Showing 21001 words to 24000 words out of 25770 words

Chapter 8 - CANJIN RAYUWA BOOK 2 COMPLETE BY HALIMA ABDULLAH MASHI

su na'ima daidai lokaci suka dawo gida don za a kai ta gidan miji.nan fa aka turo motoci
don daukar amarya. an dauke ta zuwa gidanta da ke asokoro.jamaa sun yaba gidan.ga
motocinta guda biyu,daya na lefe,daya ta gurin dad dinsu. kawayenta da yan uwa sai murna
suke yi mata.karfe tara daidai abokan ango suka rako shi zuwa dakin amarya.ango abbas
wanda yake jin yau tamkar ranar mutuwarsa ba ranar aure ba,ya zauna a falon yana kallon su
usman suna yi da kawayen na'ima.shi haushi ma suke ba shi kwarai.ya kosa su gama
shirmensu su tafi don ya gaji,barci yake ji. suna tafiya,ya nufi sama inda nan ne dakinsa
da komansa yake yayi kwanciyarsa,ya bar amarya tana ta jira sa.duk da azabar daurin
dankwalin kanta ke yi mata,shiru da ta ji yayi yawa,shi ne ya sa ta tashi tana lekawa har sha
biyu.sai lokacin ta kira momy nafisa.lta ma lokacin tana dakin dad,wanda ke kwance jiki babu
dadi.ta daga wayar ta ce,na'ima yaya ne?na'ima ta ce,momy ban gan shi ya shigo ba.tunda ya
tafi raka abokai.ta ce ki duba dakinsa mana.na'ima ta ce,ai ban san ina ne dakin nasa ba.ta
ce,ki duba mana,ke da gidanki.ni ina nan gurin dad dinku ne, jikinsa babu dadi sam. na'ima ta
ce to a gai da shi. Daga nan ta soma neman dakin maigidan. ta binciko dakin mijin,sai dai
yana kulle.ta kwankwasa sau uku,yayi magana cikin dakewar murya,waye a nan?ta ce,ni ce.ya
ce,ke ce wa?ta ce,na'ima.ya ja dogon tsaki,don allah bar nan gurin.waye ya neme ki da za ki zo
ki ta da ni daga barci?ta yi tsuru cikin fargaba.ta ce,yi hakuri,ina jin tsoron dakin ne.ya ce,ina
ruwana da tsoronki.da ma abin da kike sone kara taba min kofa.dole ta juya,ta sauka ta koma
dakin cikin firgici ta kulle,ta sake kiran wayar momy a kashe.sai ta hakura ta kwanta. Zainabu
tana kasa inda kicin dinsu yake, tana ta kici-kicin dora katuwar tukunyar da suke dafa
abinci.mudu takwas suke dafawa in shinkafa ce suna yin tazarce ne daga rana har dare.ln tuwo
ne,
[7/27, 11:11] A~PROF: (39)Suna tuke mudu hudu ko hudu da rabi.tana hada ice,alhajin ya
shigo.sallamar sa kawai ta ji,gabanta ya fadi take ta soma kuka,don ta san abin da ya maido shi
gida,ci gaba ta yi da aikint uwargida wadda suke ce mata maman bishira ta ce,zainabu ki je
mana ga alhaji can ya dawo.ta kalle ta cikin raunanniyar murya ta ce,wallahi na gaji.lnnar su
bishira don allah ki bashi hakuri.ta katse zancen, sakamakon kira da ya kwala mata.ke
zainabu,ni saanki ne,kina kallo na shigo kin tsaya?mama bishira ta ce,je ki zan sa miki
hannu.laure da ke wanki wadda ita ce ta biyu ta ce,kwadayi mabudin wahala.zainabu ta shiga
dakin tana ja baya,tana fadin sannu da zuwa.ya ce,rike sannunki,ba na so.sai da na kira ki,za ki
zo?ta ce, ina sanwa ne,da ma zan zo.ya ce,to mu je!ai kin san abin da ya kawo ni ko?ba ta da
zabi face mika wuya. shi sam bai san wani wasanni ba.auka wa iyalinsa kurum yake yi.ln ya
cimma burinsa sai ya kakkabe jikinsa ya tashi. Rayuwar zainabu a gidan alhaji lawal,abin
tausayi ne.ga girka babbar tukunya,abin da bata saba ba,ga fama da wannan miji,uwa uba ga
su laure. suke dame ta da nuna kishinsu a kanta.don haka in ba girkinta ba ne, ba ta
saukowa,sai in su laure ba sa nan.wani lokacin kuma in yarasu sun shiga dakinta su yi ta wasa
ta biye musu. amma duk wanda ya san ta kallo daya zai yi mata ya san cewa ta rame.ta yi
baki,kyawunta da cikar budurcin da ta soma,duk komai yayi lakwasa. cikin haka ne wata
rana kannanta suka zo.ganin ta suka yi cikin yanayin suka je suka sanar da lnnarsu. washgari
sai ga ta salati ta zabga tare da fadin na shiga uku ni.yasu zainabu kin yi ciwo ne?ta ce,aa ta
soma kuka,wallahi innarmu na gaji da zaman gidan nan.mutumin nan bashi da imani,don allah
ki tafi da ni.kullum sai ya zazzage ni.ga matansa biyu kullum sai su yi ta min habai ci tun ban

gane da ni suke yi ba, har na gane.lnna ta ce,duk wadda ta yi miki ki rama ai zamansa suke
yi,ke ma haka.to ki fada masa mana. sallamar maman bishira ce,ta katse su.ta shigo suka gaisa
[01/10 10:34 pm] Abdul: (40)Zainabu ta ce,lnna wannan ce uwargidansa,ita dai tana taimaka
min sosai. lnna ta ce,na gode baiwar allah,amma su sauran ta ce,suna yi mata habaici.na ce to
ba zan lamunci wannan ba.sai in zo in same su har nan don ba ni da hakuri.maman bishira ta
ce,ita zainabu yarinta ke damun ta.lnda tana da wayo,za ta ke masa faran-faran,ta daina jin
tsoronsa. to da su kansu ba za su soma yi mata haka ba.tsoro za suji kar ta fada masa.kafin
wani lokaci za ta dan samu abin da ta samu.amma ita sai raki da tsoro.nan suka yi ta shirya
mata yadda wai a ta yi masa.jinsu kawai take yi, ba ta jin za ta iya kallon alhaji da wata kauna
ko birgewa.lta dai kullum zuciyarta tana gurin dan kyakkyawan farin saurayinta lsma'il.
Ismail shi da hamisu direba suna jin MIMI duk wayar da take yi,don tana yin maganarta kai
tsaye ne,ba tare da wani noke-noke ba.a nata ganin wannan malam lsmail din shi ne wa har da
za ta ji shakkar sa.ya san dai ita ba saar aurensa ba ce.ln ma ya ce zai kalle ta a matsayin mata
zai bata wa kansa lokaci ne.shi kuwa lokacin fargaba ne ya sake dabaibaye zuciyarsa.tabbas
shi rin guduwa take yi,ba ta zo zama ba.tambayar da yake yi wa kansa,yaya ke nan?yaya zai
yi,ta nina zai bullo wa lamarin?a filin ya ce,allah da kai na dogara. ya ciro waya ya sake
neman mahmud.bayan a dauka ya amsa sallamar, sai ya soma zolayar sa,ango,ango!ya ce don
allah ka bar fada min kalmar.da ma zan sanar da kai ne cewa muna hanya. yanzu haka mun
kusa kaduna.za dai mu iso dare yayi ne.don allah ina son ka dan tsaya a dakina,mu same ka a
nan.ya ce ba damuwa.sai ma in dan share kafin ku iso.cikin zolaya mahmud yayi zancan.tsaki
isma'il ya ja,ya canza harshe zuwa larabci, inda yake fada wa mahmud cewa MIMI din nan aka
bashi fa tare da sanar da shi halin damuwar da yake ciki da duk yadda abin ya faru a takaice.sai
dai bai ja sunan MIMIN ba.ya yi masa misali ne yadda zai gane.bayan sun yi sallama ne hamisu
ya ce,ka san allah malam in kana larabanci kyau kake kara yi mi kamar.
[01/10 10:34 pm] Abdul: (41)Balaraben da ma amma ku fulani ne ko?yayi murmushi tare da
fadin ta wurin uwa ba.da yake lsama'il saurayi ne kyakkyawa sosai,sak ya debo mahaifiyarsu
wadda ta kasance fulanin daura.ga shi da tsafta sosai,ga ilimin addini.na zamanin ma yana kan
nema,don duk biyun yake da burin ya hada.yana da tsare gida sosai.amma akwai farin jinin
jamaa.duk inda ya shiga mutane suna son sa.kodayake halayyar shi ta janyo don yana da son
jamaa da son yi wa jamaa nasiha.ba ya ganin kuskure yayi shiru.ko ina ya shiga da wuya ya bar
gurin bai samu wanda ya amshi lambarsa ba ya ce za mu dinga gaisuwa.tare da haka sam ba
ya son raini ko cin mutunci ko wulakanci.yam mata da dama suna son sa,musamman dalibai.sai
dai ba ya bada fuska, kasancewar ba abin da yake kai shi makaranta ke nan ba.zainabu ya
soma so amma ga yadda rayuwa take canzawa,abu ya juye,ya je abuja neman kudin aure,ya
dawo da mata.takwas daidai suka shigo kaduna.lsmail ya ce lallai su tsaya su yi salla. hamisu
ya rada masa cewa kar mu fita ta gudu. lsmail ya ce,ka rufe motar mana,ka je ka yi.ln ka idar ni
ma sai in je in yi.daga nan suka dauki hanyar katsina.jefi-jeri lsmail yana jin MIMI tana tambayar
khalil sun kusa kaduna. sha biyu da minti goma suka shiga katsina,lokacin khalil ya kira
MIMI wai bai sami motar katsina ba.sai dai ya sauka a kaduna. kuma ya je gida, mahaifinsa ya
yi tafiya,don haka kai tsaye ya wuce gurin hajiyarsu don ya san za ta hakura ba,sai ya bata
gold dinta.ya ce da safe zai kaita gurin wanda ya saida mawa.da haka ta yi ta yi masa fada da
nasiha. ba ta san shi ba abin da ya dawo da shi gida ke nan ba.ya dawo ne don ya dauki
mota.ya san ta da barcin safe.don haka sai da ya karya ya fita ya duba lafiyar motar,ya koma

dakinta ya ci saar ganin makullin motar tata a kan madubi.ya fita ya dauki motar.maigadi ya
ce,ina za ka?ya ce,hajiya ce ta aike ni in sha mata mai.sai bayan ya zo zariya ya tsaya ya sha
mai.yayi tambayar ina zai bi in za shi katsina?aka nuna masa wata mota aka ce ya bi ta.
[01/10 10:34 pm] Abdul: (42)Sha biyu da minti goma suka shiga katsina,lokacin khalil ya kira
MIMI wai bai sami motar katsina ba.sai dai ya sauka a kaduna. kuma ya je gida,mahaifinsa yayi
tafiya,don haka kai tsaye ya wuce gurin hajiyasu don ya san za ta tausaya masa.ya ba ta
hakuri,ta ce baza ta hakura ba.sai ya bata gold dinta.ya ce da safe zai kaita gurin wanda ya
saida mawa.da haka ta yi ta yi masa fada da nasiha.ba ta san shi ba abin da ya dawo da shi
gida ke nan ba.ya dawo ne don ya dauki mota.ya san ta da barcin safe.don haka sai da ya
karya ya fita ya duba lafiyar motar,ya koma dakinta ya ci saa ganin makullin motar tata a kan
madubi.ya fita ya dauki motar maigadi ya ce,ina za ka?ya ce,hajiya ce ta aike ni in sha mata
mai.sai bayan ya zo zariya ya tsaya ya sha mai yayi tambayar ina zai bi in za shi katsina?aka
nuna masa wata mota aka ce yabi ta.lokacin ne kuma ya kira MIMI ya fada mata ya taso daga
zariya.su kuwa yadda suka yi jiya,suna isa katsina hamisu ya ce,to yanzu kai ne zaka yi ta
mana kwatance har gidanku.haka kuwa aka yi. unguwar shiru.kowa ya rufe gidansa,tunda
lokacin sha biyu ta wuce,ga kuma yanayin sanyi.lsmail ne ya fita ya je ya turra kofar
gidansu,don ya san bata rufuwa da sakata.mahmud ya bude kofar dakin lsmail ya fito.kana ciki
ke nan? mahmud ya mika masa hannu tare da fadin gaskiya kun sha hanya. lsmail ya ce,to bari
mu kwaso mata kayanta.suka fito.tare da wayarsa yayi amfani ya haska,ya bude murfin gefen
da MIMI take zaune ya ce,ki fito.ba ta yi musu ba.ta sauko.sai dai tana saukowa ta toshe
hanci,ya haska mata har ta shiga zuren gidan.ya nuna mata dakin.ki shiga nan.a fili ta
ce,tafdi!ta shiga tana kallo ko'ina na dakin ta ce,na yarda dad ba ya kauna ta sam.ko
tantabaruna dakinsu yafi wannan.lsmail dai ya juya. jiki a sanyaye ya nufi waje.suka soma shigo
da kayanta.can ta rakube da bango a kan katifar,tana sake kallon ko'ina a yatsine, hawaye na ta
zuba daga idanunta,tana kara karfafa wa kanta cewa lallai gudu shi ne abin da ya halasta ta yi.
[01/10 10:34 pm] Abdul: (43)A wannan gidan,a wannan dakin za ta yi rayuwar aure?suka gama
shigo da tulin jakunkunanta da kayan takalmanta,suka loda su a gefe.lsma'il ya ce. mahmud
kuje da hamisu ya kwana gurinka.da safe zai dauki hanya.mahmud ya ce,ba damuwa.mahmud
ya kalle ta,to amarya,an iso lafiya?da sauri ta dago idanunta ta balla masa harara,tare da jan
dogo tsaki,ta ci gaba da latsa wayarta.haka suka fice.lsmail ya raka su mota, suka shiga suka
tafi.shi kuma ya dawo ya dauki buta ya fita waje yayi alwala ya shigo ya ra sakata.duk da yana
ta addua,gaban sa bai daina faduwa ba.yayi shafa'i,ya daga tsohuwar akwatinsa ya dauko
bargo ya kalle ta,ga abin rufa.ta yi masa hararar sama da kasa,ta ce,tunda dai ka ji ban ce
maka komai ba.to ka gode wa allah.amma kar ka sake ka kara yi min magana.ka ga na yi kama
da tsumman bargonka ne?lsmail ba ya daukar raini sam don haka ya ce,za ki iya ce masa
tsumma,amma naki sabon ina yake?kar ki cuci kanki,ki amsa ki rufa don ana sanyi sosai.ta yi
masa wata harara irin ta sama da kasa,ta ce,kar ka zata wai an daura maka aure dani, shi ke
yake ba da damar in zama matarka.ya ce,na nawa kuma?sai dai in kar a kara,amma aikin gama
ya gama.ta ce,ai ba bisa yardata aka yi ba,don haka babu aure.yayi yar dariya,yadda kika ce
ba.amma aure daram, musulunci ya kulla shi.kuma nine kadai zan iya warware shi ta hanyar
saki.ta ce,to maza ka warware shi.don ni da gari ya waye zan kama gabana.ya ce,da hakan za
ta yiwu tun daga abuja zan yi hakan.sai dai kash na riga da na yiwa mahaifiyarki alkawari.ta
daga murya,kai ni yanzu ba ni da wata mahaifiya,ban da iyaye,ban da kowa. mahaifiyar da tana

zaune aka gama cin zarafina.ban ji haushinta sosai ba,dama can na san ba wai tana so na
bane.don haka zan fi son in tafi inda babu wanda zai ji labarina. ya sake mika mata bargon,ki
rufa,sanyi yayi yawa.ta ce,ka bar shi in ya so sanyin ya zama ajalina.lsmail ya ce,ni ma dana
huta da tunanin nan. [01/10 10:35 pm] Abdul: (44)Ta kalle shi sannan ta ja dogon tsaki.tabarma ya shimfida.bata
bude sosai ba, don dama gurin da ya rage bai fi gurin salla ba.ya dauko wani zanin gado ya
shimfida,ya dauki filo daya ya saka.tunaninsa daya,duk tsananin sanyi,shi ba maabocin yin
barci da kaya ba ne,sai dai ya rufa.har ya kamanta haka,dole ya tashi ya cire riga,ya kwanta da
dogon wando.lta dai tana inda take rakube,iyaka dai kau da kanta tare da tabe baki.sama-sama
yake yin barcin saboda ba ya kwanciyar kasa har ya zuwa lokacin da ya saba tashi don yin
nafilfili.ya yi mika,ya saka rigarsa ya waiwaya ya kalle ta,ta takure,kanta yana cinyarta, wayar ta
fadi can gefe.da alamu sanyi sosai take ji.ya daga akwatinsa ya ciro malumalun dinsa a
goge,tana ta kamshin turaren da yake sawa a kayansa,ya lallaba,ya rufa mata.ya fita don yo
alwala. ko da ya dawo ta zame ta kwanta,ta kankame filo,ko fuskar ta ba a gani.yayi sallarsa,ya
gabatar da adduoinsa ga mahalicci.abin da yafi alheri kawai yake ta roka tsakanin sa da
MIMI.ya sake kwanciya yana fuskantar inda take kwance.bai iya ci gaba da barci ba,sai
hasashen me zai faru gobe da jibi?lna zai samu kudin da zai ci da ita irin cimar da take ci?lna
zai samu kudin irin tufaein take sawa zuwa kayan shafanta wanda a gabansa ta ce dubu dari
albashinsa shine kudin kayan safanta.a haka har asubhi tayi.ya kulle dakin ta baya,ya tafi
masallaci.a can suka hadu da yan uwansa,wato yayyinsa maza,suka gaisa. suka yi masa
murna mahmud ya zo ya fada musu cewa maigidansa ya ba shi yarinya.ya ce haka ne.babba
ya ce.amma ai mu ne ya kamata mu zama wakikanka duk lalacewarmu.lsmail ya gano sun
dauki zafi ne,don haka ya fada musu yadda abin ya taso amma duk da haka cewa kurum suka
yi,allah yasa alheri ba don sun yarda ba.daga nan gidan yaya amina ya wuce.idar da sallarta ke
nan yayi sallama,ta amsa,suka gaisa. cikin murna ta ce,sai ga labari mai dadi.ya ce,uhum yaya
ke nan.ta ce,mene ne uhum,kun zo da amaryar ne?ya ce,eh,tana dakina.amma matsalar ba ta
so na.
[01/10 10:35 pm] Abdul: (45)Ni ma sam bana son ta ko da wasa.nan dai ya fada mata komai.ta
ce.to allah dai ya daidaita ku.ka tashi ka je kar ta farka.yanzu to me zaka bata na kari?ya ce,sai
dai na je na ji daga bakinta,don ban san da me za ta karya ba.nan suka yi sallama ya nufi
gida.kai tsaye cikin gida ya wuce,fatu tana kicin ya ce mata ina kwana?ta dago ta dube shi,aa
yan abuja ne?sai muka ji aure.na ce kila dai don mu bamu da zanin zuwa abuja ne.yayi dan
murmushi ya wuce.saura suka fito su ma dai ya gaishe su,amma sai sakin magana suke
yi.dakin lnna ya shiga tana kwance,ga rushi a gabanta,ya zauna ya gai da ta.ta ce,sai kuma
mamuda abokinka ya zo mana da labarin aure.ya ce,eh.abin allah ya kawo shi kafin a yi shiri.ya
ce,to allah ya ba da zaman lafiya.mu da har muna cewa kila ka canza dangi ne.ya ce ba haka
ba ne.ni ma abin ya zo min ne ba shiri.tana ciki ai tana barci.ta ce,to kuma a nan dakin za ku
zauna?ya ce,eh,to sai dai yau zuwa gobe za mu fara neman daki.ya mike,bari in gani ko ta
farka. ya sa makulli ya bude dakin.har lokacin bata tashi ba.ya kira mahmud yana
tambayar sa ko hamisu ya tashi?ya ce tunda suka yi salla ya koma.ya bar shine ya dan
warware gajiya tunda hanya zai kara bi. sai karfe goma da kwata,lokacin tuni lsamail yayi
wanka,yayi shirinsa cikin shada mai ruwa siminti.yayi kyau yana ta kamshi.ta farka,mika tayi ta
yi tsaki.ya ce,ai kamata yayi ki yi adduar tashi daga barci,ba tsaki ba.yanzu da kin bude ido kin

gan ki a kabari fa?ta tashi zaune,da sai na fi murna fiye da in gan ni a dakin nan.da sauri ta
shiga neman wayarta.ta dauka ta soma kiran layin khalil,ya katse.ya kira ta, lokacin ne yake
fada mata ya taso daga zariya.ta ce, shi ke nan zamu yi ta waya har ka iso.ya ce,shi ke nan,sai
na iso din. lsmail ya ce,wai da wa kike ta yin waya ne?ta harare shi,na ce ka daina yin
min magana ko?ya ce,to ki tashi ki yi salla.ta harare shi,ta ja tsaki,ba zan

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login