Showing 18001 words to 21000 words out of 25770 words
Chapter 7 - CANJIN RAYUWA BOOK 2 COMPLETE BY HALIMA ABDULLAH MASHI
ga yadda wannan fim din zai
kare.suka sa dariya gami da shewa,ita da kawayenta.ta kalli wata hajiya nana,ba ni wayata!ga
ta nan kusa da ke in sanar da ubanta.ln ya zo fim din zai fi dadi kallo. shine nan ta fito da
gudu.a daf da hawa sama ne ta iso ta rungume MIMI ta fashe da kukan karya.lna kika shiga ne
yata?me ya sa kika yi haka?abdulkarim ya ce,momy sake ta mu je sama.sake komawa za ta
yi.abba cikin fushi ya ce,ki wuce mu je mana!don shi yana jin haushin momy nafisa ta taimaka
gurin lalacewar MIMI.momy nafisa ta sake ta suka iza keyarta zuwa sama. abdulkarim yana rike
da jakarta.momy nafisa cikin kukan ta kira alhajin ya ce? tana sheshekar karya ta ce,ka zo
gida,ga MIMI nan ta dawo su abba suna ta dukan ta ya ce,haka shi ne daidai.na gode musu.ya
kashe wayarsa. hajiya sauda tana inda take zaune ba ta tashi ba tunda ta yi sallar
azahar sai ko ga MIMI ta shigo da gudu.a gaban hajiya sauda suka yi mata duka.dama
kowannensu yana da haushinta.hajiya binta ce ta kwace ta.ko kallo bata ishi hajiya sauda
ba,bare ta yi magana.hasana da usaina sun yi jungum-jungum cikin tausaya mata ta rakube
gefen kujera tana ta kuka. abba ya ce,wawiya mara hankali kin bata sunanki a duniya.kin
zubar da mutuncin kaki.abdulkarim ya ce,sosai kuwa,duk yarinyar da ta gudu ta bar gidan
iyayenta,ai sunanta yar lska.hajiya binta ta ce, gaskiya baki kyauta ma kanki ba MIMI.ba ki yi wa
mahaifinki adalci ba lrin son da alhaji ya nuna miki,ln kina da hankali,ko wuta ya hura ya ce
MIMI shiga,ba za ki yi tsalle ki shiga ba,bare aure?
[01/10 10:34 pm] Abdul: (30)Sai lokacin hajiya sauda ta yi magana,ta ce. ai shi yasa haihuwa
ma da yawa take da dadi.ln wani ya saka kuka wani sai ya share maka hawaye.na'ima ta kai
yar albarka.allah ya bata zama lafiya a gidana,ke kuma sai ki zauna mu gani,wanda kika bijire
mawa din kika watsa masa kasa a ido,kika so ki kunyata shi zai ci gaba da jiyar dake dadi,gami
da nuna miki kauna kamar da. Daidai lokacin alhaji ya shigo yana cewa,ba ta da mazauni a
gidana.ta zo ta fita ta ko inda ta fito.na sallamawa duniya ita!hajiya binta ta ce,haba alhaji
wannan ma ai ba mai yiwuwa ba ne.ka yi mata afuwa,ta yi kuskure.alhaji ya isa gabanta,ke
khadija!na ce ki zo ki bar gidana!sunan uwata kika ci,ni uwata ta dade da mutuwa.don haka
yadda kika yi min abin da ba zan manta ba.haka nan ke ma zan yi miki abin da ba za ki manta
ba.MIMI ta mike ta zo gabansa tana kuka a tsugune,dad don allah ka yafe min.wallahi dad na
yarda na dawo,zan auri duk wanda kake so.dad ya ce,me abbas zai yi da ke a halin yanzun?kin
je kin kwana da wani ki zo ki ce kin yarda!cikin tashin hankali MIMI ta ce,wallahi ban kwana da
wani ba.na rantse maka dad! hajiya sauda duk dauriyarta ba ta san lokacin da ta soma
zubar da hawaye ba.su usaina suka je jikinta suna bata hakuri. abba ya ce,daddy to kawai ka
daura mata aure da shi wanda ta bi din mana.dad ya sake daga murya,har abada wallahi!ba
zata aure shi ba.yadda bata yi min abin da nake so ba,ita ma har abada ba zan taba yi mata
wanda take so ba. momy nafisa ta shigo tana kuka,tana ba alhaji hakuri. ya ce,na yi
rantsuwa,yau dole yarinyar nan ta bar gidana,ko da ita kadai na haifa.yarana ashiri da biyu. don
na rasa ita kadai bana jin cewa nayi asara. Hajiya binta ta ce shi ke nan za mu wuce da
ita gidana can malumfashi.ya ce,gidanki ko gidana?can ma gidana ne,don haka ba ta ba shi.ta
gama cin arzikina,don ko gidan mahaifiyarta na yi mata tsakani da shi.abba ya lumshe ido,yana
tunanin dad ya tsaurara da yawa.don haka ya ce,
[01/10 10:34 pm] Abdul: (31)Dad shi ke nan bari mu wuce da ita,in tafi da ita gidana.alhaji bishir
ya girgiza kai,ban lamunta ba.ln kuma ka yi hakan ba zan yafe maka ba.ka sa min idanu kaga
irin hukucin da zan yi mata.hajiya binta ta ce,don allah alhaji ni dai kar ka ce zaka kore ta a
gidanka,ka ji?momy nafisa ta shigo cikin kuka tana cewa,don allah alhaji kayi hakuri,ka yafe
mata,tunda na'ima ta riga ta auri abbas din sai a bar zancen.MIMI ta zo tayi shirin komawa
makaranta.cikin zafin rai,ya waiwayo,wace makarantar?nafisa za ki sa in tafka miki ashariya!ya
nuna MIMI,wannan yarinya don ubanta ta gama boko a gidana,ta je tayi zaman aure.yau din
nan zan aurar da ita ko ma ga uban wane ne.bana son kowa ya ce,min uffan.a kalle ni da
hukuncin da zan yanke duk inda na bada ta da sunan aure.na gindaya allah ya isa ga duk wani
ahalina da ya je,ko na sani ko ban sani ba.sai lokacin hajiya sauda ta daga ido ta kalle shi,duk
da halin MIMI,amma da da mahaifi sai allah.ta ce,alhaji kana ganim wannan hukuncin bai yi
tsauri ba?a fusace ya kalle ta,bana bukatar ki sa bakinki a cikin lamari,kamar yadda tun farko
kika ce ba ruwanki ke yar shawara ce.to don allah ina son shawarar ma ki bar ta.kina da kima
sosai a idona bana son mu fara abin da bamu yi a da ba.za ta yi magana.abdulkarim yayi mata
alama da hannu wai ta yi shiru.don haka sai ta kulle bakinta.shi kuma alhajin ya fita yana fadin
zata gane ba ta da wayo. Hajiya sauda ta kalli MIMI maganinki ke nan!hajiya binta ta ce,ni fa
ina zargin cewa MIMI shigo-shigo ba zurfi aka yi mata. momy nafisa ta ce,me kike nufi?ke nan
ni na sata bijirewa mahaifinta?hajiya binta ta ce,komai zai iya faruwa.yaran da suka tashi a
karkashin tarbiyyarki me zai sa na'ima ta lankwasu, amma MIMI ta kasa lankwasuwa?hajiya
sauda ta ce,ku bar zance nan.laifi dai duk na MIMI ne.ban ji haushin alhaji ba,duk hukuncin da
ya yanke mata.da ta tsaya a kan bata so,sai ya fi mata a kan gudun da tayi.wa ya san abin da
ya faru a gudun da ta yi?MIMI ta ce,hajiya ku yarda da abin da zan ce
[01/10 10:34 pm] Abdul: (32)Na rantse muku babu wani abu da ya faru da ni.ni kadai na kwana
a dakin da na sauka.abba ya ce,kin dai cuci kanki da kika sa kafa kika bar gidan mahaifinki,kika
bi wani kato. kuma duk sunan da aka kira ki da shi dole ki amsa. abdulkarim ya ce.alhakinmu ne
yasa ta yi wa alhajin haka.don haka ni duk mai zai mata ba zan ji haushi ba.usaina bata ce,yaya
ni kuma a nawa ganin tunda wannan ne karo na farko da sis MIMI ta soma saba masa da ya
yafe mata,sai in ta kara.momy nafisa ta ce,yawwa usaina,abin da ni ma nake so ke nan.
shi kuwa alhaji ya fita ne da niyyar ba ta duk wanda ya ci karo da shi.babu abin da ta fi tsana a
duniya kamar talaka,don haka za ta dandana rayuwar talauci.har zai fita gate,sai idanunsa suka
hango lsmail yana alawala,tamkar an tsai da shi ne,ya tsaya cak, yana kallon lsmail.sai ya tuna
ta taba furta masa cewa ta tsani lsmail. murmushin takaici ya yi,ya ce,malam lsmail yana kan
wanke kafafu,ya dago da azama ya karasa,ya mike cikin girmamawa yake cewa,alhaji barka da
arziki.na ga MIMI ta dawo.alhaji yayi yake,tare da cewa,barka ka dai.wato malam lsmail kamar
kai ne kake fada min an aurawa budurwarka wani ko?lsmail sam baya ko son tuna lamarin don
haka sai ya ce,ni ne alhaji,amma na dangana.haka allah ya hukunta.alhaji ya ce,wane ne
wakilinka wanda zai amsar maka aure?gaban lsmail ya fadi,cikin in-ina ya ce,alhaji ban gane
ba.ka ce mene ne?ya ce,kar ka damu,in mu i sallar laasar ka samu ko baba maigadi ne ka
wakita shi ya amsar maka aure.kar ka ji mamaki hausawa suna cewa wani hani ga allah baiwa
ne.sai kawai alhaji ya wuce ya bar lsmail tsaye,zuciyarsa cike da tambayoyi,amma bai san wa
zai amsa su ba. Maigadi da hamisu suka nufo lsmail suna cewa, malam lokaci fa,baka yi
kiran salla ba.maigadi ya ce,kodayake alhaji ne ya tsai da shi ko?lsmail ya ce,ku ji alhaji wai in
samu wanda zan wakilta ya amsar min aure,wai ko kai. su ma suka cika da mamaki.hamisu ya
ce,ko cikin yan aikin gidan ne tunda ya san kayi rashin budurwarka?
[01/10 10:34 pm] Abdul: (33)Isma'il ya ce,ni don na riga nayi fushi da soyayya, don ma kar in ce
na daina yin ta ne,a ce na dauka da zafi.hamisu ya ce,tunda ya zabe ka zai yi maka alkhairi kar
ka ce aa,ka yi shiru.lsmail ya ce,ba zan iya musu da shi ba,dana yi tun tuni.ku taya ni adduar
allah yasa in ci jarabawar don ina cikin gwaji.suka ce,amin allah ya sa ka ci. bayan sun
idar da salla,alhaji ma ba a nan yayi sallar ba.kamar minti goma,sai ga alhaji da abokansa hudu
da kuma kaninsa kawu shafiu wanda daki lsmail yake kwana tunda suka zo bikin.nan alhaji ya
ciro naira dubu talatin,ya mika wa maigadi.sadakin malam lsmail ne.ga wanda zai ba da auren
nan,ya nuna kaninsa cikin masallaci suka koma,inda aka daura auren KHADIJA DA ISMA'iI duk
ba su yi saurin dago wace ce khadija ba,saboda sunan MIMI ya boye.sun fito suna tambayar
juna,alhaji kuma da kaninsa suka shiga gida. daki lsmail ya shiga yana kai-komo a fili ya
ce,kaddara ta kawo ni abuja.ya dauko wayarsa yana ta zufa,ya kira mahmud ya sanar da shi
komai.cikin murna ya ce, allah ya sanya alherh.lsmail ya ce,ba na son wulakanci jaje ya kamata
ka yi min ba murna ba.mahmud ya ce bari in sanar da malam, in kuma je gida yaya amina in
fada mata.lsmail ya ce,ni damuwata ko daki ban kama haya ba ban san ma yaya zan yi
ba.amma komai ake ciki zamu yi waya.alhaji kam da ya shiga ciki,shi da dan uwansa kai tsaye
suka wuce saman MIMI,inda su hajiya sauda suke.alhaji ya ce,mika wa binta sadakin, duk suka
zura ido,hajiya sauda salla take yi,amma sai da ta ji kamar ta fadi.momy nafisa da ke biye da su
alhajin don tana falon kasa da baki suka shigo,ta ce,wane ne mijin alhaji?ya ce,zai shigo ai lna
take MIMI?hasana ta ce,ta shiga cikin tana wanka.ya ce,to in ta gama ku fada mata ta shirya
maza-maza alhajin ya sake sauka ya bar su nan cirko-cirko shi ma dan uwan ya basu kudin,ya
fice.
[01/10 10:34 pm] Abdul: (34)MIMI tana fitowa wanka,hasana tana shiga dakin ta ce,in ji dad ya
ce ki shirya.MIMI ta zaro idanu, zuwa ina?hasana dai ta ce,haka dai ya ce,amma ban sani
ba.riga doguwa ta zura ta zauna bakin gado tare da yin tagumi.hajiya sauda ta idar da salla ta
zabga tagumi,tana hawaye,lalle alhaji.jim kadan ya sake hawowa, wai ina su abba ne?usaina
ce ta iya cewa,sun tafi tun dazun.sun ce za su je suyi salla su wuce.ya sake sauka ya
fita.hamisu ya samu a bakin gate,ya ce, malam hamisu ga shi ka je ka cika tankin motarka.don
allah ka zo ka kai amaryar katsina.lna shi lsmail din yake ne?hamisu ya ce,yana dakinsa.ya
ce,to ka je ka ce masa na ce ya shirya kayansa,ya zo ina nemansa.yan kayansa da ma basu da
yawa,ya tattara su,ya zuba a jaka,ya fito ya tsaya a wajen su maigadi,shi kuma hamisu ya tafi
siyan mai. Alhaji ya sake fitowa ya yafito lsma'il da hannu. lsmail ya nufi alhaji cikin
faduwar gaba yana cewa,kaddara da ta same ni,allah ka duba min.ya isa gurin alhajin.ya
ce,biyo ni. suka ratsa falon.har yanzu da mutane,amma sun ragu ba kamar dazun ba. matakala
alhaji ya soma takawa,shi ma ya bi shi.ya waiwayo ya yi masa alama da kai. suna shiga
alhaji ya kalli usaina, kira min MIMI.hajiya binta ta ce,alhaji wai me kake nufi ne?momy nafisa ta
ce,kana nufin wannan ne mijin? usaina ta shiga ta same su da hasana ta ce,sis MIMI dad yana
kira.da sauri ta mike,kanta babu dan kwali,ta fito a firgice.duk zatonta zai ce ta koma gidan
mamanta ko gidan hajiya binta.tana fito ta kalle shi,ga ni dad.ya ce,ki shirya ga mijinki nan za ku
wuce.ta zaro ido,tare da fadin dad me ka ce?na shiga uku!dan da nan sai kururuwa,ta zube
kasa.su hajiya binta suka nufe ta, suka daga ta suna salati. Momy nafisa tana fadin sam
alhaji ba zai yiwu ba. tsaki ya ja,kar ki bata min rai nafisa.ku yayyafa mata ruwa ta farfado da
wuri.ku hada mata komai nata, katsina ba nan ba ce.ya kalli lsmail,wanda tsabar firgici ya hana
shi magana, ya ce,kai kuma daga yau na sallame ka daga aiki.
[01/10 10:34 pm] Abdul: (36)Kuka MIMI ta saka. momy nafisa ta shiga cewa, ai ni kuma na
shiga uku,watan kuma nawa ne tunda na'ima ta auri abbas, amma ia na ga dai ita MIMIN ba
son shi take yi ba. ta ja tsaki,ta fice fuu.su hasana ne suka shiga shirya wa MIMI kayanta na
sawa da irin abin da ya danganci na karatu.tana ta kuka alhajin ya sake sawowa lokacin hamisu
ya dawo.ya shiga har dakin MIMI ya ce,ta ba shi katinan ATM duka.ta ba shi tana kuka tana
rokon sa.ya amshi duk wani abu da ya danganci dukiya. gwalagwalanta kuma hajiya sauda ta
amsa. hasan suka ce hajiya da kin bar mata.ta ce,duk ku rufe min baki.suturun MIMI ma ba
duka suka dibu ba.an dai cika duk akwatunanta. takalma da kayan shafa duk an diba.sai lokacin
ta tuna da wayarta.jakarta kuma da kudi,ta kalli hasan, ina jakata?hasana ta fita falo ta dauko
mata.sai ta tura ta cikin wata jakar bayan ta cire wayarta wada take a silent.miss call din khalil
ya fi hamsin.kuka ta soma.a zuciyarta ta raya yanzun kam babu makawa za su gudu.
Haha aka yi ta fita da kayan MIMI ana zubawa a bayan mota da kuma bayan boot.lta kuwa
banda kuka,babu abin da take yi. hajiya binta ta yafa mata mayafi.dad da kansa ya tasa ta har
mota.duk 'yan bikin sun fito sun yi cirko-cirko suna kallo.ya ce,ko da sunan wasa ba na bukatar
sake ganin ki a gidana har sai in ni na bukaci ganin ki.ya dubi lsmail,kai ma ina kara ja maka
kunne ka kula,don na san sai ta ce za ta gudu.ya ce,insha allahu alhaji,har motar za ta tashi,sai
ga hajiya binta da gudu da kudin sadakin ta damka wa MIMI,ga shi an manta ne.MIMI ta amsa
don ta san tana bukatar kudin. motar babba ce,cikin ta da boot dinta duk kaya ne,sai gurin da
mutum biyu za su zauna,MIMI ta zauna,lsmail yana gaba tamkar zai saka ihu bakin ciki.alhajin
ya sake zuwa kusa da shi,na ga duk ka damu.yanzun mene ne babbar matsalarka? lsmail ya
dube shi da sauri,babbar matsalata ita ce inda zan ajiye ta.ya ce, ba kuna da gida ba?ya ce,
muna da shi,amma dakina a soro yake.alhaji ya ce,kar ka damu,ka ajiye ta a nan....!
[01/10 10:34 pm] Abdul: (37)Ya ce,shi ke nan alhaji na gode.tunda suka taso MIMI kuka take yi
har suka yi nisa.lsmail sai dai ya waiwaya ya kalle ta,ya kasa yi mata magana. tsakani da allah
shi tsoron ta ma yake yi yanzun. hamisu direba ya ce,ka bata magana mana.ai sai ka lallashe
ta.lsmail ya ce bar ta kawai ta yi ni kaina ji nake tamkar in saka kuka wallahi.hamisu ya saki
dariya,ya ce wane irin kuka kuma?kai ko yau da wanda ya kai ka farin ciki? tsaki ya saki,ya
ce,yau sai dai in daidaita ta da ranar da mahaifiyata ta mutu. hankalin MIMI ba ya tare da su
don haka ba ta san me suke fadi ba.ta ciro wayarta,ta cire ta a silent. layin khalil ta soma kira.a
ringing na biyu ya daga cikin sauri ya ce,MIMI kina ina?ta ce ka san wani abu ne?ya ce,aa ta ce
yanzu muna hanyar katsina.ka shigo motar katsina ka biyo mu,zan ta yi maka kwatance.za mu
bar garin nan.ya ce,shi ke nan.ln ban samu ta katsina ba,za hau motar kaduna.ln na sauka
komai dare zan hau ta kaduna.ln ban samu ba,zan je gidanmu,ko a boye ne in dauki mota.ta
ce,kar ka je gida a gan ka.ba zan so su tsare ka ba.abubuwa da yawa sun faru zuwa na gida.na
yi danasani matuka, amma in mun hadu za kaji.don allah ka yi alkawarin za ka zo?ya ce,in biye
da ke,kar ki damu.ta ki fada masa cewa an daura mata aure ne.kar ta kashe masa guiwar zuwa
gurinta. Su kuwa su hajiya sauda nan take suka soma shirin tafiya su ma.hasana da
usaina suka zazzabi kaya cikin kayan MIMI,suka fito.sam hajiya sauda bata bi ta kan alhaji
ba,ta ce, su tafi kawai ko a motar haya ne.momy nafisa dai ta biyo su tana don allah su kwana.
hajiya binta dama ko sallama ba ta yi wa nafisa ba.sauda ce ta tsaya yin sallama.nan take ta
dauki waya ta soma kiran alhaji.ya daga ta ce masa,ga fa su hajiya sauda nan za su wai tafi
gareji su hau mota.nan da nan ya kira hajiya sauda wai su jira karfe shida zai yi musu booking
din jirgi.ta ce, wa hajiya binta,ba komai mu jira.ai shi mijinmu ne.dole mu ji maganarsa.hajiya
binta ta ce,shi ke nan.
[01/10 10:34 pm] Abdul: [7/27, 11:10] A~PROF: (38)Shida daidai suka nufi katsina a jirgi.su
kuwa