Showing 15001 words to 18000 words out of 23138 words

Chapter 6 - Celebrity Farashin Tasiri By Mrs Sadauki

sunan ki?”
“Meelat!”
“Wato Meelat tuntuɓe na yi da sonki ƙaunarki kuma ta min dabaibaye tun a kallon farko”
“Allah sarki” na faɗa ina ƙare masa kallo,fari ne tass ya na da ƴar ƙiba ga saje da jan leɓo sai na
ji ina sha'awar sumbatar su.

“Don Allah ki taimaka ki amince min”
Na saki makirin murmushina wanda na koya gun Momah tare da ƙanƙance ido ina tara wasu
ƙwalla na ɗauke hankali,na karyar da wuya na ce “Allah shige mana gaba”

Cikin jin daɗi Bashir ya karɓi lambar wayata,sai a lokacin na sanar da shi kuma University zan
je.


Daidai ƙofar makarantar ya ajiye ni tare da fiddo dumbujen kuɗi ya zaro min 20k ras,ko irin ɗan
jan ajin nan ban yi ba na karɓe shegu.Ina ƙoƙarin fita ya ce “mi zan sayo miki matsayin
tsaraba,sannan please ina son zuwa gidan ku tun yau”

Kalmar zai zo gidanmu ya saka ni jin wani mugun daɗi,nan na yi masa kwatance cewa Zariya ta
uku nake.
“Abin da zan sayo miki fa?”
“Duk abin da ka sayo Meelat na son shi” na faɗa ina murmushi.
“Don Allah turo min hoton ki kafin ki tafi”
“Bari na tura ma ta WhatsApp kawai tun da ka ban lambar ka” na faɗa tare da kunna data,ban
tafi ba sai da na tura masa hotuna.


Ina shiga ciki na zame ɗakin Raheela inda take kwana.A kwance na tarar da ita ta yi wanka ta
shirya ta na duba takardu .
“Jameela babu ko sallama?” ta faɗa tare da tashi zaune,cike da murna na zauna kusa da ita ina
cewa “Heelat na yi babban kamu yanzun nan bisa hanyata ta zuwa makaranta na haɗu da wani
kyakkyawan saurayi fari mai saje”
“Shine sai ki shigo babu sallama?”
Na tamke fuska na ce “ke fa matsalata da ke kenan! To maganar sallama ba ta wuce ba,in ba ki
ji daɗin ganina ne ba sai na fita na bar miki ɗakin ki” na faɗa cikin fushi.

“Allah baki haƙuri ina son dai sanar da ke ne muhimmancin sallama” Raheela ta sake faɗa.
“To sai ki yi ai !” na faɗa tare da fara danna waya sai na ga Bashir shi ma ya turo min hotunan
shi.
“Masha Allah! Kyakkyawa kuwa da shi amma Jameela wannan kamar ya na da mata” Raheela
ta faɗa.
“Ina ruwana da matar shi tun da ba auren shi ba zan yi! ”
“Jameela...” na yi saurin katse “Meelat za ki ce ban son sunan Jameelar nan”

Sai da Raheela ta yi dariya sannan ta ce “sunan kuwa na ƴan gayu! Amma don Allah da gaske
ba auren shi za ki yi ba?”
“Kuɗinsa kawai zan ci.Heelat dubi laɓansa uwannan sai sun yi daɗin sumbata” na faɗa ina cije
leɓena na ƙasa.

“Kin ce ba auren shi ba za ki kuma ki na zancen sumbata”

“Au! Aure kawai yake sa a sumbaci mutum Heelat?”
“Wai ni ce Heelat ɗin?”

“Eh ko bai yi daɗi ba?”
“Yayi sosai ma.Mu tashi mu tafi ko ƙarfe bakwai har da minti ashirin ” ta faɗa ta na kallon
agogon wayarta.

“Ina wacce kuke kwana ɗaki guda?” na tambaya.
“Ta fita tun ɗazu wai motsa jiki”
Na miƙe ina cewa “ba ta son ta yi ƙiba ne halan?”
Ba ta ban amsa ba har mu ka fito ta rufe ɗakin,mu ka nufi ɓangaren da ake karatu.


Duk ko wane ɗalibi sai duba takardu ake,mu kam zama mu ka yi ina ta baiwa Raheela labarin
Alhaji Nera yadda yake kashe min kuɗi amma ban sanar da ita ya na nemana ba.Mu na nan
zaune sai ga Sadiq da Hafiz ,ko wane facing budurwar shi ya zauna kafin mu fara taɓa hirar da
su.
Shigowar malamarmu ya sa kowa ya nutsu,kamar yadda mu ka yi tsammani ita ma jarabawa ta
rubuta mana ta na mai cewa “Ya kamata ku dage sosai ku ƙara hazaƙa don kun kusa tafiya
stage za a kai ku asibitoci ku ga yadda aikin likita ke gudana”

Cike da murna na cewa Heelat “na matsu na saka farar rigar nan”
“Za ta yi miki kyau sosai,amma ai ba sai mun sa ba”

Malama ta ci gaba da cewa “ku yi shiru ku ci gaba da aikin gaban ku,in an tashi kowa sai ya
nemi farar rigar likitocin ” sai kuma ta fara zagayen ajin.
Duk tambayoyin na san su hakan ya saka na riga kowa idawa na baiwa Madam na fice.
Alhaji Nera na yi text na shaida masa ina jin yunwa,ya kuwa ce na jira zai kawo min.An ɗauki
kamar minti ashirin sannan ya zo,har cikin makaranta ya shigo na je na karɓo sannan na zauna
kan dakalin nan mai kamar kujera da ake yi cikin makaranta.


Ina tsaka da cin frite da dunƙulalar kaza, Heelat ta fito.Zama ta yi mu ka ci gaba da ci,dai hirar
jarabawar mu ke.
Bayan mun gama mu ka hauda da exotic,sai a lokacin na sanar da Heelat cewa Alhaji Nera ya
kawo min.

“Ƙawata Alhajin nan na ji da ke gaskiya,to amma ya za ki yi da Bashir?”
“Kowa da matsayinsa” na bata amsa.
“To wa kika fi so?” dariya kawai na yi na ce “so? Tabbb ! Ba ki taɓa bani labarin soyayyar ki da
Hafiz ba”
“To ai a gaban ki ake komai” cewar Heelat ta na mai fara duba wayarta sai kuma ta ci gaba da
cewa “jarabawar ta yi wa Habibyna wuya bawan Allah ”
Ci kan ki ban ce mata ba na yi kamar ban ji ba,don na ga alamu irin rawar kan amare ce take
son nuna min .

Bayan kowa ya fito sai kuma mu ka ci gaba da yin cours har lokacin tashi yayi .Yau ban je
koyon mota ba direct gida na wuce,a falo na tarar da Hajiya ta na cin dambu,“Jameela har an
sauko? Ina kwanon da na zuba miki abinci?”
Gabana ya faɗi don kuwa na manta shi a motar Bashir,ban sani ba yawan shirun da na yi ne ya
saka ta ce “kar ki min ƙarya”
Hakan yasa kuwa na faɗa mata gaskiyar inda na manta shi sai na ƙara da cewa “ya ce zai zo
yau ,in sha Allah zan ce ya biyo min da shi”
“Ya na da kuɗi sosai kenan?” Hajiya ta faɗa ta na washe baki,ganin haka ya sa na zauna ina ta
bata labari har da kuɗin da ya ban.


“Ah to yanzu na ji zance! Shi wancan faƙirin yaron ki fita harakar shi,yo yaushe ya gama karatun
har ya nemi aiki har ku yi auren” cewar Hajiya ta na mai ƙara ƙawata min auren mai kuɗi.
Da na gaji dai na je na yi wanka sannan na zo na ci abinci.





Da dare misalin ƙarfe tara Bashir ya zo.Ya samu kyakkyawar tarba gun Hajiya don har ciki ya
shigo ya gaisheta bisanin mu koma can waje cikin motar shi.
“Ɗazu sai kika bar wa mijin ki abincin breakfast” ya faɗa ya na murmushi.
Na ce “Eh wlh manta wa na yi sai da na dawo gida sannan Hajiya ta tuna min”
“Abincin yayi daɗi ga kwanon nan na gode”

Nan mu ka fara yin hira sama-sama har motar Alhaji Nera ta zo ita ma.Duk da ya na dare akwai
hasken ƙwan fitila,yadda yayi tsaye ya na kallonmu ya saka Bashir cewa “bari na fita na gaishe
shi” bai jira cewa ta ba ya je ya gaishe da Alhaji ,shi ya shiga gida yayin da Bashir ya dawo.
“Gida zan shiga na ga dare ma ya soma yi” na faɗa zuciyata na ɗan dokawa.


“Daddyn ki na da tsanani halan? Allah sa dai kar ya min iyaka da ke” cewar Bashir kamar zai yi
kuka.
“Kar ka damu” na faɗa tare da ɗaukar kwanon na buɗe mota.Bashir ya miƙo min wata leda na
karɓa na shige gida.



“Sarai kin san yarinyar nan amana ce aka kawo mana shine za ki barinta fita zance to daga yau
sai yau kar na sake ganin wani ɗan iska ya zo min gida” shine abin da kunnuwana suka jiye min
tun kafin na shiga cikin ɗakin.
A falo na tsaya na sunne kai ina sauraren masifar da Alhaji ke yi wa Hajiya kafin ya dawo
kaina,da ya gaji kuma ya shiga cikin ɗakinsa.

Hajiya Turai ta ce “kar ki wani damu! Yo jiƙa ki za mu yi mu sha! Kawo mu gani mene ne ya
kawo miki ”
Ledar na miƙa mata ta buɗe,ɗinkuna ne na atamfa guda uku sai gizner wacce ba a ɗinka ba da
kuma less.
“Masha Allah! Ki na ji yanzu in kin shiga ɗaki ki kira shi ki ce saura kuɗin ɗinki in ya bada sai na
kai miki gun tela a yi miki ɗinkin ƴan gayu ”

Sosai na ji daɗin yadda Hajiya ta ɗaure min gindi,ina shiga ɗaki na gwada kayan duk sun yi min
cicif sannan na ɗauki waya na ce masa saura kuɗin ɗinki ko? Kawai ya kira ni.
“Su sauran ba su yi miki ba ne?” ita ce tambayar da ya fara yi min.
“Sun yi mana sosai ma”
“Shine ba za ki iya yi min godiya ba? ”
Ji na yi kamar ya watsa min petur,cikin masifa na ce “ka zo ka karɓi kayan ka in ka bani ne don
na dinga ƙasƙantar da kaina wurin ka....” sosai na yi ta masifa.
Bashir ya ce “Meelat? Meeeela!” sai kuma na yi tsit,yadda ya kira ni cikin salo na fizgar rai sai
na ji wani abu ya caki ruhina.

Da kuma na tuna da huɗubar Hajiya Momah kawai sai na fashe da kuka ina jan majina.Ina jin
yadda Bashir ke sauke ajiyar zuciya.
“Yi shiru mana my Meelat! Ban son kukan ki! Amma don Allah ina miki kyauta ki dinga cewa kin
gode”
A shagwaɓe nace “na ƙi ɗin! Kuma wlh sai na cije ka tun da ka bari na yi kuka”
Ya saki murmushi mai sauti ya ce “oh! My shagwaɓaɓiya irin wannan ai sai ki sa na zauce na
dawo gidan ban shirya ba”
Cak na tsaya da kukan sangartar na ce “wai gaske ka na sona sosai?”
“Fiye da tunani! Yanzu dai sai da safe zan shiga gida ki kula da kan ki”
Haka kawai na ji haushi,amma na danne na ce “kai za ka kai ni makaranta gobe”
“Ok babu damuwa,zan fito zuwa shidda da rabi hakan yayi”
“Eh sai da safe” ƙittt na kashe kiran.
Text ɗin Alhaji Nera ne ke ta shigowa,ni dariya ma ya ban yadda yake nuna kishinsa a kaina
ƙarara.
Ciki da izgilanci na tura masa “Ni ka yi wa faɗa ko? To yau babu inda zan je sai dai ka rungume
pilow”
Ina gama tura masa saƙon ko minti ɗaya ba ayi ba ya kira ni,na ɗaga.
“Wallahi! Wallahi in ba ki zo ba in na fasa fita yanzu na je na shaida wa Hajiya Turai ke
karuwata ce Shege Kuluwa ta haife ni.Wato Meelat ba ki son zaman lafiya! Duk gama ni da
Sadiq bai ishe ki ba sai kin rakito min wani farin buzu wanda ka na ganinsa ka ga jarababe ”
Na tuntsire da dariya na ce “au! Buzaye jarababu ne kenan? Hum! Alhaji ni ka kira da karuwa? ”
“Ki dai fara shirya wa yau tun ƙarfe goma nake son ganin ki a ɗakina ”
“Ba zan zo ba”
“Sai kin zo!”
“To sai na gani in dole za ka yi min”
Ina gama tura saƙon na kashe wayata na je na yi wanka,cikin kayan bacci na shirya tsaf na

kwanta tare da rungume pilow na fara tunanin Bashir .
Na lumshe ido ina ayyana cewa shi ne na rungume,tarau na buɗe ido tuna ya na tare can da
matar shi na ja tsuki a fili na ce “wlh ba zan so ka ba!” sai kuma na turo baki gaba ina jin haushi.
Cikin wannan tunanin bacci ɓarawo ya ɗauke ni,jin ana hura min iska a fuska ya sa na fara
buɗe idona a hankali da Alhaji Nera na ci karo durƙushe a gabana,ina shirin tambayarsa lafiya
kawai ya sukuce ni yayi waje da ni.

Ina kiciniyar direwa mu ka yi kiciɓis da Hajiya Turai wacce ta fito daga kitchen,ruwan da ke
hannunta ta saki yayin da shi kuma Alhaji Nera ke gyara min zama a ƙirjinsa.
“Alhaji mi nake shirin gani?”
“Abin da idon ki ya gane miki ai ba baƙon ki ba ne” ya gama faɗa ya nufi ɗakinsa da ni,kunyar
duniya ta ishe ni tuni na fara hawaye. A ranar na tabbatar idon Alhaji Nera a ƙyanƙyashe
suke,na yi tunanin Hajiya Turai za ta tayar da hankali ta zo ta yi ta kishin ƙofa sai kuma na ji
tsit.A ranar ɗakin Alhaji Nera na kwana,mun kashe arna fiye da tunani inda a ƙarshe yayi min
alƙawarin zai canza min gida na koma can da zama .

Washegari
Bayan na yi wanka a ɗakin Alhaji na saka doguwar rigarsa na fito,ɗakina na shiga na shirya tsaf
tare da haɗa duk wasu kayan jikina da takarduna kamar yadda Alhaji ya faɗa.
Bayan na gama komai na fice zuciyata duk babu daɗi,duk da Alhajin ya tabbatar min ita Hajiya
ko a kwalar rigarta zaman ta ci mai kyau ta sha mai kyau ne take da shi ta kuma rufa wa kanta
asiri .

Sai na zo bakin titi sannan na kunna wayata ,nan kiran Bashir ya shigo ya tabbatar min ya na
hanya .Ko da ya zo na shiga motar,ban cikin yanayi mai daɗi Bashir kuma ya fahimci haka don
ya na ta tambayata amma ban basa amsa ba kawai sai ya wuce da mu filin ƙwallo na Maraɗi
yayi parking mota ya ce na fito. “Mene ne wai? Kin shigo mota kamar kurma,ina tambayar ki kuma kin yi shiru!” ya faɗa ya mai
jingina da mota.
Ido na zuba masa nan na ƙara yarda da mai kyau ne na ƙarshen lamba,an ce so ya na shiga a
kallo ɗaya kamar shigar sarɗe to ni ma hakan ce ta faru da ni.Ban san ya zan yi ba kawai na
faɗa jikin Bashir ina mai fashewa da matsanancin kuka......



#Mafarin ƙaddara Meelat da Bashir


Nan zan tsaya da page na kyauta wato free page,duk mai so za ta biya kuɗin karatu only 300
via 3184721842
Bala Maryam Mikailu first bank sai ki turo da shaidar biya ta WhatsApp +22795045822 ko kuma
katin MTN,ƴan Nijar carte airtel ta 300f.

❌Kawai ki yi transfer don Allah ko kuma ki turo da kati

NB: da zarar na kammala book 500 ne
[04/09 à 16:07] MRS SADAUKI :
*FARASHIN TASIRI*
```celebrity```️

*Gajeren labari*️

MRS SADAUKI ✍️

FCWA ☀️

Special gift fo my VIA FANS

My book is only 300 via 3184721842
Bala Maryam Mikailu first bank,sai ki turo da shaidar biya ta WhatsApp +22795045822. Ko
kuma katin MTN,ƴan Nijar kuma carte airtel ta 300f

*Zuwa goma zan tsaya duk mai so ya biya kuɗinsa*


Page 9


Duk yadda Bashir ke ƙoƙarin cire ni a jikinsa amma abu ya cuttura, saboda ba ƙaramin
ƙanƙamesa na yi ba.
Wani abu nake ji wanda ban taɓa ji a ko wane namiji ba,a can ƙauyenmu na yi samari nan ma
birni amma karon farko da na taɓa jin wannan lamari wai shi ƙwayar so.

A hankali na sassauta riƙon da na yi masa na ɗago jajayen idona da suke ta shatatar da
hawaye.Gashin idona ya jiƙe sosai,shi yasa nake ganin fuskar Bashir dishi-dishi.Da mugun
sauri na lumshe su jin ya na hura min iskar bakinsa bisanin ya sa tattausan hannunsa ya fara
goge min ƙwallar.
Na ja da baya kaɗan amma za mu iya jin hucin juna.“Dubi yadda kika ɓata kwalliyar ki? Faɗa
min mene ne ke damun ki?”
“Alhaji ne! ” sai kuma na yi shiru tuna Bashir kallon mahaifina yake yi wa Alhaji Nera.
“Wane Alhaji?” ya tambaye ni ya kamo hannuna.
“Daddy mana! Bai son na fara zancen soyayya ya fi son sai na gama karatu! Amma don Allah
kar ka rabu da ni ina son...son ..kaaa !” Na yi ƴar gargada a kalmar ƙarshe saboda yau ne karon
farko da na furta wa wani ita .

Daɗi sosai ya bayyana a fuskar Bashir ,a ɗan ruɗe ya fara tambayata “Meelat da gaske ki na
sona? Za ki aure ni ? Wayyo Allahna! ”

Kai na jinjina masa ina murmushi sai kuma ya buɗe min mota na shiga,shi ma ya hau mazaunin
direba.
Mu na tafe mu na tsara yadda rayuwarmu za ta kasance tare da yin soyayya a ɓoye ba tare da
Alhaji ya sani ba har mu ka iso makaranta.Da zan sauka ya ban 2k don na ci abinci,yau ɗin ma
ban yi masa godiya ba sai ce masa da na yi “sai an jima ka kula da kan ka!”
Ya saki murmushi mai sauti ya na cewa “na gode my Meelat ke ma ki kula min da kan ki banda
kula samari”
Na yi ƴar dariya kafin na wuce ɗakun Raheela.


A tsakiyar ɗaki na tarar da ita ta baza kaya,“lafiya sai kace an fasa dilar Makka ?” shi ne abin da
na faɗa daga shiga ta.
Yau ba ta yi ƙorafin sallama ba ta ce “yawwa don Allah Meelat zo ki taya ni zaɓar kayan da zan
saka,kin san yau zan je gaida mahaifiyar Hafiz”

Na ɗan taɓe baki bisanin na taya ta duba kayan,don zuwa yanzu ita ma babu laifi Hafiz duk
kusan ya canza mata sutura.Wata atamfa ƴar côte d'ivoire na zaɓa mata,da murna ta shiga
shirya wa.
Na dubeta na ce “Yanzu za ki tafi gaishe ta ɗin?”
“Eh mana ko ba ki son yau babu makaranta ba?”
“Don

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login