Showing 9001 words to 12000 words out of 39148 words
Chapter 4 - Zawarci Book Compelet by Mrs Sadauki
abar ai ta san wake nake ci mi yasa ba ta dafo ba?”
“Yi haƙuri Mamuh gobe sai a daf....” bai rufe baki ba Mamuh ta saka kuka yana cewa “ shinenan
tun da mata ta fi uwa”
Da mugun sauri Sakeenatu ta ce “ bari na koma gida sai na dafo mata”
Abbas ya ce “ to ki yi sauri” ta yi tunanin shi zai kai ta amma sai kuɗin ɗan sawu ya bata,tana
zaune tana hawaye har suka iso gida ta biya shi kuɗin kafin ta wuce ciki.
A gaggauce ta soma aikin tana mita “ an yi tsohuwa kamar mayya kullum wake yanzu nan in
ban wanke shi ba sai ta sani mtsww ” ta ja tsuki tana dirje waken amma jin ita ma an ja mata
tsuki yasa ta zabura tana dube-dube sai dai babu kowa.Watsar da tunanin ta yi ta ci gaba da
aikinta wani tsukin ta kuma ji sannan ana magana ƙus-ƙus,gabanta ya faɗi jin tamkar ana tafiya
cikin falo.Tana shirin fitowa aka ɗauke wuta,lalubo ta soma yi cikin duhu ko Allah yasa ta ɗauko
wayarta ta kuwa yi sa'a ta samu jakarta hannunta har rawa yake ta zuge zip ta ciro wayar sai ta
ga saura ƙiris batirin ya mutu alhalin a cike ta bar ta.Tana ƙoƙarin ganin ta kunna fitilar ta ji
tamkar saukar huci kusa da ita,ta wani juyo da sauri ta inda take jin abin tare da haska hasken
screen babu kowa sai ƙafafuwan ƙofato da ta yi arba da su babu kuma gangar jiki.......
My book is only 500 via 6042551755
Hassana ibrahim
Keystone bank,DM +22795045822
[26/09 à 08:25] MRS SADAUKI í ½í²«: *ZAWARCI*
LoVe aNd HoRrOr StOrY☠️
*Mallakar:* Chamsiya Laouali Rabo
(MRS SADAUKIí ½í²«✍️)
*Lambar waya:* +22795045822
*FIRST CLASS WRITER ASSOCIATIONS☀️*
Home Of Qualities And Trusted Writer's Of The Nation.
*Sadaukar wa:* Rahama Sabo Usman
_____________________
26/09/24
9
Babu shiri Sakeenatu ta saki wayar ta arta a guje,sai dai ta nemi ƙofar fita ta rasa saboda
mugun duhun da ya mamaye gidan baki ɗaya.Cikin ƙanƙanan lokaci duk ta firgice,dakyar ta iya
samu ta fito tsakar gida da lalabe zuciyarta sai ƙara tsananta gudu Waige-waige ta fara sai ta
ga ashe kaf unguwar ne babu wuta,ba ta gama daidaita numfashinta ba wata baƙar mage baƙa
ƙirin ta soma yin kuka miyau!miyau! Kukanta duk ya cika gidan.
Ta ɗaga kai dakyar ta dubi inda sautin kukan ke fitowa,ido huɗu suka yi da magen wacce
hasken idonta yake kamar na lantarki sai canza kaza suke.A hankali ta sauko daga katangar ta
soma nufo inda Sakeenatu ke tsaye da gajiyayun ƙafafunta,Allah ya gani ba ta wani ba wai
karatun addini muhimmanci ba dukkan lokacinta da hazaƙarta ta zuba su ne a harakar boko
wannan ya sa ba ta iya wasu addu'o'i ba .A halin yanzu da take tsaye ta yarda kuma ta aminta
rayuwarta na cikin haɗari,tabbas ta san wannan magen ba normal ba ce muguwa ce cutar da
ita za ta yi.
Ta na dab da ta kawo kusa da ita ta samu bakinta na furta “ la haula wala ƙuwata illa billah!!!”
ƙiiii magen ta wani ci burki tana mai canza salon kuka zuwa na jarirai amma sam Sakeenatu ba
ta yi gigin yin shiru da bakinta ba sai ma ƙaimi da ta fara wurin maimaita addu'ar.A gaban idonta
magen ta soma mayar da idonta kamar na mutane kafin ta ruga a guje ta yi tsalle ɗaya ta haye
katanga,daidai nan kuma aka maido wuta yaran unguwa suka hau ihun murna.Sakeenatu ta ja
ajiyar zuciya tana mai yin hamdala ga Ubangiji,bakinta bai gushe ba yana ta furta lahaula wala
ƙuwata illa billah a haka ta koma can ciki.Gas ɗin ta kashe saboda muguwar gajiya da ta saukar
mata wacce ba ta san dalili ba,wayarta ta ɗauka Allah yayi sa'a babu abin da ya same ta abun
mamaki kuma yanzu cajin wayar a cike yake saɓnin ɗazu da aka nuna mata ta kusa mutuwa.
Lambar Nafisa ta kira,tana ɗauka babu wani tsaya wa gaisuwa ta ce “ Nafi ki turo min karatun
nan da kike saurare don Allah duk dare”
“Anty Sakeena lafiyar ki kuwa?”
“Ki turo min karatun dai don Allah ina son saurare ”
“Ok to bari na hauda data yanzu zan turo miki”
“Yawwa ina jira” ta faɗa tare da kashe kiran,ita ma datar ta kunna babu jimawa kuwa karatun ya
shigo suratul Baƙara ce ta turo mata sai Yasin .Tamkar abun tsiya network ɗin ya ɗauke ɗif ko
ɗaya babu wanda ya buɗe,juyin duniya ta yi amma sun ƙi buɗewa har wayar ta kashe ta kunna
amma network ɗin ya ƙi yi.Cike da damuwa ta sake kiran wayar ƙanwarta,tana ɗauka sai ta rasa
abin da za ta ce mata kawai ta fashe da kuka.Daga can ɓangaren Nafisa ta ce “ subahanallah!
Anty Sakeena don Allah mike faruwa? Mike damun ki?”
Cikin muryar kuka take cewa “ Nafisa tsoro nake ji! A tsorace nake ji nake kamar ba ni ɗaya ba
ce cikin gidan nan tamkar ina ....inaaa” ta kasa ida maganar saboda motsin da ta gani ana yi
can cikin labule wanda ta tabbata kuma ba ɓera ne ba saboda girman halittar.Ihu ta fasa ganin
ƙatuwar gafiya ta faɗo timmm da ƙasa,yayin da kuma wata ta biyu ita ma ta sake fitowa a guje
ya kama waccan wacce ta faɗo a gaban idonta suka soma faɗa suna cizon junansu.Babu shiri
Sakeenatu ta haye ɗaram kan bed ta na kuka,Nafisa na jin haka ta ziri hijabi ta fito ko Mamarsu
ba ta sanar ma ba ta fito ta samu ɗan sahu.Allah yayi sa'a ba wani nisa ne sosai a tsakaninsu
ba,da gudu ta shigo gidan tana ambaton sunan Allah daidai nan gafiyoyin suka yi ɓatan dabo
hatta.
Nafisa ta je ta rungume ƴar uwarta wacce da ace tana da cutar asuma da tuni numfashinta ya
fita,“ yi shiru don Allah ya isa yi min bayanin mike faruwa? Ina shi Abbas ɗin?”
“Yana asibiti wurin Mamuh,na dawo na dafa mata wake da shinkafa ne shi ne ake ta firgita ni”
nan ta kwashe duk abin da ya faru ta shaida wa ƙanwarta.
Nafisa ta ja dogon numfashi bayan ta saurare ta,sannan ta ce “ wannan duk sharrin miyagu ne
shi yasa a kullum ake son bawa ya keɓe wani lokaci don nemawa kansa kariyar ruhi da gangar
jiki ba wai gyaran duniyarka ba kawai.Ni wallahi na fara zargin Mamuh ɗin nan,kina dai ganin
yadda Ma'idah ta caka mata cokali da dukkan alamu ta hango abin da idanunmu basu gani.In
ba masifa ba cikin daren nan za ki dafa mata wake kamar mayya,ke ƙila ma ita ce.Tashi mu je ki
yi alwala ai zama bai gan ki ba tun da kin ji kin gani aure a inda ba a ƙaunar ki”
Da taimakon Nafisa ta yo alwala dama ita Nafisar kusan kowanne lokaci tana da alwala mace
ce mai riƙo da addini ba ta da sake,hasali ma malamar makaranta ce a wata islamiyya.
Karatun Alkur'ani ta soma koya wa Sakeenatu kamar wata ƴar yarinya haka take biyawa inda ta
yi kuskure kuma ta gyara mata.
“ Ki kasance kullum cikin tsarki bima'ana alwala saboda tana da muhimmanci sosai wurin bada
kariya,ko sheɗanu suna shakkar mutum mai zama da alwala a koyaushe,ke ko period kike to ki
yi abarki sannan ki riƙe azkhar na safe da maraice”
“Amma ai kin san ban iya su ba ko?”
“Ki koya mana anty Sakeena ,shi ilimi ai bai da ƙa'ida shekaru ko tsoho ɗan shekara ɗari zai iya
shiga makaranta ballantana ke da ko talatin ba ki kai ba”
“ Ni rubutun larabcin ne ke bani wuya ”
“Zan nemo miki littafi mai fassarar Hausa ,sai na dinga koya miki yanzu bari na tura miki app ɗin
Alkur'ani sai ki dinga saurare ”
Ta karɓi wayarta ta tura mata tare da saita mata komai ta kunna sautin ya soma tashi,ta ce “ to
ni zan tafi gida ko Mama ban sanar ma ba”
“ Don Allah Nafisa kar ki tafi ki bar ni ki jira har Abbas ya dawo,bari na kira Mamar na shaida
mata” haka suka yi kuwa,tun suna jiran Abbas har ƙarfe sha biyun dare bai zo ba a tare suka
fito suka rufe gida da ko ina sannan suka je suka kwanta.
A can asibiti kuwa bayan fitar Sakeenatu,Gwaggo Rahamu ta yi wani kishingiɗa ga kujera
kamar mai bacci nan kuwa ruhinta ne ta soma fitar wa daga gangar jikinta.Sawun Sakeenatu ta
bi,hasali ma ta rige ta zuwa gidan duk abin da take yi akan idonta hanyar farko da ta soma bi
shi ne tafiya ta shiga tunanin mai kula da nepa na unguwar ya ɗauke wuta ba tare da shi kansa
ya san dalili ba a cikin wannan duhun ne ta yi ta yi wa Sakeenatu mugunta.Da ta koro ta da
addu'a shine ta biya wurin wasu miyagun ƙawayenta ta basu address suka je a siffar gafiya,su
ma ba su bar gidan ba sai zuwan Nafisa.
Abbas na daga can gefe Mamuh na yi masa hira tana murmushi saboda duk abin da ke faruwa
ita tana gani saɓanin shi Abbas ɗin.Bayyanar esprits biyun yasa yanayin shaƙar iskan ɗakin ta
sauya saboda tsabar muguntar su, wannan karon hatta Abbas sai da ya ji wani iri.Har yanzu
Gwoggo Rahamu ba ta farka daga baccin ƙaryar da take ba,cikin hirarsu ta ƴan duniyar ɓoye
suke bata labarin yadda suka firgita Sakeenatu tana ta yin kuka.
“Na gode sosai ƙawayena,kar ku manta in kun gama yawon Maitar dare ku biyo ta nan mu sake
komawa mu uku mu haɗa ƙarfi mu shayar da ita mamaki” baƙin ruhin Gwaggo Rahamu ya faɗa
,suka yi dariyar mugunta tare da ɗaukar mata alƙawari kafin su bar wurin.Cikin ƙwarewa ta
dawo da ruhinta a gangar jikinta,ta dubi Abbas tana mai cewa “ bacci ya ɗauke ni duk yau ban
rintsa ba,ina sauran waken ni ma na ci yunwa nake ji”
Shi Abbas sam ya manta da wani zancen wake saboda yadda Mamuh ke masa hira,sai yanzu
ya tuna Sakeenatu ta je gida dafawa.Da ya duba agogon hannunsa ransa ne yayi mugun ɓaci,“
uwar tamu ai ba ta dafo ba tana can tana gantalin da ta saba,ah to dama su likitoci ba su da
kamun kai tsakaninsu da abokan aikinsu suke neman juna in aka ce miki tana can asibiti wani
ƙato ya taushe kar ki yi gardama” Mamuh ta faɗa ,yayin da Gwaggo ta karɓe “ i sosai ita ma
wannan shegiyarta ta ai shugabansu ne ya ɗirka mata cikin ya bar yaronmu da wahala,wai
Abbasi wai ya ƙaƙaba maka aurenta?”
Kasa cewa komai yayi,haushi goma da gomiya tara ya rasa da wane zai ji abin ka kuma da
zuciyar namiji sai ya ji zargi ya ɗarsu a ransa.Da ya nuna zai je gida Mamuh ta hana shi tafiya
ta hanyar amfani da tsafinta,haka suka dinga kwaso sharri iri-iri suna yaɓa ma Sakeenatu sosai
kuma suke samun gurbi a zuciyarsa.Can waje ya koma ya kwanta kan wani banci yana ta
tunanin rayuwa baya yadda neman aurensa ya kasance yadda sam Sakeenatu ba ta samu
shaidar ƙwarai ba ga mutanen unguwa amma ya rumtse ido ya ce sai ita .
Ƙarfe biyu da rabi na dare ƙawayen Gwaggo Rahamu suka biyo mata,kafin su yi tsinke gidan
Sakeenatu.Sai da suka shiga kitchen suka cinye kaf abincin da ta dafa sannan suka dawo falo
suka fara shawarar abin da za su yi mata,suna dariyar mugunta suka tura ƙofar falon sai dai da
zarar sun yi niyyar ɗora ƙafarsu a tile ɗin bedroom sai su ji tamkar cikin garwashin wuta ne suke
ɗora su.Gwaggo Rahamu ta ƙanƙance ido tana kallon gefen Nafisa inda kusan kanta ta ɗora
wayarta ne sautin karatun Alqur'ani na tashi a hankali wanda ba ma a jinsa sosai,kamar ta san
suna nan kuwa sai ta kai hannu ta ƙara volume a tare suka saki wani ihu wanda sai da gidan ya
girgiza a firgice Sakeenatu ta farka tana zarar ido
My book is only 500 via 6042551755
Hassana ibrahim
Keystone bank DM +22795045822
[28/09 à 08:36] MRS SADAUKI í ½í²«: *ZAWARCI*
LoVe aNd HoRrOr StOrY☠️
*Mallakar:* Chamsiya Laouali Rabo
(MRS SADAUKIí ½í²«✍️)
*Lambar waya:* +22795045822
*FIRST CLASS WRITER ASSOCIATIONS☀️*
Home Of Qualities And Trusted Writer's Of The Nation.
*Sadaukar wa:* Rahama Sabo Usman
_____________________
28/09/24
10
A wahalce Gwaggo Hajara ke bin bango don isa ɗakinta,fatar nan tata ta tsakaka duk ta yi wani
taushi ta fara fitar da wani fanko.A yadda bango ke zuzar fatar cikinta ji take kamar ta yi ta
ƙurma ihu sai dai ba dama sata lahira! Tana isa ɗakinta ta ɗauki siffa ta mutum nan ne fa ta yi
tozali da yadda duk jikinta ya kumbura yayi ja kamar wacce aka soya,mai ta ɗauko ta shafe
jikinta da shi tana matsar ƙwalla tare da jin tsanar Safeenatu na sake feso mata daga can ƙasan
zuciyarta.
A fili ta furta “ sai na wulaƙanta rayuwarki,sai na saka kin tozarta a duniya,sai na shayar da ke
gubar azaba wacce sai kin gwammaci mutuwa akan rayuwarki. Ke kan ki Habibah ba zan bar ki
ba zan ɗora miki karatu da alamu har yanzu ba ki ji jiki ba shi yasa kike taimaka wa wata wurin
ruguje plan ɗina” shiru ta yi jin an turo ƙofa.Daddy ne ya shigo da sallama a bakinsa,ba ta amsa
ba sai ma saurin jawo hijabi da ta yi ta saka duk ta luluɓe jikinta.
“Ni kam Hajara lafiya kike? Kin ga yadda fuskarki ta yi suntum sai huci take kamar ƙullun wainar
da ya ji yis?” Daddy ya faɗa yana ƙare mata kallo.Wani ƙululun baƙin ciki ne ya ƙara turnuƙe
Hajara ta ce “ uwar waina ce....” ba ta ida kai aya ba ta ji yatsun Daddy biyar kan
kuncinta,shaye da mamaki take kallonsa nan ta hango wani baƙin tauraro tsakiyar goshinsa
wanda ko shakka babu aikin Habiba ne ta tura masa shi.
Ba ta gama dawowa daga duniyar mamakin da ta je ba Daddy ya soma magana cikin masifa,“
wato abun naki ya fara zama iskanci,daga tambaya shine za ki zagin uwata saboda kin san yau
za ta zo.To tsaya ki ji Hajara duk wata tijararki ki tattara ta ki ajiye wuri guda muddin Hajiya ta
koma da baƙin cikinki gida to wallahi akan aurenki.Ki tashi ki ɗora girki tsabar lalaci muna da
mai jego a gida amma kin zo kin shige ɗaki kin haye gado tare da saka hijabi kamar matar liman
kowacce za ta yi aikin ƙwarai” yana gama faɗa ya nufi ƙofa,sai kuma ya juyo ya ce “ Murjanatu
na kan hanya sai ki fara shirin tarben ta” kawai ya fice.
Gwaggo Habibah da ke zaune kan kujera a falo ta saki wani irin murmushin nasara,tun da
uwarta ta haife ta yau ce ranar farko da ta juya taurarinta na baiwa ta yi aiki da su.Tun bayan
da ta yi wa Twins wanka ta shirya su sannan ta bai wa uwarsu abin da za ta ci kawai ta fito falo
ta zauna,Daddy na fitowa ta soma yi masa transfer ɗin tauraron ta hanyar kallonsa tsakiyar ido
da farko har ya tambaye ta lafiya sai kuma yayi shiru jin sabon abu a tattare da shi.
Duk abin da yake faɗa wa Gwaggo Hajara sarai ta ji alamun aikinta yayi kyau,ta saki
murmushin nasara tana mai cewa ‘ mijinki zai zame miki kumurci,da haka zan raunata muguwar
zuciyarki’
“Habibah karɓi wannan ko kuna da buƙatar wani abu sai a ɗauka ciki” Daddy ya faɗa yana mai
katse mata tunanin zuci.Ta karɓa tana mai cewa “ Yaya Ɗayyabu na ce bayan biki sai
Safeenatu ta koma can gida wurin Hajiya ko?”
“Saboda me? Ba a nan za ki zauna ba?”
“Eh to ni ma da haka na ce ɗin amma sai na ga kamar anty Hajara ba ta son zamana tun da na
zo idonta kamar za su faɗo tsabar yadda take jifana da mugun kallo”
Ran daɗi ya ɓace, yanayin fuskarsa ya canza tuni tauraron goshinsa ya ƙara yin baƙi ba tare da
ya ce komai ba ya ƙara komawa ɗakin Gwaggo Hajara ita kuwa Habibah har da wata dariyar
mugunta ta yi tare da tashi tana taka rawar murna.
Daddy na shiga ɗaki ya yi wa Hajara wankin babban bargo,ko ina ana jin muryarsa yadda yake
yi mata masifa in ta je yin magana kuma sai ya gwaɓe bakin.Da wannan baƙin cikin ya fita ya
bar ta,sai da ta sha kuka wiwi sannan ta fito ta ɗora girki babu jimawa kuwa sai ga Hajiya ta zo
.A ladabce Gwoggo Hajara ta gaishe ta wanda sosai ita hajiyar ta yi mamaki don rabon da ta yi
mata irin wannan ladabin tun ranar da Ɗayyabu ya kawo mata ita a matsayin matar da zai
aura.Cikin sakin fuska ta amsa tare da cewa “ to barkarmu Safeena an sauka Allah raya kan
sunnah,kin samu mai taya ki aiki da kuma miji” Hajiya ta faɗa tana murmushi a doli ita ma ta yi
murmushin yaƙen a can ƙasar zuciyarta tana cewa ‘ an haifo mana masifa dai aljanar jaririya
muguwa wacce ta yi gadon jaraba ’
“Zan shiga daga ciki” hajiyar ta faɗa tare da nufar ɗakin Safeenatu,cike da murna ta zauna tana
kallon jariran Gwaggo Habibah ta ɗauki namijin ta bai wa Hajiya ta karɓa tana mai kai masa
sumba haɗi da yi masa addu'a sannan ta miƙa shi.Ana ɗora mata macen jikin Hajiya ya ɗau
kyarma kamar mazari,murya na ɗan rawa ta ce “ wane suna za a saka musu?” “Basheer da Baseerat ” Habibah ta bata amsa tana murmushi tana kallon mahaifiyarta wacce
kambun muguntar Gwaggo Hajara duk ya dabaibaye ta yanzu