Showing 15001 words to 18000 words out of 25770 words

Chapter 6 - CANJIN RAYUWA BOOK 2 COMPLETE BY HALIMA ABDULLAH MASHI

yawa. yanzu
dai likita ya dora ni kan magani da dokoki da kuma abincikan da zan kiyaye.hawaye suka zubo

a idon sauda.ya dafa ta,aa kar ki yi kuka sauda,insha allah zan warware,ta ce, allah ya baka
lafiya.ya ce, amin.ya kalli abba,ina takwarana?abba ya ce, suna gida.za su zo da mamansa.alhji
ya ce,madallah,allah yayi maku albarka.kun ji abin da MIMI ta yi min ko?ya dinga kallon su da
dai-dai,ya dan sunkuyar da kai.na san har da hakkinku.lna mai baku hakuri.abba ya ce,haba
dady babu komai.allah ya ba ka lafiya.sauda ta ce,to yanzu ya ake ciki?ya ce, na me fa?ta ce
na bikin ya ce,na'ima za a daura da ita.ya kalli abdulkarim ya nuna masa wayarsa.miko min
wayar can.ya miko masa.ya bata,bude ki ga sakon da yarinyar nan ta turo min.hajiya sauda ta
kammala karantawa cikin kuka.ta ce,alhaji ba zan gaji da fada maka,laifinka ne kai da nafisa
ba.kun gina ta a kan yi mata duk abin da take so.ya kamo hannuwanta,na yarda laifina
ne.nafisa ta biye min ne don ganin haka nake so. abba ya ce,to dady ka ce ta dawo mana.ln
yaso ka bata shi wanda take so din,tunda na'ima zata auri wanda ba ta so din. ya kalli
abba,ba canji ke nan.zan ci gaba da yi mata abin da take so ke nan?ai yadda ba ta yi min abin
da nake so ba,haka nan ba zan taba yi mata wanda take so ba ai ta yar da wannan gatan da
kanta.lta ma zan mata abin da ba za ta manta ba,kamar yadda ni ma ba zan manta da abin da
ta yi min ba. hajiya sauda ta ce,yanzu a ina take?oho!in ji alhaji.
[01/10 10:34 pm] Abdul: (21)Suna idar da sallar asubahi lsmail ya ce wa hamisu direban
yara,don allah kai mu asibiti mu duba alhaji.har da kanin alhaji da 'ya'yansa mata suka tafi
tare.sun samu alhaji yana salla.don haka suka zauna momy nafisa ce ta kwana a gurinsa.lta ma
tana sallar ne.bayan sun idar ta leka ta ce.ku shigo mana.suka shiga suka gai da shi.ya ce. na
samu sauki.nan da karfe bakwai zan koma gida.a ci gaba da biki kun ji na'ima ta share min
hawaye ko? lsmail da bai san kan maganar ba,sai ya kalli alhaji daidai lokacin da kanin alhajin
ke cewa,mun ji zata auri shi yaron da waccan ja'irar ta gudu domin sa.yanzu ai sai ta
dawo.alhaji ya ce,ta dawo ina?ai ko ta dawo,ita ma sai nayi mata abin da ta yi min.suka ce
hakuri dai za a yi.lsmail yayi wa alhaji addua.suka ce za su koma. alhaji ya ce,malam lsmail na
gode.sai na zo. suna komawa gida lsmail ya kira layin hajiya sauda.har sau biyu
bata daga ba.don haka ya bari. yana gugar kayansa,sai ga kiran ta.ya daga suka gaisa. ya
ce,kin samu labarin ciwon alhaji?ta ce tun jiya.yanzu maga mu nan ni da yara za mu biyo jirgin
karfe takwas.yaya jikin nasa?ya ce,da sauki.ta ce,an ji labarin MIMI?ya ce, eh to,na ji dai an ce
tunda ta yi masa text ne cewa ba za ta dawo ba sai in zai yi mata abin da take so,shi ne ya
fadi.amma yanzu na'ima ta yarda za ta auri wanda MIMI ba ta so. hajiya sauda ta ce,oh ni
saude!allah ya shirya wannan yarinyar.shi ke nan sai mun iso. bakwai da rabi alhaji ya iso
gidansa,jamaa sai shigowa suke.yayi wanka,ya karya.ya sha magani,ya dan kwanta kafin
tara.daurin auren sai karfe biyu,in an idar da salla a babban masallacin abuja.tara saura hajiya
sauda da abba da abdulkarim da su hasana da usaina suka shigo.na'ima ta rungume su
hasanan,ta gai da hajiya ta ce,lna momy taku?ta ce,tana dakin dad.dukkan su suka shiga.ya
tashi barci suna magana da nafisa momy nafisa ta ce,oyoyo, sannun ku da zuwa.nan yaran
suka gai da ta,suka nufi gurin dadynsu.lta kuma ta ci gaba da yi wa hajiya sauda mita.
[01/10 10:34 pm] Abdul: (23)Jiya dai an ce suna kaduna.hajiya sauda ta ce, allah ya
kauta.daidai lokacin wayarsa ta yi ringing,momy nafisa ta shigo tana cewa, alhaji kana da baki.
Duk tare suka fito.hajiya sauda da su hasana saman MIMI suka nufa saboda gidan da
mutane.har an soma cin abinci dangin momy nafisa sun fi yawa. usaina ta kalli hajiya sauda
bayan sun zauna,hajiya ki kira ta mana a waya,ki ce ta dawo.ni na ga na'ima kamar tana murna
da hakan.ta ja mu tana nuna mana lefen sis MIMI,wai nata ne.ga mota can a gare ji,an zuba

dukiya a gidanta. abdulkarim ya ce,ai ni na yi murna da faruwar hakan.shi dad din yanzu yayi
nadama ai.abba ya ce,ni zan zo ma in ma koma ne fa hajiya.don ba zan kwana abuja ba.
gaskiya tunda ya samu sauki,ga shi ma sai bikinsu suke yi.sai ga masu aiki da kulolin abinci,wai
a kawo musu.hasana ta tashi ta shige dakin barcin MIMI. usaina ta biyo ta.hasana ta kalli
usaina,gaskiya sis MIMI bata duba wa kanta ba. kalli fa dakinta.dubi duk nan bangaren ta ne,ya
fi ko'ina kyau a gidan nan,amma ta kasa yi wa dad biyayya. allah ta ban kunya.usai ta ce,ai ga
shi nan na'ima ta yi abin da ita ta kasa.na san ko moy nafisa za ta iya sa ta ko don su birge dad.
Hasana ta ciro wayarta, mu gwada kira mu gani ko za ta daga.nan suka soma kiran layinta.yana
ta ruri yana tsinkewa,ba ta daga ba.daidai lokacin MIMI tana gado asibiti kwance. damuwa ce ta
sa take jin ta babu wani sauki.duk wanda ya kira,tana kallon kisansa.yanzu haka tana kallon
lambar usaina, hawaye suka soma zubo mata.yaran da bata damu da su ba,ashe suna son
ta.lta yanzu tana jira ne ta ji kira momy nafisa don ta san matsayin da take.ln dad dinta ya
yarda,kai ko bai yarda ba,yadda take jin zuciyarta za ta koma gida ne kawai.khalil ya dauki
wayar bayan ya ji shigowar sako.ya ce,sako ne dear.ki duba ko momy din ce ko?cikin sauri ta
amshi wayar.usaina ta gani.har ta ajiye wayar sai kuma ta bude.ga abin da usaina ta ce:
[01/10 10:34 pm] Abdul: (24)SIS MIMI DON ALLAH KI DAWO DAD BA LAFIYA YA FADI
SABODA JIN CEWA KIN GUDU NE,BA SACE KI AKA YI BA.ANJIMA ZA A DAURA AUREN
NA'IMA DA ABBAS. Ihun da MIMI ta yi ne yasa khalil mikewa. tambayar ta yake
yi,me ya faru?cikin kuka take fadin, dad ba shi da lafiya.ni zan koma gida ne kawai.khalil
hankalinsa ya tashi.ya shiga lallashin ta.ki yi hakuri mana dear.za mu koma ai.amma bari su
neme mu.ta ce,ba ni wayata.bari in kira dad din.ya ce,aa kar ki kira shi tsaya ki ji.MIMI ta tsaya
tana kallon sa ya ce,ki kira su usaina din kiji komai daga bakinsu.nan suka kira layin.hasana ce
ta daga wayar:MIMI cikin kuka ta ce, usaina!hasana ta ce,ni ce ba usaina ba ce,ta ce,yanzu
wane hali dad yake ciki?hasana ta ce ya ji sauki,babu laifi,amma ya kwana a asibiti ne.ya ji
zafin sakon da kika turo masa cewa kin tafi saboda wani.usaina ta amshi wayar tana cewa,sis
MIMI ki dawo kawai zai fi miki. dad ya ce,ba zai damu daki dawo ko kar ki dawo ba, don na'ima
ta gama fitar da shi kunya,ta amince anjima za a daura aurenta da abbas.MIMI ta kasa magana
kuka kurum take yi.suka nufi hajiya da wayar usaina ta ce.ga sis MIMI tana jin lokacin da hajiya
take fadi me za a yi mata don ga ta a waya?abin da ya kamata ta yi ta kasa.don haka bani da
lokacin sauraron ta.ubanta ma da ya nuna mata so,ta yi masa butulci, bare wani.da allah kashe
wayarki!hasana ta katse wayar.kuka sosai MIMI dinga yi tun khalil yana bata hakuri,har yayi
shiru ya tsaya yana kallon ta.sai da ta gaji don kanta,ta kalli khalil ni zan koma gida.ta sauka ta
soma duba jakarta.zan koma gida khalil in yi wa dad dina biyayya. amma har abada ka sani ina
son ka a cikin zuciyata. ya ce,ki tsaya ki ji sauki mana.ba a sallame mu ba.ta ce,ba na bukatar
sai na samu sauki zan tafi.ka zo ka kai ni gurin da zan hau mota.tana daukar jakarta,ya nufi
ofishin likitan,ya sanar da shi cewa wai tana son ta tafi.lokacin da likitan ya fito,ta kai harabar
asibitin.suka sha gabanta,
[01/10 10:34 pm] Abdul: (25)Khalil ya ce,MIMI ki saurari likitan mana.ta ce, likita ka yi min
afuwa, awanni suka rage a daura min aure.ka san cewa guduwa nayi?babana ya fadi sbd na
gudu.likita ya ce,na ji zaki koma,amma ki bari ki gama karbar allura. MIMI ta ce,bari in tafi.na yi
nadama sosai da na bijire wa mahaifina.zan koma in ba da hakuri,in nemi ya yafe min.ya aurar
da ni ga ko waye yake so. Dole likitan ya ce,ka bar ta ta tafi kawai.ba shi da zabi,dole
ya koma ya dauko tasa jakar suka je titin bypas don samun motar zuwa abuja.suna cikin motar

ne ta sake kiran usaina,karfe nawa za a daura auren?ta ce,bayan azahar ne a babban
masallaci.mu ma hajiya ta ce,da an gama daure aure za mu koma gida.ta ce,shi ke nan sai na
iso.ta kalli khalil,ina za ka tsaya?ya ce zan je har gaba mahaifinki, yayi yadda ya ga dama da
ni.amma na gama hango mutuwata,in har na rasa ki. ta kalli agogo,yanzu sha biyu da wani
abu,kana ganin har za mu je abuja ba a daura da na'ima ba?ya ce zan fi kowa so in hakan ta
kasance.ki yi adduar allah ya sa ni ne mijinki.daya saura alhaji ya shigo gidan don shirin zuwa
masallaci ko kuma in ce gurin daurin aure.daidai lokacin ne kuma hajiya binta ta shigo,ita da
yaranta. mamakinta da tunaninta alhaji ya rasu ne?ko an ga amaryar ana ci gaba da biki,shi
yana asibiti?ta ga harabar gida an zuba kujeri da rumfuna,ga mutane da yara.suka shiga
falo.nan ma duk jamaa.dakin nafisa hajiya bintar ta nufa.cike da manyan kawayenta,tana zaune
a gaban madubi,ta yo wanka ana yi mata kwalliya.hajiya binta ta ce,nafisa wai biki ake yi ne?ta
mike da sauri,sannun ku da zuwa kun iso?eh,kin san tafiyar mota,tun bakwai muka fito.ban
gane ba,wai bikin ake yi ne?eh bikin na'ima.cikin mamaki, hajiya binta ta ce,na'ima kuma?momy
nafisa ta karaso gurin ta cikin murmushi,eh,kin san MIMI ta gudu.shi ne na'ima ta zabi ta fitar da
mahaifinta kunya. hajiya binta ta ce,to shi alhajin wane asibiti yake?ta ce,ya shigo yana
gefensa,zai yi wanka.
[01/10 10:34 pm] Abdul: (26)Tun jiya aka sallamo shi.yana jin na'ima ta yi wannan furucin,sai ya
gyare.wata daga cikin matan da ke zaune a kan gadon ta ce,yarinya ai ta share wa ubanta
hawaye. wata ta ce,ai ko ta yi saa jiya maigidana ke ba ni labarin irin gudummawar da abokan
kasuwancin alhaji suka yi ta ba amarya. babban dan kasuwan nan wanda yafi kowa shahara a
afrika an ce zunzurutun kudi miliyan ashiri ya ba da, banda motoci.hajiya binta dai ta ce,bari in
duba alhaji. momy nafisa ta ce,to ki duba shi.yawwa hajiya sauda ma suna saman MIMI to
kawai hajiya binta ta ce, ta nufi sasan alhajin,cikin al'ajabi.gani take yi momy nafisa murna take
yi da aure ya juye a kan 'yarta. Ta kalli yaranta ku hau saman sis MIMI,hajiya sauda tana
nan.da farko har za su noke,don suna tsoron MIMI,tunda bata kula su.amma jin cewa sauda
tana nan,sai suka nufi saman cikin murna.suna son hajiya don in sun zo hutu ba sa son tafiya.ta
iya tafiyar da yara sosai. Ta samu alhaji ya fito wanka,ya ce,aa ku ma kun iso?ta
ce,eh,alhamdulillah sam ban zaci zan samu jikinka haka ba.na ji an ce sugar,mene ne mene
ne.ya ce,da sauki.da ma karin damuwar kunyar da MIMI ta so ta ba ni ce,sai kuma na'ima ta zo
ta tare matsalar.yanzu dai burina a daura auren nan.zan koma asibiti,likita ya duba ni yadda ya
kamata.ta ce allah ya sawwake.to,yanzu mene ne labarin MIMI? ya kalle ta.bayan ya gama
saka wando,yana tura singiletinsa,ba ni da labarinta, kuma bana bukatar in sani.hajiya sauda
sun zo da su abba.lna zaton suna saman.hajiya binta ta ce,to bari in ji gurinsu.ta samu su abba
za su fito.nan suka tsaya suka gaisa.suka ce bari su fita su yi salla.ln an daura aure za su
wuce.hajiya binta ta ce,wai ni hajiya yaya lamarin ya zama haka?ba kya tunanin cewa nafisa ta
san komai a kan gudun MIMI ko bijirewarta?ba na tunani,in ji hajiya sauda.ba na zargi a kan
abin da ban ji ban gani ba.abin da na sani kawai alhaji shi ne silar komai.haka nan kullum ina
cikin adduar allah ya shirya MIMI.ya bata miji na gari.
[01/10 10:34 pm] Abdul: (27)Ban yi fushi ba ko da aurenta bai kasance da dan gidan minista
ba.kila ba alherinta.hajiya binta ta ce, haka ne allah zai amshi adduarki,domin bakin mahaifiya
yana da karfi a kan yara.hajiya sauda ta kalli usaina wadda ke dube-dube a kan kwamfutar
MIMI,ta ce,ku sa wa yaran nan abinci ga shi nan.hasana ta sa wa hajiya binta.hajiya binta ta
ce,ni duk damuwata ta a ba na jin yunwa.sauda ta ce,damuwar me,bayan ga jikin mijinmu da

sauki? hajiya binta ta ce,batan MIMI ai abin tunani ne.ko kusa,in ji hajiya sauda,guduwa ta yi,ba
bata ta yi ba.kin ga kwanukan da su abba da abdulkarim suka ci?cewa suka yi tunda jikin
dadynsu da sauki a sa musu abinci su ci.ni ce ma ban riga na ci ba.na fi son abu mai ruwa da
safe,mai kuma dumi kamar shayi.hajiya binta ta ce,ya fi dadi ai hasana sa min wainar allah ya
rufa asiri.suka ce amin. Duk da gudun da motar da su MIMI suka shiga take yi,gani
take yi kamar ba gudu ba.ba ta taba shiga motar haya ba tunda aka haife ta sai yau.bugu da
kari bata taba shan wahala ba a rayuwarta tunda take kamar wannan lokacin da ta bar gidan
iyayenta.shiru da ta yi daga zaune abubuwan da take lissafawa ke nan.duk da tsananin son da
take yi wa khalil ba ta jin za ta sake barin gida,ba tare da yardar mahaifinta ba.abin nufi ba tare
da sun yi mata aure ba.cikin haka ne ta ji mutanen cikin motar suna salati,wadansu kuma
wadanda ba musulmi ba suna ambatar abin da suka yi lmani da shi.ta zaro idanu,lokacin da ta
ga motar ta su ta saki hanya, sosai ta firgita,ta soma fadin wayyo allah!daf da wani rami motar
tasu ta tsaya cak.wai ashe taya ce ta fashe,tana duniyar tunani,bata ji kara ba.babu wanda ya
zaci motar nan za ta tsaya.motoci suka tsaya ana ta yi musu allah ya kyauta.hankalin MIMI ya
sake tashi.har aka canza taya jikinta bai daina bari ba.haka nan duk lallashin da khalil ke yi
mata bata daina kuka ba.shi kansa yayi dana sani sosai na tahowa da ita.da kyar ma ta yarda
ta sake shiga motar suka nufi hanya.karfe biyu daidai aka daura auren.
[01/10 10:34 pm] Abdul: (28)Karfe biyu daidai,aka daura auren na'ima da abbas.daurin auren
mai dimbin tarihi irin manyan mutanen da suka halarci gurin.babbar matsalar angon yaki
halartar daurin auren,yana gida kwance,lta kuwa na'ima suna can gidan yayar mommy nafisa
suna cashewa da makadan da suka dauko.sun koma can ne wai kar a ce suna murna da auren
ya koma kan na'ima.wani karin abin aushin ma na'ima ita da abbas din ba su taba yin magana
ko da ta waya ba. kuma daga momy har na'ima ba su taba tunanin cewa wannan wata matsala
mai zaman kanta ba ce.uku saura tasi din da suka dauka shata ta karyo kwanar
layinsu.kasancewar layin baya fita,sai ta tsargu da ganin motocin da aka ajiye a layin,ga mutane
ta ce,me ke faruwa?ba dai dady ya mutu ba?dan tasi din ya ce,gaskiya ina zaton ba mutuwa ba
ce,sai dai biki.ta ga nisan su karasa har kofar gidan,don haka ta ce,tsaya ina zuwa.yana
tsayawa ta dauki jakarta,ta zura da gudu.kofar gidansu duk jamaa.gate dinsu a bude.tana shiga
da malam lsma'il ta soma yin ido hudu. mutane ba su gane ta sosai ba,saboda ita ba
maabociyar saka hijabi ba ce.lsma'il ya ce,daga ina kike?ta ce,me ake yi a nan gidan?ya
ce,auren na'ima ta zaro ido,an daura da na'ima?ya ce,tabbas!sai ta juya,yana cewa ke!za ta fita
ke nan su abba da abdulkarim za su shigo don yin sallama da hajiya sauda don basu so su kai
wannan lokacin ba a abuja.dad ne ya tsare su,wai sai an gama daurin aure.yana ta nuna su ga
abokansa, wadanda a da MIMI suka sani,basu san ma yana da wasu yaran ba.sai abokansa na
tun farko irin su alhaji lsa.abdulkarim ne ya gane ta,don abba ne a gaba,amma bai kalli fuskarta
ba,kuma hijabin da ta sa ya kara boye ta.da karfi abdulkarim ya rike hijabinta,har ta dan gota
shi.ya jawo ta ya falla mata mari.sai da ta ga wani haske,ya ce,gidan uban wa za ki koma?ta
tsala ihu,wanda ya janyo hankalin duk mutanen da suke harabar gidan.lsmail ya iso gurin yana
cewa a yi mata hakuri.abba ya ce, haka shi ne daidai da ita. suka iza keyarta tana kuka, suna
rankwashin ta,gami da zagi.
[01/10 10:34 pm] Abdul: (29)Momy nafisa ta fito da gudu,domin wata kawarta ce zata tafi
gida,sun yi sallama.amma tana fitowa ta ga MIMI a hannun su abba.sai ta koma da gudu ta
sanarwa momy nafisa cewa ga fa MIMI.da farko momy nafisa idanu ta zaro,tana cewa,na shiga

uku!me zai sa yarinyar nan ta dawo yanzu?sai yarta ta ce,kar ki damu tayi ta dawowa.an riga an
daura aure.momy nafisa ta ce, kuma fa haka ne.bari in fita in

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login