Showing 15001 words to 18000 words out of 27745 words

Chapter 6 - AUREN RABA GARDAMA BOOK 1 HAUSA NOVELZ BY MAMUHAGGE .pdf

Mamughe   

22 Nov 2025

943

sbd zazzabin daya fara saukar mata sbd tsoro,abincinma kasa ci tayi ta
takure guri daya tana hawayen son kasancewa tareda dadynta ko wani daga 'yan uwanta.
Inama ya jabeer ko ya zubair na aura daban auri wannan mai fuska biyun dabansan ko
wayeba.

Sallar isha'i aka kira ta miqe da kyar tayi.
Tana idarwa ta dunkule a gurin tana rawar sanyi.

Sabon kuka tasaki sbd tuna irin gata da lallaminta akeyi hardai idan batada lpia.
Amma yau babuma Wanda yasan halindatake ciki.




***********

Qarfe goma ya gama ganawa da baqinsa a babban kamfaninsa dake Lagos din,
Kai tsaye hotel din da dady yake yaje yana isa dady yakallesa yace,
Yaseer inason zanyi magana dakai.
Alh nasan abinda zaka tambaya shine ni waye?
Daga ina nake?
Me yasa nashigo rayuwarku amatayin mai gadi?

Hakane yaseer saidai koma meyene ni banajin wani mummunan nufi atare dakai sbd alh
babba ya Nina yarda da amincewa dakai sai dai kamar ko wane uba inason sanin komai
dangane dakai sbd lailata dake aurenka.





Mamuh & zinnie
[3/4, 14:04] +234 818 350 7088: 🌕🌕 *AUREN RABA GARDAMA* 🌕🌕


Na
Mamuh geee🌕
&
Zinnie smart


81~85
Agent Yaseer ahmad waziri shine cikakken sunana.

Saurin dubansa dady yayi yana cewa,
Ahmad waziri 'dan alh qarami?

Eh dady kaman yanda kasani alh qarami kakana da alh babba mahaifinku uwarsu daya ubansu
daya.

Tun bayan rasuwar alh qarami da dadyna nida mum da salman muka koma new York da
zama.acan naqatasa karatuna harna fara aiki a matsayin kwararen FBI officer kafin daga baya
nazama CIA agent.

Five years daga karbar duka 6 stars dina nakoma Miami tareda mum nabar salman ya qarasa
karatunsa acan america kafin yadawo Miami gurin mum sbd ni bancika zamaba.

Ina zuwa Nigeria sosai sbd dukiyarmu dake nan.
Alh babba yasan Inda muke kuma muna waya dashi sosai hakama duk Nazo Nigeria nakan xo

nagaidasa amma ba gidaba munfi haduwa a masallaci.
Ahaka wani kamfanin qera motoci suka aikamin da gayyata akan wani binciken sirrin Neman
maqudan kudade kimanin 200 million dasuka 6ata a kamfanin.
Bincike ya fara nuna alh naseer modibo shine first suspect dan haka na karbi wannan aikin
da kaina bansaka yarana ba sbd family nane ake magana akai duk da Ku bakusan niba.
Alh babba nakira nayi masa bayanin komai batareda dogon zanceba yace,
Ya amince Nazo nayi aikina na bincike batareda kowa yasaniba.



Hamdala dady yayi yana jinjina alamarin kafin ya kalli yaseer din yace,

Yaseer nagode Allah daya tabbatar da alherinsa akan lailata domin kuwa nayi farin ciki sosai
Jin kai din family ne.
Yaseer ina qara roqon alfarmar kula da lailah,
Nasan halin lailah shiyasa nake qara nanata maka,
Lailah marainiyace wadda ke buqatar tarbiyantarwar dabata samuba sbd zamanta cikin turawa.

Shiru yayi yana tunanin maganar dady dakuma alqawarin daya daukar masa na canza rayuwar
lailah xuwa mai nutuwa.
Tabbas zai canza rayuwarta amma da nasa salon dan saiya saitata kafin yatafiyarsa.


Airport yakai dady jirginsu na tashi ya juyo ya nufo masaukin nasu.


Yana parker mota ma'aikatan suka taso dakatar dasu yayi ta hanyar 'daga musu.

Tura qofar yayi yajita gam arufe.
Ransane ya 6aci yafara knocking.
Five minutes yana knocking babu motsi ko alamar zata bude.

Manager yakira ta wayarsa tareda cewa,
Akawo masa wani key din daikinsa.

Tun kan akawo key din yafara tunanin abinda ya hanata bude 'dakin.

Ana kawowa yamatsa gefe suka bude 'dakin batareda sun shigaba suka bar gurin.

Tura qofar yayi yashiga tareda rufowa
Kwance take aqasa kamar matacciya.

Qarasawa yayi tareda saka qafa ya turata sai yaga bata motsaba.

Durqusawa yayi da sauri ya jawota tareda girgixata nanma shiru ba motsi.

Da sauri ya cicci6eta ya kwantar da ita kan gado tarereda lullu6eta da bargo yaciro waya yakira
abokinsa Dr isma'il dake nan Lagos.

Kaida kawo ya Hau yi yana kallon agogo sbd gani yake Dr ya dade bai qarasoba.

Yanajin knocking yayi saurin bude kofar.

Zama gurin kanta shikuwa Dr yahau dubata.

Magani yaciro yabasa bayan yayi mata allura.

Fever ne kawai sai yunwa amma data farfado kabata tea ko abinci tukuna wainan drugs din
zataji sauqi insha Allah.
OK thank you Ismail.
Ure always welcome my friend duk da kayi aurenka without informing us.

Murmushi yayi yana basar da zancen.

Bayan fitar dr Ismail wanka yayo tareda saka farar vest da farin boxer's yakwanta gefenta.



************
Qarfe 'daya da Rabi na tsakar 'dare ta farfado cikin tsananin rawar sanyi.

Da....dy, da...dyna.

Daqyar maganar ke futa sbd kakkarwar da jikinta keyi.

Duqun qunewa tayi cikin jikinsa tana kakkarwa sbd bata hayyacinta gaba daya.

Ahankali ya bude ido tareda tashi zaune yana jijjigata ahankali yana kiran sunanta sbd gaba
daya bata hayyacinta sai sambatu take tana kiran dadynya da mamata data rasu.
Jawota yayi jikinsa yana shafa bayanta tareda lullu6esu.

Ahankali zazzabin yafara lafawa har bacci ya daukesu su duka.


Mamuh & zinnie
[3/4, 14:04] +234 818 350 7088: 🌕🌕 *AUREN* *RABA*
* *GARDAMA*🌕🌕

Na

MAMUH GEE
And

ZINNIEE SMART


86~87

Sanyin da yaji yamasa yawa ne yasa yabud'e idonsa, a hankali cike da barci,

Hasken da yaganine yasa yafahimci cewar anyi sallah,

Maida idonsa yayi kan Laila wacce tabi ta kwakumeshi, tamkar tana tsoron asaceta,

A hankali yafara zameta daga jikinsa...... cikin rashin sani hannunsa yata'ba wani abu mai tudu
da d'anbanzan laushi


Saurin kai idonsa yayi a gurin aikuwa kamar yadda yayi tsammani Boob's d'inta yata'ba wani irin
abu yaji tundaga 'kafarsa harzuwa Kansa....

Kasancewar wannan ne karo nafarko daya taba kai hannunsa jikin wata ya
macce,musamman ma a irin wannan gurin,


Jikinsa a sanyaye yajanye hannunsa yana 'kokarin tashi,

Murginowa tayi cikin jindad'in baccin tasake 'kwa'kumeshi,

Ido ya zubamata ido....ganin tasake komawa ne yasa ya mi'ke a hankali yanufi toilet d'in da ke
cikin d'akin domin yin alwala,

Yana fitowa yanufi inda Laila take,Sai faman baccinta takeyi hankali kwance,

Pillown da take kai ya daka,
A firgice ta farka had'i d kiran, Dady........

Dallah tashi kije kiyi sallah, yafad'a a tsawace had'i da doka tsaki,

Gun sallaya yanufa yad'auka ya shimfid'a had'i d yin i'kama yatada sallarsa,

Itakuwa ido ta zubamasa a zuciyarta sai Allah y isa takemasa,

Tagaji da zama sannan ta mike had'i da janyo hijab d'inta ta sanya tanufi toilet,

Harta fito yana kan sallayar saidai ba sallah yake ba dn Qur'an ne a hannunsa yana karatu,
cikin muryarsa mai dad'in saurare da
Kamala,

Maya finta tad'auko ta shimfid'a ta tada sallah,


Bayan ya kammala ne yamike yanad'e sallayar sannan yajuya yadubeta a da'kile yace,


Yakike jin jikin?
Yakike jin jikin??ta maimaita a ranta tace kai lallai wannan yacika d'an rainin
wayau.......maganarsa ce ta katseta,

Ko bakyajinane ko salon rainin hankalin ne?yafad'a in a serious tone

A da'kile itama ta amsa banajin komai,

Kafad'arsa yad'aga alamun I don't care,

Ordering d'in break fast yayi musu, ana kawowa ko kallonta baiba yad'au chips yafara ci yana ci
yana kur'bar ruwan tea,

Laila kuwa d yunwa ta kamata jikin ta har rawa yake Allah Allah take yafita ko tasamu itama tayi
break,

A fuska kuwa sai faman yatsina take kamar taga kashi tanata wani basarwa,


Yana gamawa yajanyo tissue yagoge bakinsa d hannunsa,

Mi'kewa yayi yanufi Barth room ,

Ai kuwa dama jira take yana rufe 'kofa ta nufi kayan break d'in d hanzari takeyin komai,gudun
kar yafito yganata,

Tayi sa'a kuwa harta gama bai fito ba ,koma kan gado tayi had'i da kwanciyarta,

Bata dad'e da gamawa ba yafito ,hamdalah tayi a ranta da baizo yasameta tana karyawa ba,

Idonsa ne suka sauka akan kayan break d'in murmushi yayi dn shi abun dariya yabashi a ransa
yace da kitsaya dai inyimiki tayi,



A fili kuwa bata fuska yayi yace ke ta tashi ki karya, dad'ine yakama laila ganin bai fahimci tayi
break ba,

Itama fuska ba walwala tace banajin yunwa,dariya ce ta tashi su'buce masa ganin yadda tawani
d'aure fuska,ala dole bataci komai ba,

Magani zaki sha kuma kinsandai ba a taking drugs ba aci komai ba so dole kitashi kici abinci
kisha mganinki,

Nifa bazanci ba, dan ba a dole,ta fad'a had'i da murgud'a baki,

Aikuwa dole kici, yafad'a daidai lokacin d yake saka aninin rigarsa,

To tunda ana dolene ni ka kyaleni ai dai cikina ne...............

Finciko ta yayi tunbata 'karasa ba, janta yari'kayi har gun da kayan suke sannan yadangwarar
da ita, hannu yakai zai bude warmer d'in da chips ke ciki,

Dasauri tari'ke masa hannun, nidai umhumm na ce maka na 'koshi tafad'a tana shirin yin
kuka,

Wata dariya ce tazo masa sai yayi hanxarin maidata, fuskarsa yad'aure yace ok tom leave my
hand,

Ni zanci da sauri tad'ago kai tace ba kaciba kuma........saurin yin shiru tayi ganin tana shirin
yin kato'bara,


Murmushi yayi sannan ya jaye hannunsa, had'i da d'aure fuska yace any way ni nafita idan
kingadama ki karya kisha mganinki idn kuma kinso ma karki sha matsalar ki ce,

Duk abunda kike bu'kata kikira za akawo miki......

Daga haka yasa kai yafita abunsa,

Yana fita wani irin kewar gida yashigeta ta fashe da kuka,

Tana nadamar dawowarta Nigeria d duk haka bata faru d ita ba...................











M&Z
[3/4, 14:04] +234 818 350 7088: 🌕🌕 *AUREN* *RABA*
*GARDAMA*🌕🌕


Na
MAMUH GEE
And

ZINNIEE SMART



🌕 *masoya* *AUREN RABA* *GARDAMA* 🌕 *hakika* *munajin* *dadin* *yadda* *kuke*
*nuna* *mana soyayya da* *wannan littafi* *muna godiya *kwarai d gske ba* *abunda zamuce*
*Sai Allah y barmu* *tare* ���😘


�🏻 _Dan Allah_ _kuma kuri'ka_ _mana uzuri_ _abubuwan ne _da_ yawa_ �🏻

*M* & *Z* *love* *u* *fans* *sossai* *sossai* � *�* �🌕



88~90


Haka, ta'kari kukanta tayi shiru dn wani irin zazzabine yarufeta lokaci d'aya,


Bai dawoba Sai guraren5na yamma, da sallamarsa yashigo tamkar bayason bud'e baki,

Ko kallon gun da take baiba jakar laptop d'insa yajanyo, yabud'e yacirota yafara danne danne,

Ga dukkan alamu Abu mai mahimmanci yakeyi, dn da sauri yakeyin komai,


Wayarsa ce tayi ringing, screen d'in wayar yakallah d gefen idonsa sunan da yaganine yasa,
yayi hanxarin dauka,


Assalamu'alaikum

Yafad'a a ladafce,
Bnji me akace a d'ayan 'bangaren ba nadai ji yana cewa.....................
Eh insha'Allah UMMA OK tom Sai munyi waya,
Ajiye wayar yayi yaci gaba da abunda yake,

Tarinda takeyine a wahalce sabida xaxxabin da yake jikinta yasa ya tuna ma d wata aba a
d'akin d'an karamin tsaki yaja,

Had'i da kai idonsa gefen da take ganinta a 'kudundune yayi cikin blanket, wani tsakin yakoma
ja had'i d cewa wata 'kila ko wanka bataiba 'kazama,

Mtsss...ke!ke
Jin shiru bata amsa bane yasa yamike yanufi inda take a fusace janye blanket d'in da tarufa
dashi yayi,

Hannunsa yakai zai d'ad'a mata duka dn shi a tunaninsa baccin rainin wayau take........

Wani hucin zafi yaji ya ziyarcesa hakan ysa yayi sauren janye hannunsa,had'i d zama kefen
gadon kad'an yad'an sake matsawa inda take yabubbuga pillow d'in da take kai,ke ke ke,

A hnkali ta bud'e idonta da sukayi jajawur tsabar kuka d tasha ga zazzabi kuma ,

Me yasameki.......
Maganarsa ce ta tsaya lokacin da tasaki wani tari d amai lokaci guda,

Baisan lokacin da ya rungumota jikinsa ba,aikuwa kamar jira take tasake shega wani aman
Sai a jikinsa,shikuwa tamkar baiganiba,

Sai dad'a ri'keta yake yana fad'in
Sorry sannu haka yaketa faman maimaitawa,

Saida ta amaye kaf abunda taci a cikinta sannan ta koma talafe a 'kirjinsa Sai ajiyan zuciya take
tamkar wacce tayi tsere,

Ganin tagama ne yasa yace, tashi muje ki wanke jikinki,

Jiki ba 'kwari tamike yataimaka mata ta shige bndaki ya had'a mata ruwa yace kiyi wanka kai ta
gyad'a masa,

Rufe mata 'kofar yayi sannan yanufi kan gadon ya yaye bedsheets d'in da blanket
yahadasu guru d'aya yacire rigarsa, dagashi Sai singlet,

Ma aikatan hotel d'in yakira yabasu kayan yace sukawomasa wasu, Minti biyar Sai gashi sun
kawo wasu karba yayi ya shimfid'a,

Yasawa d'akin room fresh nandann dakin yad''au 'kamshi, ta dad'e a toilet din kan tafito,

A hankali take tafiya kasancewar batajin 'karfin jikinta, sanyin 'kafartane yahad'e d tail's d'in
d'akin yaja ta luuuuuu tatafi zata fad'i da hanzari yayi wani irin sufa ya tarbota, Allah ytaimaketa
tafad'a kan 'kirjinsa madadin ta fad'i a 'kasa,

Ganin yadda tawani narke ajikinsa ne yasa ya 'bata fuska,

Ke dallah malama d'agani kinyi wani bakebake kamar kinsamu katifa mtss

Yafad'a had'i d d'an hankad'ata,haushi ne Yakama Laila,duk da tanacikin ciwo Sai da ta
mirgud'a baki sannan tace,mtsss da can ma wa yace kazo gun da nake harda wani tarboni ai
dakasani kabarni infad'i mana,

Tafad'a cike d tsiwa,jakar kayanta ta janyo tad'auki wata doguwar riga tanufi toilet,


shikuwa tunda
tafara mgana yake kallonta har ta nufi toilet d'in,

Wani irin killer smiling yayi yace hmmmmm yarinya zakiyi bayani,

Tana fitowa ta tada sallah domun rama sallolin da ake binta tana gamawa ana Kiran magrib
mikewa tayi domin tayi magrib d'in shi kuwa masjid d'in hotel d'in yanufa,

Bai dawo ba Sai after isha itakuwa tunda ta kammala sallolin tayi kwanciyarta anan kan praying
Mart d'in,

Fad'awa tayi duniyar tunani, ba abunda ke mata gizo kamar time d'in da take vomit takula da
yadda yashiga damuwa matu'ka me hakan ke nufi?? To kodai tausayi na yake?? Au, to dama
meye tunaninki Laila?zuciyarta ce kemata wannan tambayar, to Allah natuba Niko cewa yayi
yana sona basai na tsinka mai rashin mutumci ba hmmmmmm mudai koma KANO ai dole
yabani takardata,mtssss wannan 'kadararren auren wahala..........'karar 'kad'a yatsu da taji akan
fuskarta ne yadawo d ita daga duniyar tunanin da ta Lula

Shine du'ke a gabanta yana wannan murmushin nasa mai fad'ar mata da gaba.....he
yafad'a yana janyo ha'barta kasancewar ta kawar da fuskarta gefe,

What are u thinking for????uhmmm, *yaseer* yafara tausayina? *yaseer* yafara sona??
Meyasa *yaseer* yadamu dn banida lapia???

Hmmmmmm Laila mai bahagon tunani to ga amsoshinki abakin yaseer da kansa, yaseer, baya
tausayin wanda baya so Wanda saninkankine ni yaseer bnsan da 'kaddararen aurenki ba,
secondly, ke kinsan yaseer baya sonki dn ke ba maccen da tadace da shi bace,Abu na 'karshe
ni yaseer bankula ki dn komaiba da bakya da lfy Sai dn darajar iyayenki da
kikaci...............maganarsa ce ta tsaya ganin yadda take kallonsa hawaye nasauka akan
fuskarta,kallonsa take cike da tsana,jikinsa ne yayi sanyi amma hakan bai hanashi cigaba da
mganaba.........


Wata sakararriyar dariya yasaki yace to Laila kuka kuma ayyah Laila dazakiyi 'ko'kari ki
Adana hawayenki dan tabbas there is time for cry but not yet,hannunsa yasa yana sharemata
hawayen,

A zuciye tasa hannunta ta bige nasa hannun,

Allah yawadaran ragamun dakake i'kirarin kanayi,ko a mafarki zuciya ta tayi tunanin fara son
Wanda baidace da itaba .............saida ta ja majina sann ta cigaba, to saina hukuntata,ballanta
na kuma ace wai Kaine,time din kam I will a sure ta gwammace bata Raye, ta'karasa cike d
tausayin kanta kuka tasake rushewa dashi maiban tausayi,dun 'kulewa guri d'aya tayi tana
kiran, Daddy,


Shikuwa mi'kewa yayi cikin halin ko inkula yafara shirin bacci.........

Ummhuumm yafad'a da alamun tunawa d wani abu,kishirya 'karfe 7zamu tashi daga haka bai
sake cewa komai ba yayi kwanciyarsa,

Ita kuwa da zata iya cewa zatai bazaniba duk da ba tasan ina zasu ba amma zuciyarta na
fad'amata cewar ba KANO bane,

M&Z🌕👌
[3/4, 14:04] +234 818 350 7088: 🌕🌕 *AUREN* *RABA* *GARDAMA* 🌕🌕


®🌲 *REAL* *HAUSA

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login
google.com, pub-9213700357025247, DIRECT, f08c47fec0942fa0