Showing 1 words to 3000 words out of 39148 words

Chapter 1 - Zawarci Book Compelet by Mrs Sadauki

[22/09 à 11:11] MRS SADAUKI 💫: *ZAWARCI*


LoVe aNd HoRrOr StOrY☠️

*Mallakar:* Chamsiya Laouali Rabo
(MRS SADAUKI💫✍️)

*Lambar waya:* +22795045822

*FIRST CLASS WRITER ASSOCIATIONS☀️*
Home Of Qualities And Trusted Writer's Of The Nation.

*Sadaukar wa:* Rahama Sabo Usman.


_____________________
21/09/24

1-2

#Damagaram

Ƙarfe uku na dare agogon ɗakin ya nuna,a sa'ilin da mutane ke kwance suna hutawa a daidai
wannan lokacin ne Hajara ta hana idonta bacci saboda yawunta da suke tsinkewa tsabar yadda
suke kwaɗayin ɗanɗanon jini.
Idonta ta fara rikiɗarwa tun farko kafin ta tura ƙofar ɗakin wacce ta yi sa'a ba a kulle ba,ɗakin
cike yake da duhu amma bai hana idon Hajara hango Safeenat ba wacce ke kwance ta tallabe
ƙaton cikinta tana sharara bacci.
Yawun Hajara suka ɗiga ga ƙasa lokacin da ta yi tozali da ɗan jinjirin da ke kwance a marar
uwarsa,ta ɗaga ƙafa da niyyar isa gare ta kawai sai ga wani haske da ba ta san daga ina ya fito
ba ya luluɓe Safeenat.Da wani mugun sauri ta yi baya tana zarar idonta da suke jawur kamar
wuta kafin kuma ta fice daga ɗakin gaba ɗaya,ba wai don ta haƙura ba sai don ƙara yin wani
sabon shirin.


“Hajara lafiya kika zo kika tsaya tsakiyar falo?” muryar mijinta Dayyabu ta daki kunnenta,da
mugun sauri ta lumshe idonta gudun kar asirinta ya tonu,ba tare da ta amsa masa tambayar ba
ta yi gaba ta koma ɗakinta ta ja ƙofa ta rufe.Sai a lokacin ta ja wani numfashi haɗi da buɗe idon,
ƙarƙashin gadonta ta je jawo wata tukunyar laka.Banda baƙin hayaƙi babu komai a ciki,wani
yare ta yi sai ga shi ta rikiɗe ta koma tsakaka haka ta fito ta fara bin bango ba ta zame ko ina ba
sai ɗakin Safeenat a karo na biyu.Har yanzu hasken bai ida gushe wa ba,wannan dalili yasa ta
sauka kan dressing mirror ta fiddo harshenta tare da fara zuba yawunta cikin man shafawa da

Safeenat ta bar shi a buɗe . Bayan ta gama ne ta ƙara bin bango ta fito mijinta ta gani ya buɗe
ƙofar ɗakinta ya shiga ya kuma fito da alamu rashin ganin ta ne yasa haka.

Da sauri ta koma ta je ta ɗauki siffarta ta bil'adama,gefen gado ta zauna tana jin har yanzu
kwaɗayinta bai kau ba.Haka wannan dare ya kasance daren rashin sa'a gare ta,sam ba ta yi
wani baccin kirki ba.


Washegari
Tun safe Safeenat ta yi wanka ta shafa mai da turare sannan ta shirya cikin doguwar riga
kasancewar cikinta ya tsufa ba ta da wata sutura mai yi mata in ba doguwar rigar ba.
Cikin sanyin jikin da ya zama tabi'arta ta fito,a falo ta tarar da ahalin gidan kan table suna cin
abinci.
“Daddy ina kwana?” ta gaishe da mahaifinta,ya amsa cikin sakin fuska yana cewa “ lafiya lau
Feenat ya ƙarfin jikinki?”
“Alhamdullah!” ta amsa tare da maida dubanta gefen Hajara ta ce “ina kwana Gwaggo?”
Hajara ta haɗe rai ta ce “ da ban kwana ba za ki gan ni ? Tsabar munafurci ba ki tashi fito wa ba
sai da baiwarki ta gama girki kin fito ki kwashi banza to ban girka da ke ba”


Feenat ta sunne kai tana jin wani irin zafi na tasowa daga ƙasan zuciyarta,babban takaicinta
kuma da ta ji Daddy yayi shiru bai ce komai ba.Yaran Hajara Munir da Munira suka shiga yi
mata dariya,ba ta kula su ba ta wuce kitchen ɗin ta nema wa kanta abin da za ta ci.Ƙasan tile ta
zauna dirshen ta soma tunanin bayan ta gama cin abincin,hawaye suka zubo mata ba ta shirya
ba da sauri kuma ta dafe ƙaton cikinta da ke faman juyawa tana jin muguwar ƙaunarsa don a
yanzu shine kawai zai rage mata raɗaɗin rashin masoyinta Bashir.



“A yi dai mu gani in tusa ta hura wuta! Yo wannan kukan shi zai maido miki mijin? Ai dama duk
abin da aka yi shi da cin amana ba zai je ko ina ba.Yanzu da kika yi sanadin hana Bashir auren
Murjanatu ina ce ya mutu ya bar ki,kuma ita Murjanatun na can Saudi Arabia cikin gata tana
auren farin ciki” Goggo Hajara ta faɗa lokacin da ta tarar da Feenat a kitchen tana kuka.Ta yi
kutufo da ƙafafunta ta ce “ ja ki ban wuri na wuce ko kuma na sabanta ki muguwa mai halin
uwarta” da mugun sauri ta janye ƙafafunta wani sabon kukan na ƙwace mata.
Cikin masifar nan Goggo Hajara ta ci gaba da balbale ta da masifa,“ ki tashi ki fitar min daga
kitchen zan ɗora girki ,ki koma can ɗaki ki ci gaba da munafurcinki”

Daga bakin ƙofa Daddy ya ce “Hajara ki zo ina son ganin ki ɗakina”

Idonta kamar za su faɗo ƙasa tsabar yadda take hararen Feenat,haka ta wuce ta je ɗakin
Daddy a tsaye ta tarar da shi ya ba ƙofa baya.

“Daddyn yara ga ni ” ta faɗa cike da ladabi.
“ Haja ki kiyaye ni,bari gani na ƙyale ki ɗazu kin ci mutumcin ƴata,na yi shiru ne kawai don in
nunawa Feenat ba ta kyauta da ta bar ki ke ɗaya ki ka yi aikin gida ba .Amma ba zan lamunci
ki tozarta min ƴa ba,nan gidana ne don haka tana da ƴanci sake wa yadda take so.Mine ne na
yi mata gori? Maimakon ki rarrashe ta akan halin da take ciki shi ne za ki tsiro mata da wata
sabuwar masifar? Ta rasa mijinta wannan kaɗai abun tausayi ne,sannan ga tsohon ciki.Na san
tun bayan da Feenat ta auri Bashir ki ka tsane ta,kin manta cewa matar mutum kabarinsa tun
can farko Allah bai nufa Murjanatun ce zai aura ba”


Cike da munafurci Goggo Hajara ta soma kuka har da jan majina kamar wata yarinya,da mugun
sauri Daddy ya juyo tare da jawo ta jikinsa yana cewa “mine ne kuma na kuka? Ke fa uwa ce
bai kamata sai an faɗa miki abin da ya dace ba,ɗa na kowa ne ba ka san mai taimakon ka ba”

“Amma Daddyn yara ka fi kowa sanin yadda na riƙe Safeenat da zuciya ɗaya amma rana tsaka
ta ruguza alaƙar nan don kawai ta ga banda burin da ya wuce Murjanatu ta yi aure”

“To ai yanzu komai ya wuce,ba ga shi ta yi auren ba? Jiya ma mijinta ya min magana kan yana
so ta dawo gida ta haihu ”

Jin ƴarta za ta dawo sai ta manta da zancen kuka ta washe baki ta ce “au ! Madallah! Yaushe za
ta zo?”

Daddy ya murmusa ya ce “a'a ƴarki ta ce kar a sanar da ke za ta yi miki bazata kawai ki zamana
cikin shiri” da wannan Daddy ya fice ya bar gidan zuwan can Company wurin aikinsa.
Goggo Hajara kuwa kitchen ta koma sai ta tarar da Feenat ta ɗora girkin rana sai gumi take
saboda zafin wutar gas,ta taɓe baki kafin ta fito.
Ita kuwa Feenat baiwar Allah sam ba ta ƙaunar tashin hankali wannan ya saka ta ɗora girkin
duk don a zauna lafiya.Kafin ta gama jikinta ya soma ƙaiƙayi, soshe-soshe ta fara yi ganin abun
na ta yin gaba yasa ta kashe gas ɗin ta fito.Ɗakinta ta je,direct toilet ta shiga ta soma yin wanka
sai dai ba ta canza zane ba sai ma wani ja da fatarta ta yi.Dakyar ta daure ta je ta ida girkin ta
zuba a kuloli ta jera kan table,da ta koma ɗaki sai ta ɗauki hoton hannunta inda alamun jan ya fi
yawa ta tura wa ƙawarta Sakeenatu tana tambayarta ko mene ne wannan kasancewarta likita
.Babu jimawa ta kira ta bayan sun gaisa ne take cewa “ sai dai ki zo asibiti a duba ki ta waya ba
a ganewa,kuma ni ba aikina ba sai dai na haɗa ki da likitan fata”

Feenat ta ja ajiyar zuciya ta ce “ KEENAT kin san Daddy ba zai bari na fita ba,kuma dama bai
dace mace mai takaba ta fita ba”
Cike da tausaya wa KEENAT ta ce “ na sani amma ai lafiya ta fi komai ,ƙila kuma kin ci wani
abu ne da ya haifar miki da hakan”
“Ban ci komai ba fa,ya aikin ana ta fama ko?”
“Wallahi kuwa,in sha Allah in na sauka zan biyo nan gida na duba ki” sosai suka yi hira kafin su

yi sallama.
Daga inda take zaune ta fara kallon hotunan Bashir inda yake sanye da Kakin soja,nan ta lalace
wurin kallonsu har sai da Munira ta shigo kiranta .Ta miƙe dakyar ta fita,a falo ta tarar da Goggo
Hajara tun da ta fito ta lura idonta na kan cikinta.Ta sunne kai tana mai karanta ‘ Hasbunallahu
wani'imal wakil ’ a can ƙasan zuciyarta,cikin nata ne ya soma yin motsi kamar zai fito mata ta
cibiya.Tsabar yadda take jin ciwon juyinsa yasa ta kai hannu ta dafe ƙasan mararta tana mai
fitar da nishin wahala,ido rufe ta ci gaba da sauraren azabar da ke ratsa duk sassan jikinta.

Goggo Hajara ta yi wani makirin murmushi tana mai cewa “ Safeenat lafiya kuwa?”
Sai a lokacin ta ware idonta da suka yi wani mugun ja,bakinta sam ba zai buɗu ba ballantana ta
iya yin magana.Bayanta da ƙugunta suka ƙage lokaci guda wanda ya haifar mata duƙawa ba ta
shirya ba,tuni idonta sun fara ganin dishi-dishi duk da wannan ne cikin farko tuni ta fahimci
haihuwar ce ta zo bilhaƙi.

Goggo Hajara ta ce “ Haihuwa ce kam,Munira fita waje bari na ɗauko leda ”
“Mama in kira mai taxi ku wuce asibiti ko?” Munira ta faɗa tana kallon Safeenat wacce tuni ta
fara wani gurnani mai haɗe da nishi.
“Uwar mai taxi za ki kira ,fice na ce” Goggo Hajara ta faɗa tana mai shiga ɗakin Safeenat ta
ɗauko robar da aka tanadi duk wasu kayan haihuwa.
Da kanta ta shimfiɗa leda ta ɗora wasu zannuwa akai kafin ta ce “ Safeenat ki cire rigar nan mai
haihuwa ina ruwanta da wata sutura” tsabar azabar da take ji yasa ba ta yi yunƙurin hana
Goggo cire mata kayan ba.

Yawun Goggo Hajara har wani dalala suke suna tsinkewa lokacin da ta ga kan ɗa ya sawo
kai.Jikinta har rawa yake wurin taimakawa yaron ya fito ,babu wani jinkiri ko ɓata lokaci ta fara
juya ido tare da soma kai wa kurwar jinjirin hari sai dai ba ta ida cin galaba ba nishin Safeenat
haɗi da kukan wata babyn ya dawo da ita hayyacinta.

Ƙirjin Goggo Hajara ne ya kusan ɓallewa zuciyarta ta faɗo tsabar firgici,jaririyar da faɗo cibinta a
yanke yake sannan kuma babu marakiya saɓanin shi namijin da har yanzu take masa reto.
Sai a lokacin ne ma ta samu zarrar yanke mahaifar,ba tare da kuma ta san dalilin kawar mata
da mugun nufinta ba ta soma kimtsa Safeenat wacce babu laifi ta dawo hayyacinta.


Goggo Hajara ta wanke kayan da kuma gyara ɗakin ta saka turaren wuta,ita ce kuma ta zaɓo
wa Safeenat riga da zane.Har da haɗo mata tea mai zafi ta sha,gefe ta koma bayan ta gama
komai tana tunanin zuci ‘ mi ya shiga kaina ni Hajara? Kamar ni kamar ba ni ce ba’ kukan
jariran ne ya katse mata tunani ,ta ce “ ki ɗora su ga abincinsu” sai kuma miƙe ta soma nuna
mata yadda za ta yi.Namijin kawai ya sha ita kuwa macen baya ga kuka babu abin da
take,Goggo Hajara na ɗaukar ta sai kuma ta yi shiru kamar ba ita ce ke kukan ba.Muƙut ta
haɗiye wasu yawu hango wani baƙin kallo daga cikin ƙwayar jaririyar da ko minti talatin ba a yi

ba da haihuwarta......
[22/09 à 19:14] MRS SADAUKI 💫: *ZAWARCI*


LoVe aNd HoRrOr StOrY☠️

*Mallakar:* Chamsiya Laouali Rabo
(MRS SADAUKI💫✍️)

*Lambar waya:* +22795045822

*FIRST CLASS WRITER ASSOCIATIONS☀️*
Home Of Qualities And Trusted Writer's Of The Nation.

*Sadaukar wa:* Rahama Sabo Usman


_____________________
22/09/24


3


Sannu a hankali Gwaggo Hajara ta soma jin wani sanyi na ratsa ɓargo da tsokarta,kamar
wacce aka yi wa doli kuma ta ƙi kawar da dubanta daga cikin idon Babyn.Idonta suka soma
kafewa saboda wata irin shaƙa da ta ji an yi wa wuyanta,babu shiri ta buɗe bakinta na maita
kurwar jaririn da ta soma cin galaba kansa ta fara fitowa daga can cikin hanjinta tana fitowa ta
bakinta .Wani koren hayaƙi ne ya soma shiga cikin jaririn wanda daga bakin Gwaggo Hajarar
yake fitowa,wata irin atishewa ya soma yi kafin ya tsala kuka.


Da mugun sauri ta yi baya ta zauna kan kujera,idonta na kan babyn wacce tuni ta soma bacci.
“Gwaggo ya ƙi yin shiru ko cikinsa ke ciwo?” Safeenat ta faɗa kamar za ta yi kuka tana ririga
yaron,ran Gwaggo Hajara ne yayi mugun ɓaci sai yanzu tunaninta ya dawo a tunzure ta ce “
uban mi zan yi masa to? Lokacin da na yi haihuwata uban wa ya kama min wurin rainon ? Ki
riƙe abin ki” ta faɗa tare da ajiye mata babyn kusa da ita,jikin Safeenat sai yayi sanyi dakyar ta
samu yayi shiru bacci ya ɗauke shi.Ta shimfiɗe shi kusa da Baby girl ɗin kafin ta je ɗakinta don
ɗauko wayarta,tana dawowa sai ta hangi maciji kan jaririyar duk ya naɗe jikinta da shi ba ta san
lokacin da ta saki wata ƙara ba wacce ta yi daidai da ɓacewar macijin.Safeenat ta zo da mugun
sauri ta ɗauki yaranta ta mayar da su ɗakinta,sai da aka ɗauki lokaci kafin nutsuwarta ta dawo
ta soma kiran mutane tana shaida musu zancen haihuwar.Hatta Daddy sai da ta kira shi ta
sanar da shi,babu jimawa kuwa sai ga ƙanwarsa Habiba ta zo gidan sosai Safeenat ta ji daɗin

ganinta musamman da ta ga har da ƙullin kayanta ta zo da alamu za ta jima.


Ruwan zafi ta je ta ɗora cikin ƙatuwar tukunya kafin ta dawo,“ Safeenat ya zama doli ki kula da
yaran nan musamman namijin don na ga shi ne mai rauni” Habiba ta faɗa tana shafar twins ɗin.

“In sha Allah Gwaggo Habibah zan yi,da alamu ma ya fi kuka dakyar na samu yayi baccin nan”
cewar Feenat.

“Hum! Baccin wahala ne,ah to ai doli ma yayi Allah dai ya kyauta”

“Amen!" Feenat ɗin ta amsa ba tare da ta san dalilin Gwaggo Habibah na faɗar haka ba.Bayan
ruwan sun tafasa ta juye su ta yi wa yaran wankan,namijin ana saka shi a ruwa ya farka tare da
canyara kuka amma ita hajiya babba har aka gama wankan tana bacci tamkar wacce ba ta
rai.Gwaggo Habibah kuwa sai murmushi take tana jin wani farin ciki ƙasan ranta,dama ita Allah
bai taɓa bata haihuwa ba .

Safeenat ma sai da ta yi wanka da ruwan zafin ta gasa kanta da kyau ta fito ɗaure da towel,sai
kuma yanzu ne Gwaggo Habibah ta lura da yadda fatar Safeenat ta yi ja.Da wani mugun sauri
ta tashi ta cabke hannunta da ke ƙoƙarin ɗaukar kwalbar mai,“ jira na duba na gani” ta faɗa tana
mai duba man ba tare da ta ce komai ba sai kuma ta fita direct ɗakin Gwaggo Hajara ta wuce
ko sallama ba ta yi mata ba kuwa ta yi tsaye kai gare ta tana mai cewa “ an gaishe da uwar
mugaye ta duniya,wato baƙar zuciyarki na nan daram babu canji .To asirinki ya tonu na ga
bala'in da kika zuba cikin man shafawar Safeenatu,sai dai ki sani sai dai ki ci kanki amma Twins
sun fi ƙarfinki ”

Da wani mugun sauri Gwaggo Hajara ta tashi zaune,dama tun bayan da ta shigo ɗaki take jin
duk jikinta babu daɗi dalilin kwancin da ta yi kenan sai kuma yanzu da ƙanwar mijinta ke feso
mata kalaman rashin mutumci.Wani makirin murmushi ta yi kafin ta ce “ da alamu dai kin manta
wace ce ni ko Habibah? Amma za ki gani” “Babu abin da zan gani sai alkhairi...”
“Eh lalle wuyanki ya isa yanka” Gwaggo ta faɗa tana juya ido,Habibah ta tuntsire da dariya ta ce
“au kin zata guntun tsafinki zai iya yin tasiri a kaina? To ki canza shawara tun wuri bai ƙure miki
ba don yanzu daidai nake da ke”



Ganin alamun tabbas ba Habibar da ce ke tsaye a gabanta ba yasa Gwaggo Hajara haƙura da
surkullen,idonta masu cike da mugunta ta tsura mata ta ce “ mi ya kawo ki ɗakina?”
“Ina so ki fita sabgar Safeenat da ƴaƴanta,in kuma ba haka ba....” sai kuma ta yi shiru tana cije
baki haɗi da jinjina kai.
“Ki tona min asiri? A tunaninki akwai wanda zai yarda? Hahaha! Yaro man kaza,Habibah kar ki
manta hatta gyatumarki a tafin hannuna take....” ta yi saurin katse ta da “sai dai shi wanda kike

tutiyar da shi mugun tsafinki bai yi tasiri kansa ba ,na san kin san haka”

Ran Gwaggo Hajara ne ya ƙara yin baƙi,duk duniyar nan Habibah ce kawai ta zame mata ciwon
ido duk yadda take son gudanar da lammuranta to muddin tana ga wuri sai ta roga su.


Ƙarar buga ƙofa ce ta maido ta daga guntun tunanin da take,ta bi bayan Habibar da mugun
kallo tana jin baƙin cikin da ba ta da MAITAR IDO (MRS SADAUKI,duk mai son complete book
ɗin nan zai iya tuntuɓa ta kai tsaye ta lambar da na rubuta a can sama) da tabbas ta jefa wa
Habibah ƙwayar cutar da za ta zama ajalinta.



SAKEENATU

Tana tashi daga aiki ta fito don samun adaidaitar da za ta kai ta can gidansu Safeenat kwatsam
sai ga kiran wayar mijinta Abbas .
“Mamuh ta ce yau ba ki bar mata abin da za ta ci ba ina

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login
google.com, pub-9213700357025247, DIRECT, f08c47fec0942fa0