Showing 12001 words to 15000 words out of 27745 words
Chapter 5 - AUREN RABA GARDAMA BOOK 1 HAUSA NOVELZ BY MAMUHAGGE .pdf
ta 6angaren sanin Rayuwa dakuma rashin sanin darajar komai
na Rayuwa.
Yaseer ga amanar 'yata nan inason ka 'doramin ita akan hanya ta sanin meye Rayuwa.
Nasan kaima bakayi na'am da wannan aureba sbd na lura da yanda kake cikin rashin nutsuwa.,
Zan baka gida da mota tareda aikinyi mai ma'ana,
Nidai roqona ka daramin lailah ahanya harzuwa lokacin dazaka samu mace daidai zabinka
saika qara da iya..
Ajiyar zuciya yayi ahankali yace,
Alh bana buqatar gida,mota da aikin yi sbd zan dora lailah akan hanya ta gari.,
Alh ni bana qarya ko 6oyon zance dan haka kayi hkr,
Maganar gaskia ni banada ra'ayi da lailah bare aurenta,
Haka nima sanin alh babba da girmansa aguna yasa na yarda nayi masa biyayya.,
Alh alh yasa nayi masa alqawarin tarbiyantar da lailah
Na amince sbd girmansa aguna.,
Alh kaima girmanka aguna babbane dan dai baka sani bane,
Na yarda dazan Dora lailah a hanya tagari kuma zanyi sbd Allah dakuma girmanku aguna.
Maganar kudi da gida kuma bana buqata inason abari ahakanma zan iya.
Nagode yaseer Allah yayi maka albarka yakuma baka ikon daurewa da halayenta.
Amin yace afili yana miqewa amma a zuciyarsa cewa yayi saina tabbatar 'yarka tayi kuka
arayuwarta harsaita roqi mutuwa da kanta.
*****************
Sati daya lailah bata zuwa ko ina sbd batasan yama za'ayi ta tambayi maigadi ba,ita batamasan
ya ake cewa maba idan za'a fita.
Wayartace tayi ringin tana dubawa taga bilal ne ke kiranta.
Tsaki taja ahankali kafin ta 'daga.
Hello bby gani nazo ina qofar gida.
Harzata kashe saikuma tayi tunanin gwara taje ko yawo yakaita tasha iska.
Miqewa tayi tareda Dora jacket akan handless gown dinta ta fito.
A waje yayi parking dan haka gate ta nufa kai tsaye ta fita.
Wayam tagani ba kowa.
Kiransa tayi awaya rai bace tace,
Meye haka zakacemin kazo....
Sorry lailah rashin sani yasani zuwa sbd maigadinku ya fito ga ganni nace masa gurinki
nazo yacemin kada nakuma zuwa gurinki wai ke matarsace an daura muku aure.
Wat"" tafada da qarfi,
Are u sure haka yafada maka?
Kashe wayarsa yayi cikin tsananin damuwa.
Har tuntube take sbd tsananin 6acin rai,
Kai tsaye 'dakinsa tayi sbd baya bakin gate din.
Fitowarsa wanka kenan yana daure da towel a quguns,
A fusace tayi kansa da jefo masa waya tana fafin I will teach u a very gud lesson today,
Hannu ta 'daga zatakai masa duka ya damqe duka hannuwanta biyu tareda matseta a bango
yayi mata runfa........
M & Z
[3/4, 14:04] +234 818 350 7088: í ¼í¼•í ¼í¼• *AUREN RABA GARDAMA* í ¼í¼•í ¼í¼•
Na
Mamuh geeeí ¼í¼•
&
Zinnie smart
71~75
Jikintane yadau rawa sbd haduwar jikinsu gashi yaseer din bashida kaya itakuma basu kayan
arziqine ajikintaba.
Shikuma kallonta yake cikin kyama yace,
Ki tattaro hankali da juriya kisawa empty brain dinki sbd am going to make your life a living
hell,
I will become ur worst nightmare.
Cikin tsananin mamaki ta kallesa sbd abinda yafada ya bata mamaki sosai.
Ya akayi yake iya wannan turancin na qwararrun turawa.
Wurgi yayi da ita yana cewa,
Get out foolish girl.
Baqin ciki ya danne mata zuciya Allah ya isa tace da qarfi tareda miqewa ta fice a fusace.
Kaida kawo tahauyi a dakinta tana tunanin irin cin mutuncin dazatayi masa dazaisa ya gudu da
kansa yabar gidan.
2 days Ltr
Zaune take a kan dinning tana qoqarin kai pancake bakinta dad yace,
Lailah meye saqonki gurin mum dinki yau zantafi Kaduna acan zanhau flight zuwa Lagos
gobe na wuce can.
Saurin aje spoon din tayi tace,
Dad pls zani.,
No my girl bakisan yanxu kingirma ba,
Kinzama matar aure.
6ata fuska tayi tace,
Dad ni kadaina fada.
Murmushin manya yayi yace,
Lailan dady learn to be a gud wife and daughter,
Sake kwa6e fuska tayi
Dad din ya shafa kanta yace,
Just give it a try my girl,
Trust me you'll experience sumtin new in life.
Safiya ce tazo cikin ladabi tace,
Alh ga yaseer nan dakace akira.
Ok kice yashigo.
Cikin nutsuwa yashigo palon tuni qamshinsa yacika palon,abinda yakeba kowa mamaki da
yaseer din shine fitinannan qamshinsa da Kwarjininsa.
Dauke kai tayi tana 6ata fuska.
Shikuwa gaida dady yayi cikin girmamawa.
Lpia kalau yaseer,
Bismillah zauna muyi breakfast.
Ba musu yaja kujera cikin wayewa ya zauna tareda gaida Anty basma.
Cikin salon yaudara yace,
Lailah kintashi lpia?
Sosai ita kanta tayi mamaki sbd tafi kowa sanin girman kansa duk da yana maigadi.
Murmushin jin dadi dady ya yana cewa,
Lailah kece yakamata ki gaidasa bashi yakamata ya gaidakiba.
Toh. Kawai tace tana turo baki.
Coffee ya kur6a yana wani irin murmushin qeta.
Sbd yasan duk wannan iskancin takusa dainasa.
Dady dan Allah kaje dani naganosu mum dasu afra nayi missing dinsu sosai kuma banaso
tasan da wani zancen aure sbd ranta zai 6aci.
Miqewa dad yayi yana cewa,
Baxaki ko inaba sbd yawo baikacekiba yanxu
Kaikuma yaseer mutafi ko.
Kallon Anty basma tayi alamar tambaya.
Antyn tayi saurin cewa,
Yes tareda yaseer zashi Lagos sbd yanaso yafara koya masa business.
Dan qaramin tsaki taja kafin ta miqe tayi hanyar hayewa stairs tana cewa,
Nidai dady bara na shiryo kobaka tafi dani America ba saiku barni Kaduna nayiwa hajiya
babba kwana biyu.
Kallon yaseer dady yayi zaiyi magana
Yaseer yayi saurin cewa,
Ba komai zata iya zuwa idan nadawo daga Lagos saina biya nataho da ita.
To shikenan tunda ka amince.
Motar dady suka tafi da ita Kuma yaseer ne ke tuqin
Lailah na gefensa dady na baya.
Suna isa Kaduna kai tsaye gidan haj babba suka nufa.
Suna pakawa maigadi yataso da sauri yana musu barka da zuwa kafin yasanar dasu yau
dinnan hajiya babba tayi tafiya gidan bakowa arufe yake.
Shiru dady yayi kafin yace,
Lailah kinga rashin jinki abinda yaja tunda dakinyi zamanki dashikenan gashi yanxu
bamusan yazamuyi dakeba kuma lokacin tashin flight dinmu yakusa.
Yi hakuri dady bansan bazamu sameta bane.,amma ai ba matsala muje airport din Ku
wuce zan iya kai kaina abuja tunda ba dare neba.
Wat". Kina tunani xanbarki kija mota ke kadai daganan har abuja.
Daddy Allah zan I......
Just shutup lailah.
Yaseer muje airport pls kafin murasa flight.
Suna isa yaseer yafice motar yanajin takaicin lailah sbd tanason 6ata masa plans dan yaso ya
huta a Lagos din idan dady ya wuce,afterall yaso ya gana da wasu baqinsa daya bawa
appointmnt.
Ticket yasiyo guda uku yadawo tareda Wanda zai karbi motarsu ya aje.
Kallonsa dady yayi yace,
Yaseer yakuma haka naganka da tickets kuma harguda uku.
Zaiyi magana aka fara sanarwar passengers na girjin Lagos su hanzarto.
Murna tafarayi dan tasan shikenan dady zatabi america dasunje lagos din.
Qudurtawa tayi idan tasamu ta tafi ba Inda zata dawo.
Mamuh & zinnie
[3/4, 14:04] +234 818 350 7088: í ¼í¼•í ¼í¼• *AUREN RABA GARDAMA* í ¼í¼•í ¼í¼•
Na
Mamuh geeeí ¼í¼•
&
Zinnie smart
76~80
Tun a airport suke ganin canje canje daga yaseer din sbd yanayinsa gaba daya bai nuna cewar
shi baqo bane a wannan fannin.
Itadai lailah ko ajikinta dan yaseer din baya gabanta bare wani baqon alamarinsa.
Dady dai alamarin ya girgixasa sosai dayaga an wuce dasu v.i.p ana nan nan da yaseer din
shikuma yana basarwa sbd kada dady yagane.
Dady kuwa yana lure da komai amma sbd ya gasgata tunaninsa saiya dan dubi yaseer din
yace,
Yaseer ina duba yanayin lapiata idan nace nabi jirgin america kai tsaye zan jigata dan
haka jirgin yawo xanbi.
Alh Ai gwara ka hau jirgin america kai tsaye tunda 8 hours ne amma idan kabi na yawo zaka iya
20 hours baka isa ba kokuma kwana ma sbd ana hutun 1 to 2 hours ako wace qasar daxa'a
tsaya.
Ajiyar zuciya dady yasaki tareda Jingina da kujerarsa yana tsananin mamaki..
Tabbas yaseer yana yawon qasashe tunda yasan yanda abubuwan suke,.
Komadai yayane zan tunkaresa kai tsaye dan yasan koshi din waye idan yadawo dan yanxu ba
lokaci.
Direba na musamman yazo daukarsu daga mutanen dady aka kwashesu zuwa wani babban
hotel.
Dady aka fara ajewa Kafin yacewa,
Driver akaisu yaseer wani hotel din dan bazai zauna hotel daya dasuba.
Batadai ce komaiba sbd duk a iya tunaninta 'dakuna daban daban zasu zauna.
Kallon direban yaseer yayi ya fadamasa sunan wani mahaukacin hotel yace yakaisu can.
Saurin kallonsa direban yayi yace,
Yallabai ba'acan aka kama muku 'dakibafa.
Nasani muje.
Kallon gurin lailah tayi ta maido da kallonta ga yaseer dantayi magana amma tuni ta hadiye
zancenta sbd wani irin 'daure fuska da yayi ,ga wani irin kwarjini da yayi mata harsaida gabanta
ya fadi sbs nantake ya canxa yakoma wani irin dan qwalisa.
Kallon drivern yayi yace,
Yatafi da kayansa baya buqatarsu.
To yace yana godiya shikam.
Kallon lailah yayi cikin tamke fuska yace,
Ki shiga hankalinki bcos if u do sumtin stupid koda dadynki zai dawo kin rasa qafa da
hannuwa dan kakkaryaki zanyi,foolish girl kawai.
Kallonsa take kamar ta6a66a sbd takasa tantance mafarki take ko kuwa.
Ma'aikatan gurin ne sukazo da sauri suna fadin,
Welcome sir.
Hannu yadaga musu tareda cewa,
Su dauko 'yar qaramar jakar lailah.
Tafe yake lailah na gefensa ma'aikatan na biye dasu da jakar lailah.
Suna shiga daidai reception din managern gurin ya iso gurinsa da sauri yana fadin,
What a pleasant surprise sir.
Cikin miskilanci Dawson taqaita zancen yace,
She's wit me abata room a VIP floor.
Sorry sir there's no room a VIP floor,infact yau gurin acike yake da governors and senators
sbd gobe akwai daurin auren 'dan governor din lagos,room dinka ne kawai empty a hotel dinnan
shima dan yazama nakane ba'a ba kowa shiyasa.
But za'a iya sa driver yakaita wani hotel nan kusa if u're.......
Tsit yayi tareda cewa, sorry sir
Sbd kallon da yaseer din ya watsa masa.
'Dayan ma aikacin ne yadanyo qasa qasa da murya yacewa managern,
Matarsa oga ce fa,they just got married.
Oh my god,am really sorry sir bansan kayi aure ba,am sorry and congratulations to
you sir.
Ku kuma kukai madam da kayan a room din sir dake last floor VIP.
Da sauri ta bisu sbd daf take da faduwa sbd sabon alamarin datake gani gashi batason ta
zuba masa rashin mutunci cikin gurinnan sbd bada kantane zatayi dan kaf gurin taga na
manyan yan boko ne,amma zaizo dakin yasameta saita zuba masa rashin mutuncin dazai kasa
bacci yabar mata dakin dan bazata kwana daki daya dashiba.
Mamuh geee & zinne smrt
[3/4, 14:04] +234 818 350 7088: í ¼í¼•í ¼í¼• *AUREN RABA GARDAMA* í ¼í¼•í ¼í¼•
Na
Mamuh geeeí ¼í¼•
&
Zinnie smart
76~80
Sosai tsarin dakin ya birgeta sbd ya hadu,komai na cikinsa tsarin na 'yan highclass ne.
Toilet ta fada tayo wanka tana fitowa yana shigowa 'dakin.,
Saurin ja da baya tayi tana harararsa tace,
Bakada idanuwane dazaka tsaya bayan kaga a yanayin danake.
Karamin tsaki yaja tareda datse wayar dayake ya juyo ya kalleta tun daga sama har qasa ya
kumajan tsaki yace,
Let me clear sumtin to you,
Nan gurin gurinane,and all the people over here respect me,
So ina fada miki ki tattara nutsuwa kisawa empty Brain dinki because if you do sumtin stupid
anan gurin to ki kuka da abinda zan iyayi miki.,and abt d looking bana tunanin kinada abin kalla
ko burgewa a jikinki.
One last thing shine idan kikamin rashin kunya anan,hadaki zanyi da masu aiki suyi abinda
sukaga dama dake.
Tsit tayi tana kallonsa cikin sanyin jiki da wani irin tsoransa daya dirar mata lokaci daya sbd
rashin sanin koshi din waye.
Qofar Toilet ya nufo a hankali ta janye daga qofar tana qanqame jikinta.
Tunanin gida tahauyi tana qoqarin zubo hawaye.
Wayarta tahau laluba amma tuni ya 'dauke wayar ya boye.
Hawaye tahauyi harsaida taji yana qoqarin fitowa tayi saurin bude wardrobe tajawo Riga
daga Jakarta tayi saurin sakawa.
Kallon kanta tayi akaro na farko kenan dataji haushin qananan kaya arayuwarta sbd rigar
iyakacinta cinya gashi batada hannu,
Qarin abin haushi duka kala hudune kayan kuma duka qanana ne sbd haka take shigarta a
gidan haj babba sbd babu kowa a gidan daga hajiyar sai masu aikinta su biyu.
Rasa abin sakawa tayi tai sallah sbd batada hijab ga kuma yanayin kayanta.
Ta madubi takallesa daidai lokacin daya fito wankan.
Hade yawu tayi daqyar sbd tsoro da kayar mata gaba da qirarsa ta majiya qarfin maza data
gani sbd towel ne fari fes daure a qugunsa.
Shikuwa ko kallan 6angarenta baiyiba ya hau shirinsa tareda fesa fitinannen turarensa daya
saka tsikar jikinta tashi.
Sallah yayi duk tana zaune tana kallonsa ta mirror.
Yana gamawa ya miqe tareda cire jallabiyarsa ya bude akwatin da yashigo dashi bayan
tabarosa reception din hotel din.
Qananun kaya yasaka wainda suka masifar yimasa kyau.
Agogon diamond qirar kamfanin Rolex yaciro yasaka tareda fesa turare ya nufi qofa xai wuce
da sauri tasha gabansa zata fara zuba masa masifar ita gurin dadynta zata amma yana kallonta
tayi saurin hadiye zancenta sbd tunowa da abinda yace.
Cikin danne masifar dake cinta tace,
Nifa banyi sallah ba sbd banida kayan dazanyi sallah dashi,kuma inajin yunwa, sannan
inaso nidai akaini gurin dadyna sbd banason nan gurin.
Kallonta yayi awulaqance tukun yace,
Ki daga waya gatacan ki kira boutique na cikin hotel din kifadi abinda kike buqata za'a kawo
miki,
Abincinma idan kinkira zasu kawo miki.maganar zuwa gurin dady kuwa kin makaro dan yanxu
jirginsu zai tashi basai gobeba.hakama idan kikayi kuskuren fita anan Lagos akwai wa'inda suka
fiki iya rashin mutunci dan yankaki zasuyi su cire bakin rashin kunya.
Ficewarsa yayi yana qara gyara daurin agogonsa.
Da qyar ta tattaro nutsuwar kiran boutique din tareda restaurant tayi making order sbd gabaki
daya ta tsorata da garin sbd cewarsa ta za'a iya saceta.
Sallah tayi da qyar