Showing 12001 words to 15000 words out of 23138 words

Chapter 5 - Celebrity Farashin Tasiri By Mrs Sadauki

gaishe ni saboda a yawon
da nake na koyon mota mu na haɗewa da Alhaji Nera a nan.


“Babyn Alhaji ina kwana! Mi za a kawo maku?”
Cike da kuri da yanga na faɗa masa ya haɗa mana couscous da kaza plate huɗu da kuma ruwa
masu sanyi na cikin bidon.


Wuri mu ka samu mu ka zauna,ko wanensu yayi shiru kamar ruwa sun ci shi har abincinmu ya
iso.
Ni da Hafiz kawai ke cin abincin nan cikin jin daɗi da walwala,saɓanin Raheela da Sadiq da ko
wane nake zargin abin da ya hana shi sakin jiki.Ita dai baƙin ciki ne da kuma ba ta yi zaton haka
ba,shi kuwa Sadiq ina tunanin kishi ne da kuma tambayar ina na samu kuɗi.

Bayan mun gama na zaro kuɗi na biya kusan 30k don ƙarfin hali da za a ban canjin da yayi
saura ce masa na yi ya riƙe.
Hankali kwance na shiga mota na zauna sai ma lumshe ido da nake zuciyata fari tasss.Wannan
karon babu mai magana a motar har mu ka isa makaranta.
Ina shirin shiga aji Sadiq ya fizgo ni na yo baya,kamar wata ɗiyarsa haka ya ja hannuna zuwa
gefe.“Jameela mene ne haka? Irin wannan uban kuɗin da kika kashe ai sai ki sa a fara zargin
ki. Ina kika same su? Ko aiken ki aka yi ?”
Na fizge hannuna na ce “mene haka Sadiq ? ”
“Yi haƙuri raina ne a ɓace ban yi hakan da niyyar kaina ba”
“Daga yau kar ka sake riƙe min hannu,dubi yadda ake kallonmu” na faɗa ina mai barinsa nan a
tsaye na shige aji.

Kusa da Raheela na zauna wacce ta game ban da can.Ni ma na shareta ina mai duba saƙon
Alhaji da ya shigo min,na saki murmushi tare da kiransa.Buga guda ya ɗaga, “da gaske Alhaji
har ka buɗe min account?” na tambaye shi saboda tun jiya na yi masa ƙorafin riƙe kuɗi a
hannuna Hajiya za ta iya shiga ɗakina ta yi bincike. “Eh tun tuni,yanzu haka na saka miki kuɗi ma a ciki”
“Ok to babu damuwa yau in na fita koyon mota sai na biya Bank na ajiye na ga hannuna”
“Ok babu damuwa amma kafin nan ina son mu je hotel mu ɗan huta”
“Ok babu damuwa,yanzu dai ina cikin aji na ga ɗalibai sun fara shigowa ƙila malamin da zai
mana darasi ya tawo” na faɗa tare da yi masa sallama farin ciki fal raina.

Ina ajiye waya kuwa malam ya shigo,darasinsa ya fara kamar kullum yau ma ina ta bada
amsoshin tambayoyi.Canjin da na samu hatta malumaina sun fahimci haka don wasu su na

nuna mamaki a fuska wasunsu kuma har tambayata suke.


Bayan mun gama ko wane darasi na fito ina daddana waya,muryar Raheela na ji a bayana
“yanzu sai gida?” na juyo na dubeta,sarai na san abin da take son sani saboda lokacin da na
ajiye waya malam ya shigo babu damar ta tambaye ni shine yanzu ta biyo ni.


Na ɗan rausayar da kai cikin kurin magana da salon da Hajiya Momah ke koyar da ni nace “zan
je restaurant na ci abinci sai na wuce inda ake koya min mota”
“Allah taimaka” ta faɗa tare da yin gaba.Sosai na ci dariya yadda Raheela ta nuna min ta ji
haushi babu ko ɓoye wa.


SADIQ

Sam ruhinsa ya ƙi samun salama,hankalinsa duk ya tashi.Ya na son Jameela sosai ta yadda ya
kasa ɓoyewa mahaifiyarsa ita.Su na tafe cikin motar Hafiz amma sai jan tsuki yake shi ɗaya.
“Abokina haƙuri za ka yi tun da dai ba ka kai kuɗin aurenta ba,sannan yadda ta waye ɗin nan
Allah sai ta ƙara kyau ai farin ciki ya kamata ka yi” Hafiz ya faɗa ya na riƙe da sitiyarin mota.

“Murna? Ni wlh na fi son ta yi zamanta a ƴar ƙauye zai fin min nutsuwa.Ka na dai ganin uban
kuɗin da ta kashe mana ko a kwalar rigarta,kuma inda ka ga wayar hannunta Galaxy ce ”

“Hhh! Kishi dai kake! Amma fa alamu sun nuna kamar soyayya take da wani Alhaji ,tun da na ji
ma'aikacin gidan abincin nan ya na kiranta da Babyn Alhaji”

“Hafiz kar ka sa zuciyata ta buga don Allah,ya isa haka ta je ta yi ta soyayya da shi ɗin.In ya na
da kuɗi ni kuma ina da Allah zan ta kai kukana wurinsa har ya bani ita”

“Wai har haka kake son Meelat?”
“Fiye da yadda kake tunani,wlh yanzu haka ji nake kamar zan kama da wuta”
“Ka zage dantse wurin ganin ka samu soyayyarta fiye da shi wancan ɗin” Hafiz ya faɗa daidai
nan ya kawo ƙofar gidansu Sadiq da yake nan unguwar Maraɗawa.
“Na gode abokina sai an jima” Sadiq ya faɗa tare da fita.
Ya na shiga cikin gida ko sallama babu ya shige cikin ɗakinsa.
Da sauri Mama ta biyo bayansa ta na tambayarsa lafiya amma ya ƙi faɗa sai ce mata yayi “ba
komai Mama ”
“Ƙarya kake yanayin ka ya canza! Ba haka ka saba shigowa gida ba.Dole da wani abu,ka faɗa
min ka ji”
Duk yadda ya so ya ɓoye wa Mama kasawa yayi saboda a soyayyar Jameela shi ɗin mai rauni
ne kawai sai ya fashe da kuka ya ce “Mama Jamee ce...” sai kuma ya kasa ida maganar.

“Cewa ta yi ba ta son ka ko? Irin wannan nacin da kake yi mata ai dole ta faɗa.Yo ayi mutum
babu jan aji kullum cikin amayar da abin da ke cikinka kake”

“Mama ba fa haka ba ne,soyayya take da wani”
Mama ta shiga taɓa hannuwa ta ce “shine kuma kake kuka maimakon ka yi tunanin hanyar da
za ka raba ta da shi? To Allah kyauta!” ta na gama faɗa ta fice.

Sadiq yayi zaune kan yamutsatsar katifar shi ya rabka uban tagumi ya na tunanin mafita.



MEELAT

Taxi na ɗauka na tafi can auto-école,cike da girmamawa aka tarbe ni bisanin mu shiga motar da
ake koya min da ita.Sai da mu ka hau titi sannan ya bani,ban sani ba ko don ina son mota ne
sosai ya saka na yi saurin iyawa oho.

“Masha Allah ki na kula da komai yadda ya kamata, Allah dai ya nuna mana ranar da za a baki
lasisin ki” cewar wanda yake koyar da ni.
“Amen na gode sosai”

Sai da mu ka yi yawo sosai sannan na wuce hotel ɗin da Alhaji Nera ke zaman jirana.
Tuni an tanadar min abinci,ya na ƙoƙarin taɓa ni na dakatar da shi saboda ina buƙatar yin
wanka.
“Ki fara da abincin Baby sai ki yi wankan” cewar Alhaji Nera.

Na buɗe abincin,ƙamshi ya bugi hancina idona sun rufe da zalama sam ban lura da garin
maganin da aka barbaɗe abincin ba.Ina gamawa na shiga na yi wanka,ko da na fito tuni Alhaji
Nera ya shirya,ya na kwance kan bed babu kaya.
Na ɗan harare shi nace “wai don Allah wannan tumbin naka ba ka iya sha masa magani ya
baje?”
“Don Allah Baby ki bar maganar tumbin nan,ki zo ki kula da ni” yayi maganar ya na jawo ni.
Bayan mun sheƙe ayarmu na kwanta luf ina lumshe ido,yau kwana goma sha ɗaya cicif da na
shiga sabuwar rayuwar da nake jin daɗinta zuwa yanzu.
Na yi fari na yi kyau,shap ɗina ya ƙara buɗe wa ya fito da kyau.
Dogon hancina Alhaji Nera ya ja ya ce “my Meelat ƴar fullo”
Na yi murmushi kawai,“ya Sadiq ɗin ko shine ake tunani?”
Na ɗan yamutsa fuska nace “don Allah daga yau ban so ka na min zancen shi”
“Ok babu damuwa gimbiya,in kin tashi tafiya ga kayan baccinki nan na sayo”
Da ƴar murna ta na tashi ina cewa “Ah! Ah! Yau Allah yayi nufi kenan?”
Ya washe baki ya na miƙo min ledar na fara dubawa,“sun yi kyau amma dai wanda Hajiya Turai
ta ɓoye sun fi kyau sosai”

“Zan bincikosu su ma,don Allah yau ki saka wannan ina son ki kwana a ƙirjina” ya faɗa ya na
nuna min wasu farare.
“A'a in fa Hajiya ta shigo ɗakina ta gan ka? Na faɗa ma haka kawai cikin dare sai na ga ta faɗo
min”
“A ɗakina za ki kwana,in za ki zo sai yi kuna pampon toilet ki yi wa ƙofar key kin ga ko ta shigo
za ta yi zaton ki na ciki ne”
Na dube shi da kyau na ce “wai Alhaji ina kake samo irin wannan dabarun?”
Dariyarsu yayi irin tasu ƴan duniya ya ce “ke dai tashi ki yi wanka na kai ki gida”
Haka kuwa aka yi,bayan duk mun yi wanka mu ka kimtsa sannan mu ka fito Alhaji ya kai ni
bank na ajiye kuɗina,sai kuma ya sauke ni a ƙofar gida.

Kiciɓis mu ka yi ni da ƙawar Hajiya Turai,ban kawo komai a rai ba na gaisheta kafin na wuce.
Mabaruka ta na fitowa ta ga Alhaji Nera a zaune,ga kuma Meelat ta shiga gida nan zargin kar
dai ace tare suke ya sakata yi wa Hajiya Turai voice lokacin da ta isa gida.


Ina shiga na gaishe da Hajiya ta ce ga abincina nan nace mata a ƙoshe nake bisanin na shige
ɗaki na yi ta baccin wahala.Wuraren sallar la'asar na farka,Hajiya Turai na gani ta na ta bincikar
min akwatin kayana.
“Ina wuni Hajiya ?”
Da sauri ta juyo ba ta yi tsammanin zan tashi ba.“Jameela kin tashi? Nace halan a ƙafa kika
dawo kike wannan mugun baccin?”

Zama da maɗaukin kanwa shi ke sa farin kai.Kasancewar ina tare da Hajiya Momah da kuma
su Rumy tuni na halbo jirgin wato Hajiya zargina take.
Sai kuwa na ce mata “Wlh kuwa Hajiya ,halan Alhajinmu ya sanar da ke ya ɗauko ni, lokacin
har na ma kusa kawowa gida.Yayi faɗa sosai ya ce miyasa ban tambaye ki kuɗin taxi ba ai ba
za ki hana min ba,ni kuma wlh Hajiya kunya nake ji yadda kuke ta ɗawainiya ina laifin ciyar da
ni da kuke hakan ma alkhairi ne.” “Amma kuma shi alhajin bai ma shigo ba,to wai ina saurayin ki ba kin ce makarantar ku ɗaya
ba?”
Na yi saurin dirowa daga kan katifa na ce “yawwa don Allah Hajiya ina neman alfarmar ki roƙa
min Alhaji kan Sadiq ya dinga zuwa zance”
Hajiya ta washe baki ta ce “ke babu damuwa kawai kar ki damu” sai kuma ta fice,na bi bayanta
da harara ,na ɗauki waya na shaidawa Alhaji komai kafin na shiga toilet.

HAJIYA TURAI

Ta na fita daga ɗakin Meelat ta kira ƙawarta Mabaruka,“ina ga babu komai a tsakanin su kawai
ya sauketa ne kawai yayi”
“Ki dai ci gaba da kulawa kamar yadda kika ce ɗin,amma yadda baƙauyar yarinyar nan ta yi
mugun canzawa da wuya in ba ta san maza ba”
“Zan kula,kin ga sai an jima bari na kira alhajin na ji shi mi zai ce” ta na gama faɗar haka ta

kashe ta kira Alhaji .
Kamar yadda Meelat ta shaida mata shi ma haka ya ce a ƙarshe kuma ya fake da yi mata faɗan
mi yasa take barin Meelat babu kuɗi ko ta manta ita ɗin amanarsu ce.
Hankalin Hajiya Turai sai ya ɗan kwanta ta basar.
Sai da na gama sallah sannan na fito falo riƙe da takardun karatu ina dubawa yayin da kuma
Hajiya ta wuce kitchen.
Ina cin abinci na miƙe na cewa Hajiya sai da safe gobe zan zana jarabawa ina son yin karatu
sosai.

Babu laifi sai wuraren sha ɗaya na tsaya da karatun da nake don wayata ma kasheta na
yi.Wanka na shiga bayan na fito na shafe jikina da mai,sannan garin da Hajiya Momah ta ban
na ɗauko shi na zuba madara na sha .Ina kunna waya Alhaji Nera ya kira ni,hira sosai mu ka yi
ta tayar da hankali don har video call ya min ya na nuna min kansa. Kayan baccin na saka farare sannan ɗora dogon hijabi a sama,na kunna pampo na ƙage ƙofar
kafin na fita zuwa ɗakin Alhaji .


Hajiya Turai kuwa sam ta kasa bacci,tunaninta na kan Meelat hakan ya sa ta fito .Jin tsit babu
muryar Meelat wacce ta yi ta ɗaga wa ɗazu ta na karatu ya saka ta saurin isa ɗakin. Wayam
babu kowa kan katifa sai tarin takardu da kuma ƴar ƙaramar waya,Hajiya ta ƙara sa ta ɗauki
wayar ta na mai kallon toilet da take jin motsin ruwa.Fitowa ta yi har za ta shiga ɗakinta sai
kuma tace bari ta dubo Alhaji Nera.......



Mu haɗe
My book is only 300 3184721842
Bala Maryam Mikailu first bank,sai ki turo da shaidar biya ta WhatsApp +22795045822
[03/09 à 08:33] MRS SADAUKI :
*FARASHIN TASIRI*
```celebrity```️

*Gajeren labari*️

MRS SADAUKI ✍️

FCWA ☀️

Special gift fo my VIA FANS

My book is only 300 via 3184721842
Bala Maryam Mikailu first bank,sai ki turo da shaidar biya ta WhatsApp +22795045822. Ko
kuma katin MTN,ƴan Nijar kuma carte airtel ta 300f

*Last Free page 8*

“Tok! Tok! Tok”

Na yi saurin tashi daga kan ƙirjin Alhaji Nera ina mai duba ƙofar wacce zuwa yanzu an dakata.
“Ka ga abin da nake guje wa ko? Hajiya ce fa ke buga ƙofa ” na faɗa ina mai jawo kayan
baccina zan maida Alhaji yayi saurin riƙe ni ya na mai cewa “ƙofar a rufe take ba za ta shigo
ba,kuma ma fa ke ce ke damun kan ki Hajiya ba ta da matsala ta sani sarai ina harakar mata”

Idonsa na kalla ko kunya ba ya ji,shi fasiƙancin ma ado yake da shi.
Jawo ni yayi ya ci gaba da cewa “kin ga har ta yi tafiyarta ko? Zo Baby ki saki jikin ki”
Ba wai tsoron Hajiya nake ba,a'a kawai ban so ace ta tarar da ni da mijinta cikin wannan halin
shi yasa na ƙara zillewa.
Nan na ga fushin Alhaji Nera ƙarara ya na cewa “wlh in ki na tsiyar zan iya buɗe ƙofar nan ta
gan ki kin ga shikenan sai mu bar ɓoyon nan”
Fahimtar ƙaramin aikinsa ne ya saka na yarda mu ka ci gaba da masha'a.
Bayan komai ya kwana na mayar da kayana,a gabana Alhaji ya jawo system ya na duba
Camera da ya saita a falo,sai kuma ya shiga ta ɓangaren Hajiya Turai ta na kwance kan bed ta
na sharara bacci.

Na dube shi da mamaki,shi kuma ya ɗagan gira ya na cewa “kin zata haka nan kawai na ce ki
fito ɗazu? Sai da na tabbatar ba ta falo ”
“Ka ce kuma ba ka tsoronta” na faɗa ina hararensa don wlh zuwa yanzu na yi mugun raina
Alhaji .

Ya ɗan bugu kumatuna da yatsunsa biyu ya ce “ita ɗin matata ce,rigar mutumcina .Ta dalilinta
ake min kallon mutumen kirki,nan da ace ban ajiyeta ba to ina mai tabbatar miki da tuni sunana
ya ɓace a gari”

“Shi yasa kake zuwa hotel kenan? Can sunan naka ba zai ɓace ba kenan?” na tambaye shi ina
mai tsure shi da ido.
“Yanzu dai wuce ki koma ɗakin ki,zan kira ki”
“Kiran mi za ka min kuma? ” bai ban amsa ba ya je ya buɗe min ƙofa na fice.

Ina komawa ɗaki na ɗaga katifa na ɗauko key na buɗe toilet.Tsarkake jikina na yi sannan na fito
na kwanta,kamar yadda na yi tsammani Hajiya ta ɗauki wayata wacce babu ko layi a
ciki,kwanciyata na yi ban ɗau lokaci ba kuwa bacci ya ɗauke ni.

Hajiya Turai

Dama kusan jefi-jefi ta na duba Alhaji don kar ya fahimci zaman kuɗi take ba wai don ta na son

shi ba.Wayar Meelat ta bincike sai dai babu komai a ciki wannan ya saka ta yi kwancinta.Sai
tsakar dare wuraren asubahi ta farka,wayar Meelat ta je ta mayar inda ta ɗauke ta.

Washegari

Kamar kullum tun safe na shirya tsaf cikin shiga mai kyau.Ƙaramar wayata na gani na ɗauka ina
murmushi,zuwa yanzu na fahimci duk wacce ta ɗauki harakar duniyanci to ta na buƙatar
abubuwa na dabaru.
Takardu na ɗauka tsaf na fito,kamar yadda na yi tsammani ta na kitchen.Na leƙa na gaisheta,ta
miƙo min abinci cikin kwano mai kyau ta na mai cewa “ga shi ki tafi da shi tun da ba ki iya jira”
Na sunne kai na ce “eh saboda kar mota ta bar ni ne”
“Oh! Na manta bari na ɗauko miki ko da 1k ne” cewar Hajiya kafin ta fice daga kitchen ɗin.


Hajiya na shiga ɗaki ta ɗauki kuɗi bisanin ta fito.
“Jameela ga wannan ki hau mota sauran ki ci abinci” na karɓa tare da yin godiya na fita.
Maimakon na tsaya jira Bus kamar kullum kawai sai na samu kaina da tafiyar ƙasa,ina tafe ina
tunani a bayana na ji Horne.
Na tsaya tare da ɗan juyowa,a hankali aka sauke glass ɗin idona yayi tozali da wani matashi a
ƙalla zai haura shekara arba'in a duniya.

“Hajiya an tashi lafiya?” ya furta cikin muryasa mai shegen daɗi.
“Alhamdullah” na amsa ina wasa da ido.
“Sai ina?” ya tambaya ya na kallon takardun hannuna,na masa wani kallo kafin na ce “suyar
awara”
Ban sani ba ko ya fahimci baƙar magana ce ba,sai ya ƙyalƙyace da dariya ya ce “ai kuwa fatar
jikinki ba ta yi kama da mai raɓar wuta ba ,ta fi dacewa da masu zama ƙasan ac.Am...in ba
damuwa ki shigo na ajiye ki mana”
Sai da na ɗan yi jim bisanin na je na shiga,“sunana Bashir Sudan,Kano-kano nake zuwa ina da
mata ɗaya da yara biyu fatan ban miki tsufa ba?”


“Daga rage min hanya sai nace ka yi min tsufa?” na faɗa tare da basarwa na yi kamar ban
fahimce shi ba.
“Mi

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login