wajen koyon gyaran TV,da yake ina son karatu sosai,sai na mayar da hankali har
na iya,da dan abinda nake samu na biya kudin makaranta. lslamiyya kuwa akwai
mahaifin abokina malam aminu shine malaminmu na lslamiyya,shi ya dauki nauyi karatu na
lslamiyyata.da ya lura ina son karatu lokacin dana kammala sakandire di nada saukar
alkur'ani.haka kuma mahaifin mahamud shi ya tsaya min na samu shiga mutawassid wato js1
na lslamiyya tare da dansa mahamud.koda yake ya ce min makarantar tana da tsada,ta yaran
masu hali ce,ya roki mai makarantar ya rage masa biyu bisa biyar na kudin. amma
fa akwai karatu,malaman kwararu ne,makarantar reshen ta yana madina.sukan bayar da tallafi
ga dalibai guda uku da suka zama zakaru a matakin difloma,don yin karatun digiri a jamiar
madina.wannan yasa na zage dantsen karatu bana wasa ba.duk da karancin shekaru na malam
aminu shine ya sake yimin hanyar koyarwa a wani gida,saboda in dinga samun na siyan
littatafai.hakanan ina koyarwa a lslamiyyar shi wanda muka yi sauka. da wannan ne nake
tallafe da rayuwata.har na kammala shekaru shida na sanawiyya,lokacin ne na samu koyarwa a
nan gidan, wanda malam lsa mai makarantar mu yayi min tayi,ya ce min yaran a makarantar sa
suke karatu, 'ya'yan bashir masari ne,in zan koyar dasu.ban yin gardama ba,don ina son ci
gaba da difilomata a nan makarantaarmu eh-mukhtar,yau wata biyu da kammala difiloma,ta
kuma nayi nasarar zuwa na uku a ajinmu,sai dai kash makarantar daza muje a madina mutum
biyu ta bukata,don haka bana ciki.sai dai ko wani lokaci zasu iya neman na uku,ina burin in
karanta larabci ko kuma tafsir. amma a yanzu ina da haddar sittin,ina da haddar hadisai da
dama.na san tauhidi da fikihu daidai gwargwado. malamai da dama suna jinjina
ma kwakwalwata. malam aminu mahaifin mahamuda yana yin tafsiri da azumi a babban
masallacin unguwarmu,sau da yawa nine,
[01/10 12:46 pm] Abdul: STEP (29)Malam aminu mahaifin mahamud yana yin tafsiri da azumi a
babban masallacin unguwarmu,sau da yawa nine nake ja masa baki. kuma zuwa yanzu
shekara ta ashirin da bakwai. ya kalli su hajiya wadanda suka yi shiru suma saurare.ya
ce,shine tarihin lsmail bin abdulrahaman.alhaji ya ce, shikenan zaka iya tafiya duk yadda kuka
yi zanji gurin hajiya.kuwa tausayin lsmail ya cika ta,ta ce,zan iya tambayarka?ya ce,eh zaki
iya.ta ce a fannin boko fa,daga sakandire ka tsaya?ya ce,eh,amma yanzu na zana jamb domin
karanta zama ban samu wancan damar ba.hajiya ta ce,ALLAH ya taimaka ya bayar da saa,zan
baka 'yar shawara ka dinga ziyartan malamai don neman karin ilimi,ya ce,ina zuwa hajiya, duk
asubahi ina daukar karatu.ta ce,ALLAH ya taimaka alhaji ya ciro kudi daga

aljuhunsa ya mika masa,ga shi ka hau mota.ya ce,ba komai alhaji da mashin nazo ka
barshi,hajiya ta ce,ka amsa sai ka sha mai. sai na ganka,ka sanar dasu. ya amsa tare da yin
godiya suka yi sallam.lsmail ya buga mashin kai tsaye gidan su mahamud ya nufa don ya kai
masa mashin dinsa.kuma ya gana da mahaifin mahamud,su kuma sake tataunawa a kan batun
tafiyarsa abuja.cikin saa yana tsayawa mahamud yana fitowa cikin faraa,suka nufi juna lsmail
ya ce,sai ka ce dama kana jiran isowa ta?mahamud ya ce,wai inna ke son alayyahu,duk ga
yaran sun tafi islamiyya,suka yi musabaha tare da gaisawa,lsmail ya ce,to hau muje a mashin
mana muje mu amso mata,sai da suka je suka dawo suka zauna a dakalin kofar gidan.
lsmail ya kalli mahamud,ka san cewa na kasa samun natsuwa da batun zuwa abujan nan?ga
shi naje da nufin ince aa ba zanyi ba, amma ban san kadarar data sana amsa ba.duk sai suka
yi min kwarjini na kasa kin amincewa. mahamud ya ce,in ka ce haka ka ban mamaki,kai dana
sani dakakke mara tsoro,naga ko a nan a lslamiyya da muke koyarwa duk yaran masu da shi
din ne,amma shakkar ka sauke yi lsmail ya ce,baza ka gane ba,ita fa yarinyar ina
zaton irin,
[01/10 12:46 pm] Abdul: STEP (30)Tabararrun nan ne ko da ban sani ba dai,amma na ga
alamar kamar uban bai so a takura mata,ga ta da alamun ta tsani talaka bata dauke shi wani
abu ba,ni kuma duk sun san hali na,bana son raini.shi yasa bana raina mutane,dalili kenan
dana keta tunanin ya ya koyarwar tamu zata kasance?mahamud ya ce, shawarata a nan kawai
ka aje duk wani waswasi kai dai ka amshi kudinka ka cika burinka. ka tuna da
karatun da muke son yi,kai ko yau jamiar madina suka kira kaza ka bukaci kudi.ga yarinyar nan
daka dauki son duniya ka dora mata, zainaba,kar ka manta da abinda mahaifiyarta ta
ce,sadakin 'yarta dubu dari, akwatin 'yarta me shida ne,lsmail ya ce,da na tuna abubuwan nike
jin cewa ya kamata in jajirce in je,yanzu dai malam nake son gani in nemi shawararsa. da ya
amince zan kara samun kwarin gwiwa.haka kuwa yana unguwar har aka yi lshai, lokacin ne
lsmail ya samu magana da malam,yayi masa bayanin komai,malam ya bashi goyon baya tare
da karfafa masa gwiwa, cikin farin ciki ya nufi gidasu dakinsa da ke soro ya bude ya shiga ya
kunna wuta haske ya gauraye dakin,ya zauna bakin katifarsa ya cire hularsa da agogo tare
kuma da wayarsa ya dora a teburin da ke gefen katifar mai dauke da tarin littafai,ya ciro kudin
da alhaji ya ba shi,da ma ya ba mahamud dari biyar daga ciki.ya dauko wani littafi wanda a
cikinsa ya ke ajiyar kudi ya dora su a kan kudin da yake ciki,ya mayar da su ya rufe,ya mayar
dashi a mazauninsa.ya dan kwanta rigin-gine gurin zainaba yake son zuwa don zuciyarsa ta
matsu da son ganinta,amma yana jin jikinsa ya gaji.wayarsa ta soma ruri,yana daukowa ya ga
hajiya ce. ya daga tare da sallama ta amsa ya gaida ta.ta ce, ka yi hakuri na kira ka
cikin dare.ya ce,ba komai hajiya. ni mana so in kira ki,sai naga bari dai in bari sai da safe.ta ce
daman na kira kane in sanar da kai cewa alhaji sun tafi dazun da mimi,ina son don mu karkare
maganar ina son in sanar da shi.ka fada min albashinka,yaushe kuma za a kai,
[01/10 12:46 pm] Abdul: STEP (31)Yaushe kuma za a kai ka abujan?saboda ku soma karatun
da wuri.lsmail ya gyara zama,hajiya batun albashi dai ni ba zan iya cewa ga shi ba,ta ce yauwa
ni ma bana son ka ce ma shi kaza ne. don alhaji in mutum yana son ya ce moriyar shi
to ya biyo shi ta haka,zan fada mishi cewa ka ce duk abinda ya ga yayi,na san zai nemi
shawarata.ni kuma na san abinda zan ce masa.labarinka daka bamu a jiya na tausaya maka,
kuma na tabbatar kana bukatar taimako,yanzu ka yi magana da malamin naku?ya ce,eh?gobe
zan je gidajen da nake koyarwa in sanar da su.ko zuwa jibi sai mu tafi abuja din.ta ce shikenan

lsmail sai ka zo jibin,ya ce to na gode, hajiya ta ce ba komai. sun yi sallama hajiya tana ji
a zuciyarta lsmail tamkar danta.washegari kamar yadda ya alkawarta ya sanar da duk wanda ya
kamata cewa,gobe zai yi tafiya zuwa abuja,ya sanar dasu zainaba kadai ta rage masa ya je su
yi sallama. da yamma laasar ya shirya zuwa gurin mahamud don ya raka shi zuwa gurin
abar son sa,su yi sallama.yana isa lslamiyyar da suke koyarwa ya samu mahamud ya fito daga
ajin da yake.bayan sun gaisa lsmail ya ce mu je ka raka ni gidan su zainab in duba ta da
jiki,daga nan in yi sallama da ita.ko ta zo lslamiyya?mahamud ya bata fuska,gaskiya lsmail ka je
kawai.ka ga ba a ma ta shi ba.ya ce amma ka fito ajin ai,wai me yasa ne ko yaushe idan na ce
muje gidan su zainab sai ka be min aa?yau dai dolenka mu je,kuma gurin ka zanbar amanar ta.
mahamud ya ce,mu je dai, amma ba ruwa na da wata batun amana.suka jera a hanya ya kalli
mahamud,ban san me yasa kuke jin haushin yarinyar nan ba.haka yaya amina kullun sai ta yi
min korafi. mahamud ya ce,ai ban boye maka dalilin ba.yarinyar tana da karancin
tarbiya,sannan 'yar mace ce.ga shi uwar ta dora dogon buri a kanta. lsmail ya ce in fadi maka ni
ba wata matsala ba ce a guri na.ni dai ina sonta don allah ita ma tana so na. ln ta zo
hannu na ba sai yadda na yi da ita ba? mahamud ya ce,haka kake fada.
[01/10 12:46 pm] Abdul: STEP (32)Mahamud ya ce, haka kake fada.suna isa kofar gidan suka
aiki wani yaro ya kira ta.ya fito ya ce an aike ta,lsmail ya ce jikin yayi sauki kenan,ya kalli
yaron,je ka ce nesa ne ta je,ko kusa ne mu jira ta?yaron ya koma,lsmail ya kalli mahamud,in
nesa ne sai mu tafi mu dawo da daddare.mahamud ya ce ka dawo dai ni kan bazan zo ba.yaro
ya iso tare da cewa da

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login
google.com, pub-9213700357025247, DIRECT, f08c47fec0942fa0