Showing 3001 words to 6000 words out of 30377 words

Chapter 2 - CANJIN RAYUWA BOOK 1 HAUSAWA NOVELS BY HALIMA ABDULLAHI K MASHI

sallamar,husna da hasina ne a
gaba,suka ce sannu da gida hajiya ta ce yawwa sannunku da dawowa yara na.ina sauran?
kafin suba ta amsa sai ga su suna ta yin sallama,da hannu ta nuna masu gurin dining,ga dadin
ku,suka nufi gurin suna gaida shi da daidaya.ya dafa kan husna da hasina, su ne kanana a
gidan, yana ta amsa masu.MIMI ta hada rai ita ba ta son hayaniya. dady ya ce,ba ku gaida sista
MIMI ba.suka kalle ta don suna tsoron ta,sannu yaya MIMI,cikin daure fuska ta ce,yawwa,na

amsa duka ne ba sai kowanne ya gaishe ni daya bayan daya ba.hasana da usaina sune 'yan
matan da suke bi MIMI a haihuwa.dad ya kale su ku shirya da kannen ku, yau yazo ya kai ku
super market ku sayo tsarabarku, don ban riko komai ba, kowa ya je ya zabo abinda ranshi ke
so. Yara suka shiga murna hasana da hussaina suka ce dad,mu kam ba zamu je ba.ya
ce,saboda me?suka ce,muna da karatun hadda gobe,malamin mu zai zo, bin
abdulrahaman.hajiya ta ce,tabbas ba ku da halin fita, in ba haka ba zaku sha dukan tsiya gurin
shi.duka kuma?in ji dad dinsu,hajiya tace sun wuce duka kenan?karatu sai da zare
ido.abdulkarim ya yi sallam, ya shigo falo suka amsa,ya iso gurin dadin shima ya gaida
alhajin.MIMI tana ta chatin dinta ba ta dago kai ba,shima bai ko kalle ta ba. ya dubi su hasana
ya ce, kun dawo?suka ce eh! yaya sannu da zuwa, dazun hajiya ta fada mana zuwan ka. mun
je dakin ku kana wanka,
[01/10 12:46 pm] Abdul: STEP (9) Kuma lokacin lslamiyya ya yi dole muka tafi.ya ce,na ji
shigowar ai, ya ya zauna,usaina na fadin,lslamiyya lafiya,munyi murajaa ne yanzun. ya ce, kun
kusa fara jarabawa kenan suka ce eh! hasana ta ce,yawwa yaya don allah ka amsar mana
hadda in anjima mun yi magariba, gobe da safe muna da malamin gida bin
abdulrahaman.abdulkarim cikin sigar tsokana ya ce, bani da lokaci,ku ce gobe zanyi kallon
duka. usaina ta ce agaji yaya abdul, bulalarshi akwai zafi,suka sa dariya tare.ya ce,bari mu yi
sallah sai in karbar maku,suka ce,yawwa yayanmu mun gode. MIMI daga wurin da take
zaune tana jin su tana kuma kallon su,sai ta soma mita,ni na san duk 'yan gidan nan ba sa so
na,dole kawai suke gani na,kalli yaya abdul,ko kallo na bai yi ba.alhaji yace,kai! abdulkrim,ya ce
naam,ya zo ga ni dad.ya ce baka ga MIMI ba ne?ran abdulkarim ya baci,nan a take fuskarsa ta
nuna,cikin wata murya marar dadi ya ce,na ganta mana dadi.shine ba za ka yi mata magana
ba? Kafin ya yi magana hajiya ta amsa da cewa, in duniya da gaskiya ita da shi wanene
gaba?shine ya kamata ya gaida ta,ko ita ce ya da ce ta gaishe shi?. alhaji ya ce,amma ita
bakuwa ce.bayan haka kuma yaushe rabonsa da ganinta?a kalla ya nu na kewarsa gare ta
ko?kan abdul yana kasa tamkar ya sa kuka don haushi da takaici.hajiya ta ce,bai gaishe ta din
ba.tafi abinka abdulkarim,cikin sauri ya wuce.su hasana ma suka yi dakinsu ita ma hajiya ta
juya zuwa dakinta,MIMI ta kalli dad,kawai mu koma kalli fa duk yanda suka watse suka
barmu,ya dafa ta karki damu ina zuwa. baki gado hajiya sauda ta zauna ta zabga
tagumi,wannan abin ya ci mata rai,a ce mutum kamar alhaji ya dinga irin wannan abu sai ka ce
yaro.kirikiri yana gani garkiya sai ya runtse ido saboda son zuciya,bai san cewa haka zai sa kan
'ya'yansa ya rabu ba ne?sallamar shi ce ta katse ta,ta dago ta dube shi,shima ya iso ya zauna
bakin gadon.haba hajiya ki sakarwa 'yarki fuska mana?ke ba abin faharin ki bane a ce nafi son
'yarki,duk cikin 'ya'ya na?
[01/10 12:46 pm] Abdul: STEP (10) Ya kama hannunta cikin sigar lallashi ya ce,haba sauda kin
fa san ina tsananin sonki, sonki ne fa ya shafe ta ko baki lura ba?ta daga ido ta kalle shi,ban
musa ba,na san kana so na,amma ni burin na shine ka yi adalci tsakanin yaranka alhaji, ko don
gudu rarrabuwar kansu. ya ce,menene na yi mata wanda ban yi masu ba?ta kalli cikin idon
shi,ai ba za su kirgu ba,banda nuna tsantsar kulawa a fili, duk cikin yaranka wanene ka kai kasa
wajen karatu bayan ita?to indan wannan ne,karatun na su na gida ya fina ta cin kudi sauda.
umm, haka dai za ka ce,tunda kana son kare kanka,ya ce, ni dai ina neman alfarma ki sakar
mata fuska ki dan ja ta a jikin ki har mu tafi.ta kalle shi,ta rasa me zata ce masa,sai kurum ta ce
to. don tana son kawo karshen zancan, ya shafi kumatun ta,na gode,ya matso da bakin shi

saitin kunnuwanta,ina son a kyuatata shimfida ta anjima. don na iso da muradin hakan.
Ta sake murmushi tare da kallon shi,wai alhaji yaushe zaa girma ne?ta yi tambayar cikin sigar
wasa. ya janyo ta jikin shi,wa ya ce miki ana girma da lada? sai dai in mutuwa ce ta dauka.suka
sa dariya tare, daidai lokacin aka yi kiran sallar.suka mike, ta ce lokacin sallah yayi bari in fita
'yan mazan nan sai nayi fama sannan su wuce masallaci.tare suka fita ya nufi dakin shi,har
lokacin MIMI tana zaune a falo.sai dai lokacin ta koma kan kujerar zaman mutum biyu tana ta
chatin. alhaji ya nufe ta yana cewa,mamana kina hutawa ne?ba tare data dago ba,ta ce
eh dady.ya ce da kyau.ya wuce dakinsa. hajiya sauda ta dube ta,ki tashi kiyi sallah,ta dago ta
kalli hajiyar ta ga fuskarta a daure,ta zabga mata harara na ce,ki tashi ki yi sallah.tsam ta mike
ta nufi dakin su usaina inda nan ne take sauka in ta zo,kayan tama cikin suke.sai dai ita bata sm
hakan saboda a abuja sasanta dabam, amma a nan hajiya ta hana a yi mata dakinta dabam.ta
sami su hasana suna sallah, ta fadi kan gado ta ci gaba da chatin dinta.ga al'ada alhaji in ya fita
sallah,
[01/10 12:46 pm] Abdul: STEP (11) Yakan kai sha biyu bai shigo gida ba zai yi ta gaisawa da
mutane, abokai zuwa 'yanuwa suka ji cewa ya shigo gari.don haka ita ma hajiya bata fito ba sai
bayan sallah isha,ta shiga daki alhaji don sake kalailai ce shi,tare da kunna turarukan kamshim
daki,ta fitar ma da alhaji kayan barci,ta dama masa fura,ta nufi dakin yaranta don ta tabbatar
suna cikin koshin lafiya.daki maza ta fara shiga, umar da aminu suna ta yin home work,
abdullahi yana kwance kan gado, sadik yana buga game a tv. ta ce,sarkin game kai ka yi home
work dinka? ya ce, eh nayi hajiya ta kalli abdullahi,kai fa bawan allah yau da wuri zaka yi barci
kenan? ya tashi zaune kaina ke ciwo hajiya shi yasa ki kaji na ce dad ya bari sai gobe mu je
super maket din.don ba zan iya kula da su ba. ta ce,ba sai kun yi haka ba,ya
ce,kin shiga daki lokacin ta ce,to ka sha magani?ya ce eh!ta ce to allah ya sawwake,ya ce
ameen.ta ce,sadik tashi ka kulle muku kofar ku sai da safe,suka ce,to ta ce,kar fa ku manta da
yin addua lokacin barci,suka ce to.ta nufi dakin su husna da hasana da kuma zainab yar gidan
hajiya binta, wace ta ki komawa wajen uwarta,tun lokacin da alhaji ya saki hajiya binta,ya kwaso
yaran ya kawo su nan.hajiya sauda tace sam ba zai yiwu ba,lallai ya mayar da ita,ta rike
kayanta. domin ita kanta ba zata sa araba ta da 'ya'yanta ba.shine da ya dawo da ita ya mayar
mata da yaran amma ban da zainab,don kuwa ta kekashe ba9a ta bi su ba. lta ta fi son
zama a nan, hajiya sauda ta rike ta,ta hada da 'ya'yanta guda goma sha biyu da ta haifa suka
zama sha uku.su kam sun fara barci.don haka ta shigo ta yi masu addua tare da kulle masu
kofar dakinsu. hasana suna zaune suna kara ma juna haddar alkur'ani mai girma, ita kuwa 'yar
gwal,wato MIMI tana kishigide kan gado.tana ta chatin,kai tsaye gurinta hajiya ta nufa ta fisge
wayar da sauri MIMI ta dubi wayar cikin bacin rai.tana ganin hajiya sai ta yi kasa da kai kamar
munafuka,kin yi sallar ne? cikin tsawa ta ji maganar MIMI,
[01/10 12:46 pm] Abdul: STEP (12)MIMI ta yi shiru, ta ce,ba ki ji niba ne?ta girgiza kai tare da
fadin banyi ba. hajiya ta rufe ta da fada bangane ba kiyi ba? Anya ma kina yin sallar na
kuwa? ta kalli hajiya cikin sauri tare da fadin ina yi mana,hajiya tace,karya ne kalli agogonki
karfe nawa ne yanzu?da har zuwa yanzu baki yi ko sallar magariba ba bare lsha.in na lura
musulunci ba ya birge ki,lslamiyya kin daina,duk wani abu da lslam yazo da shi,komi na addini
kin mayar da shi kauyanci,ke ga 'yar boko ko?MIMI dai bata dago kai ba,hajiya ta ce,na san ko
zaa kashe ki yanzu da kyar in zaki iya kawo mini fatiha cikakkiya. kin zauna kina ta
danne-dannen waya,in ba ki sani ba ne gara ki sani,kina cutar kanki ne.rayuwar daki ka daukar

wa kanki ba mai dorewa ba ce,don haka ba ta dace da ke ba.ki ta shi ki yi sallar yanzun nan,
sakarya marar hankali. simi-simi MIMI ta tashi ta nufi bandaki,hajiya ta ce,tunda abin naki ya
soma nisa haka,wayewar taki har ta kai ki da gudu salla,to nan gida za ki kare hutunki.ki dau
karatu gurin malamin yaran nan,ki koyi salla tun da bani da tabbacin kin na yi.bari baban naku
ya shigo,ta juya ta fita da wayar a hannunta.MIMI daga cikin bandaki,kuka wiwi ta dinga yi,ita
kam baza ta iya zam har ta gama hutu cikin takurar ba. a silent hajiya ta saka wayar MIMI ta
ja durowa ta jefa.MIMI tana kuka ta yi sallar,su hussaina suna kallonta,ta idar ta fada kan gado
ta ci gaba da kuka.don ita amshe mata wayar da hajiya ta yi,ya fi bata mata rai fiye da
fadan,don jin ta take tamkar an raba ta da ranta, sam bata nisa da wayarta. misalin shabiyu
saura alhaji ya shigo,tuntuni yake ta neman layin 'yar lelanshi,amma sai tayi ta ruri har ta yanke
ba a daga ba. hajiya ta shiga ta same shi tana cikin shirin barci,ya kalle ta da wayansa a
hannu,MIMI fa?ta kalle shi,in kira maka ita ne?ya lura cikin gatse ta yi masa maganar,don haka
sai ya ce,aa dama in ji ko ta yi barci ne,saboda ina ta kiran wayarta bata dauka ba.cikin jin
haushi hajiya ta ce oho..
[01/10 12:46 pm] Abdul: STEP (13)Na zata ita ma nan zamu kwana tare don kar wani abu ya
cinye ta. ya mike tare da kama hannunta,sauda kin canza sani na ba haka kike ba.yanzu kin
zama mai saurin fushi.ta kalli fuskarsa,kai da 'yarka kuka canza ni.ya ja hannunta,to zo mu
zauna in ji mai zan samu.ya basar da wancan zancen.ita ma sai ta biye masa da cewa,duk
abinda kake so.ya tallabe fuskarta kin san mene ne sauda?ta girgiza kai kullum na kalli
fuskarki.rana mai tarihi a guri na.hajiya sauda ta ce, ikon allah ni kan da a ce kalmar karatu
ce,da sai in ce,tuni na haddace ta,tun muna da kananan shekaru. ya yi 'yar dariya ina jin
dadin tuna baya,wani lokacin sai in ji tamkar in mai do lokaci.ta lumshe ido, ai alhaji kuruciya
cike ta ke da shirme,in ta wuce sai ayi ta kewarta,
[01/10 12:46 pm] Abdul: STEP (14)Ni kaina ina son tuna baya,rayuwa tana da sauri,duk da
haka in muna tare,sai in rika jin kaina tamkar 'yar kasa da shekara ashirin.yayi dariya,a haka ni
ke kallon ki sauda,kullum na kan ce, lokacin na sauri.ta kwantar da kanta a kafadarsa.allah ya
kara mana tsaw rai da rayuwa mai amfani.a kunne ya rada mata amin.da ma an ce soyaya bata
tsufa, sai dai masoya su tsufa, allah ka yi mana mai kyau. karfe bakwai alhaji bashir yana ta
shiri cikin sauri,hajiya tana taimaka masa gurin saka kaya, rokonsa take yi ya dan sa wani
abinci a bakinsa,ta ce don kai nasa a yi kunun gyada da kosai,saboda na san kana so.ya kalle
ta,ta na saka masa liks a hannun riga ya ce,ki yi hakuri mata ta,ba komai,na yi alkawarin zan
gana da wani mutum ne,wanda na fi wata guda ina neman damar ganinsa. ta ce,duk da haka
ka karya zai fi.ya ce sai na dawo,domin in na samu damar da nike nema a gare shi,kasuwanci
na zai ninka,in ko haka ta samu yaya kika gani?ta ce, umm! kai dai da ma kullum saurin ka bai
wuce kasuwanci,a kasuwanci ina ne ba a sanka ba,duk fadin afirka ina ne sunanka bai kai ba!
wane irin kudi ne baka mallaka ba kullum cikin samun riba ka ke. ta mika masa
hularsa,me ya kamata ka nema kuma alhaji?yanzu baya ga aljanna? murmushi ya yi,ba tare da
yaba ta amsar duk tambayoyin da ta jero masa ba.ta ci gaba, ni dai ba zan gaji da baka
shawarar cewa,kamata yayi zuwa yanzu kayi murabus ka bar abba da mukhtar su jagoranci
kasuwancinka.ya ce,ni kuma fa ta ce,ka zo mu zauna mu huta,mu karasa rayuwarmu,'yan
kananan yaranmu su shaku da kai.ya saki dariya tare da cewa,sauda kenan.in ki ka fadi wata
magana sai ki tuna mimi tadinmu na farko da ke.ta ce au!kana nufi maganar ma dana fada
shirme ce?ya ce,kusan haka,kina cewa in bar ma su abba ragamar kasuwanci,ki na tsammanin

za su yi jarumtar kasuwanci kamar ni? bai jira amsa ba,ya ci gaba da cewa,da ma MIMI
ce babba,ko da tana mace na san za ta iya.amma su abba shirme kenan,shi yasa kika,
[01/10 12:46 pm] Abdul: STEP (15)Ga ko shawara ce na fi son yi da ita koyaushe ta na bani
shawara ta musamman yadda ake fadada kasuwanci a duniya ta cikin yanar gizo.su kuwa su
abba bakin ku daya.kullum in takaita kasuwanci a iya gida nijeriya,ni kuma na wuce nan tuni. ta
ce,ka fahimce ni ba muna cewa kar kayi kasuwanci da waje ba ne aa,ai bunkasar ka ta isa ka yi
kasuwanci da waje.harkar shigo da magunguna ne muka ce ka daina,tunda ana yawan zargin
kana shigo da haramtattun magunguna da kuma miyagun kwayoyi.ya gyara zaman hularsa,ya
sa hannu ya shafi kumatun ta, ki ci gaba da yi min addua sauda,ke ce kurum ki ke fada min son
ranki in ji ban ji haushi ba.ya cire takalminsa tana fesa masa turare ya ce,ban sani ba ko zamu
gama tattaunawa da wuri ko ba zamu gama ba, amma ko yaya ne dai daga can zan wuce
malumfashi. in duba su binta da yara sannan in kewayo gona ta, na jima ban leka ta ba.inda
lokaci zan shiga masari can ma na jima ban je ba.kin ga sai na kwana kenan,gobe zan dawo in
dauki uwata mu koma inda muka fi wayo.ta ce,allah ya tsare sai ka dawo din amma batun tafiya
da MIMI ne nake tunani a kai.ya kalle ta, kamar yaya?ta ce,sai ka dawo dai allah ya tsare,ya
dan tabe baki amin.suna fitowa falo yara suka nufo suna yi masu sannu da fitowa tare da
gaishe shi,ya amsa da daidai,ya kalli usaina,MIMI fa?ta ce tana kwance dady,ya ce,shikenan
zamu yi waya.hajiya ta raka shi har mota,ba sabon abu bane,haka ta saba tun suna da
kuruciya.falo ya kacame,yaran suna ta karin kumallo,sai hayaniyarsu da karar kofuna.MIMI ta
fito sanye ciki riga da wando masu dan kauri na barci. sauri ta ke yi,tare da fatan allah ya sa
dad dinta bai fita ba,don ba za ta taba bari ya fita ya bar ta ba.ta iso gurin hajiya,fuskar ta babu
annuri ta ce,ina kwana hajiya?ba tare da ta dube ta bata ce,lafiya lau.MIMI tayi tsaye shiru,tana
son yin magana amma tana tsoro.hajiya ta dago ta dube ta,ga kayan shayi can a kan dining,na
san ba kya shan kunu,ta ce tam!ehemm!da ma zan gaida dady ne,yana ciki ne? hajiya ta ce a'a.
[01/10 12:46 pm] Abdul: STEP (16)Ya tafi malumfashi sai gobe zai dawo.MIMI ta zaro idanu
yaya dady zai min haka ya tafi ya bar ni,ta kalli hajiya wanda ta soma watsa mata harara ta
ce,hajiya don allah ina waya ta?hajiya ta ce,sai za ku tafi zan baki,don ni ba za kiyi mani chatin
din naki ba a nan,ki karya ki je ki yi wanka,in malamin su hussai ya zo zaki bisu,ki je daukar
karatu a gurinsa.ina sa ran ma alhaji ba zai tafi da ke ba,nan zai bar ki sai kin san addininki za
ki tafi,ko da zaki cinye hutun ki a nan. cikin sauri MIMI ta koma daki cikin kuka sai da tayi me
isarta ta shiga wanka,a fili kuwa fili kuwa fadi ta ke, allah ba zan zauna ba, shi ya sa na tsani
zuwa katsinan nan.dolenta ta saka atamfa riga da siket,a cikin durowarta ta ciro don tana da
kaya a nan gida, duk lokacin da aka yi wasu usaina sai an yi mata.ta shirya tsaf ta koma kan
gado ta kwanta tana tunanin yadda za ta yi.amma ko ta halin kaka baza ta zauna cikin irin
takurar ba.can ta

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login
google.com, pub-9213700357025247, DIRECT, f08c47fec0942fa0