Showing 15001 words to 18000 words out of 30377 words

Chapter 6 - CANJIN RAYUWA BOOK 1 HAUSAWA NOVELS BY HALIMA ABDULLAHI K MASHI

jam'i,don haka ni kam zan kira sallah. lsmail ya shiga ya ga da abin
magana da komai,yana kwada kiran sallah daidai lokacin motar alhaji bashir tana kunno kai
ko da direban ya tsaya bai fito ba,sai da ya ji karshen kiran sallah,muryar tamkar balaraben
saudiyya. maimakon ya shiga gida sai ya samu kansa da nufar masallaci,gurin da aka tanada
don alwalla,nan ya je ya tattara hannu rigarsa ya soma alwalla.su hamisu suka tsaya suna
kallonsa, nan dai lsmail yaja su sallah,hamisu yayi masu ladanci,sai dai alhaji shi kadai ya tsaya
a sahunsa. suna idarwa suka fito, lsmail ya gaida alhaji,ya nuna masa jin dadinsa da sallar
da ya kira har suka yi jam'i.lsmail ya ce.
[01/10 12:47 pm] Abdul: STEP (38)Ismail ya ce,alhaji zan yi wata magana,amma in na bata
maka rai ka yi hakuri,amma hakki ne a kaina in sanar da kai.bai kamata ka tsaya ba a sahu
ba,duk da cewa mu din masu nema a karkashin ka ne,amma gurin allah ba bu
bambamci,musamman gurin sallah.sahu dole ne,na san alhaji ya sani.tuni kawai na yi
masa,alhaji ya ce.na gode ba komai,sannan ya nufi cikin gida. sai karfe tara na
dare, kuku ya sake kawo masu abinci,da ya karba sai ya fito,ya samu hamisu shi ma yana cin
nasa,ya aje ya ce, me zai hana mu rinka ci tare?hamisu ya ce,ba damuwa bisimillah.suna ci
hamisu ya ce,na ji mamaki da na ga kana magana da maigidan nan,wai me ka ce masa
ne?lsmail ya ce,wata magana wanda bai dace in fito na fada ba,a takaice kuskure ne nayi masa
tuni, hamisu ya ce tabdi,gaskiya ka yi saa,ai maigidan na mu mafadaci ne na gaske. wanda bai
son a shiga huruminsa,kuma yana da wata yarinya mara mutunci,wanda kowa ke tsoron
ta,hatta matan gida. sai dai gaskiya yana biyan kudi da tsoka,shi ya saka ga na jure,ni ne
direban yaran gidan,don haka na fi kowa wulakanta. lsmail ya ce,na san ta,kuma ni malaminta
ne,na zo in koya mata karatun addini. hamisu ya dago ya kalle shi,yayi dan murmushi, lallai ina
mai baka shawara,ka nemo duk wani hakuri da kau da kai,ka kara a kan wanda kake da
shi.lsmail ya yi 'yar dariya,ya ce,ta taba yi maka?ya ce,to da wanda ta raina ma iri na? ban
san iya sau nawa ta zuba min miyau a fuska ba.banda kalaman cin mutunci.lsmail ya ce,kai
kuma sai ka tsaya kana kallonta?hamisu ya ce,ya ya zan yi,tunda ina so,dubu talatin yake biya
na a wata,ba ko'ina zan samu haka ba.lsmail ya ce,sannu da kokari,amma ni kam ba zan dauki
wulakancin nan ba.sun jima yana ba shi labara,kafin suka yi sallama. haka da asubahi ya
kwada kiran sallar farko, MIMI wacce lokacin ta yi sallama da kalil dinta wanda suke chatin tun

misalin taran dare,ta bude idanunta tana jin sabon lamari a gidansu.ta tashi ta sauko daga kan
gado,ta kunna wutar dakin na ta,
[01/10 12:47 pm] Abdul: STEP (39)Sannan ta nufi windo,ta yaye labule tana kallon
masallacin,wanda dama saitin windon nata yake.tabbas masallacin nan ne,to wane ne wannan
da karfi hali?lta tunda ta ta so bata taba jin an kira sallah a masallacin nan ba.ta koma ta kwanta
ta saki tsaki.za ta ga mai wannan kokarin na hana mutane barci.ta fara barci ta ji an sake kiran
sallar,aka shiga masallaci aka yi sallah,ba ita ta samu barci ba sai da aka idar da sallah.
don haka bata farka ba sai shabiyu,ta yi mika tare da hamma,ta silalo kafarta kasa kan lallausar
kafet. tamkar sarauniya ta ke jan taku har zuwa bandakinta, wanda aka tsara shi da kalar
pink,kalar da take bala'in so,bandakin da yafi na kowa tsaruwa a gidan, hatta mahaifinta.ta
shiga bahonta,bayan ta cika shi da ruwan dumi,sama da awa daya ta dauka a wanka,ta
fito.gurin shafarta daya ne da kayan sawanta, bata cika yin kyale-kyale a fuska ba, hoda kadai
sai jambaki bayan mai,amma tsadarsu ta ishi talaka jari. ta saka wando baki irin mai
kama jikin nan,da riga ja,ta ja dogon gashinta ta kama shi da bakin ribbon. ta soma wanka da
turaruka.ta nufi gadonta ta dauki wayarta tana dubawa,miss call kusan goma dadin ta,da na
dear khalil,dana hajiya guda biyu. bakin gadonta zaune tana kiran layin dadinta,ya daga tare
da cewa uwata ya ya aka yi?cikin shagwaba da muryarta din nan wanda ke fid da sauti a
hankali cikin salo ta ce, dad na ga miss call din ka ne fa?ya ce,uwata har na fita baki tashi
ba,lafiyarki kalau ko?ta ce,eh dad,emm yawwa dad wane ne jiya cikin dare ya hana ni barci da
kiran sallah?ya ce, malaminki ne,gabanta ya yi bala'in faduwa ta ce,dad shine da zuwansa zai
canza mana tsarin gidanmu?mene ne nufinsa da haka?ya ce,babu komai MIMI,kin san malamai
da son masallaci,yau ni mana samu yin sallar asuba a kan lokaci,sannan makwabtanmu sun
shigo mun yi sallar tare da su.ta ce kash dad,yanzu gidanmu gurin tara mutane kenan? ya
ce,kar ki damu musuluncin kenan,ina fata za ki sauko domin daukar karatu.
[01/10 12:47 pm] Abdul: STEP (40)Gurin malamin na ki.kuyi amfani da falon baki, ko falo na ki
ke so?ta ce,aa dad ya tsaya can falon baki,ba falon ka ba,da wannan bakauyiyar kafar tashi.ya
ce,shikenan tunda naima tana gida ita mata soma karatun,in su ahmad sun dawo da yamma sai
yayi masu,ta ce,shikenan dad,bari in kira hajiya naga ta kirani.ya ce,ok nima yanzu muka gama
waya,ki ce ina gaida ta.cikin fargaba ta kira mahaifiyarta,hajiya ta daga cikin lallausar murya ta
yi sallama,MIMI ta amsa tare da cewa,ina ki ka bar waya?ta ce,ina barci yanzu nayi wanka sai
naga miss cal dinki.hajiya ta ce,na zaci kin fita gurin karatu ne?ta ce,hajiya ban san ma ya zo ba
sai yanzu dad ke fada. ln na yi break zan yi yanzu,hajiya ta ce,ki maida hankali saboda ki
san abinda zaki bauta ma ALLAH mahaliccin ki.suna yin sallama kiran kalil ya shigo sai da yayi
daf da tsinkewa ta daga,wannan wani raayinta ne.ta ce, hello dear ya aka yi?ya ce,ba komai ina
son in ji muryar ki ne?yanzu ki ka tashi?ta ce, fh,yaya hutu?ya ce,ga shi muna yi,don ALLAH ina
son in zo gidanku wannan karon,ina jin tsoro kamar zan rasa ki,kar ka damu dear na fada maka
don juna aka yi mu,ina jin haka a jiki na. ya ce, lovely har yanzu ban yi mafarkin haka ba ina
ganin sai zancen ya je gurin manyanmu.ta yi 'yar dariya, ka san fa dad naka ba zai yarda ka yi
aure yanzu ba, ni kuma in dad dina ya ganka guri na kila ya ce,zai min aure,ka ga sai matsala
ta samu. ya ce,na fahimce ki,ba na son na sha wahala a aurenki kamar yadda
na sha kafin na samu amincewar soyayarki na garu.ta yi 'yar dariya cikin salon maganarta ta
ce,dear ka manta da haka,bari na karya,ya ce,to shikenan sai in mun hadu online ta
ce,tam.cikin tafiyarta tamkar mai tausayin kasa take saukowa daga benenta,wanda ita kadai ce

a sama ta ke mallakin kato falo da dakuna uku.daya dakin barcinta daya kayan karatun ta,tun
daga computer zuwa kasa, dayan kuwa rufe yake duk da cewa shima da komai a cikinsa.
[01/10 12:47 pm] Abdul: STEP (41)Momi nafisa tana zaune tana kallon fim a cikin tafkeken tv
dake manne a bangon falon.ta waiwayo,kin fito MIMI?ta kalle ta,na fito momi an tashi lafiya?ta
ce,lafiya lau, dadinku yayi ta kiran ki baki fitoba,ta yatsi na fuska,mai kiran sallar cikin dare nan
ne ya hana ni barci.momi ta ce,ai malaminki ne,na ga dad dinki ya yaba da hakan.ta ce,na lura
da haka a wayar da muka yi dazun. ta isa gurin karin ta hada shayi tana sha,ta dubi mahaifiyar
tasu naima fa?ta ce,tana dakinta,ta dauki wayarta dake kusa da ita,ta soma kiran layin
na'ima,tana dagawa MIMI ta ce,sis zo mana,naima ta fito cikin riga mai gajeran hannu da
wandon jins damamme,kanta ita ma babu dankwali,ta kama gashinta da ribbo blue. ta
ce,sis gani,MIMI ta daga fararen idanuwanta ta kalli na'ima cikin harshen turanci suka fi yin
magana.ta ce,ki je gurin folina a kicin ki gani ko ta gasa kifin,ta ce,sis mu je snacks store mana
mu ci, MIMI ta harare ta,ki yi abinda nasa ki mana,ta daga hannu,alamun ban hakuri ta rinka
fadin sorry. folina ta zo,ta shirya wa MIMI gasashen kifi tare da gasashen biredi,tana gamawa
ta kalli naima ina son a kira mini malamin da yazo jiya,amma ban san yaya zan yi ba,don ba za
kije ba,amma ki duba in kin ga direban ku,ko wani dai ya kira shi,ta ce tam sis. lokacin da
hamisu ya sanar da lsmail cewa ya je ciki ana neman sa,sai ya ce,sai mun yi sallah tukuna. don
yanzu zan kira.bayan sun idar sannan ya ce,ma hamisu ya yi masa jagora zuwa cikin gidan.
barandar kofar falon,nan suka danna 'yar wata danja,jim kadan aka bude. naima ce ta kalle su
irin kallon da wasu 'ya'yan masu da shi suke yi wa masu yi masu hidima.ta ce, wane ne
malamin?hamisu ya nuna lsmail wanda ke tsaye sanye cikin yadi mara nauyi,hularsa ta dace da
yadin wandonsa a dage irin na ahalil sunna. ta kalle shi sama da kasa, ta ce,ina
zuwa.kamar minti biyu ta dawo ta ce,sis ta ce,ka shigo,ya shiga dankareren falo wanda tsarin
saya wuce duk tananin lsmail ga sanyi AC
[01/10 12:47 pm] Abdul: STEP (42)AC ko ta ina.ta waiwayo ta ganshi tsaye, ka bi ni mana,ya ci
gaba da binta cikin zuciyar shi yana addu'ar ALLAH ya tsare shi daga sharrin da ke cikin
gidan,alherin dake ciki ALLAH ya sada shi da shi. wata kofa suka shigo inda suka iske wani
falon madaidaici,shima ya tsaru ta ce,ka jira ta a nan. kusan minti biyar,sannan MIMI ta
shigo falon ba tare da sallama ba,rashin sallama yana kona ran lsmail,don haka bai ko kalle ta
ba.ta zauna tana kallon fuskar wayarta,ta fi minti biyar chatin ta ke yi da kalil dinta,labarin karfin
halin malamin take ba kalil.ta ce, ni da zai ci a gurin ubana, amma ni yake jira in ji da shi,kalil ya
ce,kin san talaka da girman kai.ta dago ido ta kalli lsmail wanda ya bude ALKUR'ANI yana
karantawa a zuciyarsa.ta ce,hamm mai neman taimako baya girman kai. ya dago ya kalle
ta,kafin in ce komai zan soma yi miki nasiha,da saka hijabi don suturta jikin ki. ki koyi sallama
yayin da ki ka zo gurin mutane,abu na uku,ba neman taimako na zo ba,ke nazo in taimaka ma
wa,don haka yanzu sai ki dauko littafi mu fara daga huruful ija'iyya.ta ce,ba ka isa ka ce za ka
taimake ni ba,don baka da komai,kuma ba zanyi sallamar ba,ba zan rufe jikin ba.ln baka sani
ba,barin in fada maka,na sa a kawo ka nan gidan ne saboda in tozarta ka,in nuna maka kai
kaskantacce ne.ya ce,don na miki wane laifi?ta ce,kai ne mutum na farko dana taba yin sa-in-sa
da shi.wanda ya taba kallon cikin ido na ya fada min magana,kuma ina son ka zama na
karshe,wannan shine laifin ka.lsmail ya ce, yanzu dai za ki yi karatun ko a'a?ta ce,na ce ba
zanyi ba,ya mike tare da kwashe takardunsa.ta ce,ban sallame ka ba,yayi tafiyarsa ya bar ta
zaune. MIMI ta bi shi da kallo cikin mamaki,shi wannan dame yake takama,har da baya jin

shakka ta,kamar yadda sauran jamaa suke ji?ya san wace ce ni kuwa?ya san wane ne ubana?
Ba wani ba ne uban MIMI fa ce alhaji bashir,dan asalin masari ne,karamar hukumar kafur jihar
katsina. mahaifiyarsa 'yar dabai ce,su shabiyu ta haifa,
[01/10 12:47 pm] Abdul: STEP (43)Amma yanzu saura su biyar,bakwai sun rasu,mahaifiyarsu ta
rasu lokacin ya kammala sakandire,yayyin shi. mata uku ne,sai namiji daya dake bin shi,rakiya
da basira a malumfashi suke aure, saratu kuma tana cikin kafur,malam aliyu mahaifinsu ya sake
yin aure. inda matar ta kasance mai son kanta game da son zuciyarta.wannan yasa ya bar
masari,ya soma shiga cikin garin katsina don neman abin kanshi, maimakon noma da suke taya
mahaifinsu,shi da shafi'u kaninsa. ya yi sana'o'i kala-kala, tun daga kan
kwandastan mota har zuwa dako,daga bisani ya soma bin wasu abokansa guda biyu da suka
kama shago daya su uku,da lsa mani da kabiru naalla suna harkan dabbobi. tun yana karba
yana saidawa ya cire ribarsa,har ya zo ya samu jarin kansa. sannu a hankali suka yi zangonsu
na dabbobi, lokaci bayan lokaci yana zuwa masari ziyartar danginsa da mahaifinsa kuma yana
yi masu alheri. kaninsa shafiu har yayi aure matarsa ta haihu,don haka mahaifinsa da
yayyansa kullun burinsu yayi aure.wani zuwa da yayi har mahaifinsa yana cewa,ga 'ya'yan
'yan'uwansa ya zo ya auri daya daga cikinsu,sai bishir din ya ce,yayi hakuri,shi ba ya shaawar
auren zumunta,amma duk lokacin da ya ga wanda ta yi masa,to zai yi aure,amma a yanzu
neman kudinsa ya sa a gaba. ranar wata jumaa lsa mani ya tare shi yana sauri za shi
masallaci ya ce masa,bashir ga wadansu shanu can zaa saida su a rugar fulani nan
mashi.bashir ya ce,har mashi?gaskiya da kyar zan je,lsa mani ya ce,za ka samu alheri mutumi
na,don jiya na dawo tafiya,ka sani da na saye su,amma ka daure mu je in ka dawo
masallaci.hardon gar ne ke son zuwa aikin hajji,shine zai cikon kudi.bashir ya ce,ni dai
masallaci na nufa ga shi ina jinjina zuwa mashin nan,lsa ya ce,mu je dai masallacin nan tare ma
kawai,da zanje na karfe biyu ne,in ya so daga can sai mu wuce.a masallaci suka hadu da kabiru
na'allah,inda suka nufi mashi dukkan su.
[01/10 12:47 pm] Abdul: STEP (44)Sun je rugar fulani,inda suka shiga garke shanu don duba
shanu.ya nuna masu,aka shiga ciniki, an daidaita kuma bashir yayi alwashin kawo kudi
gobe,saboda kudi suna banki.suna cikin sallama ne idon bashir suka kai kan wasu 'yan kwailoli
guda biyu,sun dawo daga tallar nono,dayar ya kure da ido, 'yar similmila ta yi masa kyau,sai da
ta bace ma idanunsa,ya bar kallonta.har lsa mani ya gane,bayan sun bar gurin ya ce,bashir
kana ta kallon 'yar mutane saboda me?kar dai ka ce min son wata kake yi daga cikinsu?bashir
ya ce laifi ne yin hakan?lsa ya ce,aa ban ce ba,sai dai ka bani dariya kawai,duk 'yan matan da
ke cikin garin katsina? ka rasa wanda za ka zaba sai wadanan 'yan ruga mitsi-mitsi da
su?kabiru na'allah ya ce,in dai fulanin nan nema,ba su son baiwa bare 'ya'yaansu.bashir ya
ce,ku yi min addua in rabo na ce za su bani,don gaskiya na ga wacce nake so.suka sa mishi
dariya. Abin ya wuce da tunanin bashir,domin ranar da tunanin 'yar fulani ya kwana,ya
kosa ya je su kai kudin shanu,don haka tun tara ya shirya ya nufi banki ya ciro kudi,daga nan
suka nufi mashi. ko da suka isa burinsa ya ga yarinyar da ta hana rayuwarsa sakat, har suka
bayar da kudin shanun suna kokarin zuba su a mota,amma bai ga giccin wani da ba.ya kama
mota zai hau sai ya hango ta tana kada nono cikin dan kuttunsu da suke cire mai,da sauri ya
fasa shiga motar ya nufi gurinta. sallama yayi mata ta dago a firgice ta ji abin kamar daga
sama,ganin mutum sai ta amsa cikin dariya. ya ce,'yan mata ya ya sunanki? ta kalle shi ta
ce, suna na?ta kau da kai,ta ci gaba da abinda ta keyi.lsa ya kwada masa kira daga nesa,bashir

ka zo mu tafi mana,bashir gani ya ke idan fa ya tafi ya bar damarsa,ya ma rasa ta kenan,shi
damuwa.don haka da ya ga abinda zai dame shi,nan da nan zai yi maganin abin,in har zai iya,
musamman in na kudi ne, tunda yanzu ba laifi yana samu. sake komawa yayi ya sa aka yi masa
sallama da ardo,wanda ya tafi don ya adana kudinsa.kabir yazo gurinsa, [01/10 12:47 pm] Abdul: STEP (45)Zo mu je in ya so mu sake dawo wa,bashir ya ce,ba a haka
da ni,ka san ni in ina son abu,zan yi duk abinda zan iya in kuna sauri kuyi gaba zan zo.kabiru ya
gane fusata ta sa bashir fadin haka,sai yayi dariya,ya yafito lsa mani da hannu, suka zosu ukun
suna jiran fitowar ardo. ya ce,da muna daki daya da ku,duk ku kayi aure ku ka
barni,dole ku yi min dariya.duk yadda suka dauki lamarin da zafi gurin ardo,maana ba sauki sai
suka ga akasin haka.ardo yana da ilimin addini,ya fahimce su,kuma yayi masu bayanin cewa
lallai sun yi dace,domin har an bayar da ita,sai wanda aka baiwa din ALLAH yayi masa rasuwa
wata biyu kenan. ya kara da cewa,in yana son ta ta amince ya

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login
google.com, pub-9213700357025247, DIRECT, f08c47fec0942fa0