Showing 6001 words to 9000 words out of 27745 words

Chapter 3 - AUREN RABA GARDAMA BOOK 1 HAUSA NOVELZ BY MAMUHAGGE .pdf

Mamughe   

22 Nov 2025

937


Itama miqewa tayi tareda Jan dogon tsaki tabar gurin bayan ta take qafarsa.

Rintse ido yayi cikin tsananin 6acin rai yanaji tsanarta tana ratsasa, karatun basuyiba kenan
aranar.




****************

iya damuwa yakai matukar maqura sbd shi mutum ne da baya tolerating nonsense amma lailah
takaisa iya maqura sbd irin mummunan wulaqancin datake zabga masa kullum gurin karatun
Kuma kullum suka zauna karatun basa farawa take fara rainin hankalinta kokuma tadau waya
tayita chatting tabarsa zaune sumtimes kuma wayarta zatayita yi da salman dinta.
Abun yakai idan suna waya da mum dinsa kullum tagane yana cikin 6acin rai a kwanakin.


Sati uku kenan kullum hakance ke faruwa,
Yauma hakance ta faru suna zama ta ciro waya tahau daukar photo tana cin cingum.

Kallon second daya yayi mata ya yamutsa fuska tareda Jan siririn tsaki Wanda ya sauka akan
kunnenta
Ta dago ahankali ta kallesa da niyyar zabga masa rashin mutunci sai taga yana mata wani
qyamataccen kallo Wanda hakan ba qaramin bata mamaki yayiba.

Miqewa tayi tsaye rai amatuqar 6ace tace,

Na rasa dalilin dayasa a Nigeria ake barin dabbobi na shiga mutane har asamu damar basu
aiki.

Daidai nan siyama da Yaya zubair tareda aishat suka iso gurin amma hakan baisa ta saurara
masa ba sbd dama babu Wanda lailah ke shakka ko shayi a gidan.

Cigagaba tayi da fadin,
All my life bantaba tunanin zan hadu da wannan bala'in ba idan nadawo Nigeria daban
dawoba sbd kwana a gidan nan in farka tareda kai is the worsed thing da yake faruwa dani a
yanxu.

Dafata siyama tayi alamar tayi hkr tabarshi haka,

Janye jikinta tayi tareda matsawa daf dashi sosai tace,

I hate you,
I hate you so very much.

Juyawa tayi rai abace tabar gurin zubair yayi saurin bin bayanta yana kiran sunanta amma ina
Ko alamar tsayawa batada.

Ga mamakin su siyama fuskar yaseer bata nuna komaiba saima lailar dayabi da kallon batada
hankali sbd ko shigar datakeyi yi yaqara tabbatar masada batada cikakken hnkli shi agurinsa.
Ra6asu siyama yayi ya wuce batareda yabari sun fadi abinda zasu fadaba.



Black pencil jeans be ajikinta da black armless shirt
Siririn gyale ne akanta dan gabaki daya ana ganin dogon gashinta data tufke a tsakar kai.
Fira suke zabgawa cikin nishadi a harabar gidan itada jabeer dan Ita tuni ta manta da wani
batun soyayya dayayi mata shikuwa saiya dauka ta amincene.

Zubair ne yashigo harabar gidan da motarsa yana hangosu ya hade rai sbd Sam ya tsani
ganinta da jabeer sbd bayason abinda zai kawo masa matsala gurin samun lailarsa.


Yana Parker mota ya fito tareda kallon gurin dasuke kaman ya share sai kuma yace,

Lailah I have sumtin for you idan kinaso ki sameni palon tsoho.

Miqewa tayi tana cewa,
Ka karbomin saqon ne?

Lailah you're not going any where,
And you zubair meye ne problem dinka sbd this is not d first time kake mun haka,
Koyaushe ka ganni da lailah saikasan yanda kayi kasa tabar gurin,
Dan haka daga yau karka sake.

O o jabeer sorry ba laifina bane laifintane dan tasan bana jimirin ganinta da kowa idan baniba
Kasan zuciya da abinda takeso.

Kallonsa jabeer din yayi da kyau dan zuwa lokacin ransa yafara baci yace,

Ka kiyaye abinda harshenka yake fada zubair
Lailah is my wife to be so be carefull wit ur words okey.

Wani iron shu'umin murmushi yasaki kafin yace,

Ina baka hkr jabeer domin ka makaro.

Yana fadar haka yabi bayan lailah domin tuni ta shige dan batanan suke tafka muhawararsu.






M & Z
[3/4, 14:04] +234 818 350 7088: 🌕🌕 AUREN RABA GARDAMA🌕🌕



Na

MAMUH GEEE🌕
And

ZINNIE SMART


41~45


BISMILLAHIR RAHAMANIR RAHEEM.




Abu kaman wasa zange ya girma dan kuwa rashin jituwa yashiga tsakanin zubair da jabeer dan
kuwa abun yayi tsananin da kowa yafara sani saidai uwar gayyar ita bata Masan akanta ake
fadan ba.


Yau abun yayi tsanani dan har abun yakai ha jabeer ya zabgawa zubair mari ya daga hannu zai
rama kenan abban jabeer ya riqe hannun ya rufesu da fada sosai.



Tsit palon yayi sbd kowa ransa amatuqar 6ace yake hardai Zubair da ummansa dasukejin

kamar su fashe tsabar haushi.

Ta 6angaren umman jabeer ma abun ya mata daidai da jabeer ya nunawa zubair matsayinsa.


Kallon kowa alh tsoho yayi cikin damuwa da fargabar abinda ke shirin faruwa da zuriarsa na
tashin hankali da tarwatsewar kai tun yana Raye bai mutu ba Wanda bazai taba daukar hakan
ba.


Gyaran murya yayi yakalli jabeer dayake babba yace,

Jabeer meya hadaka da zubair haka mai tsanani?

Sunkuyar da kai yayiyafaru
Alh akan lailah ne.

Me lailah tayi data hadaku fadan?

Ita nakeson zan aura?

Jinjina zancen yayi amma saiya juya gurin zubair yace,
Kai zubair Maya matsalarka da hakan?

Nima aurenta nakeso nayi kuma ni tuntuni ita nakeso.

Qara jinjina abun yayi sbd zancen yayi kamari.

LAILAHH,,yafada da kakkausar murya.

Na'am tace kai tsaye dan ita gaba daya zancensu bai shigetaba bare yadaga mata hankali.

Lailah cikinsu akwai Wanda yayi miki maganar yana sonki?

A'a.

To akwai Wanda kikeso acikinsu?

A'a

Toku dukkaninku kunji dan haka na soke wannan maganar daga yau kuma nabaku qanqanin
lokaci kowa ya fiddo mata a hada aurenku dana ayshat.

Abban jabeer ne ya gyara zama yace,

Alh inaga mai zai hana abawa jabeer din lailah tunda shine babba kum......

Kallon da alhajin ya wurgo masane ya sanyashi hadiye sauran zancen nasa.



Kwana biyu lailah bata saka ko dayansu a idontaba sai yau.

Zaune take a kujerar dake balcony dinta tana fira da sabuwar friend dinta dasuka hadu a
school itama kamar lailah take yar hutu da ji dakai.
Siyamace ta ukunsu dan ayshat bata cika shiga cikinsuba dan ta dan girmesu.

Red three quarter jeans ne ajikinta da farar top fara ta shaking material ko dankwali batada sai
gashinta data sako Danko dauresa yau batayiba.

Fira suke cikin nishadi tsautsayi yasata kallon saitin dakinsa gabanta ya buga da qarfi sbd
hangosa tayi daure da towel a qugunsa yafito wanka

Tsikar jikintace ta tashi sbd gabaki daya murdaden jikinsa daya bayyana ga farar fatarsa dake
sheqi.

Lumshe idonta tayi ta rufe ruf
Abu daya data lura dashi shi mutum ne maison iska sbd kullum windon dakinsa na gadi a bude
yake.


Da qawarta maryam zata tafi ta sauko dan rakata a Palo suka tarar da Anty basma na waya
suka wuce bayan sun gaisa.


A harabar gidan ma saida suka tsaya fira kafin maryam tana motarta ta fice.

Tana shirin juyawa motar jabeer tasako kai
Yana pakawa ya iso gabanta ya tsaya yana watsa mata wani shegen kallo da ba qaramin kyau
tamasa a kayan jikintaba dako gyale bata doro a kayan jikintaba.

Gaisawa sukayi yafara qoqarin kawo mata zancen soyayya tayi saurin katsesa da cewa,

Pls Yaya jabeer nafada maka banada wannan a cikin agenda na
In fact inada salman dina and I think I'm ok wit him.

Baiji haushiba yacigaba da janta fira hardasu darawa.

Hannu yakai zai tabo dimple dinta daya burgesa datana daria
Ba xato yaji an riqe hannunsa tareda ingizasa baya da qarfi.


A hasale ya dago sai yaga zubair na huci
Tsabar baqin cikin shima baisan sanda ya wazgawa zubair mari ba.

Zubair dama yanada haushin wancan Marin ga kuma wani
Shima hannun yadaga ya wazga masa nasa.
Dambe ne ya kaure tsakaninsu

Lailah kuwa ko ajikinta saima juyawa datayi ta shigewarta
A Palo tasamu Anty basma ta zauna suka hau fira kafin takira dad dinta suka hau fira tana zuba
masa shagwaba sbd baya qasar yayai tafiya.


Duk abinda yafaru a idonsa yafaru
Har shigewarta
Sai dai abun qara basa mamaki yayi yanda har wai ake fada akan wacan silly girl din.
Shima qyalewarsa yayi acewarsa qarfi sukeji tunda harsuna iya fada akan mace, macen ma
wadda shi bai dauka tanada abin burgewaba bare abin so.
UNBELIEVABLE,
yace ahankali ya yamutsa fuska.


Ayshat ce tafito tafara gani dan tuni abun yafara muni
Ihu tasaki tana kiransu umma.

Ummans jabeer CE tafara fitowa rude aiko itama tahau kuruwa tana qoqarin rabasu.

Umman zubair na fitowa tahau ihun
Wayyo jabeer zai kashe mata 'da

Kallonta umman jabeer tayi tace,

Amma dai hafsatu kinji kunya,
Shi zubair din da kike fada duk bashi ya kawo wannan balain ba.

Eh dolece tasa tunda Yaya za'a masa qwacen mata

Sa'insa ta kaure tsakaninsu suma saida Anty basma tajiyo hayaniya tafito tashiga tsakani amma
ina tuni gurin ya hautsune da tashin hankali.

Motar Abba nasir ce tashigo harabar gidan sun dawo shida alh tsoho daga gurin sallar juma'a.

A hanzarce Abba nasir din yafito mota amma daqyar ya raba tashin hankalin dan kuwa daga
jabeer din har zubair babu Wanda baiyi jina jina ba.

Shigowar motar baba abdlkrm ne yasa su umma tsaida nasu haya niyar barema sai alokacin
suka lura da alh tsoho.

Kowa taitayinsa yashiga

Qofar Palonsa ya shiga kowa ya rufa masa baya dan sauraren hukunci.







M & Z
[3/4, 14:04] +234 818 350 7088: 🌕🌕 AUREN RABA GARDAMA🌕🌕



Na

MAMUH GEEE🌕
And

ZINNIE SMART


46~50


BISMILLAHIR RAHAMANIR RAHEEM.



Tsit palon yayi bakajin motsin komai sai kukan a.c dake tashi ahankali.

Batareda tsohon ya dagoba yace,

Ayshat jeki ki kiramin lailah.

Miqewa tayi jiki a sanyaye tafice.

Minti uku saigata sundawo tareda lailah.,
Zama sukayi
ayshat a qasa ta zauna
Ita kuwa lailah kusada antynta basma ta zauna.

Rai a tsananin 6ace yafara fadin,

Yau koma bayar takai acikin zuriar nan ana fada harda duka,
Kuma qarin abin haushin harda Ku manyansu duk akan dalili daya.

Nayi baqin ciki sosai akan wannan sabon alamari,
To yau zanyi maganin wannan matsalar
Ke lailah inaso ki zabi daya daga cikinsu yanxu anan gurin.

6ata fuska tayi tareda turo baki tace,

Nifa gaskia banda time din wani soyayya ko aure dan haka ba Wanda nakeso acikinsu.

Umman zubair tayi saurin katseta da cewa,
Lailah kidaina fadar haka mana ki duba kiga yanda zubair ke....

Kunji tsiyar ai
Sbd ke kullum hafsatu ke kike kawo matsalar....

Abba nasir ne ya katsesu cikin 6acin rai yana cewa,

Ku kunzama mutanen banza tunda bazaku iya hana 'yayanku ba sai dai kuma ku hau naku abin
kunyar.

6acin ran alh tsoho ya qaru iya matuka ya miqe tsaye tareda basu baya ya fara magana cikin
kakkausar murya.

KE LAILAH nabaki nanda sati daya ki fitar da daya daga cikinsu su biyu idan ba hakaba wani
satin nakuma zagayowa zan raba gardama na aurar dake ga duk Wanda naga dama.
Yana gama fadar haka yashigewarsa dakinsa yabar baya da qura.

What"

Tace da qarfi cikin rawar murya kafin ta kalli Anty basma cikin wani irin yanayi.

Saurin kama hannun lailar tayi suka bar palon.
Da dai dai suka bar palon cikin zullumin ya zata kaya.


Suna shiga Palo tayi wurgi da wayarta a kujera tana wani fidda numfashi.
Dafata Anty basma tayi tace,

Lailah pls take it easy komai zaiyi daidai.

Anty kinajin abinda tsohon nan yafada,
Wlh ni banason kowa acikinsu in fact ni ban tashi wani aure ba,
Danasan wannan shirmen zan tarar a Nigeria daban dawoba.

Da qarfi ta kwala kiran safiya mai aikinsu
Aiko da sauri tazo dan tasan abu kadan ke hasalta lailar.

Bani ruwa mai sanyi yanxun nan.
To,, tace tareda juyawa da sauri. Lailah Waya ta dauka ta danna kiran daddynta Yana dauka ta
fashe masa da kukan shagwaba tana koro masa bayani.

Lallashinta yahauyi tareda tabbatar mata da yananan dawowa jibi.

Suna gamawa ta kira mum dinta itama tana dauka ta fara zuba mata abinda ke faruwa..

Lailahna kwantar da hankalinki ba abinda zai yiyu bane yi miki auren dole,so jst calm ur self
okey my love.

Nidai mum dan Allah kizo idan bakaba da dad yadawo zan tahowata america.

Kadaki damu my girl dazarar dad dinki yadawo baice komaiba zanzo nataho dake.
OK mum I love you.
I love u too my girl.



***********
Kwana biyu kenan da faruwar abin Sam lailah bata ko fitowa Palo sbd bata buqatar ganin kowa
abincinta ma saidai safiya takawo mata daki.


Yau tun safe ta shirya Cikin Morocco gown blue sai dan siririn gyale data daura.

Hand bag ce kawai ahannunta sai key din motar ta fito a Palo ba kowa
Dan haka bata tsaya shiga dakin Anty basma ba ta fice.

Zaune yake bakin gate yana hangota ya dauke kai sbd daga gani yau rashin mutuncin a kusa
yake.

A zazafe ta figi motarta ya bude mata gate ta fice.

School ta tafi suna fitowa lectures suka yi gurin shopping itada maryam dagacan
Bata dawo gidaba sai maraice.

A gajiye tadawo tun a gate ta bar motarta tareda jefawa yaseer mukullai tace yashigo da motar
ciki.

Karo taci da jabeer ta ra6asa zata wuce yayi saurin shan gabanta yana cewa,
Sis kwana biyu kinqi bari kowa yaganki,kin kuwa San yanda nayi kewar.....

Ya jabeer pls stop all this drama,
For god sake meyasa bazaku barni ba tunda nariga da nafadi ra'ayina.
Toh let me make sumtin very clear to u again,
Ni lailah banason kowa da aure acikinku so pls stay away,okey.

Dariyar zubair Ce tasasu waiwayowa dan basusan da zuwansaba.

Matsowa yayi zaiyi magana tayi saurin daga masa hannu tace,
Pls ya zubair you just heard what I huta,bana buqatar ko 'dayanku so kubarni na huta pls.

Juyawa tayi kan yaseer daya zo gurin a hasale tace,
And you what do you want?

Key yamiqa mata tareda juyawa.





M & Z
[3/4, 14:04] +234 818 350 7088: 🌕🌕 AUREN RABA GARDAMA🌕🌕



Na

MAMUH GEEE🌕
And

ZINNIE SMART


51~55


BISMILLAHIR RAHAMANIR RAHEEM.




Hankalinta bai qara tashiba saida dad dinta yadawo taga baice komai gameda hukuncin da
tsoho ya yanke saima lallashinta daya hauyi akan ta daure tazabi daya daga cikinsu.


Yau sati yacika dan haka tana sane taqi zuwa gaida kowa dan kowa gidan haushi yake bata.

Kwanciyarta tayi adaki tanaji wayarta na ringin taqi dagawa sbd tasan cewa xa'ayi take ana
kiranta.

Har bacci yafara janta Anty basma tashigo dakin tareda zama bakin gado tace,
Lailah ana kiranki a palon alh babba.

Ba Indi zani ni sbd gskia ni bansan dalilin dayasa ake son shiga life dinaba.

Yi hkr lailah muje kiji koma meyene kadaki manta daddynki na wajen.

Miqewa tayi tana 6ata fuska suka tafi.

Zama tayi tana yatsinar fuska sbd kowama batason gani.

Gyara murya yayi yafara fadin,

Lailah inason ki sanar damu wa kika zaba akan zancenmu na last week.

Turo baki tayi tace,
Nifa gaskia nafada banason kowa acikinsu barema wani aure.

Jinjina kai yayi yace,
To kisani kinyi wasa da damarki dan kuwa bazan janye zancenaba na aurar dake ga duk Wanda

naga damaba matuqar baki fidda daya acikinsuba.

Dan haka kowa ya shirya ranar juma'a zan aurar da ita ga duk Wanda nasama,
Haka kuma jabeer da zubair Ku fiddo da mata tare duka za'a hadaku Dana ayshat.

Da gudu tabar palon tana fasa ihu
Sauran jama'ar palon ma da dai dai suka fita sbd hukuncin baima kowa dadi ba bama kamar
dad dinta dayakeso tafara gama karatunta.



***************
3 days later,

Lallashin dunia dad da Anty basma sunyi mata amma taki daina kuka.

Yau maryam tazo tasamu ta lallabata dakyar suka fita yawo.

Sosai taji dadin yawon sbd tamanta matsalarta kuma maryam ta tabbatar matada wasace tsoho
ke mata dan ba yanda za'ayi ayi mata auren

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login
google.com, pub-9213700357025247, DIRECT, f08c47fec0942fa0