Showing 30001 words to 33000 words out of 39148 words

Chapter 11 - Zawarci Book Compelet by Mrs Sadauki

taɓa sanin haka ba sai jiya da na yi wa Maryam
shi.Bakina na ɗora kan lips ɗinta ,tun ina yi a hankali har na soma zaƙewa saboda abubuwan
da nake ji su na ratsa ni.Zuciyata ce ta ƙara ƙarfin gudu jin Maryam na mayar min da martani,ba
sai an faɗa min ba ita ma koyo take kamar dai ni tun da jiya ne muka fara sanin al'amarin.Kiss
ɗin ne na ji bai isa na haɗa da romance,rigar jikinta na yi nasarar cire wa na soma sarrafa
ta.Kuka ta soma yi min wannan yasa na mirgina baya ina mayar da numfashi,ta tashi zaune ta
ɗauki rigarta ina kallonta na ga ta mayar da abar ta kafin ta dire daga bed ɗin.Sam ban yin
ƙoƙarin hana ta ba sai ma haushin kaina da na ji,ƴar ƙanƙanuwa yarinya ta kwance min tunani
abun takaicin kuma ƙanwar abokina.Na ja wani numfashi tare da ɗauko pilow na rungume.Shiru
na yi ina tunanin kaina ‘ yaushe na samu wannan canji? Sanina dai sai lokacin damina kawai
sha'awa ke damuna,ko kuma in an yi ƙololuwar sanyi’ sai kuma na ja tsuki a fili wani sashen
zuciyata na bani amsar da ‘ ƙila don yanzu an yi maka aure ne an gama ka da mace ɗaki guda’
da sauri na miƙe na shiga toilet jin abin na sake yin gaba-gaba.
Shower na sakar wa kaina,ina tsaka da wanka na soma jin wayata na ruri.Kiran Ammy ne don
waƙarta ta musamman ce,a gaggauce na yi wankan na fito.Ina maida kiran amma ba a
ɗauka,gabana ne ya shiga faɗuwa ina shirin aika wani saƙon text ɗinta ya shigo ``` Heemu ƴan
ta'adda sun tare motarmu a hanya ba zan iya ɗaukar kira ba don tuni sun sauko mu ƙasa an
fara lalubar wasu ma```


Ji na yi kamar an buga min wani ƙaton dutse a kai,da sauri na saka kakina na soja da
bindigogi.Jikina har rawa yake,ko kallon inda Maryam take ban yi ba na fita da gudu-gudu.Ina

cikin mota na kira Daddy na shaida masa amma yake min zancen banza wai kar na je na jira
zai tura sojoji amma ina tuni na soma bibiyar layin Ammy na ƙure gudun mota.

Tsawon lokaci ina sharara gudu kafin kira ya shigo da lambar Ammy,na ɗauka da mamakina sai
na ji muryarta ce.“Sun yi tafiyarsu sun gudu! Sun bar mu lokaci guda bayan sun yi mana mugun
duka Heemu ” na rumtse ido haɗi da jan wani dogon burki ina sauraren yadda Ammy ke rera
kuka,dakyar na ce “ gani nan zuwa Ammy don Allah ki bar kuka ki na ɗaga mini hankali” “ Kar ka zo Heemu yanzu ai za mu tashi daga nan...” daidai nan kiran ya katse,a ta na'urar da
na jona nake bibiyar Ammy na ga sun fara gusawa daga wurin alamun motar ta tafi.Amma duk
da haka bai sa na koma ba,haka na ci gaba da gudun kusan a tare muka shiga gidan Bus ɗin ni
da motarsu.
Ko jira ban yi ba na nufi motar,ana buɗewa na shiga ciki na riƙo Ammy.Fuskarta ta yi ja sosai ga
sawun yatsu nan kwance raɗau,haka na fiddo ta na kai ta motata ina jin haushin kaina.Asibiti na
wuce da ita duk ƙoƙarin hana ni da ta yi a cewar ta lafiyarta lau kawai kanta ke ciwo,sai ga shi
da muka je asibitin an ce jininta ya hau.Ƙarin ruwa suka saka mata,ina daga gefenta zaune ina
saƙar zuci so nake yi na yi mat tambayoyi amma ina jiran har ta dawo hayyacinta.
Kamar ta san abin da nake saƙawa a rai sai cewa ta yi “sun tafi da wasu daga cikinmu Heemu”
Na dube ta da sauri,idonta na lumshewa take ci gaba da cewa “da dukkanmu za su tafi da mu
sai ogansu ya samu kira bayan ya dawo daga wayar ne yake cewa a tafi da iya maza kawai a
bar matan”
“Da yayi wayar ba ki ji abin da ya ce ba?”na yi tambayar zuciyata na mugun bugawa,Ammy ta
ce “ban ji ba,sai dai lokacin da ɗaya daga cikinsu yake tambayar ogan mi yasa ba za a tafi da
mu duka ba sai ya ce umarnin Dagaci ne”
Dagaci babban ɗan ta'adda ne shine shugaban duk wasu manyan-manyan ƴan daba don
ƙungiyarsu guda ce. Shiru na yi ina wani tunani haɗi da zargin da ban son ya zama gaskiya ,sai
dai duk yadda nake son tunkuɗe zargin abin ya cuttura sai ma wasu abubuwa da suka faru
masu kamanceceniya da suka shiga dawo min. Ganin Ammy ta samu ta yi bacci na miƙe na fita waje na kira lambar Daddy,bugu biyu ya ɗauka
kafin ya ce “ina jin ka” sam yanzu babu alamar tashin hankali ba kamar ɗazu da na sanar da shi
an kama Ammy kuma gani a hanya zan je ƙwato ta.


“Ya ake ciki ka aika sojojin ne?” na jefo masa tambayar ,shiru yayi bai ce komai ba har sai da na
sake maimaita tambayar sannan ya ce “ka ga Abraheemu aiki nake ” ƙittt ya katse kiran.Na bi
screen ɗin wayar da kallo ina juya maganar Daddyn.Karon farko da na tuna ina da wasu abokai
na biyu bayan Abakar ,zama na yi na dinga gwada wayarsu babu wacce ta shiga sai ta mutum
ɗaya ya na ɗaga wa ya ce “ya ne Soldier Man ya ƙarin haƙurinmu?”
“Alhamdullah! Shamssudeen don Allah ina son ganin ka akwai aikin da nake son ka yi min”
Ya ce “yanzu dai ina kan hanya mun je Katsina wani aiki sai gobe za mu koma Kano”
Na ɗan nisa na ce “fatan kun yi nasara?”
Ya ce “eh mun kama biyu daga cikin yaran Dagaci”
Da sauri na ce “yaran Dagaci ka ce?”

Ya ce “eh zuwa jibi za a wuce da su Abuja”
Wani irin daɗi na ji ta faɗi gasasa kenan.Na ce “to kawai zan bari har ku ƙaraso Abujar ido da
ido ma za mu fi fahimtar juna” nan muka yi sallama sai a lokacin kawai na je na yi
sallolina,Ammy na farkawa na bata jus ta sha magani kafin mu wuce gidanta.....
[01/10 à 12:03] MRS SADAUKI 💫: *IBRAHEEM*
```soldier man```

© Chamsiya Laouali Rabo
#MRS SADAUKI💫✍️

*FCWA ☀️*

#Sadaukarwa ga duk waɗanda suka taɓa rasa wani jigo nasu a soja.Allah jadadda rahama a
gare ka Yayana AbduRashid😓



9-10





Maryam ganin irin halin da Heemu ya fita duk sai hankalinta ya tashi,don ba za ta manta ba
irinsa ne Yayanta Abakar ya fita lokacin da ya samu kiran da za a aika su can wurin yaƙi.
Tsoro,fargaba da kuma yunwar da take ji duk suka taru suka yi mata mugun bugu.Sallah ma
dakyar take tashi ta yi,ga yunwa sai addabar ta take amma ba ta iya sauka ƙasa.Sai dab da
magrib ne Granny ta hauro sama,shi ma don ta yi wa Ibraheemu tsiya ne ta ce tun da yayi aure
shikenan sai ya ƙumshe a ɗaki .
Maryam ta gani a yashe kan capet ,ta nufe ta da sauri ta na tambayar ta lafiya.Lumsasun idonta
ta zubawa Granny kafin ta buɗe baki dakyar ta yi mata bayani,Granny ta shiga taɓa hannuwa ta
na cewa “ shine sai ki zauna yunwa ta kashe ki a ɗaki? Ko ki na tsoron saukowa ai kya yi
magana ƴan aiki su kawo miki.Shi ma dai Baba da nasa laifin ka aje ƴar mutane ka yi tafiyar ka
shiru ” sai kuma ta fito ta sauka ƙasa ta sa cikin masu aiki aka haɗa abinci aka kai mata can
sama,dakyar Maryam ta haɗa tea ta sha ai kuwa ta soma jin hanjinta na kuka.Babu jimawa fara
kakarin amai,da sauri ta miƙe ta shiga toilet ta amaye shi.
Ƴar aikin da aka turo ta soma yi mata sannu,Granny ma ta shigo toilet ɗin tare da cewa “ki haɗa
mata ruwa masu ɗon ɗumi ta yi wanka”
Cike da ladabi ta ce “ to Hajiya ” sai kuma ta nufi bahon wankan ta soma haɗawa ta na zuba
kayan ƙamshi da sabulu da ta gama duk suka fita.
Maryam ta cire kayanta sannan ta shiga,ta jima sosai ruwan na ratsa ta kafin ta soma cuɗa
jikinta.Ta zubar da ruwan sannan ta ƙara tara wasu ta ɗarwaye jikinta sannan ta ɗaura towel ta

kuma yi alwala don tuni an soma kiraye-kirayen sallar magrib.

Ko da ta fito doguwar riga ta saka ,ta yi sallah ta na nan zaune Granny da ƴar aikin suka shigo.
“Ki zuba mata kunnun in ta sha sai ta ci abincin,ya jikin naki Maryama? Ko sai an kira likita?” da
sauri ta girgiza kai ta ce “ ai na yi dama kawai dai Yaya Heemu nake son gani” sai hawaye
shaaa .
Granny ta ja ajiyar zuciya kafin ta ce “ bari na kira Isah na tambaye shi ina kuma ya tura miki
miji daga farfaɗowar shi daga jinyar damuwa,kika ce kakin soja ya fita?” Maryam ta gyaɗa kai
alamun eh sannan ta karɓi kunnun wanda ake yi da fulawa da madara ta soma sha.
“Je ki ɗauko min waya ta tsakar falo na kira na ji” Granny ta faɗa sai dai kuma kafin ma ta tashi
jiniya ta cika gidan mai nuni da Daddy ne ya dawo “ bari ma ga shi nan ya dawo bari na sauka
na ji” ta faɗa tare da tashi ta sauko ƙasa.


Babu jimawa kuwa Daddyn ya shigo maƙarabansa na take masa baya,ya na ganin Granny ya
sallame su duk suka fita daga falon.
“Barka da shiga dare Mama” ya faɗa da murmushi kan fuskar shi.
Ta ce “ yawwa! Ina ne ka tura Babana ya fita hankali tashe?”
“Babu inda na aike shi Mama,wani abu aka yi?”
“Maryama ta faɗa min ta ga ya fita cikin kakin soja”
“Ibraheem ne bai ji ko kaɗan Mama,ko na hana shi abu sai yayi” ya faɗa tare da nufar sashensa
don ya matsu yayi tozali da abincin ruhinsa.Granny ta bisa da kallo kawai kafin ta je ɗauko
wayarta,lambar Heemu ta kira amma ba ta shiga haka ma ta Ammy a doli ta koma can wurin
Maryam.

“ Mi ya ce?” Maryam ta jefo mata tambaya, Granny ta ce “ lafiyarsa lau kin san halin Babana
komai cikin sauri,abin da bai kai a ɗaga hankali ba shi wurinsa babba ne”
Maryam shiru ta yi kawai,ɗan salade ɗin da ta soma ci ta ture kafin ta tashi da gudu ta koma
bedroom ta haye gado ta shiga raira kuka.


Hankalin Granny duk ya tashi ta rasa yadda za ta shawo kanta kawai sai ta zuba mata ido,har
ƙarfe ɗaya na dare Maryam ba ta yi bacci ba ta na ta tsumayen zuwan Heemu amma shiru bai
dawo ba.Zuwa wannan lokacin ƙarfin kukan ma ya ƙare sai hawaye kawai,farashin zazzaɓinta
kuwa sai ƙara hauhawa yake.Bacci ne ɓarawo ya kwashe ta,yayin da Granny kuma ke kan
sallaya ta na ta yin addu'o'in tsari wa jikanta don ita ma hankalin ta ba kwance ba.

DADDY

Yadda ya tarar da Zee cikin muguwar shigar nan,ya sallama kawai yau ba zai samu jam'in
sallah ba.Abun nema ya samu sai wani shagwagwaɓe wa yake kamar wani ƙaramin yaro, Zee
na basa abinci a baki bai san ta haɗa masa tarko iri-iri ba sai da suka shiga turaka Zee ta soma

zayyano masa irin style ɗin da take so.
A matuƙar buƙace yake amma sam ba zai iya yin abin da take so ba,a shagwaɓe ta ce “ Baby
ka na fa iyawa kawai tsoro kake ji ”
Ya ce “ ki duba shekaruna mana Baby,ki tausaya mini na yi aiki na gaji sosai”
Ran Zee yayi matuƙar ɓacewa don ita fa ta fi son style irin na turawa,dakyar ta danne zuciyarta
ta basa haɗin kai amma fa sai ta nuna ta yi fushi ta barsa nan bedroom ta shige toilet ta na ta
rusa kuka da ta gaji ta shige cikin bahon wanka a nan ta yi baccinta

#SOKOTO

Tsawon wannan wunin bisa kulawa ta Ammy ta yi shi,har ta shiga baccin dare ban bar gadinta
ba.Wuraren biyu na dare na yi alwala sannan na kwanta kan doguwar kujerar da ke nan
falo,kwanyata na buƙatar hutu amma sam na kasa bata shi shuɗaɗiyar rayuwarmu nake tuna
wa ni da Abakar tun daga ranar da Daddy ya zo ya ɗauke ni. Muna wasa ni da Abakar mun dawo daga makaranta,daidai ƙofar gidanmu Daddy na gani a
tsaye ya na murmushi ya ce “na zo tafiya da kai IBRAHEEM zan tafi da kai babban birnin Abuja
na mayar da kai SOLDIER MAN ”
Abakar na kalla yayin da shi kuma yayi saurin saka hannu ya riƙe ni gam alamun kar na
barsa,kai na girgiza wa Daddy na ce “ a'a ni ba zan je na bar ƙanena ba” don haka nake kiransa
zan girme masa da shekara biyu haka.
Daddy ya ɓata rai kafin ya je ya fizgo ni ya raba mu ni da abokina,ko Ammy ban yi wa sallama
ba haka ya saka ni mota ya tafi da ni Abuja .Makarantar yara ya saka ni wacce tun nan ka zama
soja sannan yayi tafiyarsa,duk wani horo da ake mini ina daurewa ne saboda yadda zuciyata ta
dake su kuwa sosai suke jin daɗin haka ba su yi ƙasa da gwiwa ba suka sanar da Daddy a
ranar da ya kawo min ziyara sai dai sun faɗa masa da matsala don ko bacci nake ina yawan
kiran sunan Abakar.
Kimanin watana biyar kenan da zamana soja na koyi abubuwa da dama daga ciki akwai rashin
tsoro,ido na tsura masa babu tsoro ko shakka na ce “ ina son Abakar shi ɗin ƙanena ne amma
ka raba mu,muddin ka na son na ci gaba da zama a nan to shi ma ka kawo shi ”
“ Kar ka damu yarona in dai wannan ne babu matsala in dai iyayensa sun yarda” “na sani sam
Umma ba za ta ƙin yarda ba Please Daddy ” sumba ya mini a goshi ya ce “ farin cikin ka shine
nawa Heemu” jin haka yasa na saki raina na soma karɓar aikina yadda ya kamata ashe duk
idonsu na kaina ko motsi na yi sai sun sanar wa Daddy. A ranar da na cika shekara ɗaya ,a kuma wannan ranar aka kawo Abakar .Da murna muka
rungume junanmu ya ce “ aboki duk ka yi baƙi ka ƙara tsayi”
Na sakar masa murmushi na ce “kai ma haka za ka koma” mun yi hira sosai kafin a ja shi izuwa
sashen ƴan level ɗinsu.Duk yadda kuwa na so mu kasance tare doli aka raba mu don ba lokaci
guda aka ɗauke mu ba,wuraren da muke haɗuwa su ne cin abinci,wanka da kuma training.
Abokan karatu waɗanda muke level guda tuni sun fara sabawa da Abakar,ko irin in muna hira in
na yi fushi in su na son na sauka daga fushin sai su yi min hirar Abakar .Cikin soja muka ida
wasarmu ta yarinta,haka cikin soja muka girma duk inda za mu je a tare muke zuwa Ammy da
ummar Abakar sau ɗaya kawai suka taɓa kawo mana ziyara a shekaru biyar ɗin da muka
kwashe a ciki.

Sai da muka mallaki hankalin kanmu ne sannan aka fara barin mu fita.

“Heemu ba ka kwanta ba?” muryar Ammy ta katse mini tunanina.Na ja ajiyar zuciya na ce “
Ammy har kin tashi wai?”
Hawayen fuskata ta goge kafin ta ce “ mine ne haka Heemu? Kamar wata mace shine kake
hawaye?” na riƙo hannuwanta na ce “ na tuna abokina ne ”
“Ka yi masa addu'a ta fi wannan hawayen ”
Na ce “ Ammy Abakar ma ya na cikin waɗanda ba a samu gawarsu ba,sai nake ji a jikina
tamkar zan iya ganinsa a kowanne lokaci ”

“Na dai fi son ka sa a ranka ya rasu,tun da akwai waɗanda boom ta tashi da su ƙila shi ma ya
na ciki”

Na ja wani gwabron numfashi ina tunawa na ga agogon Abakar a ofishin Daddy.
“Ka je ka kwanta don gobe za ka yi sammako”
“Zuwa ina?” na yi saurin tambayarta.
“Ban son muso za ka koma ” daga haka ba ta ƙara cewa komai ba ta yi gaba.

Washegari kuwa tun da safe ta tirsasa mini doli na bar Sokoto zuwa Abuja,sai da na tsaya na
sha mai sannan na ɗau hanya.Ko da na iso gida rana ta yi wantsar,ko da na shiga falo babu
kowa direct kuma na wuce can sama.Ina tura ƙofar na soma jiyo shashekar ta,Granny ta juyo
muka haɗa ido ta saki murmushi ta ce “ alhamdullah ga Babana ɗin nan ya dawo sai ki yi
breakfast ɗin ai yanzu”
Maryam ta dubo ƙofa da sauri kuma ta tashi ta rugo kamar za ta faɗi ta yi wani tsalle ta riƙe ni
gam.Na lumshe ido ina mai sa hannuwana na tallabo ta da kyau,wani siririn kuka ne take
rerawa wanda yake samun wuri a zuciyata.
” Yi shiru mana ai gani na dawo” na faɗa ina mai bubuga bayanta,Granny ta tashi ta fice ni kuwa
a hankali na soma takawa da Maryam tallabe a ƙirjina har na isa bedroom.Kan gado na kwantar
da mu har yanzu kuma ta ƙi sakinazafin jikinta kuma na ratsa ni.Na ja ajiyar zuciya tare da ɗan
jaye ta muna kallon juna da idonta da suka yi ja tsabar kuka,“ mine ne?” “Tun jiya ka tafi ba ka dawo ba na ji tsoro sosai kar kai ma....” ban bari ta ida furicin nan ba da
na san ba mai daɗi ba ne kawai na ɗora bakina kan nata.Shiru ta yi sai yanayin sheɗarta da ya
sauya,sama da minti biyar ina kissing nata kafin na janye na miƙe tsaye kan ƙafafuna.Daga inda
take kwance take kallona ta na murmushi,ni kuwa kayan jikina na rage na shiga toilet ina wanka
ina tunanin sabon al'amarin nan da ke faruwa da ni.Tun da nake ban taɓa yin budurwa ba
amma mugun son kasancewa nake yi

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login
google.com, pub-9213700357025247, DIRECT, f08c47fec0942fa0