Showing 12001 words to 15000 words out of 30377 words

Chapter 5 - CANJIN RAYUWA BOOK 1 HAUSAWA NOVELS BY HALIMA ABDULLAHI K MASHI

nisa,suna juyawa da niyyar tafiya. sai ga ta dauke da tire
goro,ta tsaya cikin daburcewa irin ta marasa gaskiya.sam ba ta tsammaci zuwan su ba.don bai
cika zuwa da yamma ba.ran mahamud ya yi matukar baci.duk da irin yarjejeniyar da muka yi?da
ma karya ne lafiyarki lau,ki ka dain zuwa lslamiyya? zainab cikin in-ina ta ce,dama gidan wata
tsohuwa kadai na kai, amma bana zuwa talla.ya ce,karya kike yi,in mutum daya zaki kaima
wa,ya ya baki sa a leda ba?sai ki dora tire a kai,bayan kuma na fada miki babu abinda nafi
tsana irin in ganki da wannan tiren a kai. kuma na fada na sake fada,bana son talla.kun
dora min dari uku kullum, na yarda,kuma ina baku,shine zaki munafunce ni?ta sassauta murya
ta ce,ka yi hakuri,ya ce,ke malama ba wani hakuri jeki yi min sallama da innarki,don bazan tafi
in bar baya da kura ba.ta nufi ciki tsaki mahamud yayi,ya ce kalli irin gidan daza ka nemi aure. a
ce uwar daza tayi wa yayanka tarbiya?wai kyan take birge ka ko me? lsmail ya ce,don ALLAH
mahamud ka bar ni in ji da abu daya.kalli wulakancin, sama da wata takwas duk sati biyu sai
naba su dubu biyu da dari daya ko dari uku.ko da ba zan ci ba, ba zan sha ba,sai na basu kudin
nan.don kawai ta daina talla,ashe suna nan suna yaudara ta ne. mahamud ya be duk
kai ka so,yaran mata gasu nan a fadin garin katsina masu tarbiyya da ilimi,ka kau da kai a gurin
su,na san dai ka san cewa,in ba nema wa 'ya'ya uwa ta gari.lsmail ya ce,baza ka gane ba,ina
yiwa yarinyar wani mugun so ne,ba zan iya rabuwa da ita ba.mahamud ya daga kafadunsa
guda biyu tare da fadin ruwan ka.
[01/10 12:46 pm] Abdul: STEP (32)Daidai lokacin zainab ta sake fitowa ta ce, shigo daga
soro,nan suka tsugunguna.lta ma innar ta tsuguna.suka gaishe ta,lsmail ya soma magana cikin
fushi,inna nazo ne nayi wa zainab sallam zan tafi abuja.sai kuma na ganta da tiren goro,bayan
na san mun jima da wuce maganar talla.eh.nina ce ta zaga da goro tunda tun shekaranjiya ya
kamata ka aiko da kudin amma shiru. lsmail ya sake shakar takaici,ciki sauri ya ce,amma inna
ko na sati biyu na tara ina badawa ko? ya ci gaba gaskiya bai kamata a saba mun kaida ba.inna

in na bar gari sai yaya kenan,bai da be fa a saba mun alkawari ba. lnna ta dago ta dube
shi, aikin gwamnati ka samu a can abujan?ya dube ta,ya sunkuyar da kai ya ce,aa koyarwa
ce.ta ja tsaki ta ce,ana nan dai.ta mike ya ce,inna zan bata kudin ta kawo,ni dai roko na kada ta
dinga daukar tallar nan. ina hijaban dana dinka mata ne,yau na ganta da gyale?ta daga masa
hannu,dakata kai lsmail,ba fa ka bada sadakin zainab bane daza kayi ta sa mani dokoki iri-iri a
kan 'yata,kuma bazan gaji da fada maka cewa ba zan bayar da 'yata inda zata sha wuya
ba,kamar yadda ni na sha wahalar talaucin ubansu.'yata tana da kyau, baza maida ta baya ba.
lsmail ya mike shi dama mahamud tuni ya kai waje. ranshi ful takaici,zuciyarsa tana tafasa.
zainab dake cikin gida kusa da soro ta leko cikin damuwa ta ce,innarmu don ALLAH ki daina
wannan zancen,wai ke kullum in zaki yi magana sai kin sako babanmu?lsmail yasa hannu cikin
aljihu,zainab zo in baki sako,innar ta koma cikin gida.zainab ta kalle shi,malama don allah kayi
hakuri,ya ce,zainab ni dai rokon da zan miki,don ALLAH ki rike min amana. ya sake yin kasa
da murya,kin dai san ina sonki ko?ta kalle shi da manyan idanunta na sani malam.to ki kula min
da kanki,yasa hannu cikin aljihu ya ciro dubu uku,ki cire kudin sati, sai ki rike saura.in na dawo
zan saya miki waya saboda mu rinka gaisawa, zan turo iyayena.ta ce,to nima zan fi son ka turo
din,don allah kayi kokari ka dan yi kudi ko.
[01/10 12:46 pm] Abdul: STEP (33)Da ba masu yawa bane,saboda innarmu ta daina yi maka
haka. ya ce,kar ki damu shi arziki na allah ne yana bayar da shi ga wanda ya so kuma a
lokacin da ya so.muna rokon shi ya bamu na halas,ta ce amin.yawwa a gidanku wace ce
fatu?ya ce,me ya faru?ya tattara hankalinsa gurinta,sun hadu ne a gidan wani biki can kofar
marusa,shine take cewa innarmu wai kar ta yadda ka aure ni,wai wuya zan sha baka da
komai,sai dan daki daya daka gada a zaure.baka da aiki,sai kalallahu,kala rasulu.lsmail ya
lunshe ido na dan lokaci, ya bude tare da furzar da huci mai zafi.ya ce,zainab don ALLAH ki
toshe kunnuwanki,wadannan abubuwan duk kafin in mallake ki ne.da zarar kin zama mata
ta,dole kowa ya zura mana ido.ta ce to shikenan amma wace ce fatu din?ya ce,matar wa na
ce,kar ya dame ki,ni zan tafi ta ce to shikenan. sai yaushe?ya ce,sai dai na zo, don sai naje
naga yanayin gurin,har ya kai bakin kofa ta ce,malam don allah kar ka manta ka samo kudin.
bai iya cewa komai ba.ta shiga cikin gida shi kuma ya je ya samu mahamud suka
wuce.mahamud ya kasa yin shiru,suna tafe ya ce, lsmail don ALLAH dubi irin wulakancin,don
ALLAH ka yi zuciya ka bar mata yarinyar ta.lsmail ya ce,hmm ka san na sha yunkurin yin
haka,amma sai in samu kaina cikin tashin hankali,ban san lokacin da na soma son ta ba.ka yi
hakuri mahamud ban ki batunka ba,abin ya wuce duk yanda kake tunani.kai dai ka gode ma
ALLAH tun da baka da matsala da iyayen rabia. mahamud ya ce,ko da ina da matsala da su
bazan dauki haka ba,sai in bar su da yarsu.kaima ina mamakin duk zuciyar da kake da ita,ya
dafa mahamud kar kaji komai,ka sa ni cikin adduarka. mahamud ya ce,ka binciki
asalinsu?lsmail ya ce,yaya amina ce ta binciko,ranar take gayamin wai ubansu bakano ne.dan
wani kauye wai shi kurje keya.ita kuma uwar 'yar ruma ce,can wajen safana.ya auro ta lokacin
yana da abin hannunsa.'ya'yansu shida maza uku mata uku,maza ne manya mata kuwa zainb
ce babba,tunda arzikinsa ya karye sai buga-buga sai ta raina shi.
[01/10 12:46 pm] Abdul: STEP (34)Sai ta raina shi, 'ya'yan ma suka raina shi,sai abinda ta ce.ta
dauki dogon buri ta dora a zainab,don kuwa ta ga yarinyar tana da kyau,ita sam ba za ta ba
talaka ba. sannan yaran babu tarbiya babu karatu sai talla.maza kuwa daga kwandasto sai
kwasan bola,sai karamin su mai sayar da rake.ka ji bayanin da yaya amina ta yi min. mahamud

ya ce,tabdijan kuma ka ji ka gani?lsmail ya ce,to yaya zan yi?ba ni da zabin da ya wuce
aurenta.buri na shine in ta zama tawa zan tsaya mata ta yi karatu duka biyu.mahamud ya
ce,ALLAH ya taimake ka. bayan sallar lsha suka yi sallama da mahamud kan cewa sai gobe
in sun hadu, kafin lsmail din ya tafi gida, gidan yaya amina ya nufa, a tsakar gida ya same su ita
da yara suna cin abinci. nan yaran suka shiga yi masa sannu da zuwa.ya ciro naira dari ya ba
sadam babban,je ka sayo maku biskit,ya ruga da gudu yana murna,yaya amina ta ce,ba ka
gajiya ne?haba dai.ta ce aisha dauko ma kawunku tabarma.bayan sun gaisa sai yake sanar da
ita batun tafiyarsa abuja.ta ce, gaskiya na yi murna.ALLAH ya sa alheri ne ya kira ka
abujan.lsmail ya ce,amin yaya ina son in na dawo in tura gidan su zainab.yaya ta ce,umm!kai
dai kana son wannan zainb din yayi dan murmushi,ku taya ni da addua ALLAH ya sa haka
shine mafi alhari.ta ce.umm to amin,sun jima suna hira sannan suka yi bankwana ya tafi.yana
shiga gida ya kunna wayarsa ya shiga soro su ya ciro makulli dakin ya bude.ya dubi makunnin
wutar ya kunna haske ya wadace dakin ya shiga.ya dauki buta ya fita zuwa cikin gida don
zagawa ban daki.a tsakiyar gidan matan yayyin sa ne da 'ya'yansu suke ta hira,ya yi sallama
suka amsa yayi masu sannunku ya wuce.don shi dama tsakaninsu bai wuce haka ba,sai da ya
fito bandakin sannan ya nufi dakin inna,ya yi sallama tana ta gyangyadi.sallamar shi ce ta tashe
ta,ya shiga ya gaida ta,ta amsa tare da cewa kananan?ya ce eh na shigo da safe ki na bandaki.
ta ce,haka dai ka ce,indai nina haife ka ai don ina bandaki ka jira ni.yayi dan murmushi,
[01/10 12:46 pm] Abdul: STEP (35)Zuwa yanzun ya saba da halin inna.ya daina jin haushin
maganganun da take fada masa marasa dadi.dama zan sanar da ke ne gobe in ALLAH ya
kaimu zan tafi abuja.ta ce habuja?kai ko me zaka yi a habuja?ya ce,koyarwa na samu a wani
gida zan dinga koyar da yaran gidan ta tashi tsaye,can kuma ka kutsa,lallai ba shakka,ya
mike,ya jima da sanin inna zai yi wuya tayi masa adduar ALLAH ya sa alheri. ya fito yasa
takalmi tare da daukar butarsa.tun kafin ya bar tsakar gida yana jinta tana cewa kunji mutan
gidan nan,samail ya samu koyarwa a habuja,ya fadawa mazajenku?fatu ce ta soma
magana,lallai ba shakka,ya fadawa mazajenmu su a su wa?ke ma don kar a ce dai bai fada
bane,kala bai ce ba ya wuce dakinsa. Da safe sai da ya shirya tsaf,sannan yayi wa
yayyansa maza sallama,su kam sun yi masa ALLAH ya sa a dace.gidan su mahamud ya
nufa.yayi sallama da malam aminu mahaifin mahamud sannan suka nufi gidan hajiya
sauda.mahamud ya goya shi a mashin,kuma sun yi shawara a kan mahamud zai ci gaba da
koyar da su hussaina. A waya ya kira hajiya ya fadi mata ya iso,ta sa ya
shigo,kar ya damu ai shima tamkar shi dan gida ne.suka shigo falon baki nan ta same su,ya
gabatar mata da mahamud,bayan sun gaisa ta kuma kara rokonsa a kan ya tsaya mata sosai a
kan MIMI,duk lokacin data yi yunkuri ko barazanar koran shi,to ya kira ta.ta ce nasan aiki ne na
baka mai wahala,amma kamar jihadi ne,ya ce,na yi miki alkawarin zan tsaya a kanta kamar
kanwa ta,zan jure saboda ALLAH da kuma halaccin da ki kai mun.ya'u direba ne zai kai shi,sai
da motar ta tashi sannan mahamud ya buga mashin cikin kewa.suna tafe suna labari shi da ya'u
cewa yayi,gaskiya ina yi maka jajena kan wannan aiki,gara in yi aikin kwasar kashi don na tsani
wulakanci,lsmail ya ce,hmm ni fa gani nake kamar wata kaddar tasa zan je koyar da yarinyar
nan. wata zuciya kuma tana fada mini ALLAH zai taimake ka.ina tunawa ni NAMIJI
ne,sai inga to wai meye ne abin tsoro.
[01/10 12:46 pm] Abdul: STEP (36)Ya'u ya ce,ba za ka gane ba,ai ubanta zata sa ya tozarta
ka.ga zagin wulakanci,lsmail ya ce, ALLAH ta zage ni sai na mare ta.ya'u don dariya sai da

motar tayi kamar zata sullube masa.ya ce gaskiya kar kayi wannan kuskuren, lsmail ya
ce,nanne kaduna? ya'u ya ce,eh amma ba garin kaduna ba ce zariya ce,nan dama baka taba
zuwa ba?kai ni ina zaton sokoto kawai muka taba zuwa yin gasar karatu lokacin ina SS1.ya'u ya
ce gaskiya ni ban zata ba,in na kalle ka sai ka ce ka taba fita kasashen duniya. lsmail ya ce,ni
kifin rijiya ne ban san ko in ba.in mun zo kaduna ka nuna min ina jin labarin garin ina son zuwa.
ya'u ya ce,shike nan za nuna maka,tun daga na yake nuna masa garuruwa har suka isa
kaduna.ya ce, bari in bi da kai ta cikin garin maimakon by pass tunda kana son ganin garin.
shikenan lsmail sai kalle-kalle ya ke yi.ya ce,garin ya birge ni.amma duk a zato na ya fi
haka,yadda sunan kaduna ya cika ko ina.ya'u ya ce,zaman garin yana da dadi saboda ba su
shiga harkan abinda bai shafe su ba.lsmail ya ce,wani ya taba bani labarin garin 'yan karya ne
ko?ya'u ya ce eh, to ni ma dai haka na ji ana cewa,to muna da 'yan'uwa. suna zuwa katsina
gurin innarmu,mu ma mukan zo,ba wasu masu karfi ba ne,amma komai za su yi sai inga suna
son yin wanda yafi karfinsu,ni ma sai na amince 'yan karya ne.amma daga baya lokacin ina yin
tuki a nan kaduna a wata unguwa wai ita unguwa rimi sai na gane ba wai karyace da su ba,yin
hakan a jinin 'yan kaduna ne yake.ka gane malam lsmail? su mutane ne masu
son yin komai me kyau,kuma basu da kyashin sayan duk abinda ransu ke so,ko da kudinsu
kenan idan za a aje maka dan kaduna mai dubu dari biyar,da dan wani gari mai milyan biyar,za
ka ce dan kadunan ne mai milyan biyar,wancan mai dubu dari biyar.lsmail ya ce na gane,in ko
haka ne sun burgeni.saboda ni mai irin raayi na kenan,arziki na ALLAH ne,in na samu zanyi
abinda nake so da halas di na.haka suka yi ta labarin 'yan kaduna har suka kai abuja garin
manya.
[01/10 12:47 pm] Abdul: STEP (37)Shi kam a ranshi 'yan kaduna sun yi mashi, yana son
mutane masu test,wadanda ba komai ne ya yi masu ba. Tafkeken gida ne na gani
na fada,tunda suka doshi gidan lsmail ke mamaki sai ka ce fadar shugaban kasa,duk yadda
yake kisima gidan a rashi ya wuce nan,tun kafin su shiga ma kenan.su na shiga sai ya ga ma
kamar wata sabuwar duniya ce,wannan mutumin wane irin kudi ya mallaka?lsmail ke tambayar
kanshi. dama tun kafin su kara so ya kira hajiya ya fada mata cewa sun iso unguwar,ita kuma
ta kira momi nafisa ta sanar da ita.lsmail ya na jingine jikin mota,wani matashi ya iso wurinsa ya
ce,wai wanene malam lsmail?ya ce,ni ne. ya ce,to zo mu je,ya kalli ya'u direba zo muje, ya
ce,a'a,ni dama aiki na shine na kawo ka,kuma na kawo ka,yanzu zan juya.lsmail ya bashi hannu
suka yi sallama bayan gidan suka nufa inda suka nufa gefen yara, suka je ya bude wani
daki, an ce ka shiga nan.lsmail ya kalle shi,ba mu gaisa ba?ya mika masa hannu suka gaisa.ya
ce,suna na lsmail,kai fa?ya ce hamisu, kuma nine direban yaran gidan nan.ga daki na nan kusa
da na ka,mu biyu ne a cikin dakin,ni da me share-share,game da kula da fulawoyi.lsmail ya ce,
ALLAH ya sa mu amfani juna,hamisu ya ce,amin. lsmail ya shiga yana kallon dakin
tamkar ba dakin masu aiki ba,hamisu ya ce,ai kurar dakin ba ta yi yawa ba,don kanin momi bai
yi sati da tafiya ba,da cikin dakin yake.lsmail ya ce,kurar ba tada yawa ma kenan,amma duk da
haka bari in dan kakkabe,ya shiga ciki sosai,hamisu ya ce,in zaka yi sallah ga bandaki
nan.lsmail ya ce,tunda muka taso,duk inda sallah ta same mu,sai mu tsaya muyi ta.ya ce,
shikenan baka da wani nauyi a kan ka.lsmail ya gyara daki mai dauke da katifa katuwa,sai
duruwar ajiye kaya,sai kuma dan teburi a gefan katifar. hamisu ya ce,bari in sa a sanar da momi
cewa ka iso,kuma naba ka masauki, yanzu saura abinci. kusan minti ta latin da fitar
hamisu,sai ga wani kuma dauke da plate a rufe da cokali da kuma ruwa.suka gaisa,

[01/10 12:47 pm] Abdul: STEP (37)Kusan minti ta latin da fatar hamisu,sai ga wani kuma dauke
da plate a rufe da cokali da kuma ruwa.suka gaisa,sannan ya ce,ga abincin ka.shi ma nan haka
lsmail din ya sake gabatar masa da kansa, suna na lsmail kai fa?ya ce, suna na jabiru,kuma
nine mai dafa abincin rana da dare,lsmail ya bashi hannu suka gaisa.bayan fitan sa ne ya bude
plate din abincin, dafa dukan shinkafa ne,ta ji kifi da alayyahu,ya ci ya koshi,ya sha ruwa ya
koshi.daga nan barci ya sace shi, saboda gajiya bai taba yin doguwar tafiya kamar haka ba
daga katsina zuwa abuja. can da ya farka ya kalli agogo,sai ya ga lokacin sallah
ya karato,nan da nan ya tashi yayi alwala,ya fito waje bakin gate don ya ga karamin masallaci a
gurin. hamisu yana zaune kusa da maigadi suna hira,yayi masu sallama,suka amsa. ya
ce,hamisu ina ladani ya kira mana sallah lokaci yayi, hamisu ya ce,ba a fa kiran sallah a
masallacin nan,sai dai kawai kowa yayi alwalarsa ya shiga yayi sallah.lsmail ya ce,saboda
me?hamisu ya ce,ni dai haka na tarar suna yi,to ai duka-duka mu uku ne ke yin sallar,ni da
maigadi da mai shara.ko maigidan ba kullun yake sallah a cikin masallacin ba,ya fi yi a cikin
gida.yaron sa namiji daya. ya kai shekara shabiyu, amma ko shi ba a turo shi. lsmail ya ce,ko
ku uku za ku iya

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login
google.com, pub-9213700357025247, DIRECT, f08c47fec0942fa0