Showing 24001 words to 27000 words out of 31752 words

Chapter 9 - Masarautar Gobir Book Complete By Mrs Sadauki

aka yi ƙafafunka suke na jaki?”
“ Ki tambayi Anaba ita ai ta san ni ”
Anaba sunan Kaka ne,jin furicinsa yasa na kai dubana ga naman da yake sayarwa duk babu
ɗaya na ƙwarai mushe ne yake sayarwa in rago ya mutu ko saniya haka zai je ya ɗauko su inda
aka jefar ya gyara shi ya zo ya na sayarwa ko da kuwa ya fara lalacewa shi zai san yadda yayi
ya maida shi mai kyau a idon mutane irin shine kuma sai ka ga ka ci ka faɗi rashin lafiya. Ban ankara ba ashe har mutanen da ke zagaye da shi duk ya sallame su sai da na ji muryar
anty Sailuba na cewa “ Sarah ke? Tun ɗazu fa nake yawon neman ki” sai kuma ta harari mai
sayar da naman kafin ta ja hannuna mu wuce.Sai da muka yi nisa na tambaye ta “ amma anty
mi yasa ba ki sayi namansa ba ? Na ga ya fi kowa arha” Ta ja baki ta ce “ arhar ce ke kai mutane ga hallaka,ni ma na taɓa saya lokacin da abokan Bilal
za su zo amma abun mamaki suka ƙi ci wai naman nan da na saka ya lalace ko ban jin
warinsa.A ƙarshe dai barina suka yi da shi sai ni da Bilal muka ci daren ranar kuwa muka dinga
ƴar rige-rigen shiga banɗaki” na ƙyalƙyace da dariya kafin kuma na ce “ to anty mi yasa kuka ci
alhalin an faɗa muku ya lalace?”
Shiru ta yi ba ta bani amsa ba, wannan kuma yasa na lalubo amsar da kaina ‘ saboda ita da
mijinta normal mutum ne!’ sai kuma zuciyata ta bada darammm ‘ to in haka ne su abokan Bilal
waye ya sanar da su? Sai in kuwa su ma matsafan ne!’ duk a zuci na yi maganar har muka kai
gida babu wanda ya ce komai.
Mijin anty Sailuba ya karɓi kajin ya fita waje wani ya kama masa ya yanke,ni kuwa ƙatuwar
tukunya na ɗora ta ruwan zafi .Sai da suka tafasa sannan na soma fige su yayin da anty
Sailuba kuma ta ɗora girkin rana ,muna aiki muna hira har muka gama.
Sai bayan mun ci abinci ne na kama mata ta tsaga cikin ta fiddo hanji ,su ma duk muka gyara
su sannan ta wanke ta ɗora kan tukunya.Tafarnuwa ta miƙo min ita ma na gyara ,aikin da nake
ganin mai sauƙi ne sannu-sannu sai ga shi ya ɗauki lokaci don bayan ta dafa kajin sai da ta

soya su sannan ta ɗora miya bayan ta gama kuma ta tsumbula su ciki.




#GIDAN ANTY HINDA


Cike da iya yi Sharifa ta cika bokiti ta je ta yi wanka,ragowar ruwan kuma waɗanda duk sun yi
farin sabulu ta kawo wa anty Hinda su ta juye cikin miya sai murna suke.
Sharifa ta ce “Mama in muka ɗora da yin haka ai hajjin bana da mu za a yi”
Ita ma Hindar ta ƙyalƙyace da dariya ta ce “ai kuwa dai musamman yanzu da na rabu da jikar
bokanya ”
“Dama haushi take bani,yadda kullum cikin datti ko wanka ba ta yi”
Hinda ta ce “miƙo min ƙatuwar muciya na motso miyar nan ” muciyar ta miƙo bayan ta motsa
miyar ta sa murfi ta rufe kenan ai kuwa sai ganin leda suka kuwa daga sama ta faɗo kan
tukunyar miyar kwacaaaa.

Duk suka yi baya a tsorace su na zaro ido ganin kashi duk ya ɓata murfin tukunyar .
Cike da ƙyanƙyami Hinda ta ɗauke murfin ta je ta wanke shi,Sharifa kuwa cewa ta yi “Allah ma
dai yayi sa'a ba a ciki ya faɗa ba”
“Ɗauko muzubi ku juye min miyata Allah kaɗai ya san abin da za a jefo min kuma nan gaba”
cewar Hinda , Sharifa ta ɗauko ta dinga kwashe miyar dama ta dafu.

Ita ma Hinda wankan ta yi kafin su ɗora abincin kan baro,almajiri ya tura masu shi inda suke
sayarwa .Sharifa an ci wuyar kwalliya,mutane ne suka fara zuwa su na saye kamar kullum sai
da Hinda ta buɗe baki ta na zage-zage “ ƴan hassada ƴan baƙin ciki,to sai ku je ku sake biyan
wasu kuɗin wannan aikin bai yi ba.Ni za a yi wa turen aljanu daga ganin kasuwata ta bunƙasa” Customer ɗinta kuwa har da masu shigar mata,kafin kuma wurin yayi tsit babu wanda ya ƙara
saya ga abinci jibge har bayan sallar Asar sai ƴar kallon-kallon suke ita da Sharifa.
“ Na fa ji tsoro kar aje dai ɗin sun ƙara tafiya sun kai wasu kuɗin wurin Malam,dubi shiru babu
masu saya”
Sharifa ta turo baki ta ce “ ai ke ce da masifar tsiya tun da kin ga abun bai yi aiki ba ai sai ki yi
shiru da bakin ki”
“ Ƙirga kuɗin mu ga nawa aka samu” cewar Hinda . Sharifa ta ɗauki robar kuɗi,yaji ta gani
tsidagu babu wani tunani ta ɗauke shi ta jefar kuɗin ta ƙirga ta na turo baki gaba saboda ko icce
ba za su saya ba.Ta miƙa wa Hinda “ tsidagun mine ne kuma za ki aje min cikin kuɗi?” Hinda ta
tambaya ta na mai ɗauka ita ma ta jefar a ƙasa. Sharifa ta ce “ na fa jefar da shi”
“Ƙafafuwa gare shi ballantana ya sake tsalle ya shiga?”
“Allah Mama na cire”
“Kin ga tashi mu je gida kin ga duk wasu masu sayar da abinci sun sayar sai mu”
“To wannan ɗin ya za mu yi da shi?”

“Ko almajirai sai na rabawa ”
Abincin suka mayar a baro suna gaba almajiri na bin su a baya har suka isa gida, Sharifa ta
cika bokiti ta je ta yi wanka tun a cikin banɗaki ta ƙurma uban ihu ta na kiran Hinda .
“ Ke lafiyar ki? Ko ƙadangaren ne yau ma ya sake faɗo miki?” Hinda ta tambaya, Sharifa ba ta
amsa ba sai fitowa ta yi da ɗaurin ƙirji ta na soshe-soshe.

“ Mama sosa mini ƙaiƙayi duk jikina ƙaiƙayi yake na shiga uku na lalace” haka take faman faɗa
,da farko Hinda ta ɗauka wasa ce sai da ta ga Sharifa na kuka har da majina sannan ta soma
tayata, Sharifa ba ta samu sauƙin abun ba sai da jikinta ya bushe babu damshin ruwa.Tsabar
wahala har sai ta rame,ta koma gefe ta na jan numfashi.
Hinda kuwa alwala ta yi don yin sallah nan ita ma ƙaiƙayi yayi mata wuf duk inda ke da damshin
ruwa.Soshe-soshen ta yi ita ma har sai alwalar ta bushe,suka kalli juna ita da Sharifa “ ina jin
tsoro Sharifa kar ace tsidagun da muka ɗauka ne”

“Shi ne mana Mama,kuma abin da na fahimta sai da ruwa suka taɓa mu ne muka ji ƙaiƙayin”
Sharifa ta faɗa ,Hinda kuwa don gaskata maganar sai ta watsa ruwa a ƙafarta ai kuwa ƙaiƙayin
ya sake dawowa sabo wannan karon Sharifa har sai da ta dara.




# GIDAN BILAL


Bayan sallar magrib anty Sailuba ta gama komai,an gyara ɗaki sai ƙamshi yake yayin da kuma
aka jera kwanonin abinci kan table ɗinta mai kujeru huɗu.Sai da ta yi kwalliya sosai ta saka
kaya masu kyau,abincina ta zuba mini kafin ta ce “ ki zauna ɗakin ki kar ki fito har sai baƙin nan
sun tafi ” Na gyaɗa kai na ce “ to anty ” fita ta yi ni kuma na zauna na soma cin abincina,sai murmushi
nake yadda na ji idona na wannan zuuuu ɗin na tabbata su anty Hinda ana can cikin
uƙuba.Sosai nake jin daɗin mugunta a fili na ce “ ku da yin wanka kuma sai ta Allah,kuma sai
kun dawo irina kun zama ƙazamai kun yi baƙi ƙirin” sai kuma na yi shiru jin muryoyi na tashi
alamun baƙin ne suka zo.
Ina jin su na zolayar anty Sailuba “ irin wannan kwalliyar matarmu ai sai ki sa mu kasa fita”
“Ina ji fa saboda matarmu ba ta son tsufa shi yasa ta ƙi barin ta haihu”
“ Ai kuwa dai in haka ne za mu kawo wata matar”

“ Allah ina son haihuwa sosai zuwa dai ne ba ta yi ba” sai yanzu kawai anty Sailuba ta yi
magana.
“ Ba ki dai je neman ta ba” ɗaya daga cikinsu ya faɗa.
Bilal mijin anty Sailuba ya ce “ yanzu dai mu fara cin abinci tukuna”

Tsit falon ya ɗauka na wani lokaci kafin kuma wani irin gurnani ya ɗauki hankalina har na ji ina
son leƙawa na ga su waye waɗannan baƙi.Labule na ɗan buɗe a hankali,su uku ne gami da
mijin anty Sailuba su huɗu.Zaune suke su na cin abinci babu mai yin magana,amma ni kuma
tambayata ita ce ‘to wannan sautin daga ina yake fitowa?’ ina shirin sauke labule daidai kuma
lokacin ɗaya daga cikinsu ya ɗan tada kai tsabar tsoro har sai da na dafe zuciyata.Ido uku ne
da shi,biyu irin na mutane ɗayan kuma can tsakiyar goshi ban ida shiga firgici ba sai da na ga
wani abu na fitowa ta idon ya na cin abinci nan na fahimci shine ke fitar da gurnanin.
Da sauri na saki labulen ina mai tambayar kaina ,“ina kuma Bilal ya kwaso matsafan nan?” shiru
na yi sai yanzu na gane wato shi yasa anty tace suka ƙi cin abincin sai ita da mijinta suka ci
saboda su idonsu uku ne biyu na nan duniyar ɗayan kuma na ɓoyayyar duniya.

Tunani na soma yi mine ne dalinlinsu na abota da Bilal tabbas akwai wata a ƙasa,tunanin nawa
ne ya tsaya cak jin ɗaya daga ciki ya na tambayar anty Sailuba “ni kam ku nawa ne cikin gidan
nan? Ko kun samu ɗan hutu ne ?”
Ba ta kai ga basa amsa ba shi ma wani ya ce “ƙamshin Gombowa ”
“Tun shigowar mu na ji ƙazinin ɗan ƙabilar Gombo”

A karo na biyu kenan da na ji kalmar sunan Gombo ɗin nan,a hankali na ƙara buɗe labule ina
leƙo cikin rashin sa'a hasken idona ya sauka a rigar ɗaya daga cikinsu,raɗam ya fito kamar
fitilar nan da aka yi yayi mai hasko hoton Obama.Ɗayan ne mai face da wanda hasken idonsa
ya sauka kan rigarsa ya juyo baya,muka haɗa ido da shi .........



Nan na kawo ƙarshen free page duk mai son ci gaba zai biya 500 via 2670215530
ZULFAU YAHAYA Ecobank sai ki turo shaidar biya ta WhatsApp +22795045822 ko kuma katin
MTN ,ƴan Nijar kuma carte moov ko airtel ta 500f.

NB:Daga lokacin da book ɗin nan ya zama complete 800 ne.


29 jully 2024


MRS SADAUKI ce 🌚
[09/09 à 10:39] MRS SADAUKI 👑M~SHURAIMí ¾í´�: *MAITAR IDO*

HoRrOR story☠️

Na
© Chamsiya Laouali Rabo
#MRS SADAUKI💫✍️

*FCWA ☀️*


9-10


Ko da muka koma ciki mijinta bai falo alamun ya na can ƙurya ,anty Sailuba ta kai ni wani ɗaki
ɗan madaidaici babu komai cikinsa sai dangin abinci.Ta je ta ɗauko tabarma da kuma wani
ƙaton bargo ta shimfiɗa min,“ ki kwanta a nan zuwa gobe da safe in Allah ya kai mu za mu sake
yin magana” kai na jinjina mata ta fice ta bar ni nan.
Na haye shimfiɗar na kwanta ina tunanin furicin Kaka wai ba ta haɗa komai da ni ba tsintata ta
yi.Na juya kwanci wani sashen zuciyata kuma na hasko min wulaƙanci da Sharifa ta yi min ƴar
anty Hinda.Na lumshe ido ina mai kai hannu na riƙe munduwar wuyana,‘ ko ya ake yi mutum ya
je wannan duniyar da Kaka ta kai ni ? ’ na tambayi kaina a zuci abun mamaki kuwa zuciyata ce
ta soma yin nauyi kamar an ɗora dutse kafin in samo amsar tambayata .Cike da jin daɗi na yi
bacci wannan daren,tun da asubah anty Sailuba ta shigo ɗakina “ tashi ki yi sallah” shine abin
da ta faɗa ,duk da ban taɓa yin ta ba hakan bai hana ni miƙewa ba na fito.Ƙofar falo na ga a
buɗe hakan yasa na fita,banɗaki na shiga har zan hau masai sai na tuna mafarkin da na yi a
jiya an nuna mini yadda zan ɗauki fansa ta wajen su anty Hinda .Na fita na samo baƙar leda
sannan na koma banɗaki,a cikinta na kasaye duk abin da ke cikina sannan na miƙe ina dariya
ni ɗaya.Da ido na yi wa ledar umarni ta ƙulle kanta kafin kuma na aikata can gidan anty Hinda.

Na fito na wanke jikina na koma ɗakina,gari na wayewa anty Sailuba ta sake shigowa tare da
samun wuri ta zauna.
Ta ɗan ja ajiyar zuciya kafin ta ce “ da farko dai ina yi miki godiya game da abin da kika yi min
jiya,na biyu kuma abin da zan ce miki babu kyau cutar da mutane ki bari”

“ Shikenan ya bar zancen auren?” ita ce tambayar da na yi mata.
Ta ce “ eh ya bari sai kuma ya ɓullo da wata matsalar wai za mu tashi daga nan mu koma can
gidan da ɗan uwansa ya gina kin san nan haya muke”
Na ce “ to ai hakan ba matsala ba ce kin ga kuɗin da yake biya na haya sai ku yi wani abu da
su”
Ta girgiza kai ta ce “ uwar mijina ƴar masifa ce ta bugawa a jarida,kuma kin ga ita ma a can
take.Yanzu dai mu bar maganar nan zo ki yi mini wanki ki share gida da kuma wanke-wanke kin
san halin Bilal shi ma wani sa'in bai da mutumci shi yasa kawai na ce masa ƴar aiki na ɗauke ki”
Tashi na yi tsaye na ce “ babu matsala anty in dai zan zauna a nan ko ƴar aikin sai na zama”
tulin kayanta da na mijinta na wanke ,na yi shara na yi wanke-wanke a ƙarshe na je na yi wanka
sannan ta zuba mini waina da miya sosai na ci na ƙoshi.“ Ki shirya za mu je kasuwa abokan
Bilal yau a nan za su ci abincin dare” Na ce “ kenan yau ba za mu buɗe shago ba?”
“ Eh gaskiya tun da kaji za mu sayo sai kuma mun yi gyaran su”

Da muka fito za mu tafiya kasuwa ta ƙofar gidan anty Hinda muka wuce,tun daga nesa na
hango ledar kashin da na yi tanadi ta na nan tsaye kamar haure jira kawai take lokacin da na
ƙa'ide ta faɗi ƙasa.Na yi murmushin mugunta har na matsu ƙarfe sha biyu ta yi,da muka shiga
kasuwa kuwa na yi ta gamuwa da abubuwan mamaki waɗanda normal mutane ba su iya
gani.Yawancin ƴan kasuwa duk su na da layar da za ta jawo musu customer su sayi kayansu ba
tare da sanin ita fa wannan layar ta na ɗauke ne da aljanu su ne kesa mutane sayen kaya ko ba
su shirya ba,wani abun ma bai da amfani sai ka je gida ka yi ta tunanin mi yasa ma ka saye shi
da ka bar kuɗin ka.

Kaji muka saye manya guda uku anty Sailuba ta miƙa min su na riƙe,daga nan muka wuce
wurin ƴan yaji.Mun yi tsaye ta na cinikin nawa tiyar yaji,yayin da ni kuma idona ya sauka kan
yaji wanda ake kira tsidagu irin ƴan mitsimitsi ɗin nan.
“ In ɗauki guda?” na tambayi mai sayar da yajin yayi murmushi ya ce “ ɗauka mana”
Cike da masifa anty Sailuba ta ce “ mi za ki yi da tsidagu kuma?” na ce “ kawai ya burge ni ne
sai na ɗauki ƙwaya gudan.Haka dai muka yi ta zaga kasuwa har muka zo wajen ƴan sayar da
nama,yadda na ga mata sun yi dandazo wajen wani alhalin duk ga ma su nama nan yasa na ji
ina son ganin shi ɗin kuma wace irin laya yake amfani da ita.Kamar dole haka na duƙa ina
kutsawa har na shigo gaba,sai dai kafin na miƙe tsaye sai idona ya sauka kan wasu ƙafafuwan
jaki a tsaye daram,a hankali na miƙe sai na ga ashe mai sayar da naman ne .Ido huɗu muka
haɗa da shi da farko ya ji tsoro kafin ya soma yi min magana da ido ba wai a bakinsa ba
ballantana ace mutane za su ji.
“ Mi kuma ya kawo macen Siren cikin mutane? Ko da yake ba abun mamaki ba in ka shigo
kasuwa babu kalar jinsin da babu”
Ni ma ta idon na mayar masa “ wane ne kai? Ya aka yi ƙafafunka suke na jaki?”
“ Ki tambayi Anaba ita ai ta san ni ”
Anaba sunan Kaka ne,jin furicinsa yasa na kai dubana ga naman da yake sayarwa duk babu
ɗaya na ƙwarai mushe ne yake sayarwa in rago ya mutu ko saniya haka zai je ya ɗauko su inda
aka jefar ya gyara shi ya zo ya na sayarwa ko da kuwa ya fara lalacewa shi zai san yadda yayi
ya maida shi mai kyau a idon mutane irin shine kuma sai ka ga ka ci ka faɗi rashin lafiya. Ban ankara ba ashe har mutanen da ke zagaye da shi duk ya sallame su sai da na ji muryar
anty Sailuba na cewa “ Sarah ke? Tun ɗazu fa nake yawon neman ki” sai kuma ta harari mai
sayar da naman kafin ta ja hannuna mu wuce.Sai da muka yi nisa na tambaye ta “ amma anty
mi yasa ba ki sayi namansa ba ? Na ga ya fi kowa arha” Ta ja baki ta ce “ arhar ce ke kai mutane ga hallaka,ni ma na taɓa saya lokacin da abokan Bilal
za su zo amma abun mamaki suka ƙi ci wai naman nan da na saka ya lalace ko ban jin
warinsa.A ƙarshe dai barina suka yi da shi sai ni da Bilal muka ci daren ranar kuwa muka dinga
ƴar rige-rigen shiga banɗaki” na ƙyalƙyace da dariya kafin kuma na ce “ to anty mi yasa kuka ci
alhalin an faɗa

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login
google.com, pub-9213700357025247, DIRECT, f08c47fec0942fa0