Showing 27001 words to 30000 words out of 31752 words
Chapter 10 - Masarautar Gobir Book Complete By Mrs Sadauki
muku ya lalace?”
Shiru ta yi ba ta bani amsa ba, wannan kuma yasa na lalubo amsar da kaina ‘ saboda ita da
mijinta normal mutum ne!’ sai kuma zuciyata ta bada darammm ‘ to in haka ne su abokan Bilal
waye ya sanar da su? Sai in kuwa su ma matsafan ne!’ duk a zuci na yi maganar har muka kai
gida babu wanda ya ce komai.
Mijin anty Sailuba ya karɓi kajin ya fita waje wani ya kama masa ya yanke,ni kuwa ƙatuwar
tukunya na ɗora ta ruwan zafi .Sai da suka tafasa sannan na soma fige su yayin da anty
Sailuba kuma ta ɗora girkin rana ,muna aiki muna hira har muka gama.
Sai bayan mun ci abinci ne na kama mata ta tsaga cikin ta fiddo hanji ,su ma duk muka gyara
su sannan ta wanke ta ɗora kan tukunya.Tafarnuwa ta miƙo min ita ma na gyara ,aikin da nake
ganin mai sauƙi ne sannu-sannu sai ga shi ya ɗauki lokaci don bayan ta dafa kajin sai da ta
soya su sannan ta ɗora miya bayan ta gama kuma ta tsumbula su ciki.
#GIDAN ANTY HINDA
Cike da iya yi Sharifa ta cika bokiti ta je ta yi wanka,ragowar ruwan kuma waɗanda duk sun yi
farin sabulu ta kawo wa anty Hinda su ta juye cikin miya sai murna suke.
Sharifa ta ce “Mama in muka ɗora da yin haka ai hajjin bana da mu za a yi”
Ita ma Hindar ta ƙyalƙyace da dariya ta ce “ai kuwa dai musamman yanzu da na rabu da jikar
bokanya ”
“Dama haushi take bani,yadda kullum cikin datti ko wanka ba ta yi”
Hinda ta ce “miƙo min ƙatuwar muciya na motso miyar nan ” muciyar ta miƙo bayan ta motsa
miyar ta sa murfi ta rufe kenan ai kuwa sai ganin leda suka kuwa daga sama ta faɗo kan
tukunyar miyar kwacaaaa.
Duk suka yi baya a tsorace su na zaro ido ganin kashi duk ya ɓata murfin tukunyar .
Cike da ƙyanƙyami Hinda ta ɗauke murfin ta je ta wanke shi,Sharifa kuwa cewa ta yi “Allah ma
dai yayi sa'a ba a ciki ya faɗa ba”
“Ɗauko muzubi ku juye min miyata Allah kaɗai ya san abin da za a jefo min kuma nan gaba”
cewar Hinda , Sharifa ta ɗauko ta dinga kwashe miyar dama ta dafu.
Ita ma Hinda wankan ta yi kafin su ɗora abincin kan baro,almajiri ya tura masu shi inda suke
sayarwa .Sharifa an ci wuyar kwalliya,mutane ne suka fara zuwa su na saye kamar kullum sai
da Hinda ta buɗe baki ta na zage-zage “ ƴan hassada ƴan baƙin ciki,to sai ku je ku sake biyan
wasu kuɗin wannan aikin bai yi ba.Ni za a yi wa turen aljanu daga ganin kasuwata ta bunƙasa” Customer ɗinta kuwa har da masu shigar mata,kafin kuma wurin yayi tsit babu wanda ya ƙara
saya ga abinci jibge har bayan sallar Asar sai ƴar kallon-kallon suke ita da Sharifa.
“ Na fa ji tsoro kar aje dai ɗin sun ƙara tafiya sun kai wasu kuɗin wurin Malam,dubi shiru babu
masu saya”
Sharifa ta turo baki ta ce “ ai ke ce da masifar tsiya tun da kin ga abun bai yi aiki ba ai sai ki yi
shiru da bakin ki”
“ Ƙirga kuɗin mu ga nawa aka samu” cewar Hinda . Sharifa ta ɗauki robar kuɗi,yaji ta gani
tsidagu babu wani tunani ta ɗauke shi ta jefar kuɗin ta ƙirga ta na turo baki gaba saboda ko icce
ba za su saya ba.Ta miƙa wa Hinda “ tsidagun mine ne kuma za ki aje min cikin kuɗi?” Hinda ta
tambaya ta na mai ɗauka ita ma ta jefar a ƙasa.
Sharifa ta ce “ na fa jefar da shi”
“Ƙafafuwa gare shi ballantana ya sake tsalle ya shiga?”
“Allah Mama na cire”
“Kin ga tashi mu je gida kin ga duk wasu masu sayar da abinci sun sayar sai mu”
“To wannan ɗin ya za mu yi da shi?”
“Ko almajirai sai na rabawa ”
Abincin suka mayar a baro suna gaba almajiri na bin su a baya har suka isa gida, Sharifa ta
cika bokiti ta je ta yi wanka tun a cikin banɗaki ta ƙurma uban ihu ta na kiran Hinda .
“ Ke lafiyar ki? Ko ƙadangaren ne yau ma ya sake faɗo miki?” Hinda ta tambaya, Sharifa ba ta
amsa ba sai fitowa ta yi da ɗaurin ƙirji ta na soshe-soshe.
“ Mama sosa mini ƙaiƙayi duk jikina ƙaiƙayi yake na shiga uku na lalace” haka take faman faɗa
,da farko Hinda ta ɗauka wasa ce sai da ta ga Sharifa na kuka har da majina sannan ta soma
tayata, Sharifa ba ta samu sauƙin abun ba sai da jikinta ya bushe babu damshin ruwa.Tsabar
wahala har sai ta rame,ta koma gefe ta na jan numfashi.
Hinda kuwa alwala ta yi don yin sallah nan ita ma ƙaiƙayi yayi mata wuf duk inda ke da damshin
ruwa.Soshe-soshen ta yi ita ma har sai alwalar ta bushe,suka kalli juna ita da Sharifa “ ina jin
tsoro Sharifa kar ace tsidagun da muka ɗauka ne”
“Shi ne mana Mama,kuma abin da na fahimta sai da ruwa suka taɓa mu ne muka ji ƙaiƙayin”
Sharifa ta faɗa ,Hinda kuwa don gaskata maganar sai ta watsa ruwa a ƙafarta ai kuwa ƙaiƙayin
ya sake dawowa sabo wannan karon Sharifa har sai da ta dara.
# GIDAN BILAL
Bayan sallar magrib anty Sailuba ta gama komai,an gyara ɗaki sai ƙamshi yake yayin da kuma
aka jera kwanonin abinci kan table ɗinta mai kujeru huɗu.Sai da ta yi kwalliya sosai ta saka
kaya masu kyau,abincina ta zuba mini kafin ta ce “ ki zauna ɗakin ki kar ki fito har sai baƙin nan
sun tafi ” Na gyaɗa kai na ce “ to anty ” fita ta yi ni kuma na zauna na soma cin abincina,sai murmushi
nake yadda na ji idona na wannan zuuuu ɗin na tabbata su anty Hinda ana can cikin
uƙuba.Sosai nake jin daɗin mugunta a fili na ce “ ku da yin wanka kuma sai ta Allah,kuma sai
kun dawo irina kun zama ƙazamai kun yi baƙi ƙirin” sai kuma na yi shiru jin muryoyi na tashi
alamun baƙin ne suka zo.
Ina jin su na zolayar anty Sailuba “ irin wannan kwalliyar matarmu ai sai ki sa mu kasa fita”
“Ina ji fa saboda matarmu ba ta son tsufa shi yasa ta ƙi barin ta haihu”
“ Ai kuwa dai in haka ne za mu kawo wata matar”
“ Allah ina son haihuwa sosai zuwa dai ne ba ta yi ba” sai yanzu kawai anty Sailuba ta yi
magana.
“ Ba ki dai je neman ta ba” ɗaya daga cikinsu ya faɗa.
Bilal mijin anty Sailuba ya ce “ yanzu dai mu fara cin abinci tukuna”
Tsit falon ya ɗauka na wani lokaci kafin kuma wani irin gurnani ya ɗauki hankalina har na ji ina
son leƙawa na ga su waye waɗannan baƙi.Labule na ɗan buɗe a hankali,su uku ne gami da
mijin anty Sailuba su huɗu.Zaune suke su na cin abinci babu mai yin magana,amma ni kuma
tambayata ita ce ‘to wannan sautin daga ina yake fitowa?’ ina shirin sauke labule daidai kuma
lokacin ɗaya daga cikinsu ya ɗan tada kai tsabar tsoro har sai da na dafe zuciyata.Ido uku ne
da shi,biyu irin na mutane ɗayan kuma can tsakiyar goshi ban ida shiga firgici ba sai da na ga
wani abu na fitowa ta idon ya na cin abinci nan na fahimci shine ke fitar da gurnanin.
Da sauri na saki labulen ina mai tambayar kaina ,“ina kuma Bilal ya kwaso matsafan nan?” shiru
na yi sai yanzu na gane wato shi yasa anty tace suka ƙi cin abincin sai ita da mijinta suka ci
saboda su idonsu uku ne biyu na nan duniyar ɗayan kuma na ɓoyayyar duniya.
Tunani na soma yi mine ne dalinlinsu na abota da Bilal tabbas akwai wata a ƙasa,tunanin nawa
ne ya tsaya cak jin ɗaya daga ciki ya na tambayar anty Sailuba “ni kam ku nawa ne cikin gidan
nan? Ko kun samu ɗan hutu ne ?”
Ba ta kai ga basa amsa ba shi ma wani ya ce “ƙamshin Gombowa ”
“Tun shigowar mu na ji ƙazinin ɗan ƙabilar Gombo”
A karo na biyu kenan da na ji kalmar sunan Gombo ɗin nan,a hankali na ƙara buɗe labule ina
leƙo cikin rashin sa'a hasken idona ya sauka a rigar ɗaya daga cikinsu,raɗam ya fito kamar
fitilar nan da aka yi yayi mai hasko hoton Obama.Ɗayan ne mai face da wanda hasken idona ya
sauka kan rigarsa ya juyo baya,muka haɗa ido da shi .........
Nan na kawo ƙarshen free page duk mai son ci gaba zai biya 500 via 2670215530
ZULFAU YAHAYA Ecobank sai ki turo shaidar biya ta WhatsApp +22795045822 ko kuma katin
MTN ,ƴan Nijar kuma carte moov ko airtel ta 500f.
NB:Daga lokacin da book ɗin nan ya zama complete 800 ne.
29 jully 2024
MRS SADAUKI ce í ¼í¼š
[09/09 à 10:39] MRS SADAUKI í ½í±‘M~SHURAIMí ¾í´�: ```MRS SADAUKIí ½í²«✍️```
My book is only 500 via
2670215530
ZULFAU YAHAYA Ecobank,ko kuma katin MTN na 500₦ ƴan Nijar kuma carte airtel ko Moov ta
500f sai a turo da shaidar biya ta WhatsApp +22795045822,in kin san ba ki biya kuɗin karatu ba
kar ki karanta min littafi domin mallakina ne .
*FCWA ☀️*
11-12
https://chat.whatsapp.com/FMimfpwTVDDBjZmDZw2Uhs
*Inda muke turo available products din mu don ki gani, ki zaɓi wanda kike so sannan ki siya ko
ki tallata kema kisami naki*í ¾íµ°
*Kayan mu order muke daga ƙasashen waje, foreign ne masu kyau da quality*
*Duk abinda mukayi posting available ne, daga kin siya za'a turo miki abinki ba ɓata lokacin
jira*.
08032350261
í ½í¸�í ½í¸�í ½í¸�DAMARKUCE LOKACINKUNE MUN RAGE FARASHI SOSAI DAN KUMA KUSAMU
KOMAI DA KUKA SANI ZAKU SAMESU KWASHA KWASHA ARHA GARABASA
í ¾í´�í ¾í´�í ¾í´�KUMA DUK INDA KIKE KAYANMU ZASU SAMEKU CIKIN AMINCI DA YARDAR
ALLAH
Da sauri na saki labulen ina jin zuciyata na dukan uku-uku,ina nan daga tsaye dafe da saitin
zuciya na ƙara jiyo amon muryar su “ zarginmu ya zama gaskiya fa mine ne abun yi?”
“ Ta fito kawai mu gane wa junanmu tun da duk bisa hanya ɗaya muke”
“Hhhh ai kuwa dai ƙila ita ma da nata plan ɗin a kansu”
Shine abin da na ji su na faɗa ,amma na yi mamakin haka a gaban sun anty Sailubar suke faɗar
haka ko dai sun tashi ne? Don gusar da zargina sai na ƙara kama labule don na sake
leƙawa,ina buɗe wa na yi tozali da ƙaton ido manne a jin ƙofar ɗakin nawa ban san lokacin da
na fasa wani matsanancin ihu ba da ya karaɗe duk illahin gidan.Ruwa ne suka soma ɓulɓulowa
su na cika gidan ga baki ɗaya hatta cikin ɗakuna.
Tuni siffata ta canza zuwa kala biyu bindin kifi ya fito min,ruwan su suka ja ni izuwa falo.
“Waooo!” suka haɗa baki su na kallona sai nitso nake ina kaɗa bindi cikin ruwan,sai wannan
lokacin kuma na ankare anty Sailuba da mijinta Bilal sai bacci suke yi kamar waɗanda ba su da
rai.
“ Azo ka na gani abin da nake gani?”
“Yes Musty ina gani”
“Naser kai fa?”
“Ina gani ni ma ” duk suka tsoma bakinsu a nan ne na san sunan kowa daga cikinsu.
Musty ɗin alamun ya fi su ƙarfi da surutu ya dube ni da kyau ya ce “ muna so mu san plan ɗin ki
akan wannan ahalin?”
Idona na buɗe ina kallonsa waɗanda har yanzu ba su bar mugun hasken nan ba,“ku fara sanar
da ni naku plan ɗin tukuna” na faɗa tare da dukan ruwa da bindina suka bada wani bacaaal.
Suka ƙara kallon juna kafin shi Musty ɗin ya ce “ ki yi mana alƙawari za ki taimake mu”
Na juya baya ina mai cewa “ tun da ba za ku faɗa ba kun ga tafiyata”
“Tsaya mana ,Musty kawai mu sanar da ita zai fi.Muna zuwa nan ne don jawo hankalin Bilal ya
shigo a tsagenmu amma mun gagara yin galaba kansa,ruhinsa na da mugun ƙarfi shi da
matarsa”
Na juyo ina duban Naser ya faɗa wanda na fahimci kuma duk cikinsu ya fi sauƙi don ya na da
tsoro.“ Ta ya aka yi duk ƙarfin ikon ku amma suka fi ƙarfin ku?” na jefo tambayar ina kallon
Naser ,sai da ya ɗan yi shiru kafin ya ce “ kin san su na da yawan addini su na salloli kan lokaci
”
Na lumshe idona ko da ya zo nan da zancensa,ina jinjina wa anty Sailuba wacce ta yi riƙo da
Addini duk matsatsin aikin shago bai hana ta yin sallah muddin lokacinta yayi na fahimci hakan
tun lokacin baya da nake wuni wurinta kafin na soma yi wa anty Hinda aiki.
“Na san ke ma shine dalilin da ya hana ki cin galaba kansu duk da ba mu san ke mi yasa kike
bibiyar rayuwarsu ba” Azo ya faɗa ya na matso wa kusa da ni.
Wani irin zafi ne na ji gangar jikinsa na fesar wa duk da kuwa ina cikin ruwa,na ce “ ta ya aka yi
ka san ina bibiyarsu?”
Yayi murmushin gefen baki ya ce “ in ba haka ba mine ne zai fito da ke daga can cikin asalinki ki
zo nan? Tun daga Gombo kike sannan a yadda kike Siren kika juri zama a wajen ruwa kawai
don ƙudirin ki.Faɗa mana mine ne shi?”
Ban da lokacin tunani ,na kuma fahimci ko masu ganin abin da normal mutane ba su gane ba
komai ne suke da sanaya a kai ba.Ba don haka ba tabbas da za su fahimci ban zo nan da
niyyar cutar da su anty Sailuba ba,amma don kar su raina mini fiƙirata sai kawai na ce musu “
yanzu dai kawai mu zama ƙawaye daga baya duk za mu tattauna akan abin da ya shafi
duniyarmu,tun ɗazu kun saka bayin Allahn nan bacci ya kamata ku tashe su haka”
Azo yayi wata dariya ya na mai cewa “ da alamu fa Siren tausayin su kike”
Na girgiza kai na ce “ ko ɗaya,kawai ban so su zargi wani abu ne”
“Kuma kin yi gaskiya komawar ki ɗakin ki”
“Kafin nan ta janye ruwan nan da ta cika mana ɗaki da su”
Murmushi na yi ina mai kai hannu ina taɓa Munduwar wuyana haɗi da kallon ruwan da ido ina
basu umarnin su koma,a haka na shige ɗakina ni ma tuni ruwan kuma sun ƙwafe tsab .Na
kwanta kan shimfiɗata ina kallon rufin ɗakin ina cewa “ karo na biyu kenan da na ji sunan
Gombo,shin ina ne ? Wace ƙabila ce?” ban ida rufe bakina ba kafin wani girgije ya danno kai
tamkar shine rufin ɗakin.Munduwar wuna ta soma zuƙo girgijen nan a hankali ya soma
tarwatsewa na zamar haske mai kamar mai sai kuma ya shiga radadowa ina fasa ƙirjina ya na
shiga “ Mamaaa!” na furta da ƙarfi saboda amon muryarta da ya cika mini kunnuwa ,yayin da
kuma hoton siffarta wacce take flou ta bayyana gare ni ga wani Baby a hannunta kafin ta aje shi
tsakiyar daji ta ce “ sunan ki Sarah !”
Hawaye suka zubo mini kan kumatuna,na samu abu na farko daga cikin tarihina wato jefar da ni
mahaifiyata ta yi sai dai ban san dalilinta na yin haka ba.
Daga can falo ina jin su Musty na yi wa su anty Sailuba sallama,babu jimawa kuwa ta shigo
ɗakin ta na mai kiran sunana “ Sarah taso ki yi kallo baƙin sun tafi” na girgiza mata kai saboda
ba na cikin yanayi,“ fushi kika yi don na hana ki fitowa?”
Kai na girgiza tare da tashi na zo na rungume ta da ƙarfin tsiya ina mai cewa “ anty Sailuba ina
son ganin Mahaifiyata,ina jin kewarta.Ina son jin soyayyar nan da ke tsakanin uwa da ƴa amma
ni wurin Kaka Anaba na taso wacce babu alaƙar jini ko ɗaya a tsakanin mu”
Anty Sailuba ta riƙe ni ta na cewa “ haba Sarah kar ki sa na yi kuka mana,kin ga dama yanzu
haka ina cikin wani yanayi.Sannan wa ya faɗa miki Kaka ba jininki ba ce,ƙila ta faɗi haka ne don
ta hora ki ”
Na sake ta na ɗan ja baya ina mai girgiza kai na ce “ a'a gaskiya ta faɗa don yau ɗin nan aka
nuna min lokacin da Mamana ta jefar da ni a cikin jeji”
Anty Sailuba ta jefo min wani kallo “ don Allah kar ki sa na fara jin tsoron ki,wa ya sanar da ke
to?”
Shiru na yi don ni kaina ban san ya ko wane ne ba.
“ Kin ga sai da safe bari na je na yi karatu ” har ta kai bakin ƙofa na tsayar da ita ta hanyar kiran
sunanta,ta juyo na ce mata “ ki ƙara dagewa da addu'a haka ma mijinki” ba ta ce komai ba ta
fice.
Sailuba
Ita tun farkon zuwan su Naser gidanta sam ba ta so haka ba,sai dai babu yadda ta iya saboda
su ne manyan abokan mijinta duk da ba ta san su ba kafin aurensu da Bilal amma a yanzu bai
da wasu bayan su.
A duk lokacin da za su kawo musu ziyara haka za ta kwana cikin kasala da mugayen
mafarkai,sai dai ba ta taɓa alaƙanta hakan da su ba abu guda kawai ta riƙe shi ne addu'a
sannan ta na yin sallolinta kan lokaci wannan kuma na ɗaya daga cikin turbar da Bilal ya ɗora ta
don shi Ustaz ne ya na da karatu sosai saɓanin Sailuba