Showing 207001 words to 210000 words out of 318483 words
Chapter 70 - ABBAN SOJOJI (Takun Karshe) COMPLETE BY BOSS BATURE.docx
Dafa kafaɗarta abu tayi"Ni dai shawarar da zan baki shi ne,Ki samu wani babba ki sanar dashi komai dangane da ita....."
A ruɗe sehrish tace"Wazai yarda dani Oumma!idan har na faɗi cewa Azmee ƴar uwar sayyadi ce,kuma ina zarginta da mutuwar Junaid"
"Tabbas kuwa babu wanda zai yarda dake a halin yanzu,a ƙarshe ma reshe zai iya juyewa da mujiya,Zata iya ɗaura maki laifin kinsan fa shi mugun mutun hatsari ne shi,balle su da suke da tsafi,duk da dai mu mun dogara da Allah ne,babu ja da baya Allah shi zai bamu kariya,"
"Yanzu ya zanyi!inaso naci gaba da bincike akanta,Saboda inaso na tambayeta dangane da zoben Junaid dake a wurinta me yakai shi cikin kayanta,"
"Nace maki karki kuskura ki ce zaki nuna cewa kinsan wani abu game da ita,in ba haka ba zatayi maki mummunar illane,Nidai shawarar da zan baki A yanzu ki damƙa binciken nan a hannun ɗaya daga cikin mutanen gidan nan,Zaifi ma ki sanar da Daddynku,Zan ma yi mashi magana,nasan zai yarda dani sosai'
Shikenan Oumma,Yanzu zan iya zuwa ɗakinta in kwanta"?
"Me zai hana amma dai ina ƙara jan kunnanki akanta,karki kuskura ki tsananta bincike akanta,Don zata ganoki ne,"gyaɗa kai Sehrish tayi tare da saukowa daga saman gadon ta nufi hanyar fita daga ɗakin,ruƙo handle ɗin ƙopar tayi,bayan ta fita taja ƙopar ta rufe,gyara kwanciya Oummansu tayi saman gadon,ita kanta abun ya razanar da ita,Ta yadda akai har ƴar uwar sayyadi ke aiki acikin gidan,daƙyar bacci yayi awon gaba da ita,
Tafiya sehrish takeyi kamar wadda aka zarewa lakar jikinta,komai ya tsaya mata Cak,don abun ya girmi tunaninta,a ƙopar ɗakin Azmee ta tsaya gabanta na faɗuwa a hankali ta furta"La'ila ha illa anta subhaka inni kuntu minazzalimin,tana kai ƙarshen addu'ar ta tura ƙopar ta shiga daga ciki,abun mamaki bata samu kowa ba acikin ɗakin,Ranta ne ya bata cewar kodai ta shiga toilet ne,
A wauta irin na Sehrish,maimakon tabi abunda Oummansu ta sanar da ita,Sai ta soma tunanin Yin bincike acikin ɗakin don a qagare take da ta gano gaskiyar wacece AZMEE,
Agaban bedside drawer ɗinta ta zuƙunna jikinta na kerma,ta shiga bubbuɗe drawer chest ɗin,Yawanci duk tarkace ne na magunguna sai ƴan ƙulle ƙulle kamar na maganin Zafi,gida na ƙarshe ta bincika anan ne taga abun daya ɗaure mata kai,Ƙura ido tayi tana kallon Galleliyar wayar dake ajiye a wurin,Ƙirar i phone 13pro
Batasan lokacin da ta furta"Ya Allah!dama Aunty Azmee tana da waya?Amma meyasa ban ta6a ganin wayarta a hannunta ba,"ta ƙarasa maganar tare da zura hannunta ta ɗauki wayar,ta kunna power ɗinta,Nan take haske ya kawo,Gabanta ne ya faɗi Ganin Hoton dake ajikin Wallpaper ɗinta,bakowa bane face Fuskar HAROON,da ƴar ƙuruciyarshi,nan fa tashiga ruɗanin abun al'ajabin da take gani,Menene Alaƙarta da haroon da har ta ɗaura hotonshi a fuskar wayarta?dama ta jima tana zargin haroon ba mutumin kirki bane,kodai hadashi atare suke shirya maƙarƙashiyarsune?
Tana cikin wannan wasi wasin,kira ya shigo cikin wayar da baƙuwar lamba,kwata kwata babu sautin ringing an sanya wayar silent,Yadda ko an kira baza'aji ƙararta ba,
Sehrish da karanbani sai ta ɗaga kiran tare da kara wayar a kunnanta,
Shiru tayi tana jiran jin wanene zaiyi Magana,
Cikin harshen fulatanci taji ana magana,gashi ita bata iya yaren ba,Tunani ta shiga yi dama azmee bafullatana ce?dama ta ta6a ganin Zanen kalangu a gefen fuskarta,
Tana cikin wannan zancen zucin tajiyo takun tafiyar mutun yana tunkaro ɗakin,Ba shakka Azmee ce,A tsananin tsorace Sehrish ta katse kiran,gashi wayar akwai password,babu yarda za'ae ta goge kiran da akayin,dole idan aka shiga Call log agane cewa An ɗaga kiran da akayi,
A matukar firgice Sehrish ta tura wayar acikin drawer ɗin,Duk tabi ta ruɗe ta rasa inda zata dosa,A ƙarshe ta faɗa toilet ta rufe,tana faman sauke ajiyar zuciya,jijiyoyin wuyanta duk sun fito saboda tsabar tsoro,Tayi danasanin ɗaga kiran wayar Azmee da tayi,
A hankali Azmee ta turo ƙopar ɗakin ta shigo,Jikinta sanye da baƙaƙen kaya,Jallabiya ce tare da mayafinta,kamar wadda taje anguwa,zama tayi daga gefen gadon,tare da kai Hannu jikin drawer ɗin ta ɗauko wayarta,dannata ta shiga yi,kafin ta danna call,
Sehrish dake la6e acikin toilet ɗin da alama mutumin da ya kira Sehrish ta ɗaga shi Azmee ta kira,Addu'a sehrish tashiga yi hannunta na kerma ido ya raina fata,tuni zufa ta wanke mata fuskarta,Ga fitsari daya matse,ta kasa tsugunnawa tayi futsarin gudun kada azmee taji ƙarar fitarshi,
Ba ƙaramin haushi Sehrish taji ba lokacin da Azmee ta soma Magana Cikin harshen fulatanci,taso ace da yaren hausa tayi maganar don ta samu taji abunda zata ce,yanzu ta ƙara ƙarfafa zarginta akan Azmee,
*Boss Bature*
Around 10pm
Jami'an da Sgr ya sanya su tsare grave ɗin Junaid,sunyi 6adda kama yadda kasan ba Sojoji ba,kowannansu na sanye da Kaya namu na hausawa,riga da wando na yadi,ɗaya daga cikinsu yana zaune saman dogon benci yayin da ɗayan ke zuƙunne agaban bencin gefenshi kayan Shoe shiner ne,Yana goge ma na saman bencin Takalminshi,dayake akwai hasken street light,Bakomai suke jira ba fa ce wannan mai zuwa yana yin zarya a ƙabarin nasa,bisa Command ɗin da Sgr ya basu nasu sanya ido akanshi idan ya ƙaraso,Su sanar dashi yana so yaga ko wanene,Suna zaman jiran zuwanshi,Aikuwa cikin sa'a ƙarfe goma na bugawa,kamar yadda ya saba zuwa,Sai motar nan ƙirar Venza ta shararo da gudu izuwa titin,tunkan ya ƙaraso ɗaya daga cikin sojojin wanda ke zaune saman Bencin yace"Gashi nan!yakamata mu sanar da Sgr,tun kafin ya kufce mana"
Wanda ke goge mashi takalmin yace"sai munyi taka tsantsan if not zai gudu ne,"
Koda ya ƙaraso wurin ƙabarin slowly yayi parking ɗin Motar a gefen titin batare daya fito ba,
A hankali Sergeant ɗinnan dake zaune saman bencin ya ɗauko wayarshi tamkar yana dannata,message ya turawa Sgr,bayan ya kammala tura saƙon Ya mayar da wayar cikin trouser ɗinshi,
Buɗe murfin motar yayi tare da saukowa daga cikinta,kamar yadda ya saba zuwa haka yau ma yazo,Ya sanya face mask a fuskarshi yayin da idanuwanshi ke sanye da glass baƙi,Jikinshi na sanye da Crazy jeans tare da T-Shirt purple,tafiya ya soma yi har izuwa gefen bishiyar nan inda aka kewaye ƙabarin Junaid,tsayawa yayi kamar mai neman wani abu,hada ruƙe qugu,kusan minti 5 kafin ya soma zagaye bishiyar yana jinjina kanshi,
Miƙewa ɗaya daga cikin Sojojin nan yayi,A hankali ya nufe shi batare daya ankara ba,koda matashin nan Ya lura da cewa wani na tunkaroshi,Aikuwa da gudun gaske yabar wurin bishiyar,Sojojin nan suka bishi a guje,duk yabi ya rude ko motarshi bai tsaya ɗauka ba,a rikice ya faɗa saman titin yana gudun ceton rai kamar zai tashi sama,da gudu suma suka bi bayanshi don karya kufce masu,yana gudu yana waiwayen bayanshi,Unfortunately Yana ƙoƙarin karya kwana,Adai dai Lokacin Motarsu Sgr ta shawo kwanar,Kwatsam ya faɗama motarsu ta bugeshi sosai,ya saki wata irin razananniyar ƙara tare da zamewa ya faɗi wanwar ƙasa,Ƙarasowa Sojojin suka yi suna faman sauke ajiyar zuciya,Ta kwana gidan sauƙi,
Fitowa Sgr yayi daga cikin motar,Armstrong ma ya fito,Atare sojojin suka sara mashi,Kafin ɗaya daga cikinsu ya nuna saurayin dake a kwance ƙasa yana bullayi"Sir,Wannan shi ne wannan matashin dake zarya a ƙabarin ƙaninka,rashin gaskiya yasa yana ganinmu ya zabura zai gudu",
Zuba mashi ido Sgr yayi yana bin shi da kallon ƙurulla,tun kafin ma Ya cire mashi face mask ɗin fuskarshi,Ya shaida shi,zuƙunnawa yayi saman guiwarshi ɗaya,tare da kai hannu Ya zame face mask ɗin saurayin tare da cire glass ɗin fuskarshi Yayi throwing dinshi saman titin,runtse idanuwanshi yayi jikinshi sae kerma yake yi,
A hankali Ya furta sunanshi"HAROON" kamar bashi ba,Ya rame,yayi baƙi,jin muryar Sgr yasa haroon ware manyan idanuwanshi masu kama dana mujiya,koda yayi tozali Da Sgr a hargitse Ya tashi daga zaune yana kallonshi yayin da yake faman zazzare ido,wata irin zufa ce ta soma tsastsafo mashi agefen fuskarshi,.
"Dama kaine"?cike da mamaki Sgr yayi tambayar,
Shiru Haroon yayi bai tanka mashi ba,
"Me kake yi a wurin grave ɗin Junaid"
Daƙyar ya iya furta"ƙabarin junaid kuma?yayi maganar tamkar baisan akan me suke magana ba,
ɗagowa Sgr yayi tare da kallon sojojin dake tsaye suna ta faman haki"Zaku iya komawa bakin aikinku,"juyawa su kayi da sauri suka bar wurin,
"U will explain it don ubanka,I have been suspecting you for a while,Zuba maka ido nayi kawai inga ƙarshen gudun ruwanka,abunda ka aikata ne yasa ka gaza samun natsuwa acikin ranka That's why kazo kana zarya akan ƙabarinsa"?
Waro ido haroon yayi amatuƙar tsorace Yayi yunƙurin miƙewa ya gudu,damƙar ƙafarshi Sgr yayi hakan yasa ya gaza motsawa,
"Amstrong,ɗaukarmun shi ka sanyamun shi acikin mota,"
Gadan gadan Amstrong ya tunkareshi,Yadda kasan ƙaramin Yaro haka ya ca6eshi asaman kafaɗarshi,Ya turashi cikin motar Sgr,Front seat suka shiga,Sgr da Amstrong Tada Motar yayi da gudun gaske ya fisgeta,
"Wai ina zaku kaini ne?Motata fa?kun barta a wurin"shiru su kayi mashi babu wanda ya tanka mashi,
"Wlh kada kuce zaku ta6ani,Rafayet ku sauke ni in kama gabana!Ni bansan akan me kuke magana ba"Sai faman sambatu yake yi,zufa duk ta wanke jikinshi"
Har Lokacin basu tanka mashi ba,ƙoƙarin buɗe motar yayi donya buɗe,amma yaji ƙopar adatse ta ko'ina babu hanyar da zai gudu,
Da gudun gaske motarsu ta shigo cikin gidan A lokacin Sehrish na la6e cikin toilet ɗin Azmee,Har cikin kunnanta tajiyo sautin Shigowar Motar Sgr,kamar ta fasa ihu haka take ji ga Azmee taƙi yin bacci bare ta lalla6a ta gudu,Sae dannar wayarta take yi,Yadda kasan tasan da zaman wani acikin ɗakin,
Window ta hango acikin toilet ɗin,Da gudu ta nufe ta,so take ta leƙa window ɗin don taga idan shi ne ya dawo dagaske,net ne ajikin tagar,kuma tagar tayi nesa,Tsawon sehrish bazai kai ta leƙa tagar ba,Lalla6awa tayi cikin sanɗa ta ɗauko bokiti,Ta kifa shi ajikin bangon,Sannan ta daddage ta haye saman bokitin cike da tsoran karya fashe bokitin,
Ƙura idanuwanta tayi tana leƙan wajen gidan daƙyar take hangen wurin da motar Sgr take,fitowa yayi daga cikin motar tare da zagayawa ya Shaƙo wuyan rigar haroon ya wurgo shi waje,gaba ɗaya ya kife ƙasa a susuce,Gabanta ne ya faɗi rass!lokacin da taga Ya damƙo rigar haroon,Tabbas ranta na bata cewar Sun kamoshi ne a matsayin me laifi!tsoranta kada Sgr yayi kuskuren raunata shi,wata'ƙil Sunji kalamanshi ne dayake cewa zai kashe Farin cikin mutanen gidan Shiyasa suke tuhumarshi,kamar ta bur6a tagar ta fito haka take ji,
Ɗaukarshi Sgr yayi asaman kafadarshi Ya wuce dashi cikin gidan Amstrong na biye da bayanshi,ɗakin horon nan nasu Ya shiga tare dashi,ɗakinda idan aka rufe ƙoparshi ko ihun mutun ba'aji,
Sauke shi yayi yana tangal tangal Zai faɗi ƙasa,Nuna mashi ɗaya daga cikin kujeru biyu dake kallon juna yace"Ave a seat,magana nakeso nayi dakai,"
"Nifa bansan komai ba!meyasa ka shigo dani wurin nan"?
Wani irin kallo da Sgr ya wurga mashi yasa shi lalla6awa ya zauna,jikinshi nata kerma,kai cike da iskanci ga shegen tsoro
Zama Sgr yayi suna fuskantar juna yayin da Amstrong ke atsaye yana kallonsu,
Sai faman mazurai haroon keyi,irin na marasa gaskiyar nan,
"Meyasa ka aikata hakan"?girgixa kai ya shiga"Ni wlh ban aikata komai ba,Nifa bansan komai ba,bansan akan me kake magana ba"
Tsabar takaici ne yasa sgr ware yatsunshi Biyar ya kwasa mashi mari asaman fuskarshi,nan take le6enshi ya fashe,hannu yasa ya dafe kuncinshi saboda zafin daya ji,
"Ka faɗamun meyasa ka kashe junaid"?
"Rafayet ba zaka ta6a jin komai ba,a abakina"Duk da halin da yake ciki hakan baihana shi gaya magana ba,
..rai amatuƙar 6ace,Sgr Ya damƙi kwalar rigashi da iya ƙarfinshi na ƙarshe ya daddaɗao da haroon a zafafe ya tunkari faskeken Madubin dake a aɗakin,Gaba ɗaya ya rotsa kanshi acikin glass ɗin,Wata irin gigitacciyar ƙara Haroon ya fasa yana fadin"Nashiga uku!Rafayet ka kashe ni!Na bani Na Lalace!!!.."kafin Haroon yayi wani yunƙurin kwace kanshi tuni Sgr ya ƙara Tarwatsa kanshi Acikin glass ɗin madubin,Nan take jini Ya soma tsastsafowa Asaman kanshi,Ya hada mashi Jini da Majina,Fitsari ya saki a wando ya shiga zubowa Zirrrrr yana kawarara Yaji bala'e,
Naushin cikinshi sgr ya shiga yi gaba ɗaya,Duk In ya naushe shi sai Jini ya fito ta bakinshi,Ganin yana ƙoƙarin kashe shi yasa Amstrong Yin saurin dakatar dashi Ta hanyar ruƙo damtsen hannunshi"Allah ya huci zuci zuciyarka,Bai kamata ya mutu a yanzu ba,Still bamu samu bayanan da muke son samu a wurinshi ba,"
Ranshi amatuƙar 6ace yake magana"Kabarni in kashe wannan mugun mutumin Mara imani da tausayi!In har ban kashe shi ba,bazan samu kwanciyar hankali ba,Bazan cigaba da jure ganinshi yana yawo araye ba,
Haroon dai tuni ya fita hayyacinshi sai faman ambaton Innallahi wa'inna ilaihirraji'un yake yi acikin bakinsa kamar wani musulmin ƙwarai,Jini duk ya wanke mashi fuskarsh,
Daƙyar Amstrong ya samu ya shawo kanshi,Ya haƙura da zancen kashe haroon,Zuƙunnawa yayi agabanshi Yana kallonshi,Idanuwanshi tuni sun jima da juyewa,Yayi bleeding sosai,
"Sir!ya rasa jini sosai,Yakamata Abashi Emergency treatment,don ya dawo cikin Hayyacinshi,idan yaso sai mu tuhu me shi daga Baya,
Hannu Sgr yasa tare da kinkimar haroon ya wuce dashi medical Room ɗinsu,Ba don yaso ba haka ya shiga duba shi,Uban bandage ne akan goshinshi,duk ya cire mashi pieces na gilashin daya Sossoke shi,biji biji yake kallonsu
Zama daga gefen gadon Sgr yayi,yana kallonshi cike da jin tsanarshi acikin zuciyarshi,
"Najima Ina samaka ido haroon,ban ta6a ɗaukar mataki akanka ba,saboda ina zargin cewa Ba yin kanka bane,Akwai wanda ke take maka baya kana aikata hakan!
"Nazo nigeria ne saboda in ƙarfafa bincikena akanka,kafin na yanke maka hukunci,Na sanya maka ido sosai duk wani motsinka acikin garin nan ko ince acikin ƙasar nan a idona kake yinshi!!"
Haroon dai sai binshi da idanuwayake yi,sunyi jawur dasu ga raɗaɗin ciwon da yake ji,ga wani nishi da yake saki don ba ƙaramin jiki yaji ba,
"Tun lokacin da ka sanyawa yarinyar can ido,Ka takura mata akan cewa ta amince ka kusanceta ko kuma Ka tona mata Asiri,Anyi haka ko ba'ayi ba"
Waro ido waje haroon yayi Yana kallonshi,hankalinshi a matuƙar tashe,
Cigaba da magana Sgr yayi"A kwai ranar dana sanya ta kawo mun injection inyiwa kaina,Saboda bata iya karanta hand writting ɗina,Sai kayi mata wayau da nufin zaka taimaketa,Shi ne ka bata allurar Maye ta kawomun,bisa rashin sani har nayiwa kaina"!
Wani irin wahalallan Yawu haroon ya haɗiya,abun yayi mugu mugun ɗauke Mashi kai!Taya akai duk yasan da wannan?mutun sai kace Aljani
Cigaba da magana sgr yayi"Bayan wannan,Kayi masu Twins barazana akan su baka 80million ko ka fallasa porn video wanda ka ɗauka a hotel room ɗinsu yayin da suke aikata Homo!Anyi haka ko ba'ayi ba'?
Tashin Hankali,kasa buɗe baki Haroon yayi sai faman wurga idanuwa yake yi,
"Kullum kalamanka sune zaka kashe farin cikin gidan na,kayi niyar kashe junaid sai kuma ka fasa saboda ƙaunar da yake nuna maka,Har so kayi ka shiga Jikinshi donka cutar dashi Amma ka gaza yin hakan saboda sonshi da kakeyi,Daga baya kuma Sai wani abu ya faru tsakaninka da Marshal Omar sakamakon marin da kayiwa Reesh,Shi da Uncle suka kwasa maka mari a lokaci ɗaya,bayan haka kuma Omar yayi maka bugun tsiya,wannan yasa ka dawo da wannan mummunan ƙudirin naka na son kashe Junaid....."tunkan yakai ƙarshen maganar Haroon daya gama razana yace"Duk ya akai kasan da wannan?kuma meyasa tun lokacin baka hukuntani ba?bayan kasancewa Ni maƙiyinku,Na tsaneku bana son farin cikinku,banda burin daya wuce inga na tarwatsa farin Cikinku,Kuma nayi nasara akanku tunda har na Kashe junaid,Ko yau nafaɗi na mutu na gama daku,
A fusace Amstrong ya zabura zai ɗauke shi daga saman gadon don ya rugurguzashi dasauri Sgr ya dakatar dashi"Ka barni dashi,Na ishe shi,"
"Bansan wanene yake tunzuraka ba haroon,Amma inaji araina cewa Sanyaka akeyi kana yi,Laifin me muka aikata maka?da har muka cancanci hakan a wurinka?me junaid ya aikata maka da har kayi silar mutuwarshi?duk irin halarcin da akayi maka acikin gidan karasa dame zaka saka mana sai wannan?Da wani ido kake tunanin Abbanmu zai kalleka?Ya ta6a banbantamu dakai ne"?
"Banbanci kuma na yaushe?babu mai sona acikin gidan nan,ba ku damu dani ba,bakusan halin da nake ciki ba,kowa kuna nuna mashi so da ƙauna acikin gidan nan,Ni kaɗaine kuka ware kamar wani bare,"yana magana yana kuka
"Nikaina bada son raina nayi silar mutuwar junaid ba,ɗacin raɗaɗin ƙuncin da kuke cusa munne yasa har nasa aka bi takanshi da mota,Yanzu bana jin tsoran kowa yaji cewa Na kashe junaid,Saboda nima so nake na mutu,tun ranar dana kashe Junaid na gaza samun kwanciyar hankali,duk wani mugun abu da nake aikatawa na daina duk don saboda shi,haƙƙinshi kaɗai ma bazai barni inyi rayuwa cikin salama ba,Duk ni najawa kaina wannan masifar da nake ciki........"sosai ya fashe da matsanancin kuka,gaba daya basu yarda da kalamanshi ba,Yana yin magana tamkar wanda yayi danasani,
"Ka fadamun wanene yake baka Command kana aikata hakan?idan har ka faɗamun zan ƙyaleka kayi tafiyarka,"
Girgiza kai Haroon ya shiga yi yayin da hawaye ke kwaranyowa daga cikin idanuwanshi"Wlh bazan iya faɗa maka ba!bazan iyaba,da ace zan iya dana fada maka,Amma bazan iya ba,"
Jinjina kai Sgr yayi tare da miƙewa tsaye yana kallonshi"its okey,tunda baza ka faɗamun ba,Amstrong ɗaukarshi ka mayar dashi ɗakin horon nan,".
Fashewa haroon yayi da matsanancin kukan Yana ƙoƙarin dakatar da Amstrong akan karya ɗaukeshi,abun ba ƙaramin ɗaure masu kai Yayi ba,
"Leave him,"Ya ambaci hakan tare da dakatar da amstrong daga ɗaukarshi,"
Allura Sgr ya ɗauko,Aikuwa a firgice haroon ya shiga girgiza mashi Kai yana fadin"kada ka kashe ni dan Allah,kabarni da raina,inason Na nemi yafiya a wurin Abba kafin nabar duniya...."
"Kasan daɗin ranka meyasa shi junaid ka kashe shi baka bari ya gana da iyayenshi ba?Haroon Rayuwarka bata da amfani"Turmushe shi Amstrong yayi,Sgr ya Caka mashi allurar a wuyanshi,lokaci guda jikinshi ya saki gaba ɗaya,Lokaci guda idanuwanshi suka kakkafe,daga bisani ya sanƙare babu numfashi,
Tashin Hankali!Haroon Zai rayu Koya mutu?Ya sehrish ƙare acikin toilet ɗin Azmee ga futsari ya matse ta,Junaid Yana raye Koya Mutu?Am confused
*Ga duk maison Abban sojoji ya tuntu6i Layina whatsapp message kawai banda call 08103884440*
[3/19, 2:57 PM] +234 810 388 4440: 💋𝔹𝕠𝕤𝕤 𝔹𝕒𝕥𝕦𝕣𝕖💋
𝑗𝑜𝑖𝑛 𝑡𝒉𝑖𝑠 𝑙𝑖𝑛𝑘 𝑡𝑜 𝑓𝑜𝑙𝑙𝑜𝑤 𝑚𝑦 𝑇𝑖𝑘𝑡𝑜𝑘 𝐴𝑐𝑐𝑜𝑢𝑛𝑡👇
https://www.tiktok.com/@boss_bature?_t=8WKx0lm4jaP&_r=1
قصة حب رومانسية بين سحريش