Showing 303001 words to 306000 words out of 318483 words
Chapter 102 - ABBAN SOJOJI (Takun Karshe) COMPLETE BY BOSS BATURE.docx
kanshi ya zura matasu ajikinta,cikin sanɗa ta fito daga part ɗinshi ta sauko downstairs,sai da tafara zuwa kitchen ta ɗauki mayafinta tukunna ta wuce ɗakinsu,
Bayan Kammaluwar Sallar asuba,matafiya suka shirya tsaf,domin tafiya Airport,Dukansu matan suna sanye cikin jallabiya baƙa,Sun laga gyale akansu,Sgr Da Omar suna sanye cikin Shadda,Junaid kuma yana sanye cikin suit farare,
Gaba ɗaya mutanan gidan Sun hallara a babban Falon gidan, lokacin da kowa ya kammala fitowa,Suka ɗunguma izuwa Wajen da motocinsu suke,kusan dukansu zasu yi masu rakiya,Amma banda Amaren Gidam,tun anan Sukayi bankwana dasu,Amrish tasha kuka sosai,haka Amal ma,
A motar dr harris,gwaggon katsina da abu suka shiga,tare da saude wadda ke zaune A gefenshi
Abba kuma tare da mommy suka shiga motar Fawan,
osman da adam a motar kanal Yusif suka zauna,
Najeeb kuma a motarshi Talal Da junaid suka shiga,
Sehrish da Jahad da hosana,Suna zaune a motar abusufyan Dakanshi zaiyi driving ɗin ya'yanshi,
Hajiya azeema tana acikin motar su twins,Jahan ne ke a mazaunin driver Ayaan na a gefenshi,
Akwai motocin Security dake gaba da bayan motocinsu,
Sgr yana acikin motarshi,motarsu Marshal Da major tana a bayan tashi,
Slowly motocin suke tafiya ajere har suka fito daga cikin babban gate ɗin gidan,koda su Jahad da sehrish suka ga An fita daga gate ɗin gidan sai suka fashe da kuka atare,Abusufyan sai lallashinsu yake yi,Shi kanshi daurewa kawai yake yi,idanuwanshi cike suke tab da kwalla,
Lokacin da suka ƙaraso Airport ɗin at the same time su kayi parking ɗinsu,A tsanake duk suka fito daga cikin motocin,idanuwan kowannansu Yana akan Katafaren Privet jet ɗin da aka tanadar masu,wanda ya kasance Mallakin Rafayet ne,jigunannan gaske,Mai ɗauke da Sunanshi Ajiki da manyan haruffa akayi rubutun SGR
Tunkafin su iso Airport din junaid keta kukan rabuwa da abbansu da ƴan uwanshi,Kowa jikinshi yayi sanyi,
Rungumeshi abba yayi sosai ajikinshi yana shafa sumar kanshi,
"Junaid so kake nima inyi kukan ko"?
Cikin shessheƙar yace"Abba bansan na tafi nabarka,"
"Junaid aduk inda kake a faɗin duniyar nan,inaso ka sanya aranka cewa Muna atare da juna,zan dinga zuwa akai akai ina ganinka,"daƙyar abba ya samu ya lallashe shi,bayan ya saki abbansu Ya rungume Fawan yana kuka,kowa yayi tsaye cirko cirko gwanin ban tausayi,
Bubbuga bayanshi fawan yayi"be a man mana,Kada ka bani kunya,dan Allah kadaina kukan nan,"
"Ya fawan,tafiya fa zamuyi,"
"Tafiya ae ba mutuwa bace junaid,just calm down ur mind,Da zarar babynka ta haifu zan wanko ƙafa inzo suna"cikin raɗa yayi mashi maganar a kunnanshi,har sai da junaid yayi dariya,bayan ya rabu da fawan ya rungumesu twins atare yana raira masu kuka,
"I love u so much Ya jahan da Ya ayaan,Zanyi missing ɗinku sosai,"
Atare suka haɗa baki wurin cewa"We love u so much Our shagwa6a boy,"
Bayan yabar wurinsu Ya nufi kanal Yusouf yayi hugging dinshi"yaya yusif yanzu shikenan.....'
"Junaid banaso kana zubar da hawayenka,inda rai da lafiya wata rana zamu zo,kaima kuma zakazo,"
"Amma ae bazan dinga ganinku kullum ba,"ashagwa6e ya ƙarasa maganar,ba wanda junaid ya bari,ɗaya baya ɗaya sai da ya rungume kowa hadasu uncle da hajiya azeema dasu Osman da Najeeb,
Bayan ya kammala nashi,Su Sehrish suka Soma bin kowa suna yi mashi sallama,Gwaggon katsian hada kukanta,Za'a tafi da ƴa'ƴan abusufyan ɗinta,Sosai ta rungumesu ajikinta,Suna kuka tana kuka,babu mai lallashin wani,daga wurin gwaggo wurin hajiya azeema suka wuce,Ta haɗasu duka ta rungumesu,tana lallashinshu,daga wurinta suka nufi wurin Mommy,Itama ta rungumesu ajikinta,daga wurin mommy suka nufi wurin saude ta rungumesu,Sai da suka gama da kowa tukunna suka nufi Oummansu,ta haɗasu duka ta rungumesu,hawaye jaga jaga akan fuskokinsu,bayan sun gama da matan suka nufi wurin Daddynsu da abbansu,Kowa ya sanya masu albarka,ɗaya bayan ɗaya suka bi mazan suna yi masu bankwana,a lokacin Junaid yana manne da oummansu,ta rungumeshi sosai,kamar zai koma cikin cikinta,
Sai daga bisani Omar da Sgr suka soma bin kowannansu suna yi mashi bankwana,Lokacin da suka zo wurin abba Ya shafa sumar kan kowannansu kafin yace"Omar Rafayet"ya ambaci sunansu,Suka amsa mashi,
Kafin yaci gaba da cewa"A matsayina na mahaifinku babu abunda banyi maku ba,duk wani nauyi naku dake akaina na sauke shi,Saura ku ya rage naku,Ga Amanar ƴan uwanku nan,Ku kula da rayuwarsu,saboda ƙaunar dake a tsakaninku dasu yasa zasu bar kowa nasu,iyayensu danginsu,zasuyi rayuwa daku a inda basu da kowa sai Allah daku ɗin nan,Ku ruƙe amana,kada ku bari koda kwallarsu ce ta zuba kasa,Ku share masu hawayansu,in suna da damuwa kuyi ƙoƙari wurin faranta masu,da zarar kun bar ƙasar nan basu da wani makusanci daya wuce ku ɗin nan,Kune a matsayin Iyayensu, kuma danginsu........"sosai amma yayi masu nasiha,duk ya kashe masu jikinsu,
Lokacin da suka je wurin abusufyan,Ya kirasu Su jahad suka jera dasu,ya kuma kira junaid shima Yazo,Ruƙo hannun junaid yayi idanuwanshi cike tab da kwalla ya ruƙo hannun Jahad ya haɗasu wuri guda,Muryarshi na kerma yace"junaid ga amanar Jahad nan na baka,"kallon juna Junaid da jahad su kayi,idanuwan kowannansu cike tab da ƙwalla
"Na yarda dakai sosai,Nasan Zaka ruƙe mun amanarta,"
Jinjina kai junaid yayi"in sha Allah uncle,zan ruƙe maka ita amana,bazan ta6a bari tayi kukan rashinku atare da ita ba,"
Kowa dake a wurin saida ya saki murmushi,Jin abunda junaid yace,Yayi magana ta hankali,
Sakin hannunsu Abusufyan yayi,ya kuma ruƙo hannun Omar Ya ruƙo hannun hosana dake ta kuka ya haɗasu wuri guda,
"Omar Na yarda dakai sosai,na yaba da kyawun halayanka,Ga amanar ƴata nan,na baka,"
Tuni idanuwan Omar suka ciko tab da kwalla,daƙyar ya iya buɗe baki yace"In sha Allah Uncle,Zan maye gurbinku a wurinta,Zan bata kulawa fiye da yarda zan kula dakaina,"
Murmushi abusufyan yayi bayan ya saki hannun Omar ya ruƙo hannun Sgr,tare dana Sehrish wadda ke ta faman shessheƙar kuka ya haɗa hannayensu cikin na juna,Kallon Sgr yayi yayin da shima Idanuwanshi na akan fuskar Uncle ɗin
Cikin Zolaya abusufyan yace"Surukina nakaina"murmushin gefen fuska sgr ya ɗan saki,
Mayar da idanuwanshi yayi kan Sherish"My daughter,"cikin shessheƙar kuka ta amsa mashi"Na..na...am daddy.."
"Rafayet Bana kokwanto akanka,Na yarda dakai kuma na yarda da irin ƙaunar da kake yi mata,Ga amanar Sehrish nan na damƙa maka,"
In sha Allah Uncle,i will take care of her,bazan ta6a bari tayi maraici atare dani ba"
Murmushi abusufyan ya saki tare da cewa"Allah yayi maku albarka gaba ɗayanku,"sosai yayi masu addu'a,Kafin daga bisani su kayi Sallama da kowa,Omar na ruƙe na hannun Hosana suka nufi stairs ɗin jirgin,Junaid yana abayansu hannunshi ruƙe dana Jahad,Sgr na ruƙe da hannun Sehrish,a haka suka hau matattakalar jirgin, sai da suka kusa shiga ciki,Suka juyo su dukansu suna kallon Iyayensu da ƴan uwansu,Atare suka ɗaga hannu sunayi masu bye bye,
Suma su Abba suka Ɗaga hannuwansu suna yi masu bankwana,da gudu abu ta shige cikin motar abusufyan tana kuka,komawa su kayi cikin motocinsu,A jere suka bar Airport ɗin,Tun suna akan titin komawa gidan,Jirginsu Sgr Ya gifta ta Saman iska,Suna jin ƙararshi,🛫😭
Bayan sun koma gidan babu wanda ya iya cin abinci acikinsu,tamkar anyi mutuwa,gidan duk babu daɗi,Babu Junaid babu Ya Omar babu Babban Yaya,Babu Sehrish babu hosana babu Jahad,Kewarsu duk ta kama ƴan gidan,oummansu har maganin ciwon kai tasha Saboda kukan da tayi,
Los Angeles
California🛬
💫💥💫💥💫💥💫💥💫💥💫
*_ALBISHIRINKU MATAN AFRICA DA KEWAYE , SHAHARARRAR KUMA KASAITACCIYAR MAI SAIDA KAYAN MATAN NAN WADDA KUKAFI SANI MAMAN YUSUF YAR SOKOTO TANA YI MAKU ALBISHIR DA CEWA ZAKU IYA SAMUN KAYANTA ADUK INDA KUKE CIKIN FADIN NIGERIA DA NIGER KARKU MANTA MACE MAI KYARA KANTA BATA BORANCI_* 💃💃💃💃💃💃💃 07069711327
_Akwai zafafan kayan Mata masu kyau da arha cikin sauki da rahusa Kuma duk inda kike zamu aika maki kayanki cikin aminci da yardar Allah ba cuta ba cutarwa don a Dade anayi sai gaskiya uwargida da amarya ku garzayo Kar abaku labari_
Munada kalolin Kaya kamar haka💥💫💥💫💥💫👇🏻👇🏻
Maganin sanyi sahihi Mai fatattakar sanyi cikin kankanin lokaci na maza Dana Mata
Maganin gyaran nono domin dawo da martaban nononki hadin gargajiya da bashida illah ajiki
Maganin hips Mai tado da hips cikin kankanin lokaci
Maganin kiba Wanda zaisa ki ciko dai dai misali kiyi kyau kema ki shigo cikin jerin Mata masu aji
Maganin rage kiba da tumbi Wanda zaisa ki sace ki koma Yar dai dai abin alfaharin kowane namiji,
Akwai kalolin gumbuna masu kyau da saukar da ni'ima
Maganin matsi masu ciko da gaba da matseki Kamar Yar budurwa uwa uba zasu Baki dandano Mai gamasar da maigida
Kalolin garrika masu bawa mace niima da jimawa ajiki
Kalolin tsumi Sha yanzu magani yanzu dasa Mai gida ihun Dadi
Zumar mallaka
Zumar goron Tula
Zumar ridi
Zumar Mai rubutu
Hadin mallaka
Turaren mallaka
Shu'umar humra
Turaren AL'AJABI
Matan gaske
Ak 49
Sirrin tafin k'afa
Turaren fuska
Hatsabibin turare
Kwallin mallaka
Zoben mallaka
Jigidar maida tsohuwa yarinya
Maltinar Mata
Karya gado
Yajin Mata (yajin Mai ciko da mace)
Yajin maza (domin Karin k'arfi)
Muna dahuwar Kaya kamar haka💫💥💫💥👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻
Dahuwar zabo (mallaka)
Kazar Yar gata
Yan shila
Ciccibi
Dambu
Zuciya
Yan ciki
Kwai ukku
Tsoka Tara
Kifi
Da sauransu
Akwai sirrika sosai da muke hadawa ga wacce kishiya ta addabeta ko wadda take fama da butsarin namiji ko mafadacin namiji ko namiji Mai yawon dare ko Wanda yake bin Mata insha Allah duk zaku samesu Kuma da yardar Allah za'asamu biyan bukata
Muna bada magani ga yarinyar da tsautsayi ya fad'a Mata ta rasa budurcinta ta hanyar fyade ko yaudarar da namiji Kuma insha Allah zaadace da yardar Allah
Abubuwan da yawa gsky Wanda in nace Zan lissafasu sai nakwashi tsawon lokaci maiso tabini PC don ganin kalolin kayan da muke dasu ,
Karku manta mace Mai gyara kanta Bata boranci taku ce maman yusuf Yar mutan sokoto 07069711327
.
Don Allah wadda Bata shirya ba tabari sai ta shirya sannan tayimun magana🙌🏼🙌🏼🙌🏼🙌🏼🙌🏼ngd
07069711327
[3/19, 9:44 PM] +234 810 388 4440: 💋Boss Bature💋*
Join this link to follow my tiktok acct👇
https://www.tiktok.com/@boss_bature?_t=8WKx0lm4jaP&_r=1
قصة حب رومانسية بين سحريش والجراح العام رفايت💋💘❤🤍❤💕💖*
*Father of soldiers*
*🔥TAKUN ƘARSHE🔥*
Zazzafar haja daga Minjibir ventures,Ina masu buƙatar siyan kayan sallah Kada ku bari a baku Lafiya,Ga kaya na kece raini Na shiga tsara,Koda kudinka sai da rabonka,Kadan daga cikin abubuwan da muke siyarwa akwai Lace
Veils
Atamfa
Shoes
Bags
Address
Hotoro ladanai kan titin ring road
Chat 09126570345
Call 09136122503 saikun Zo💃💃💃💃
_California🛬_
_Los Angeles International Airport _
Alhamdulillah matafiya sun sauka Lafiya,lokacin da jirginsu yayi landing,Airport ɗin cike yake maƙil da dubban Sojoji sanye cikin kakinsu,ba masaka tsinke,danƙara danƙaran motoci tsadaddu kuma haɗaɗɗun gaske masu numfashi a jere,wasu daga cikin Sojojin hannunsu na ruqe da Flower,Abun gwanin burgewa,wasu kuma suna ruqe da Welcome Symbols Mai ɗauke da Sunan SURGEON GENERAL ALEXANDER AND MARSHAL OMAR,dama da zarar yabar Nigeria Sunanshi ya tashi daga Rafayet ya koma Alexander saboda shine real name da yake using dashi kafin ya musulunta,daga cikin waɗanda suka zo tarbarsu hada Uncle Donald tare da Matarshi da kuma ƴa'ƴansu guda biyu Eva da Jessy,gaba ɗaya kowannansu fuskarshi ɗauke da tsantsar farin ciki,don ba ƙaramin kewarsu sukayi ba,baka jin sautin komai saina National Anthem ɗinsu,
Lokacin da suka saukko daga saman jirgin hannuwan kowannansu na ruƙe dana matarshi Dubban Sojojin nan suka buga ƙafa tare da Sara masu,Su sehrish sun sha ruwan mamaki,Ganin Yadda Sojoji suka cika Airport duk don saboda Zuwansu Sgr,Lokacin da mutane suka fara Lura da Zoben Hannun Sgr Abun yayi matuƙar ba kowa dake a wurin mamaki saboda basu san da zancen Auranshi ba,Zoben hannunshi ne Yasa suka gane cewa Yayi aure,Don Bai ta6a sanya zobe ba dama su saida dalili ko soyayya ko aure kesa a liƙa shi a hannu,Mafi akasari ma Sai zasuyi aure suke sanya ring a yatsansu,Tun a cikin jirgi kafin su ƙaraso,Yaba sehrish Diamond ring ɗin agogonsa ta sanya mashi a hannu,Saboda bayason yasha wahalar yi masu bayanin cewa yayi aure da zarar sun gani a hannunshi zasu fahimci komai,Aiko dai sunsha ruwan mamaki,tunda Eva ta ankara da zoben hannunshi,taga kuma ya ruƙe hannun Sehrish,Sai ta fashe da matsanancin kuka,da gudu ta koma cikin motocinsu,shi kanshi Uncle ba haka yaso ba,Yayi burin Sgr Da Omar su auri jininshi saboda shi ya raine su,kuma ƴa'ƴanshi duka suna matuƙar ƙaunarsu,musamman Eva saboda Sgr taƙi yin aure,takusa shekara arba'en babu aure duk don saboda Shi,ta ƙwallafa rai Akanshi taƙi kula kowa,Baiwar Allah,
Sam basu nuna komai a fuskarsu ba,Sunyi masu kyakkyawar tarba,Su Jahad sunƙi sakin jikinsu duk sunsha jinin jikinsu musamman da Eva ta juya tana kuka,Sun jima a Airpot ɗin Suna gaisawa da mutane Kafin daga bisani suka shiga cikin jigunannun motocin da akazo ɗaukarsu dasu,Wai ina Hosana,duk tabi ta furgice,taƙi yarda Omar ya saki hannunta,ta ƙanƙameshi,
Kaitsaye Suka wuce Gidan Uncle Donald,katafaren gidane haɗaɗɗen gaske,An ƙawata gidan sosai duk don saboda zuwansu Sgr,koda suka shiga cikin gidan Su Sehrish Sunƙi sakin jikinsu,Tsoronsu ma suke ji,gani suke kamar zasu cutar dasu ne,Lokacin da aka shirya masu breakfast,Ƙin ci suka yi,Kowa tace ta ƙoshi,Mommy Sai lalla6asu take yi tana faɗin Su saki jikinsu su ƙaddara kamar suna a gidansu ne,Amma suka ƙiya,kwara ma Jahad ta ɗan ci abinci,ita hosana abincin nasu ne baiyi mata ba,ta dai ci wani abun wanda ta saba gani a gida Nigeria,wani kuwa ko son kallonshi bata yi,ita kuma sehrish taso ta ci,wani irin tashin zuciyane yazo mata, daga tayi yunƙurin ci sai tafara yunƙurin amai,Wannan dalilinne yasa taƙi cin komai amma tasha Lemu mai sanyi,tasha fruit,
Haɗaɗɗen Bedroom aka basu inda zasu zauna,koda suka shiga ɗakin,Hosana ta rufe ƙopar wai kada a shigo akashe su,Saboda ta kalli wani film na turawa da suke nuna wariyar launin fata,😂
Sai da Uncle Donald ya tarasu yayi masu fada sosai akan auran da sukayi batare da saninshi ba,Yaso ace sun sanar mashi da ba abunda zai hana ya hallacci ɗaurin Auransu,Baiji daɗin hakan ba,duk da haka sai da Ya shirya masu Party A washe garin ranar da suka zo,Acikin gidan Akayi shi,Musamman aka ɗauko Makeup artists suka yima su Jahad kwalliya,Aka Sanya masu wedding gown,Mazan kuma Suka shirya cikin suits farare,manya manyan Mutane suka halarci partyn,hada shuwagabaninsu na Sojoji,abun ya ƙayatar sosai,An ci An sha,Anyi rawa,An kuma Yi hotuna,daga cikin hotunan da suka yi hada wanda Sgr da Omar suka yi da kakinsu,Hosana da Sehrish ma Aka basu Uniform na mata suka sanya,sunyi kyau over kamar Sojojin gaske,Shima Junaid sai da yasa Rigima Aka bashi Uniform ya sanya Jahad ma ta sanya aka ɗaukesu hotuna,Sun ji daɗin ranar sosai,kowa sonsu yake yi,duk inda suka shiga nuna su akeyi da Hannu,kowa so yake ya ɗauki hoto dasu,sun samu kyaututtuka masu tarin yawa,ɗaukaka Iya ɗaukaka,
Rayuwarsu acikin gidan duk atakure suke yinta,babu yadda Mommy batayi dasu ba akan su saki jikinsu Amma sun ƙiya,Hatta Eva daga bisani da Sgr Ya lallashe ta,Ta sassauto kuma har wurinsu tazo don su gaisa,Daƙyar suke yi mata magana,rashin sabone duk ya jawo hakan,Kwanansu Uku Sgr Ya yanke shawarar zai ɗaukesu daga gidan Ya mayar dasu Katafaren Gidanshi,
Haɗaɗɗiyar Daula ce,Aljannar Duniya,Hamshaqin Gidan Sgr na bugawa a Jarida,Tanƙameman gidane Gari guda,Idan nace zan tsaya bayyana kyawun gidan To tabbas A iya wurin bayaninshi Littafin Zai ƙare Har ma a shiga littafi na Huɗu,Baki bazai iya kwatantashi ba,
domin kuwa Ganinshi Yafi jinshi,duk wani abu daka sani na more rayuwa Na jin daɗin Duniyar nan to akwaishi aciki,Kai idan mutun ya tsinci kanshi acikin gidan nan,Sai ma Ya manta cewa da tur6aya aka halicceshi,saboda shagala.
Rana ta farko da suka fara kasancewa a cikin gidan,hadda Family din Uncle Donald Suka yi masu rakiya,Basu bar gidan ba sai wuraren Ƙarfe 6 na marece,Su Sehrish sunyi murna kamar kamar me,Gidan Yayi masu kyau sosai,Atare da Junaid suka shiga zagaye gidan,Ko rabi basu yi ba suka fara gajiya a ƙarshe sai dai suka hakura,Gobe sun dasa daga inda suka tsaya,Amma fa sunsha Yawo,Security guards din dake tsaron gidan A ƙalla Sunkai mutun 20,Waɗanda ke kula da cikin gidan tundaga kan 6angaren Kitchen,Gyaran Gidan,A ƙalla sunkai Su goma sha biyar,In mutun na rayuwa acikin gidan nan ko tsinke wannan sai in yaso zai kawar dashi,musamman inya kasance malalacine shi,
Kusan 3 weeks da zamansu acikin gidan,Kullum sai sun zagaye shi,Wani lokacin Har Video Call Suke kiran su Oummansu Suna nuna masu abubuwan ban sha'awa na cikin gidan,tunda suka dawo Zama acikin gidan Omar da Sgr basu zauna ba Saboda Uban aiyukan dake jiransu,Idan suka fita da safe sai cikin dare suke shigowa cikin gidan lokacin duk sunyi bacci,Yanzu basu da wata sauran damuwa,Suna samun kyakkyawar kulawa ta ko'ina,A irin rayuwar da suke yi agidan tamkar Princesses ne in their Own Palace,Abunda suke so shi za'ayi,Masu aikin Gidan Command ɗinsu kawai suke Jira,
Yau tun safe aketa Tsuga ruwan sama,Ni'ema ta sauka ta ko'ina,yanayin weather ɗinsu gwanin ban sha'awa,Wata irin ni'imtacciyar iska mai sanyaya zuciya mai ratsa sassan jiki,irin wannan yanayin yafi da cewa da ma'aurata,
Kwantar da kanshi yayi jikin ƙopar ɗakin jikinshi na sanye da pyjamas,Ya jima atsaye yana ta yi mata magiya akan ta buɗe mashi ƙopar ɗakin ya shigo amman tayi kunnan uwar shegu dashi,Gashi yau a matse yake baya jin zai iya haƙuri wannan daren Ya wuce batare daya kar6i hakkinsa ba,A shagwa6e yake ambaton sunanta"My juliet pls,wlh ba abunda zanyi maki fira kawai nazo in tayaki,"Jahad dake ƙudundune cikin bargo ta kasa kunne tana sauraronshi,tsananin tausayinshi ne ya kamata,Amma bata jin zata iya buɗe mashi ƙopa,tsoranshi take ji saboda tasan halinshi bazai raga mata ba,Kamar yadda ya saba faɗi mata,shiyasa kullum da zarar dare yayi take kulle ƙopa don karya shigo ya addabeta,
"I know you're hearing,pls My Juliet,wlh in baki buɗe ƙopar nan ba,Zansha poison..."Murmushi Jahad ta saki,daɗin sauraron muryashi take ji,ita kanta tana buƙatarshi amma akwai wasu dalilai dayasa take gudunshi,na farko tana fargabar kasancewa dashi,Na biyu kuma tana kunyar ta samu cikinshi,da wani ido zata kalli su babban yaya idan suka gane tana ɗauke da cikin ƙaramin ƙaninsu wanda ko School bai kammala ba,duka cikin ƴan kwanakin nan zai fara zuwa University Of Southern California,Itama kuma zata cigaba da karatun Secondary ɗinta,abunda take yima fargaba kenan,in har ta samu ciki abubuwa bazasu tafi