Showing 6001 words to 9000 words out of 25770 words
Chapter 3 - CANJIN RAYUWA BOOK 2 COMPLETE BY HALIMA ABDULLAH MASHI
in koya maki yadda zakiyi.
ta CE, to, amma ka bari zan kiraka.
Khalil, ta kira, ta fada masa ko mai.."
[01/10 9:45 pm] Abdul: ki fada wa Allah da muwarki.
in sha Allahu Allah zai yaye maki halin da kike ciki.
sanan ki yawaita zikirin Allah da karatun Alkur'ani mai girma.
ba wai sai can cincikin Alkur'ani ba, ko kanan surorine kiyi ta karanta su, Zaki sami waraka.
Mimi dai shiru, tayi, yana magana ita tana kuwa tana tunanin ta daban...to, shi wanan malamin
da yake cewa tayi sallah, baya ganin cewa da ba ta damu da yin sallah ba, yanzu da matsala ya
sameta, sai kuma ta wai wayi sallar...?...tam kar ya shiga zuciyar, ta, ya CE, kar ki dubi yawan
zunubin ki, matsawar kika t ba, Allah zai yafe maki kurakuran ki sanan, yana da kyau kiyi adu'ar
istihara, wato Neman zabin Allah kafin kikyi zabin mahaifin ki.
ta CE, to malam AI ni ban iya ba...duk abin da ka CE min inyi din nan bansan ta inda zan fara
ba...
ya CE, in kin amince sai in koya maki yadda zakiyi.
ta CE, to, amma ka bari zan kiraka.
Khalil, ta kira, ta fada masa ko mai.."
[01/10 9:45 pm] Abdul: Shi ya sa kike son shi,to ki ba abbas dama ki ga irin tasa.MIMI ta ce,ke
yanzu za ki so a raba ki da faisal?ta ce,aa. amma in ta kama zan iya sadaukarwa.ina nufin dad
dinki ya cancanci sadaukar da soyayyarki don ki faranta masa rai. MIMI ta ce,na yi
yunkurin haka,amma na kasadon haka yanzu mu tsai da shawara ta karshe,ni da khalil.kuma ita
ce mafita. mina ta ce,me kuka yanke? MIMI ta ce,kar ki damu,ba sai kin ji ba.suna yin zantukan
nan ne a inda suka kebe kansu lokacin da abbas da abokansa suka je gurin manajan hall din da
su mina suka ce yayi musu. Duk komai mina da na'ima suka zaba,MIMI ko kallon su ba ta
yi.sai kusan daya saura suka nufi gidan da za su zauna.ba su da nisa da gidan iyayen mina. sai
murna take yi,wai za ta dinga zuwa a kai,a kai,ga shi gidan ya burge ta.ko MIMI ta yaba gidan a
zuciyarta,amma ba ta nuna ba. abbas ya zo kusa da ita,dear ya kika ga
gidan naki?saman nan naki ne ke daya,falulluka uku,duk naki ne.da na lura kina son zama a
sama,shi ya sa kike abar so kamar tsuntsaye.MIMI ta kau da kai,ina jin yunwa,don haka zan je
gida.ya ce,bari mu je gurin cin abinci,mu ci mana. ta ce,aa ba na cin abincin ko'ina,ba komai
nake ci ba. ya ce,shi ke nan bari mu fara kai mina ko?ba ta kanka ba ta nufi fita. sun
fara sauke mina wadda take ta yaba wa abbas,har MIMI ta soma jin haushinta,ya sauke
abokansa gidan cin abinci, ya ce bari ya kai ta gida ya dawo,zai same su a nan.duk zantukan
da yake mata tun sad da suka taho ba ta tanka shi ba,har suka zo gidan,yana yi mata
magana,ba ta tanka shi ba. ta sauka ta nufi ciki. ko da ya koma,abokansa korafi suka yi
masa a kanta.munir ya ce,don tana da kyau sai ta hada da iskanci?don wannan ya wuce jan
aji,tana kallon mu sai ka ce ta ga kashi.ya ce,ku yi hakuri abokaina.tana cikin fushi ne,amma
lokaci kadan za ku ce tafi kowa kirki a nan gaba.dariya suka yi masa,don sun gane yayi nisa a
soyayya.
[01/10 9:45 pm] Abdul: Isma'il yana murna zai soma cusa tauhidi a zuciyar MIMI,ya tanaji
abubuwan da zai fada mata don kara cusa mata ALLAH a cikin lamurranta.ya yi ta jiran
kiranta,amma shiru.bayan laasar sun fita shi da direban yara,hamisu ke nan, don in an aike shi
ko zai kai yara wani gurin,lsma'il kan bi shi don ganin gari.ya kosa su dawo don ya kira ta.haka
kuwa aka yi.suna dawowa ya shiga daki,sai da ya zauna tsakiyar katifa ya nemi layinta ya
kira.gab da za ta tsinke,ta daga.ya yi sallama.a kagare ta amsa.ya ce,ya ranki ya dade na ji
shiru ne?ta ce,malam ka bar shi kawai.mun canza dabara. khalil ya ce naka zai ci lokaci.lsma'il
cikin sauri ya ce,amma nawa shi ne mai tabbas,ln kin yi sabanin abin da na fada miki,karshe ki
yi nadama.ba lalle ba ne adduarki ta dauki lokaci, domin ALLAH mai jin kan bayinsa ne.ba ki da
wata dabara sabanin yi masa biyayya.ta yi jim,ta ce,don ALLAH ka bar shi kawai malam.sai ta yi
tsaki.ta kuma kashe wayarta. Ta ko'ina abubuwa sun dauki zafi,domin ko can katsina
tuni an daura auren zainab da alhaji lawal.an kuma kai ta gidan.matansa uku ga yara nan
kwatsam. gidan bene ne hawa daya. dakinsa ne a saman,sai matarsa ta ukun,sai kuma dakin
zainabu.a kasa matansa biyu ne da 'ya'yansu da kuma 'ya'yan wasu matan da suka fita.
tunda aka kai zainabu take cikin kuka.bayan kowa ya kama gabansa,ta tashi ta datse dakin
alhaji lawal ya taho misalin karfe sha daya da tsarabar kazarsa da abin sha.ya murda kofar
amarya,ya ji ta gam.ya yi ta bugawa tamkar zai balla kofar ta ki budewa.ba zainabu ba,ina zaton
duk matan gidan suna jin irin zagin da yake surfa wa amaryar tasa.fadi yake,ni zaki kawo wa
rainin wayo don ubanki?yar matsiyata, ba za ki bude ba?ln kika bari na balla kofar nan na
shigo,sai na karairaya ki,ko in sa a daure iyayenki har sai su biya ni abin da na kashe.lta dai
zainabu jikinta sai bari yake yi,tana ta kuka.alhaji cikin takaici ya nufi dakin matarsa ta ukun ya
sauke mata wahalar da ya debo ta magungunan da ya dankara.
[01/10 9:45 pm] Abdul: Zainabu har goman safe ba ta bude kofa ba.sai da ya bar
gidan,uwargidan ta zo ta buga,ta ce,bude yarinya ni ce,shi ya fita. matar ta shiga dakin,tana
kallon zainabu cikin tausayi,ta ce,ALLAH sarki, ashe yarinya ce karama.ke ko me ya kai ki
auren alhaji?cikin kuka,zainabu ta ce dole aka yi min.kudi ya nuna wa iyayenalna da wanda
nake so,yake so na.ta ce,amma iyayenki ba su bincika ba ne?ta ce ni fa ban san komai a kan
auren nan ba.ta ce,kai iyaye da yawa suna yin kuskure.da zara sun ga kudi,sai su tura
'ya'yayensu kawai,babu bincike. zainabu cikin tsoro, ta ce don allah hajiya me yake yi?ta ce,ba
komai,kar ki damu.shawarar da zan ba ki,kar ki sake rufe masa kofa.duk abin da ya ce,ki yi,kar
ki ke yi masa gardama hakan zai fi miki alheri,ke da iyayenki.ln kuma kin ki,to zai tozarta ku
gaba dayanku. zainabu cikin kuka ta ce,na shiga uku!hajiya to ke 'yar uwarsa ce?aa,ni ce
matarsa ta farko.ya aure ni tun bashi da ko kwabo. 'yayana goma da shi. zainab ta zaro
ido,dama yaransa goma ya boye min?ta ce,nawa ke nan kadai 'ya'yansa ashirin da biyar,banda
masu ciki uku. zainab ta ce ban gane ba. matar alhaji ta ce,matan da ya saka goma cif.ta
karshen tana da ciki.sai sauran matansa biyu,duk suna da ciki.zainabu ta sake rushewa da
kuka,tare da cewa,ita dai za ta gudu. matar ta ce kar ki fara!zai sa a kama iyayenki,kuma ba zai
sake su ba sai ran da ya ji an ce an ganki,kin dawo dakinsa, ta mike, bari in sa a kawo miki abin
kari. zainabu ba ta ce aa ba,dm tana jin yunwa,rabonta da abinci tun jiya da safe.koko ne da
kosai,duk sun huce,yarinyar da ta kawo za ta kusan saarta.zainabu dai haka ta tuttura.
da rana lnna yalwa ta zo, aminiyar lnnarsu ce.zainbu cikin kuka ta fada mata komai.lnna
yalwa,ta ce,da allah can, duk karya ta fada miki,kika kama.kishiya ce har za ta ce miki ga laifin
miji,ki hau kai?zainabu ta ce,lnna yalwa gaske ne.ga shi nan jiya sai zagi na yake yi dana rufe
masa kofar.jiya fa na zo gidan.ln da mutunci bai dace yayi hakan ba.
[01/10 9:45 pm] Abdul: Laifinki ne.yaya zaki rufe masa kofa?lna kika taba jin haka? bayan
tafiyar lnna yalwa,ba jimawa yaran gidan suka cika mata daki, wanda gado ne kurum wanda
alhaji ya sa mai kyau ne,amma da gani ba sabo ba ne.wadda ya aura nan dakin yake kawo ta.ln
za ta tafi kuma ta bar masa gadonsa. ya shigo tana sallar magariba.ya zauna bakin
gado,yana ta huci,sai ka ce kumurcin maciji.tsoro da fargaba suka hana ta idar da sallar.sai yi
take tana sallamewa.ta sallame ta sake mikewa.ya finciko ta, ni za ki zo mawa da salon
salla?magariba dai rakaa uku ce.kuma nafilar da na sani bayan magariba rakaa biyu ce,amma
ke da na shigo kike ta zabga salla ko?cikin tsoro da kuka ta ce,aa baba ba haka ba ne. baba?ya
tambaye ta,cikin fushi.kuka ta ci gaba da yi. ya kashe ta da mari,nine babanki?to,bari in nuna
miki cewa ni mijinki ne,ba ubanki ba! da karfinsa ya yi amfani,ya raba ta da tufafinta,ya jefa ta
kan gadon.duk 'yan gida da yara suna jin ihunta.da ma ya yi mata nata shiri na musamman.don
kansa ya bar ta,ba don rokon da take masa ba,ko don wahalar da ta sha.ya bar ta yashe ba
kulawa bare tausayawa,ya nufi dakinsa. haka ta kwanta babu barci sai kuka take yi.ya fita da
wuri,don haka hajiya lndo ce uwargidansa ta zo ta duba ta,ta dafa ruwan zafi ta taimaka mata,ta
ba ta abin kari.tsawon sati guda da yayi a dakinta bai raga mata ko sassauta mata ba.haike
mata kurum yake yi.don haka ta sha azaba.tsoronsa da tsanarsa sun dasu cikin zuciyarta.
khalil ya yi nasarar goge dan imanin MIMI da dan tauhidin da lsma'il ya soma cusa mata.ya
zuwa 'yan kwanakin da suka biyo baya,sun yi nisa cikin tsarin yadda za su gudu.ko yanzu da
suke yin waya fada mata yake yi,ta nuna cewa ta amince sai daf da auren sai su gudu.suna da
bukatar kudi kafin ranar.ya ce,zan dauki sarkar mamana in kai kasuwa in sai da,sbd dad dinmu
ba shi da kudi a gida sbd siyasarsa din nan.MIMI ta ce,kai baka da naka kudin ne?ya
ce,account dina babu kudi,bai fi dubu ashirin ba.dad baya zuba mana kudi.
[01/10 9:45 pm] Abdul: (2)Dad baya zuba mana kudi sosai yanzu saboda siyasa.ta ce,ka bar
shi,ina da kudi a cikin karamin account dina.kamar nawa za mu rike?ya ce,muna bukatar kudi
sosai,sbd za mu kama guri mai kyau ne a wani state din wanda ba za su yi tunanin za mu je
ba.MIMI ta ce,ok,ka samo,ni ma zan samo,sai mu hada.ya ce,shi ke nan sai mun yi waya.
bayan sun yi bankwana ta soma tunanin yadda za ta kwashe duk wani abu nata mai
amfani.matsalarta daya.kudinta masu yawa suna cikin babban account dinta.ln kuma ta taba
dole ne mahaifinta ya ji alat. Momy nafisa an dawo daga dubai,'yan gidansu abbas sun
kawo kayan lefe.ran hajiya sauda ya baci da yadda alhaji ya nuna mata.matsayinta na wadda ta
haifi MIMI ya kyautu a bata hakkinta ko da na shawara ne,amma alhai yayi mata dif,tunda ta ce
baza ta shiga lamarinsa da MIMI ba,ita 'yar ba da shawara ce.bata fadi hakan da wata manufa
ba, sai dai nuna ma alhaji kurensa,amma ya dauka da zafi,don haka ta lashi takobi ita da
yaranta babu inda za su je,domin auren abba a nan katsina aka yi shi,na MIMI in baza a kawo
nan ba,to su je can su yi kayansu. biki saura kwana goma MIMI ta yi wanka,ciki sauri ta zura
doguwar rigarta atamfa,sai dan bakin karamin mayafi. takalmi mara tudu ta saka,ta kwashi
katinta na ATM daga jakarta da take zuwa banki,ta zuba su cikin jakarta da takan je saloom,ta
ra aya takar.ta kwashi wayoyinta.tana sauka kasa,momy zata hawo saman ta ce,aa sai ina haka
MIMI? ta ce,za ta je saloon.na'ima ta ce yayi wuri sis.saura kwana goma biki fa?MIMI ta tabe
baki,ke kika san da wani biki,ni kam ban san da shi ba. momy nafisa ta ce,ki zo ga
tela,zai gan ki sbd dinkunan kayan biki,kin ki zuwa ki ga kayan ki.MIMI ta ce.momy har da ke a
wannan maganar bayan kin san komai?ni fa ba son shi nake yi ba.momy ta sassauta
murya,yanzun dai ki bi ni kawai.ln lokacin da za ki ce wa alhaji baki son abbas yayi,zan sanar
da ke ki tubure kawai.a ran MIMI ta ce,ke ma baki san namu shirin ba.a fili ta ce,
[01/10 9:45 pm] Abdul: (3)A fili ta ce,shi ke nan momy.tela ya gwada MIMI sosai.kafin ta
fice,makullin motar momy ta dauka ta fita.lta ta ja motar zuwa bankinta na karamin
asusunta,inda ta kwashe kudinta kaf.ta nufi babban asusun da ke wani bankin daban,ta dibi
dubu dari biyu.za ta kara sai kiran dad ya shigo.ta daga ya ce,MIMI kina ina ne?ta ce, ina banki
ne.dad ya ce,yaya kika taba wannan account din MIMI?ta ce,dad ba ni da kudi ne,kuma zan yi
gyaran jikina ne.ya kalli alhaji akilu,ya ce,shi ke nan ya isa,ki bari zan ba ki kudi. kar ki kuma cira
daga wannan account din,ina son yi miki wani tsari ne da kudin.za ki yi kasuwanci kina daga
gida,kuma na manyan kudi kin gane?MIMI ta ce,eh dad ba zan kara cirewa ba.ya ce,shi ke nan.
alhaji bishir cikin dariya ya ce,ka ji 'yar kwal uba? wai tana fadin bata so,amma ta zo tana dibar
kudi wai za ta yi gyaran jiki.suka sa dariya.alhaji akilu ya ce,me na fada maka?kiyayyar mata ba
ta zuwa ko'ina.amma shi ma abbas din ai shi ya dace ya ba ta kudin gyaran jikin. alhaji bishir ya
ce,ai ita da shi duk daya ne.ka rabu da shi,zan ba ta.alhaji akilu ya kira layin abbas.bayan ya
dauka,ya ce abbas ya baka bai wa amaryarka kudin gyaran jiki ba?abbas ya ce,dad ta ki ba ni
damar in san abin da take bukata ne.amma zan ba ta anjima. ya ce,shi ke nan ka je ka ba ta.ka
lallabe ta,ka san yarinya ce.abbas ya ce, insha allah dad. MIMI gida ta wuce ta
adana kudinta da duk abin da ya kamata ta tafi da su,amma banda kaya. lsma'il ya
dangana har zuwa ranar ashirin da tara da alhaji bishir ya yi musu albashi.duk da kin karatun da
MIMI ta yi,bai sa alhaji canzawa daga dubu darin da ya alkawarta zai ba shi ba.lsma'il yayi ta
juya kudin a cikin dakinsa,yana farin ciki.sam bai taba rika su ba a hannunsa ko na wani ma
bare nasa.lalle goben nan sai katsina,ya je ya biya kudin gaisuwa,ya hada kayan sa rana,ya sai
ma zainabu waya,yayi alheri,yayi sabbin dinkuna,yana ta baje burinsa.nan ya kira mahmud ya
sanar da shi cewa gobe yana tafe.
[01/10 9:45 pm] Abdul: (4)Tun dare yake ta shirin sa,washegari ya kira hajiya sauda ya fada
mata cewa yau yana son zuwa gida ya ga 'yan uwa.ta ce ba laifi,sai ka iso.ln ka zo kuma don
allah ina neman ka.ya ce babu matsala.sai dai ina son don allah ki sanar da alhaji sbd ban san
lokacin da zai fito ba.ta ce,ya ba ka albashi dai ko?ya ce, wallahi ya ba ni.ki yi min godiya.ta
ce,to zan sanar da shi yanzun nan. ba a yi minti talatin ba, sai ga hamisu direba ya
ce lsma'il ya je in ji alhaji.a falo ya same shi.ya zauna,ya gai da alhajin cikin girmamawa.alhaji
ya ce, sauda ta kira ni,ta sanar da ni cewa zaka je gida yau. haka ne?ya ce,eh alhaji.lna son in
je in ga 'yan uwa ne. alhaji ya ce,da fatan ba mu takura maka ba ko?ina nufin ka ji dadin zama
da mu?lsma'il ya ce,na ji dadi sosai.alhaji ya ce,to ina fatan za ka dawo.lsma'il ya ce,eh to,na ji
ana cewa za a yi wa wadda na zo in koyar da ita aure,shi ne ban sani ba ko hakan yana nufin ni
ma na gama aikina ke nan?alhaji yayi murmushi,ai in na lura ita din bata yin karatun,amma
kannenta suna yin karatun. kana yi mana salla.ga yaran nan suna yin karatu sosai,suna yin
salla a kan lokaci.wannan ya fi min komai.yanzun ma da ka ce zaka je gida din,na kira ka ne in
ji ko kwana nawa za ka yi?lsma'il ya ce,to ina ganin dai zan yi kamar sati daya.alhaji ya ce,har
sati daya?na zaci baza ka wuce kwana uku ko biyu ba.har me zaka yi haka?lsma'il ya ce,eh to
ina so dai za a sa ranar aurena ne tukuna.alhaji yayi 'yar dariya,oho haka ne?to ba
damuwa.allah yasa alheri.ya laluba aljihunsa,dubu biyar ya kara masa.ga wannan kayi kudin
mota.ka amshi lambata gurin sauda.ln ya so in ka tashi kira na.sai ka kira ni kai tsaye,ba sai ka
bita gurin hajiya sauda ba.lsma'il ya ce,to na gode sosai. bayanan fitarsa ne momy nafisa ta
ce,na lura yaron nan yayi maka ko?alhaji ya ce yana da hankali sosai.lna son mutum haka.har
gareji, hamisu direba ya kai lsma'il,bayan yayi sallama da dukkan maaikata gidan.
[01/10 9:45 pm]