Showing 6001 words to 9000 words out of 39148 words
Chapter 3 - Zawarci Book Compelet by Mrs Sadauki
wannan farar tinkiyar?” ta yi
tambayar tana zunɗen Ma'idah wacce ta tsorata da ganin Mamuhn. “Ina wuni Mamuh? Fatan na same ku lafiya?” Abbas ya faɗa cike da ladabi.
“Ka bani amsa ta”
“Ma'idah ce fa ƴar wurin Keenat” ya bata amsa a sanyayye.
“Shegiya za ka ce wacce ba a san taƙamaimai wane ne ubanta ba,kai da ka iya
kwashe-kwashe ka rasa wacce za ka auro sai wadda ta gama yawon duniya ta tsiyayar da duk
ƙwayaƙwayin haihuwarta a titi.To ban yarda ban lamunce wannan tinkiyar ta zauna a gidan nan
ba” Mamuh ke faɗa cikin masifa ita kuwa Ma'idah tuni ta soma kuka musamman irin abin ban
tsoron da take hangowa a fuskar Mamuh.
Abbas ya sunne kai ya ce “ a dai yi haƙuri Mamuh dukkan bawa bai wuce jarabawa,Ma'idah ita
yarinya ce ba ta san komai ba”
“Wallahi sai ta bar gidan nan” Mamuh ta faɗa cikin ƙaraji, Sakeenatu kuwa banda kuka babu
abin da take yi .
Hannun Ma'idah ta kama da niyyar jawo ta,ita kuwa baiwar Allah cike da tsoro ta ɗauki cokali
mai yatsu ta caka ma Mamuh ita a ido da zumar ceton kanta ga dodo.
Wani uban ihu Mamuh ta yi tana cewa “wayyo idona! Ƴar daba ta kashe ni” jikin Abbas na rawa
ya je ya kamo Mamuh wacce tuni idon ya soma fitar da jini,hankali tashe ya soma goge jinin
wani na zubowa a doli ya kama ta zuwa asibiti.
Bayan tafiyarsu ne Nafisa ta soma tofa ma Ma'idah addu'o'i saboda yadda take wani irin kuka
tana firgita,cikin kuka Sakeenatu ta ce “ Nafisa ki ɗauke ta ku wuce gida don Allah”
“Ke kuma a nan za ki zauna? ”
“To ina zan je Nafisa? Haƙuri zan yi dama aure ya gaji haka sanin kan ki ne a can gidan ba wani
jituwa muke ba ni da Mama ta ɗauki ƙiyayyar ɗan farin ta ɗora min”
“To amma dai ki kula da kan ki,in kin ga abin ya yi yawa kawai ki tawo gida”
Kuɗi ta basu sannan suka bar gidan,ita kuma ta ɗauki waya ta kira Abbas don jin asibitin da
suke shi da Mamuh yana shaida mata ita ma ta fita ta je.Tuni Mamuhn ma ta yi bacci an naɗe
idon nata da bandeji ga kuma ƙarin ruwa an saka mata.
Jikinta a sanyayye ta ce “ ka yi haƙuri” Abbas ya kamo hannunta ya ce “ dama haka Allah ya
tsara,ina Ma'idah?”
“Nafisa ta koma da ita can gida”
“Don me? Zan rarrashi Mamuh na san za ta amince ta zauna da mu”
Ta sakar masa murmushi ta ce “ na gode sosai da kawaicinka gare ni” wani kallo yake aika
mata yana mirza tafin hannunta,da ido ɗayan mai lafiya Mamuh ke kallonsu tana jin wani irin
haushi da takaici.
“Mine ne haka? A asibiti fa muke ka bari har mu koma gida” Sakeenatu ta faɗa tana janye jikinta
daga nasa ganin abin zai wuce gona da iri.
“Mu je gidan to tun da kin ga Mamuh ta samu bacci ,sai mu dawo daga baya” Abbas ya faɗa
yana langwaɓar da kai saboda ba ƙaramar kewar ta yayi ba.
“To ai na farka” cewar Mamuh tana mai tashi zaune haɗi da hararen Sakeenatu,da ɗan sauri ya
miƙe yana tabayarta jiki.“ Ka kira likita ya cire min ƙarin ruwan nan sai mu wuce gidan tun da
uwarka ba za ta barin ka cikin salama ba” cewar Mamuh a zafafe,Abbas ya fita don kiran likita.
“Duk tsiyarki dai ba za ki iya canza ma tuwo suna ba,Abbasi ɗana ne ba naki ba don haka ni ke
da iko da shi ba ke ba.Kuma wannan shegiyar taki sai ta san ni ta caka da cokali sai na shayar
da ke mamaki”
Da wani mugun sauri Sakeenatu ta je gaban Mamuh ta tsuguna ta ce “ don girman Allah
Mamuh ki yi haƙuri , Ma'idah yarinya ce ba ta da wayo ko me za ki yi to ki yi min amma kar ki
taɓa ƴata” ta ƙarashe maganar hawaye na zubo mata saboda zuwa yanzu ta yarda Mamuh
muguwa ce.
Kafin ta kai ga bata amsa Abbas ya shigo shi da likita,ya ce “ sai kin yi kwana uku sannan za
mu sallamar ki”
“To ka sanar da uwarmu wacce ta matsa mu je gida” Mamuh ta faɗa a zuciye tana hararen
Sakeenatu.
Likitan yayi murmushi ya ce “ yanzu yadda za a yi sai ka nemo wacce za ta zauna da
Mama,amma gaskiya ba za mu sallame ta ba yau” sai yayi wa Mamuh allurar bacci,duk yadda
masifa ke cin ta haka ta haƙura saboda ƙarfin allurar.
Shi kuwa Abbas Gwaggonsa ya kira wacce ke nan Damagaram ita ke bi ma Mamuh,babu
jimawa kuwa ta zo .Ya ja matarsa zuwa gida,cike da zallar soyayya suka gamsar da junansu.
SAFEENATU
Tun bayan da kowa ya watse aka bar su ita da Gwaggo Habibah sai ta nutsu sosai kafin ta ce “
Gwoggo ni kam ɗazu wani abin ban mamaki ya faru,maciji na gani ya naɗe Baby girl ɗin nan ina
yin ihu ya ɓace kamar aljani ”
Gwaggo Habibah ta yi murmushi ta ce “ kar ki wani ji tsoro,sannan ina so ki kwantar da
hankalinki duk wani abu da za ki gani ki yi shiru da bakinki.Duk kusan ƴan biyu suna da wannan
baiwar,to ke macen ce ke da shi don haka ki shirya ganin abubuwa iri-iri wasu na tsoro wasu
kuma na almara”
Safeenat ta ja wani numfashi kafin ta ce “ to Allah cire min tsoron” ba ta ida rufe bakinta ba
hasken ɗakin ya ɗauke duhu ya turnuƙe shi kai ka ce dare ya tsala.Duk tsit suka yi babu wanda
ya ce wani abu,sai kukan jaririyar da ya soma tashi sannu a hankali tsawon minti biyu kafin ta yi
shiru.Hasken ɗakin na dawowa Safeenatu da Gwoggo Habibah suka yi ƴar rige-rigen ɗaukar
babyn duk suka yi tsaye suna kallon yadda goshinta ke fitar da wani haske yana ƙyalli a gaban
idonsu ya ɗauke sai ga shatun haƙoran maciji ya bayyana raɗau .Safeenat ta kai hannu ta shafi
wurin sai kuma ya ɓace,ta ja ajiyar zuciya tana mai ɗaukar jaririyar ta soma shayar da ita.
Daddy ya yi sallama ya shigo,duk suka gaishe shi kafin a basa babys ɗin ya gani.Sosai yayi
musu addu'a sannan ya fita,haka suka ci gaba da yin hirarsu har dare ya tsala.Duk sun yi shirin
bacci za su kwanta amma ita Baby kamar ɗiyar aljanu ta ƙi baccin sai ma wani kuka-kuka da
take yi.
“Safeenat ki bata abincinta mana” Gwaggo Habibah ta faɗa tana shirin tashi ta kunna wuta.
“Ina ta ƙoƙarin bata ta ƙi karɓa” cewar Safeenar.
Kusa da ita ta zauna tana shirin ɗaukar babyn sai ta lura da yadda hannunta na hagu ke fitar da
wani zane mai hasken wuta kamar ta murhu.Wani irin murmushi ne ya suɓuce wa Gwaggo
Habibah ba tare da ta shirya ba cike da murna ta jawo hannun jaririyar ta riƙe sannu a hankali
har zanen ya fito raɗam letter M ta fito sai a lokacin kuma jaririyar ta yi shiru sai ajiyar zuciya da
take saukewa.
A ɗan ruɗe Safeenatu ta ce “Gwaggo mine ne kuma wannan?”
Sam Gwoggo Habibah ba ta bata amsa ba sai safar hannu da ta je ta binciko cikin kayansu ta
saka wa hannun mai zane.“Daga yau kar ki ƙara barin hannunta a buɗe ki dinga saka mata
safar hannu ”
“Gwaggo ina tambayar ki mine ne ba ki bani amsa ba”
“Alama ce ta prophétie/prophecy,da yawan ƴan baiwa tana soma aiki ne in sun kai shekara sha
takwas amma ke yarinyarki tun farkon dirowar ta duniya tata baiwar ta fara aiki.Ta ceci ɗan
uwan tawaicinta sannan kuma ta ceci ƙawarki Sakeenatu ”
Ba don ta fahimci zancen da kyau ba ta ce” mi ya samu Keenat ɗin?”
“An yi mata ajiya cikin ruhinta ta yadda esprit zai samu damar yin yanda ya so da gangar jikinta
har ya cutar da ita”
“Ya aka yi kika sani to?”
“Safeenatu yi bacci in lokacin fahimtarki yayi babu buƙatar ki yi tambaya”
Da wannan duk suka yi bacci, Safeenatu na tsaka da yin mafarki akan goben ƴarta Gwaggo
Habibah ta tashe ta daga bacci.“Ruwan wankan ki na can toilet ta tsakar gida,ki je yi wankan
sabulu kafin na zo na gasa miki jikinki da towel”
Ta yi miƙa ta tashi a gajiye saboda kwana dare ta yi tana shayarwa,sai da ta ɗauki wani zane da
hijabi sannan ta fita ta bar Gwaggo Habibah za ta yi wa Twins wanka.
Sakeenatu na fitowa suka yi kiciɓis da Gwoggo Hajara ta gaishe ta sannan ta wuce toilet.Ita
kuwa tsabar mugunta yasa ta koma ɗakinta ta yo shirin mugunta yau ma siffar tsakaka ta ɗauka
ta yi tsinke can toilet inda Safeenatu ke wanka tun tuni.Da ga can saman katanga Gwaggo
Hajara ke ƙarewa surar Safeenat kallo,cikin salon mugunta ta mayar da harshenta dogo sannan
ta zuro shi tun daga can sama har ƙasa yana taɓa tile.
Safeenatu ta yi wani ihu wanda bai sauka ko ina ba sai cikin kunnen ƴarta jaririya,kwacaaaa
Gwaggo Hajara ta faɗo cikin ƙatuwar robar tafasasshin ruwan zafi.......
Ga masu son fara yin payment su yi min magana ta lambata na basu detail na sabon account
number da za a tura kuɗin ba waccan na Ecobank ba.DM +22795045822
[25/09 à 09:17] MRS SADAUKI í ½í²«: *ZAWARCI*
LoVe aNd HoRrOr StOrY☠️
*Mallakar:* Chamsiya Laouali Rabo
(MRS SADAUKIí ½í²«✍️)
*Lambar waya:* +22795045822
*FIRST CLASS WRITER ASSOCIATIONS☀️*
Home Of Qualities And Trusted Writer's Of The Nation.
*Sadaukar wa:* Rahama Sabo Usman
_____________________
25/09/24
8
Da wani mugun sauri Safeenatu ta yi tsalle ta koma jikin ƙofa tana kyarma ,idonta ƙur cikin
robar wacce tsakakar ke ta ƙoƙarin fitowa daga ruwan .Ganin ta soma yin girma sosai yasa
Safeenatu ta buɗe sakatar toilet ɗin zane a hannu ta fito Allah yayi sa'a babu kowa a tsakar
gidan,dakyar ta yi ɗaurin ƙirji kafin ta nufi can ciki da gudu.
“Ke lafiyar ki?” Gwaggo Habibah ta yi tambayar .
Feenat ta dafe gefen zuciyarta da yake mugun bugawa ta ce “ tsaka...ka ce ta faɗa cikin ruwan
da nake wanka”
“Shi ne kike wannan haƙin? Kai Allah ya shirya min ke ban san lokacin da za ki girma ba”
“Gwaggo ba normal tsakaka da kika sani ba ce, wannan ƙatuwa ce inda kin ga yadda halshenta
ke da tsayi ya fi pampo fa”
Shiru Gwaggo Habibah ta yi tana kallon Baby girl don kuwa a gaban idonta da tana yi mata
wanka wani mugun haske ya fita goshinta tamkar an jefa kibiya.
“Allah ni dai ba zan sake shiga toilet ɗin waje ba ƙila ma aljani ne” muryar Safeenatu ta katse
mata ɗan guntun tunaninta.
“Bari na je na gani ” cewar Gwoggo Habibah kafin ta miƙe ta fita zuwa Toilet ɗin tsakar gida,tun
kafin ta ƙarasa ciki take jin nishin wahala .
Ido huɗu suka yi da Gwaggo Hajara wacce zuwa yanzu tuni ta galabaita ta yi wani tsamo-tsamo
cikin ruwan zafin ta kasa fita . Gwaggo Habibah ta yi wani murmushi tana kallon yadda ruwan
suka yi baƙi tsabar yadda muguntar da ta shiryo ma Safeenatu ba ƙarama ba ce.
“Ƙarshen alawa ƙasa! Yanzu wa gari ya waya? Shi dama ramen mugunta an ce ka gina gajere
in kuma ka gina dogo kai za ka faɗa .Ai wallahi ba zan taimaka miki ba sai dai ki dawwama a
ruwan zafin nan,in kuma kin ga na taɓa robar nan to wallahi cikin masai ne zan zubar da ku ke
da ruwan” Gwaggo Habibah ta faɗa tana wani murmushin jin daɗi.
Kamar daga sama tsakaka ta soma magana wacce ta kasance Gwaggo Hajara ,“ ki taimaka
min Habibah na yi miki alƙawarin daga yau na zubar da makaman yaƙi”
“Kar ma ki zubar ki yi ta riƙon su har sai Mahadi ya bayyana,ba dai maita ita ce jarinki ba? Ki ci
gaba da yi wata rana mutuwarki za ki ci” tana gama faɗar haka ta fito daga toilet ɗin,sai kuma ta
tuna duk wanda ya mutu a ruwa yayi shahada da sauri ta koma ba tare da ta ce komai ba ta
ɗauko robar ta fito da ita tsakar gida tare da juye ruwan ga ƙasa. Tamkar acid haka turɓayar ta soma yin bori tana fitar da kumfa tsabar bala'in da ke tattare da
ruwan,a kunyace Gwoggo Hajara tsakaka ta soma jan ciki ta nufi hanyar ɗaki.
Ita kuwa Gwaggo Habibah ji ta yi kamar ta sa ƙafa ta laɓe shegiya kowa ya huta.Tana komawa
ciki ta cewa Safeenatu “Ki shiga toilet to kafin na juye ruwan yi miki wankan” sai kuma ta fita ta
ciko ƙaton bokiti da ruwan zafi,da ɗan ƙaramin towel ta soma yi wa Safeenatu wankan jego ita
kuma tana ihu kamar wata ƙaramar yarinya.
Macijin jiya ne ya sake bayyana a jikin macen yana wani naɗe jikinta,ita kuma ta buɗe ido taram
tana kallonsa kamar mai wayo.Tsawon lokaci ya ɗauka tare da ita yana yi mata wasa kafin ɓace
jin motsin su Safeenatu za su fito.Gefen gado ta zauna ta soma shayar da yaran kafin ta kimtsa
cikin riga da zane,sai da Gwaggo Habibah ta gama wanka ita ma ta fito ta shirya sannan ta je ta
kawo masu abinci suka ci daga nan suka wuce asibiti bayan sun karɓi kuɗi wurin
Daddy.Lafiyarta da ta babys aka duba kafin su dawo gida,tuni kuma ƴan Barka suka fara zuwa
in waɗannan sun fita wasu sai su shigo.
SAKEENATU
Tana rungume jikin Abbas ta ce “ Yau tana ɗaya daga cikin ranakun ovulation ɗina,yau na gama
period ” cikin tsokana ya ce “ period ɗin ɗaya rana ” ta ja hancinsa ta ce “ eh na dai ji,inda ina
jimawa kafin ta ɗauke ai da yanzu ba ka kasance da ni ba don jiya ne na gan ta”
Ya gyara mata kwanciya kan ƙirjin nasa yana mai cewa “ Keent don Allah ki dinga bin Mamuh a
hankali kin san ta tsufa,ban so kina yin abin da zai ɓata ranta ki guji ɓata mata don
farincikina.Ina yi miki wani mugun so ne wanda na san ke ko rabin shi ba ki yi min”
“To in sha Allah na yi ma alƙawari zan kiyaye,ai Ma'idar ma an tafi da ita”
“A'a za ta dawo,sanin kan ki ne yadda nake mugun sonta ba zan iya yin nesa da ita ba”
Wani daɗi ne ya luluɓe zuciyar Sakeenatu,ita ce shaida kan son da yake yi wa ƴarta duk da ta
fito ba ta hanyar aure ba.Za ta iya cewa halarcin bai nuna mata ƙyama ba ne ya ɗunguza ta ga
aurensa,soyayyarsa ma ba ta jima da samun gurbi a zuciyarta ba.
“Ina son ki Keenat!” furucinsa ya katse mata tunani,ta yi murmushi mai ɗan sauti ta ce “ na
gode”
“Ke ba za ki faɗa kina sona ba? Keenat sai yaushe zan ji furicin so daga bakinki?”
Ta laƙace masa hanci ta ce “ sai ranar da na haifo ma kyakkyawan Prince mai kama da kai” sai
kuma ta miƙe ta je ta shiga toilet,shower ta sakarwa kanta tana tunanin saurayinta mahaifin
Ma'idah.Ruwan hawayenta haɗi da na pampo suka haɗu wuri ɗaya suna zuba.Daga bayanta ta
ji an rungume ta,da sauri ta juyo suna fuskantar juna kallo guda yayi mata ya hango damuwa a
shimfiɗe a ƙwayar idonta.Zuciyarsa kuma ta basa ta yi kuka,bai tsaya tambayar ta ba ya ɗora
bakinsa kan nata a wannan rana a kuma daidai lokacin nan Abbas ya shayar da ita zumar
ƙauna mai haɗe da yayafin kalaman soyayya masu nuni da sadaukarwa.Ba tare da ta shirya ba
ta ce “ I love You Abbas!” numfashinsa ne ya kusan tsaya wa tsabar murna da farin ciki,kamar
wani ƙaramin yaro ya soma yi mata kuka saboda kawai ta ce tana sonsa.
Shi yayi musu wanka ya shirya su,a ranar a gida ya ja su sallah har ta isha'i .Bayan sun
salamce sun yi dogayen addu'o'i ya dube ta da kyau ya ce “ Keenat fatan bayan tafiyata duk
salloli kin yi su kan lokaci kuma kin tsare su?”
Da sauri ta sunne kai ba tare da ta basa amsa ba,yatsun ƙafarta ya soma ja mata tare da soma
yi mata nasihar da ya saba game da mai wasa da sallah a ƙarshe yake cewa “ in kuma na ga
kin ƙi yi zan kawo miki ƙanwa ustaziya” a shagwaɓe ta faɗa jikinsa ta ce “ to ai ina yi ko”
“Kina yi ko za ki dinga yi?”
“Duka biyun! Ba za ka koma asibiti ba?”
“Tare za mu koma tashi ki shirya” da “ to” ta amsa kafin ta canza kaya suka fito,sai da ya tsaya
ya saya musu fruits sannan suka isa asibitin.Da sallama suka shiga ɗakin Gwaggo Rahamu ce
ta amsa yayin da Mamuh ta juya musu baya tana jin wani irin baƙin ciki ya turnuƙe ta saboda a
yadda ta gansu cikin farin ciki suna nishaɗi ta san sun keɓe da junansu.Abbas ya ƙarasa yana
mai cewa “ Mamuh ya jikin naki?”
“Ka damu da ni ne ka sa ƙafa ka yi tafiyar ka? Wato Abbasi matarka ta fi ni ko?” ta faɗa cike da
masifa tana juyowa.
“Ki yi haƙuri Mamuh Allah dai ya baki lafiya ” ya faɗa kansa ƙasa.
Tsabar fitina ta Mamuh sai cewa ta yi “ ina wakena?” Abbas ya ɗago da sauri yana kallon ta
yana mai cewa “ wane irin wake kuma Mamuh yanzu da daren nan? Ga ayaba nan da lemu da
apple na sayo ”
“Na yi da kai na ce ka sayo? Ita waccar