Showing 21001 words to 23138 words out of 23138 words

Chapter 8 - Celebrity Farashin Tasiri By Mrs Sadauki

mutum ya zauce don Allah ki
mayar da hijabin ki”
“Saboda in faranta maka da rai na yi fa,na ga ɗazu kamar ka yi fushi” na faɗa ina zagayo

hannuna kan cikinsa.Bashir ya dube ni cikin ido ni kuwa ganin haka yasa na ƙanƙance nawa
tare da ƙara shagwaɓe su.
Lips ɗinsa da na jarabta na kai wa sumba kamar wata kura,a tare mu ka sauke ajiyar
zuciya.Bisanin mu fara sumbatar juna haɗi da romance,a ranar Bashir ya shayar da ni zuma
wacce ban taɓa sanin akwai banbanci tsakanin wanda kake so da kuma wanda kake yi don
kuɗi.

Sai bayan komai ya lafa ne Bashir ya dube ni da kyau ya ce “Meelat ina kika kai budurcin ki?”
Na sunne kai har da hawayen kissa na ce “fyaɗe aka min Bashir ”
“Amma ba ki gaya min ba alhalin har maganar aure ta shiga tsakaninmu”
“Ka yi haƙuri!” na furta ina mai lafewa jikinsa.

Zuciyar Bashir wani irin bugawa take da ƙarfi, ya na son Meelat sosai amma sam yanzu ya fara
zargin da lauje a lamarinta.Ya na ƙoƙarin tashi na riƙe shi,duk yadda ya so tafiya na hana shi sai
da mu ka je zagaye na biyu.Toilet ɗin falo ya shiga yayi wanka,bayan ya fito na saka hijabi na yi
masa rakiya har cikin mota.
“Oh Allah! Sama da appel goma,ana ta kirana ashe” ya faɗa tare da cire wayar a caji,nan kuma
wani kiran ya shigo.Ya ɗaga yadda wayar ke da ƙara sosai ni ma ina iya jiyo abin da ake faɗa.
“Bashirrr! Mon amour farin cikina tun ɗazu nake kiran ka ba ka ɗauka na sanar da kai babban
albishir ina ci..ki yanzu na yi test na gani wayyo daɗi don Allah ka zo ka kai ni asibiti a ƙara
tabbatar min” in kunnena ya jiyo min daidai shi ne abin ta faɗa.
Cike da murna ya ce “da gaske masoyiyya? Yawwa gani nan tafe” ƙittt ya kashe kiran ya dube
ni “Meelat zan tafi matata ce ta kira ni zan kaita asibiti”
Cike da murna na ce “to Allah sa gaske ne ,kar ka manta ka kira ni” sai na fita na koma cikin
gida cike da murna.


BASHIR

Ikon Allah kawai ya kaisa gida,don soyayya mai zafi suka yi shi da Mariya kafin su yi aure.Ya na
zuwa gida tuni ta shirya hakan yasa suka wuce asibiti .Dr yayi gwaji ya kuma tabbatar masu da
ciki ne ɗan wata biyu,sosai suka yi murna Bashir kuwa ya manta da zancen wata Meelat.


A can ƙauyen Takalmawa kuwa sosai aka yi shagalin tarben kayan auren Heelat.Innar Meelat
kuwa tuni ta shiga zullumi wannan ya saka ta ga ita ma gwara ta aurar da tata ƴar can ta sai ta
ƙarasa karatunta a gidan mijin.Ta samu Abba da zancen shi kuma ya nuna mata bai san
wannan ba dole ƴarsa ta ida karatu tunda saura shekara uku nan gaba. Heelat tamkar sallah haka take ji sai wani fifiko take yi wa ƙawayenta uwanda suka yi aure nan
ƙauye kasancewar duk sun zo tarben lefen.
Heelat ba ta koma Maraɗi ba sai washegari,direct makaranta ta yi tsinke.

MEELAT
Jin matar Bashir na da ciki ba ƙaramin daɗi yayi min ba,murna kawai nake saboda samun cikin
nata ya nada alaƙa da samun nawa auren.Ina ta zaman jiran Bashir ya kira ni shiru,kuma ban
so na kirasa kar ace ya na tare da matar shi kawai sai na haƙura.
Washegari kamar kullum Bashir ya kira ni akan zai zo ya kai ni makaranta,ban sanar da shi ba
mu yi ba sai da na bari ya zo.
“Jiya ina ta jira ka kira ni ka shaida min yadda ake ciki amma shiru” na faɗa ina shafa dogon
gemunsa.
Ya kashe motarsa sannan ya ce “murna ce ta min yawa amma ai gashi yanzu na zo ko?”
“Masha Allah kenan dai yanzu akwai cikin?”
“Eh haka likita ya ce watansa biyu ”
“Alhamdullah ! To ya maganar aurenmu yaushe za a yi?” na tambaya cike da murna.
“Aure kuma?” ya tambaye ni kamar bai san da zancen ba.
Na ce “eh mana! Ko ka manta ka ce sai in matarka ta haifu?”
‘Da yake banda hankali sai na auri matar da na sani tun a waje ta rabewa ƙatai jikinta’ Bashir ya
faɗa a zuci amma a zahiri sai ya ce wa Meelat “in ba abun ki ba Baby daga samun ciki shikenan
sai na kawo zancen aure yanzu? Bari za mu yi har ta haifu”
Maganar da Bashir yayi sam ban yarda da ita ɗari bisa ɗari ba,amma na share na ce “to Allah
kai mu”
Ya amsa da “amen” sai kuma duk mu ka yi shiru.
Hannunsa na ji jikina ban hana shi ba saboda ina sonsa,an ce kuma duk inda ke da so to
sha'awa na yi masa sanɗa ne.
Tsabar rashin ta ido Bashir ya nemi mu shiga daga ciki,ni kuwa na biye masa mu ka shiga ya
gama abin da zai yi ya fito.Tun daga wannan ranar Bashir ya mayar da ni matarsa ta biyu,da
zarar na yi masa maganar aure kuma sai ya ɓata rai.Gefe guda kuma Alhaji Nera mu na sheƙe
ayarmu sai dai a hotel ne bai zuwa nan,ɓarin kuɗi kuwa ta ko wane ɓangare ina samunsu.Cikin
ƙanƙanen lokaci na ƙara waye wa na goge na fito sak ƴaƴan madara rairafan capet.
Ni da Heelat wa'azi ne ke shiga tsakaninmu don zuwa yanzu duk ƴan makaranta sun fahimci
rayuwar da na saka kaina.Wasun su ma guduna suke,Sadiq kuwa ya na ta bakin ƙoƙarinsa
aikin ƙarfi yake ya na tara kuɗin aurena wanda har asusun ya nuna min.

Ba sau ɗaya ba sau biyu ba a gabana Hafiz ya sha yi masa faɗa kan cewa ya rabu da ni,amsa
ɗaya yake basa a kullum “ ita soyayyar gaskiya ba ta sauyawa ina sonta a haka da zarar na
aureta shikenan” furicinsa ya saka na basa wani keɓaɓen wuri a sashen zuciyata.




NA'ILAH POV

Tun bayan cin mutumcin da Meelat da Alhaji Nera suka yi mata ta lashi takobin sai ta aure shi

sannan ta raba shi da duk biyan sauran matan banza.Ba ta ɓata lokaci ba wurin neman bokaye
da malamai ba,babu shiri Alhaji Nera ya fara yi mata ɓarin kuɗi tare kuma da zancen
soyayya.Babu jima wa maganar aure ta shigo don har an yi komai.



★ Yau ta kama Monday ranar da za mu fara zuwa stage a asibitocin da ke kewaye da nahiyar
maraɗi.
Riga fara na saka tare da baƙin wando jeans,ƙananun kitson da aka yi min na tattare wuri guda
na tubke.Ina ƙoƙarin fita Alhaji Nera ya shigo,da mamaki na dube shi na ce “alhaji lafiya?”
“Lafiya lau! Dama mota ce na zo na kawo miki ni zan yi tafiya zuwa Dubai”
“Wai dai ko gaske ne aure za ka yi?” na tambaye shi ina mai kafe shi da ido,ya ƙyalƙyace da
dariya ya ce “Meelat kenan ! Ko ma auren zan yi mene ne? Ina ce har da maza kike shigo min a
gida duk na yi shiru ban ce komai ba” ya na faɗa haka ya fita na bi bayansa,bayan na rufe ɗaki.



Farar mota ce sai ƙyalli take an yi mata wanka,motarsa ce bai jima da sayenta ba yanzu kuma
ya ce ya bar min ita.
Key ɗin ya miƙa min ya ce “mu je ki ajiye ni gidan Bus ” da murna na karɓa na shiga,ni na yi
driving nasa har mu ka isa can.Kuɗi ya ban sannan na wuce asibitin Ali Shebu inda a nan ne
zan yi nawa stage ɗin.
Ko da na isa na tarar da Heelat kasancewar wuri guda aka kawo mu.Na parker mota na
fito,ƙiri-ƙiri ta nuna min hassada don kasa ɓoye wa ta yi har sai da tace “yo wa za a yi wa kurin
mota ai ni ma dai na iya”
Na yi dariya na ce “ke ai iyawa ce kawai kika yi ni kuma ina da motar”
“Hafiz ya ce zai saya min matsayin tukuicin daren farko” shareta na yi don na fahimci ta na son
yin magana kullum kan daren farko sanin ni banda abin da ko wace amare ke taƙama ta baiwa
mijinta.


“Ya na ga har yanzu sauran ba su zo ba? To wai nan za mu tsaya?” na tambayi Heelat ina ƙare
wa asibitin kallo.
“Sai shugaban asibitin ya zo,shi ne zai damƙa mu ga ma'aikatan ”


Ina shirin buɗe baki na yi magana sai ga motar Bashir ta shigo,ban kauda idona ba har sai da
sai da matar ta fito wanda a gaban idona yayi kissing ɗin goshinta.
Wani ƙaton dutse ne ya zo kan zuciyata ya zauna daram,ji na yi kamar na je na shaƙo shegiya
don na fahimci matarsa ce wacce akan ta samu ciki ya fasa aurena don yanzu na fahimci
Bashir ba zai aure ni ba.Kimanin sati ɗaya currr nake binsa akan ina son ganinsa ya ƙi,a ƙarshe
ya faɗan maganar da har in mutu ban zan manta ba “in na aure ki mine ne za ki ban wanda
yanzu ba ki ban ba?” shine furucinsa na ƙarshe a gare ni.

Na rumtse ido lokacin da kyakkyawar matar tasa ta zo wucewa ta gabanmu.
“Ke lafiyar ki?” Heelat ta tambaye ni,ban kai gabata amsa ba wata nurse ta kira mu.
Mu na zuwa sai mu ka tarar da sauran abokan karatun mu ashe tun ɗazu su na ciki.

Da tsiya da jaraba sai da na san yadda na yi na je ɓangaren ƴan awon ciki,nan na samu mata
sun yi layi sosai ban sha wuya ba wurin hango matar Bashir .Kamar wacce aka yi wa allurar
baƙin ciki haka na shiga mota na je pharmaci na siyo maganin zubar da ciki na dawo.
Cikin ladabi na je ina kamawa matar aiki har aka zo kan matar Bashir ,a gabana ta kwanta
Madam nurse ta mata scanning ɗan cikin sai juyi yake .
Bayan an gama aka ce na bata maganin masassara don jikinta na da zafi da kuma wasu
sauran magungunuka,cike da dubara na bata na zubar da cikin wanda in ta sha shi da wuya ma
in mahaifarta za ta ƙara ɗaukar ciki da wuri.
“Allah raba lafiya” na faɗa ina murmushin ƙeta .

Sai wuraren sallar la'asar mu ka tashi,ni na ɗauki Heelat cikin motata direct gidana mu ka
wuce.Tsoro ya bayyana ƙarara kan fuskarta ta ce “Meelat duk yadda nake tunanin ki ashe kin
wuce nan?”
Na yi murmushi kawai na wuce kitchen, Heelat kuwa sai dube-dube take kamar baƙauyar da ta
shigo birni.

Jus da kayan motsa baki na kawo sannan na kunna kayan kallo,Heelat na ci ta na min wa'azi
inda a ƙarshe take cewa “Meelat kan wannan sana'ar da kika sa kan ki tun da kin ce saboda
kuɗi kike yi mi zai hana ki buɗe shafin Tik Tok yadda kike da kyawun nan na san za ki samu
followers,cikin ƙanƙanen lokaci za ki zama *CELEBRITY* ”
Na yi shiru ina tunanin maganarta,sai na ce “a can zan samu kuɗi?”
“Milliyoyi ma kuwa”
Furincin Heelat ya saka na sauke app ɗin Tik Tok ita ta nuna min yadda ake yi komai ta ce wurin
wacce suke kwana ɗaki ɗaya duk ta koya .Kamar da wasa na buɗe shafina da sunan *MEELAT
ƳAR FULLO* .
Wanka na yi na saka wata baƙar riga marar hannu tare da wando,Heelat ta min video farko a
rayuwata na ɗora.

Sama da awa biyu har Heelat za ta tafiya sai kuma ta ce “Shiga mu ga su wa suka yi like da
comments”
Hannuna har rawa yake wurin dubawa,caaa haka na ga an yi min tuni na samu followers da
comments na ban mamaki.Daɗi na ji kamar zai kashe ni,mutanen da suka nemi na yi masu
video sun fi ɗari.Tun daga lokacin na ji kaina ya fara hayaƙi,buri da muradin zama CELEBRITY
ya danne zuciyata.......

*Yanzu ne kawai mu ka shigo labarin mun fita daga shimfiɗa,da sannu za mu ji yadda ta zama
CELEBRITY wanda in ba ku manta ba farkon labarin tuni Meelat ta fara biyan FARASHIN
TASIRI saurayinta Sadiq ya mutu,ga kuma Alhaji Nera gabansa na fitar da jini.Shin wace ce
Meelat bayan ta fara rayuwar Tik Tok? Har mene ne ya jaza mata wannan masifar da duk in ta
yi mu'amala da namiji yake mutuwa? Ya za ta yi kenan a yanzu da ake tuhumar ta da ta kashe
Alhaji Nera?*

Sai mu haɗe a PAID GROUP,only 300 ne via
3184721842
Bala Maryam Mikailu first bank , shaidar biya ta WhatsApp +22795045822 ,ƴan Nijar carte airtel
ta 300f.


NB: 300 kuɗin shiga group ne,daga lokacin da na kammala shi zai koma 500


5/9/23


MRS SADAUKI NIJAR

6
7
8

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login
google.com, pub-9213700357025247, DIRECT, f08c47fec0942fa0