Showing 213001 words to 216000 words out of 318483 words
Chapter 72 - ABBAN SOJOJI (Takun Karshe) COMPLETE BY BOSS BATURE.docx
ɗan rungumeta,
"Serish baki lafiya ne"?Jahad ce tayi tambayar,tana kallon sehrish ɗin dake manne jikin oummansu
"Bana jin daɗin jikina ne,"muryarta ƙasa kasa tayi maganar,
"Meya ke damunki ne"?ta kuma tambayarta,
"Nikaina bansani ba,kawai bana jin daɗi"
Cike da tausayawa jahad take yi mata ya jiki,
Hosana kuwa batasan ma wainar da ake toyawa ba,tana daga zaune gefen jahad tana gyangyaɗin bacci,dama daƙyar aka tashe ta don tayi sallah,
Addu'o'i oummansu ta shiga yi tana tottofa mata asaman kanta,
Dakatawa tayi da yin addu'ar,ta juya tare da kallon jahad dake a gefenta"Jahad hosana ku koma saman gado,"ta faɗi hakan ne don tasamu damar tambayar sehrish,
"To oumma," ta miƙe tare da ruko hannun hosana taja ta zuwa saman gadon,
Ɗago da sehrish tayi daga jikinta,
"Faɗamun me yake damunki"?
"Oumma na tabka kuskure,kin hanani na ƙara yin bincike akanta amma naqi ji,"
Cike da takaici abu tace"Hmmm ta kama ki ko"?
ɗaga mata kai tayi alamar eh,daganan ta bata labarin abunda ya faru jiya a dakin Azmee,amma bata sanar da ita zuwanta Ɗakin Sgr ba,Don har yanzu batasan meke tsakaninta dashi ba,
Rufe ta da faɗa abu tayi"meyasa bakin jin magana sehrish?kunnan ƙashi ko?Wannan matar da kike gani tafi ƙarfinki,Shiyasa nace ki damƙa binciken da kike yi a hannun wani,In ba haka ba zaki jama kanki ne"
"Oumma nima bazan ƙara ba"ta faɗi hakan ne kawai ba don ta haƙura da bincikenta ba,Don tayi alƙawarin saita fallasa Azmee,Koda kuwa Zata Rasa Ranta ne,
"Tashi kije kiyi alwala"acewar oummansu,
Jiki asanyaye ta miƙe ta nufi cikin toilet ɗin,Bada jimawa ba ta fito tana faman yarfa hannunta,hijab ta ɗauko cikin wardrobe ta zura ajikinta,Sannan ta dawo saman dardumar ta kabbara salla,
Till Monday in sha Allah,
Ayi hkr da wannan,daƙyar na samu nayi shi,bana jin daɗi sai a slow,
*Ga duk mai buƙatar littafin Abban sojoji yayi mun magana kai tsaye ta layina,Amma fa whatsapp kawai banda kira,08103884440*
[3/19, 2:57 PM] +234 810 388 4440: 💋𝔹𝕠𝕤𝕤 𝔹𝕒𝕥𝕦𝕣𝕖💋
𝑗𝑜𝑖𝑛 𝑡𝒉𝑖𝑠 𝑙𝑖𝑛𝑘 𝑡𝑜 𝑓𝑜𝑙𝑙𝑜𝑤 𝑚𝑦 𝑇𝑖𝑘𝑡𝑜𝑘 𝐴𝑐𝑐𝑜𝑢𝑛𝑡👇
https://www.tiktok.com/@boss_bature?_t=8WKx0lm4jaP&_r=1
قصة حب رومانسية بين سحريش والجراح العام رفايت❤🤍❤
𝐹𝑎𝑡𝒉𝑒𝑟 𝑂𝑓 𝑆𝑜𝑙𝑑𝑖𝑎𝑟𝑠
*🔥𝕋𝕒𝕜𝕦𝕟 𝕂𝕒𝕣𝕤𝕙𝕖🔥*
Cikin natsuwa ta kammala sallar,zama tayi saman dardumar ta ɗaga hannayenta sama tana addu'a,kafin ta ƙarasa yin addu'ar Abu ta miƙe daga kan dardumar,saman gadon ta koma daga gefe ta zauna tana jan casbaha,
Tana cikin yin Addu'ar ta tunano da wannan malamin nasu na makarantar Boko Ya Mu'allim,tabbas suna buƙatar taimakon malamai domin magance waɗannan miyagun mutanan,Shafa addu'ar tayi kafin ta miƙe tare da ɗaukar sallayar ta nannaɗe ta,Cire hijab ɗin jikinta tayi ta mayar dasu a wardrobe,
Komawa tayi gefen oummansu ta zauna,
"Oumma"ta ambaci sunanta,
"Na'am?ba zaki koma bacci bane"?
"Zan koma,dama wata shawara nake nema a wurinki,me zai hana mu haɗa da malamai?su tayamu da addu'a,"
Jinjina kai Oummansu ta ɗan yi"Kinyi tunani mai kyau,yakamata mu sanya manyan malamai aciki,domin kawar da waɗannan Azzaluman mutanan da suka addabi rayuwarmu,mu ma kuma mu dage da addu'a,Allah dai ya kawo mana ƙarshensu kowa ya huta,"
"Ameen Oumma,"
Ta ambaci hakan tare da gyara kwanciyarta saman gadon ta kwanta,cikin lokaci ƙanƙani bacci yayi awon gaba da ita,dama jiya bata samu isasshen bacci ba,"
A 6angaren su Amrish kuwa,mommynta bata buɗe mata ƙopar ɗakinta ba,har sai wuraren ƙarfe takwas na safe,tana cikin taji mutsu mutsun za'a buɗe mata ƙopar,dama jiranta take yi,Saukowa tayi daga saman gadon ta tsaya ruƙe da qugunta tana jira a buɗe ƙopar,
Turo ƙopar Mommynta tayi hannunta ruƙe da key ɗin ɗakin,ganin Amrish tsaye a bakin ƙopar yasa ta ɗaure fuskarta"Lafiya kika wani ruƙe qugu kamar zaki dake ni"
"Mommy yanzu abunda kika yi mun kin kyauta!kamar wata dabba dabbar ma akuya haka kika rufe ni a ɗaki batare da kinyi tunanin wani abu zai iya faruwa dani ba?meyasa Mommy?wai laifin me na aikata maki ne"?ƙarasa maganar tayi yayin da idanuwanta suka cicciko da ƙwalla,
Ta6e baki mommyn tayi dama ba imani ta cika ba,
"Rashin jinki ne yasa nake rufe ki a ɗaki,kin cika bin ƙwaƙƙwafin tsiya shegen sa ido,ga taurin kai,Ban isa na faɗa maki abu ki yi ba,da ace kina respecting ɗina as ur mother,da mun zauna lafiya,"
"Shikenan Mommy in har wannan ne dalilin dayasa kike yi mun haka,Wlh zan daina......"
Katse mata hanzarinta tayi"Zaki daina!ko kin daina,ban fahimceki ba"?
Da sauri Amrish tace"Na daina,"
Jinjina kai Hajiya Sarat tayi"shikenan,Kin ga yanzu zamuyi zaman Lafiya dake,faɗamun me kikeso na kawo maki ki ci"?
Yatsina fuska Amrish tayi still bata yarda da mommynta ba,
"Duk abunda kikeso Mommy shi nake so,Yanzu dae dan Allah mommy wayata nakeso ki bani!pls mommy nayi missing ɗinta sosai,school friends ɗina duk nayi kewarsu,ina so nayi chatting dasu,"aɗan shagwa6e ta ƙarasa maganar,
"Amrish!ni kaina bansan inda na jefa wayarki ba acikin gidan nan,Ranar kin 6ata mun raine,shiyasa Na ɗauketa,but in kinaso Zamu fita shopping atare daga nan saiki za6i wayar da kikeso,"
Daƙyar Amrish ta ƙaƙaro murmushi akan fuskarta,
"Shikenan mommy,Yanzu bari na shiga ciki nayi brush,"
"Idan kin kammala brush din,Ki jira ni a dining,"ta ƙarasa maganar tare da juyawa ta sauko Downstairs,"
Komawa cikin ɗakin Amrish tayi,tsayawa ta ɗanyi ruƙe da qugu aranta tana faɗin"Matar nan bata da gaskiya,ko su waye suka shigo daren jiya?daga gani ba abun arziƙi suka aikata ba shiyasa suka garƙame ni acikin ɗakin kamar wani ɗan kuikuyo,"
Ƙwafa tayi tare da nufar toilet,ta shiga ciki,
After ta kammala,har wanka ta ɗanyi ta zura jeans da farar vest ajikinta,Saukowa downstairs tayi atsanake take tafiya,hannunta acikin aljihun wandonta irin nigogin nan,
Tana cikin tafiyar nan kwatsam taji ta taka wani abu a ƙafarta,da sauri ta ɗan ɗaga ƙafarta tare da kai idanuwanta kan abun,Wrist watch ce da alama yarda ta akayi a ƙasa,Zuƙunnawa tayi agaban agogon sai faman ƙyalli take yi da alama ta Diamond ce,
Hannu tasa ta ɗauki agogon tana jujjuyata,Aranta tana ayyana farashin agogon,Daga gani ba ƙaramin diamond bane,Don tunda ake siya mata Diamond ba'a ta6a siya mata mai ƙyalli kalar wannan ba,Agogon ta haɗu sosai,Tayi mata kyau,
Murmushi ta saki tare cewa"Yanzu haka cikin baƙin jiya ne da suka shigo cikin gidan nan da daddare aka samu wani ya yarda ita ƙasa wanda baisan muhimmancin kuɗinshi ba,Ko kuma wanda bada guminshi aka siya agogon ba,"
Jin takun takalmin Mommynta Yasa tayi saurin,zura agogon acikin aljihun jeans ɗin jikinta
"Wlh bazan bari mommy taga wannan danƙareriyar agogon ba,Don ta burgeni da ita Zanyi Hotunan Birthday ɗina,Inyaso daga baya sai a mayarwa mai agogon kayanshi,"
Ta ƙarasa zancen zucin tare da miƙewa ta wuce dining,Kujera taja ta zauna tana jiran ƙarasowar breakfast ɗinta,
Shigowa area ɗin Hajiya Sarat tayi hannunta ruƙe da faffaɗan tray mai ɗauke da kayan kalacinsu,Saman table ɗin ta ajiye tray ɗin,
Murmushi Amrish ta saki tare da yi mata sannu"
"Yawwa Daughter,"ta amsa mata a yayin da take ɗaukar plate,warmer ta buɗe mai ɗauke da Chips ta soma zuba mata,bayan ta gama ta haɗa mata da kakkauran Tea,tare da slide bread wanda aka jerashi da wainar kwai,"
Nan fa suka hau cin abincin atare suna fira,abunda basu ta6a yi ba ita da amrish,
Wuraren ƙarfe 9,Sehrish ta farka daga bacci tana ta faman yin hamma wata irin matsiyaciyar Yunwa ce ta addabe ta,Saukowa tayi daga saman gadon babu kowa a ɗakin,duk sun fita yin breakfast,ita kaɗai ta rage,
Toilet ta shiga,shaf shaf tayi wanka after some minutes ta fito ɗaure da towel,gaban mirror ta zauna tana shafa mayukan jikinta,sai da ta kammala mulke ko'ina,Sannan ta ɗauki powder zata shafa,Kamar ance ta ɗago ta kalli mirror,kwatsam ba zato ba tsammani taga madubin ya koma mata tamkar tv,manya manyan bishiyoyi ta gani acikin daji ga wasu gwaggon burai gandara gandara masu uban gashi ajikinsu,Sae miƙo mata hannu suke yi ta cikin madubin suna kiran Sunanta"Sehrish kizo,Sehrish kizo"shi ne abunda suke faɗi
Gabanta ne yayi wani irin mugun bugu,Idanuwanta suka firfito waje tamkar ƙwayar idonta zata faɗo ƙasa sai kuma taga madubin ya koma lafiya lau,jikinta na kerma ta miƙe ta bar gaban madubin,Da sauri da sauri ta buɗe wadrobe ta ɗauko jallabiya ta zura ajikinta,Mayafin ma a hannu ta ruƙe shi,ko takalmi bata sanya a ƙafarta ba,Gudu gudu sauri sauri ta fito daga cikin ɗakin,
Lokacin da ta ƙaraso dining area din gaba ɗaya ta samu kowa zaune suna cin breakfast ɗinsu,tun daga kan Daddynsu Abusufyan,Oummansu da kuma su Hosana da Jahad,Ga Abba kuma tare da Mommynsu Alex,sai su twins da fawan kanal yousouf dasu Jabeer,Ganin Azmee tayi atsaye tana yin serving ɗinsu,Nan fa ta ƙara shan jinin jikinta,
Jiki asanyaye ta ƙarasa dining ɗin,hankalin kowa ya dawo kanta,
Fuskarta ɗauke da murmushi ta soma gaisar dasu"Abba ina kwana"
"Lafiya lou ƴan matan Abusufyan"murmushi ta ɗan saki tare da kallon Mommy"ina kwana mommy an tashi lafiya,
"Lapiya lou Daughter,"
Komawa tayi kan Daddynsu"Ina kwana daddy kun tashi lafiya,"
Fuskarshi ɗauke da murmushi Ya amsa mata"lafiya lou daughter,An sha bacci ko"?
Dariya sehrish ta ɗan yi tare da kallon Oummansu ta gaisar da ita,Sai da tabi kowa ta gaisar dashi,tana ƙoƙarin zama Abusufyan yace'baki ga Aunty Azmee bane?naga kamar baki gaisar da ita ba,"
Jimm ta ɗanyi kafin ta wurga eye balls ɗinta kan fuskar Azmee dake tsaye,murmushi ta samu akan fuskarta,
Ba don taso ba hakanan ta daure ta gaisar da ita"ina kwana Aunty Azmee,"
"Lafiya lou Sehrish,Yanzun nan nake shirin zuwa na taso ki sai gashi ma kin fito"
Baki asake Abu da sehrish ke kallonta,Ta ƙware wurin iya kisisina da munafurci,
Banza sehrish tayi,batare da ta tanka mata ba,
Zagayowa Azmee tayi wurinta tare da kai hannu ta ɗauki plate,Warmer ta buɗe mai ɗauke da farfesun Ƴan cikin shanu,Ta zuba ma Sehrish ta tura mata shi agabanta,
Zuƙunnawa tayi daidai saitin kunnan sehrish cikin raɗa tace"Nasan zaki ji daɗin shan farfesun nan,"
Tana kai ƙarshen maganar ta miƙe daga tsaye,kallon Oummansu tayi da ido tayi mata alamar ta kwantar da hankalinta,
Ajiyar zuciya ta ɗan sauke tare da zura yatsun hannunta cikin plate ɗin,A tsanake ta soma shan farfesun ba ƙaramin daɗi yayi mata ba,
Sai da ta nutsa cikin shan farfesun ta dinga jin motsin wani abu a hannunta,duk in takai hannu zata ɗebo ƴan cikin sai taji suna kufce mata daga hannunta kamar abu mai rai,hakan yasa takai idanuwanta cikin plate ɗin,Tsutsotsi ta gani suna yawo acikin plate ɗin manya manya,A wani irin firgice Sehrish tayi wurgi da plate ɗin ta fasa Uwar ƙara,Nan take ta shiga kwarara Amai,
Gaba ɗaya hankalin Kowannansu Ya tashi haiƙam,Mikewa tsaye su kayi suna kallonta,kowa na tambayar Lafiya,Da ƙarfi take ambaton Innalillahi wa'inna ilaihirraji'un Wayyo Allah na,Na bani na lalace Daddy,Oumma ku taimake ni,Naci tsutsotsi acikin cikina,
Tana magana amai na zuba daga bakinta,duk ya 6ata gaban rigarta jaga jaga,duk tabi ta gigice ta rikice,Watsa wa tayi da gudun gaske tana kuka ta nufi bedroom ɗinsu,A guje Suka bi bayanta
Toilet ta faɗa cikin fitar hayyaci ta nufi basin,Cigaba da kwarara aman tayi har saida takai ga babu abunda ke fitowa bakinta sai ɗigon jini ta ƙarar da koma da taci ko ruwa babu a cikinta,
Soso ta ɗauko tare da detergent ta zazzaga shi abakinta,Adai dai lokacin suka ƙaraso ƙopar toilet ɗin,sunyi ƙoƙarin su tura ƙopar amma ƙopar ta datse sakamakon Bugata da sehrish tayi bayan ta shiga,Ƙwanƙwasa ƙopar suka shiga yi kowa na ambaton sunanta,
'Sehrish!kizo ki buɗe mana ƙopa,kada ki Lahanta kanki fa,"muryar Oummansu ce keyi mata magana,tamkar zata fashe da kuka
Abusufyan ma murya na kerma yace"Wai baza ki buɗe mana ƙopa ba?meyake damunki ne?Dan Allah Daughter ki fito kiyi mana bayani,"
Kwata kwata Sehrish bata jinsu domin kuwa ta jima da makancewa,Ta fita hayyacinta,abunda ta gani a plate ɗinta keta dawo mata cikin kanta,
Tura soson tayi abakinta,Ta dinga gurzar bakin,har saida Le6enta suka faffashe jini ya soma zuba ta ko'ina abakinta,daga waje suka dinga jin Azababben kukan da Sehrish ke yi,na tashin hankali,
Da gudun gaske Abusufyan yabar ɗakin kaitsaye ya nufi upstairs don ya sanar da Sgr,Suzo su 6alle ƙopar kada ta kashe kanta,
Lokacin da ya shiga Part dinshi ko sallama babu,faɗawa kawai yayi gudu gudu sauri sauri ya shiga bedroom ɗinshi,Sai faman haki yake yi,A kwance ya sameshi yana bacci jikinshi sanye da jallabiya,
Tun kafin ma Ya ƙarasa wurin gadon ya shiga ƙwala mashi kira"Rafayet!Rafayet!!"
Farkawa Sgr yayi lokaci guda ya wurga idanuwanshi masu ɗauke da bacci kan Abusufyan dake ta kwala mashi kira,
"Uncle lafiya"?
"Ina fa lafiya!Ga sehrish can zata kashe kanta acikin toilet,bamu san meke damunta ba,sai ihu take tana kuka,Munyi munyi mu buɗe ƙopar ta datse ta,"
Tunkafin Ma Abusufyan yakai ƙarshen maganarshi,Sgr ya sauko daga saman gadon,da wani irin sauri ya fito daga part ɗin,gudu gudu sauri sauri Ya nufi bedroom ɗinsu,Abusufyan kuwa bai baro Upstairs ɗin ba sai da ya wuce ɗakin Omar ya taso shi daga baccin don abun kowa ta shafa,
Lokacin da Sgr ya ƙaraso ɗakin abun ya tashi hankalinshi sosai,Tunda ya shigo corridor ɗin ɗakin Ya fara jin sautin kukan da sehrish keyi,Tamkar ana zare ranta daga jikinta,
A sukwane ya faɗa cikin ɗakin,Ganinshi yasa suka matsa mashi daga wurin ƙopar,A zafafe ya daddage ya bangaji ƙopar da ƙafaɗarshi,Nan take ƙopar ta buɗe,Faɗawa cikin toilet ɗin yayi a lokacin Harta yanke jiki ta faɗi ƙasa,jinin da ya gani jaga jaga ajikin basin ɗin ba ƙaramin tayar mashi da hankali yayi ba,inda take kwance kasa ga soso nan a gefenta ga kuma ledar detergent ɗin da ta fasa,Bakinta yayi jaga jaga da jini fatar le6enta ta munana duk rauni,
Jikinshi Yayi mugun sanyi,yaso ace tun lokacin da ta fara haukan suka sanar dashi,slowly ya zuƙunna agabanta,tare da kai hannu ya tallabo kanta,da hannu ɗaya,Ɗayan hannun kuma zura shi yayi cikin bakinta Ya buɗe shi,runtse idanuwanshi yayi yayin da zuciyarshi ke ta faman tafarfasa,harshenta gaba ɗaya ya faffashe,detergent ɗin yayi mata illa sosai,duk ya sale fatar harshen nata,Yaji raɗaɗin abun har cikin zuciyarshi,miƙewa yayi azafafe ya juya yana kallonsu dayake duk sun shigo cikin toilet ɗin,Oummansu sai kuka takeyi,Haka su Jahad da Hosana ma,
"Tun yaushe ta fara wannan abun?meyasa ba'a sanar dashi ba!"a ruɗe yayi maganar
"Rafayet yanzu duk ba lokacin wannan bane dan Allah ka taimaka,kada mu rasata,"Abbansu Yayi maganar fuskarshi duk a hargitse
Juyawa yayi tare da sanya duka hannayenshi ya ɗaukota tare da ɗaurata saman kafadarshi,Ya fuce da ita daga ɗakin,A hanzarce Ya haura da ita Upstairs part ɗinshi,A saman gadonshi ya kwantar da ita,da sauri ya kuma saukowa down bayan ya ɗauki key Ya nufi medical Room ɗinsu,da kanshi Ya shiga duba Sehrish koda ta farfaɗo tana koke koke Allurar bacci yayi mata,
kowa ya shiga damuwa,abincin ma duk sun ƙoshi dashi,A ƙarshe saman Sofa kowa ya zauna cike da jimamin halin da Sehrish ta shiga,Abun ya ta6a masu zuciyarsu sosai,
Har lokacin abu bata daina kuka ba,Haka Jahad da Hosana ma
"Dan Allah ku kwantar da hankalinku,In sha Allah Sehrish zata samu lafiya,"acewar Kanal yousouf,
"Kusan kashe kanta tayi fa,Omo ta zuba abakinta ta wanke da soso,Ni bansan meke damunta ba,Sae faman ambaton tsutsa takeyi ni banga komai ba a plate ɗin abincinta,"Abusufyan ne yayi maganar idanunshi cike tab da kwalla,
"Dole akwai wani abun dake damunta,ni tsorona ma kada ta Zauce"
Abba da Mommy sai kwantar musu da hankali suke yi,
Hannun Abu sae kerma ya ke yi,acan ƙasan zuciyarta kuwa,tunanin yarda zata fallasa Azmee take yi don tasan cewa itace Silar Halin da Sehrish ke ciki,tayi jinkiri ne saboda bata jima da zuwa gidan ba,ba lallai bane su yarda da maganarta ba,
Miƙewa Tayi tare da kama hanyar zuwa kitchen,tana shiga ta samu Azmee tana gyara kitchen ɗin,hankalinta kwance,
"Meyasa kika yi mata haka"?ɗagowa Azmee tayi tare da kallon abu dake tsaye,lokaci guda ta saki murmushin gefen fuska tare da cewa"Bangane akan me kike magana ba"
"Amma baki da Imani!munafuka mai fuska biyu,kina son ki cutar da ita ne saboda kina tsoran karta tona maki asiri,shiyasa kike ƙoƙarin kashe mun ita"tana magana hawaye na zuba akan fuskarta,,
Girgiza kai azmee tayi"ko kusa ni bani da alaƙa da Abunda ya faru da Sehrish!kada kiyi mun ƙazafi,Ni bazan iya cutar da Sehrish ba,Saboda ina jinta tamkar ƴar cikina....."
Tunkan takai ƙarshen maganar a fusace abu tace"karki kuskura ki ƙara kwatanta sehrish da ƴar cikinki!mushirika kawai,muguwa kuma azzaluma!Makira!Ni bana jin tsoronki,Da Allah na dogara ba da wani tsubbace tsubbace ba irin naku,waɗanda suka jahilcewa addininsu,har yaushe ne zaku gane gaskiya ku daina aikata irin wannan mummunan zunubin da kuke aikatawa ne?Kuna ɗaukar kanku tamkar wasu shaggu saboda kawai kuna taƙama da tsafin da kuke dashi,In banda ma daƙiƙanci da jakkanci da jahilci irin naku,Kun manta cewa Allah shi ya halicce ku kuma a kowani lokaci zai iya ɗaukar ranku,Kuma zaku koma gareshi sannan ku gir6i abunda kuka shuka,akwai ranar da wannan sihirin da kuke taƙama dashi bazai ta6a amfanarku ba!tunda baku isa ko mutuwa ku hana kanku ba....."
Tunkan ta ƙarasa Maganar Azmee ta daka mata tsawa har sai da abu ta girgiza"Ya isa haka!ke baki isa ki ce zakiyi mun wa'azi ba!Idan ilimin addini kike taƙama dashi,ko ƙafata baki kama ba!ke kinsani basai na faɗa maki ba,Idan da naso tun lokacin dana zo gidanki yi maki wankan jego da tun lokacin Na murƙushe ki ke da ƴa'ƴan naki,Amma banyi hakan ba don baki acikin ainihin abun hari na,Idan har kika cika zaƙewa Wlh Zaki rasa Rayuwarki ne!Zanyi silar da zaki bar duniyar nan ne!
"Raina ba ahannunki yake ba!A hannun Allah yake,Idan har kinga na mutu to lokacina ne yayi,kuma koda ace Na mutu ta silarki,inaso ki sani kema wata rana zaki zo inda nake ne,kuma zaki yi bayani ne,banza kawai,ina ilimin da kike taƙama dashi ne?ai dake da dabba duk ɗaya kuke dan wlh ƙwara dabba dake Azmee,ita haka Allah ya halicce ta,Amma ke fa?mutunce wadda ta sani ta take sanin,ko yau kika