Showing 18001 words to 21000 words out of 22520 words
Chapter 7 - Abu Bilal Book Compelet Maryam Majidadi
riƙonta ta rasu kuma tabar
ƴarta mace mai suna RUMANA rumana kyakyawa ce ajin farko son kowa ƙin wanda ya rasa
gata da haƙuri da kuma kawaici hakan yasa na bawa Hajiya Maryam shawarar mexai hana su
haɗa auren Rumana da Aliyu,sosai tayi na'am da shawarar tace kuma xata turomun Aliyu tunda
taga ɗan gida na ne sai na masa bayani,hakan akayi tunda na masa magana bai musa ba haka
ya yarda akayi auren duk da ba Son Rumana yakeyi ba a lokacin.bayan aurensu da Sati ɗaya
kuma na haifi ɗana namiji lafiyayye yaci suna Ahmad watau sunan Abban Aliyu kenan".zaro ido
Halima tayi tana kallon Amma kafin cikin rawar murya tace"shine wanda naga pic ɗinsa ɗakin
Daddy na tambaya waye aka cemun na ajiye kawai?".gyaɗa mata kai Amma tayi tace"eh
shine,kuma yayanki uwa ɗaya uba ɗaya"."Amma meyasa kuka ɓoye mun?,kuma yana
ina?".girgixa kai Amma tayi tana ƙoƙarin mayar da hawayenta tace"saboda faɗan hakan yana
tada wani tsohon ciwo da kuma mumunan tabo ga dukkan ahalin guda biyu".shiru Halima tayi
amma ta kasa fahimtar me Amma ke nufi da hakan.ci gaba Amma tayi da cewa"bayan na gama
wankan Ahmad mahaifinki ya samu wata kwangila da zaiyi shekaru a ƙasar waje,bamu so
rabuwa da juna ba saboda zamana da Ahalin Hajiya Maryam yana mun daɗi mun zama tamkar
wanda muka fito ciki ɗaya,gadan gadan tafiya ta kama saboda shaƙuwar dake tsakanin su
Khaleem da Ahmad yasa suka roƙemu damu bar masu Ahmad har Allah ya dawo damu
lafiya,tabbas na firgita dajin wannan magana ganin shi kaɗai Allah ya bani amma Hajiya
maryam tafi ƙarfin komai a wurina a nan take na mallaka mata Ahmad kuma muka tafi muka bar
mata shi,sai dai ta waya mu gaisa.shekarar Ahmad huɗu su Khaleem kuma 6 daga lokacin ne
kuma mumunar ƙaddara ta fara faɗawa a wannan family mai cike da soyayyar juna da aminci
da zaman lafiya,kuma har lokacin bamu dawo ba ko ziyara bamu taɓa zuwa ba,Hajiya Maryam
ta kirani tana gayamun cewa Alhaji Ahmad zaiyi aure,ni kaina na shiga ruɗu amma haka na
daure ban nuna mata ba ina bata baki da haƙuri wata biyu aka yi auren Alhaji Ahmad da wata
wai Hajiya Jamila wanda harta gama zamanta a gidan ban taɓa ganin ko da hoton ta ba.a
lokacin kuma komai ya daidaita tsakanin Rumana da Aliyu yana matuƙar son matarsa yana
kuma riritata baya son abunda zai taɓa mashi ita.bayan wata biyar da Auren Hajiya Jamila
komai ya canza a gidan,Alhaji Ahmad bayajin maganar kowa sai tata,kuma sai abunda tayi a
gidan be isa ya tsallaka koda kara ta gindaya ba,kuma ta shiga ta fita ta raba shi da Aliyu sai da
yakai ko da kallo Alhaji Ahmad baya son ganin Aliyu bare kuma ya raɓesa,hakan ya dasa
muguwar gaba tsakanin Aliyu da Hajiya Jamila wanda ita hassada da ƙyashi yasa bata son
Aliyu kullun burinta bai wuce taga ya faɗi ba,haka naita bawa Hajiya Maryam Hakuri dan bana
so tabar gidan uban ƴaƴanta,a kuma lokacin ne Rumana ta kamu da wani matsanan cin ciwo ta
koma kamar mahaukaciya ta zaune,sai dai a kullun idan ciwon ya tashi a ɗaɗɗaureta da sarƙa a
kuma rufeta a ɗaki,dan xataita yagar fatar jikinta ne tana kuma neman illata kanta,wannan
al-amari ba karamin girgiza wannan ahalin yayi ba,anyi magani anyi har an gaji,wanan abun
kuma shine farkon fara tarwatsa rayuwar Aliyu duk yabi ya susuce ya lallace baya bacci be da
kwanciyar hankali saboda ciwan Rumana,har lokacin shekararsu goma sha biyu da aure amma
ko ɓari Rumana bata taɓa yi ba,kuma duk ciwanta besa Aliyu ya rabu da ita ba ko kuma ya ƙara
aure,haka yake xama ya bata abinci tana t dukansa tana yakushinsa amma be fasa kula da ita
ba,gaba ɗaya ma ya tattara yabar zuwa aiki sai kula da Rumana.a wannan lokacin ne kuma
Hajiya jamila da Aliyu sukayi wani gagarumin faɗa saboda ya kamata tana zuba magani a
abincin Rumana,ya shiga tashin hankali wanda yakai har ya mari Hajiya Jamila ita kuma tayi
amfani da wannn daman tayi masa alƙawarin zai biya marin daya mata ko ta wacce
hanya".shiru Amma tayi tana share hawayen daya ƙi tsayawa a idonta tana kallon Halima
tace"a cikin wannan yanayin kuma na haifeki kikaci sunan Ammin Faruq wanda itama a lokacin
ne ta rasu riƙon Faruq ya dawo hannuna aka dangin mahaifinsa suka kai mana shi har
Amerika,a wannan yanayin ne Aliyu ya fita dasu Ahmad ,a yarda yace ya barsu a mota kafin ya
dawo ya samu babu Khaleel ,khaleem da kuma Ahmad,yayi ruɗewa iya ruɗewa in da a wurin
suka bashi tabbacin wata mata ce tazo ta tafi da yaran,yacce suka kwatanta masa surarta
lokaci ɗaya zuciyarsa tayi na'am da Hajiya Jamila ce,gida ya dawo yana tuhumarta ita kuma
tace bata san anyi ba don duk ranar be fita ba,a kuma cikin ɗakinsa aka tsinci kayan su
Khaleem ɗuk jini da wasu irin abubuwa da suke bada tabbacin Aliyu ya faɗa kungiyar asiri
ne,sosai hankalin kowa ya tashi da ƙyar Abba ya kira Daddy yake gaya mana mutuwar su
Khaleem da kuma Ahmad,ya girgiza sosai amma sai ya ɓoyemun yaƙi sanar da ni case ɗin
dake faruwa kuma ya hanani yin waya da kowa.sam Aliyu ya birkice yaƙi ansar laifinsa ya kuma
ɗauki alƙawarin ɗaukar mataki akan Hajiya Jamila ,a wannan lokacin kuma wani tashin hankalin
ya doso kai in da Abba da kanshi ya kama Hajiya Jamila tana ihu a ɗaki ga Aliyu kwance
kwance a ɗakin akan gadonta yayin da take fitar da jini tana ihun Aliyu yayi mata faɗe".wani irin
miƙewa Halima tayi da sauri tace"be yiwuwa,wannan ba gaskiya bane,Yaya Aliyu bazai taɓa
aikata haka ba ".ta ƙare maganar hawaye na zubowa a idonta.girgiza kai Amma tayi ta kasa
tsayar da hawayenta tace"Ayyah Halima ki daina saurin yanke hukunci haka,mahaifiyar data
haifesa ita da kanta ta bada shedan Aliyu yayiwa Hajiya Jamila fyaɗe".daskarewa a wurin
Halima tayi ga tsananin tsoro daya bayyana ƙarara a idonta da ƙyar ta haɗiyi wayu mai masifar
ɗaci cikin rawan murya tace"yaya za'ayi uwar data duƙa ta haifi ɗanta wanda tafi kowa yarda da
ɗanta ta bada wannan ƙazamar shaidan ga ɗan data haifa da cikinta,anya Mamy itace
mahaifiyar Yaya Sudais kuwa?".
ALLAH KA GAFARTAWA IYAYENMU KAYI MANA KYAMYAWAN ƘARSHE
2152592149 Maryam Ismail UBA bank 300nairah, VIP 500,shaidar biya da Kuma masu son
tura kati(300) ta wannan layin 07033636337.
[11/13, 23:34] Jordan: 16
Kallonta kawai Amma tayi tace"wannan kuma ko waye ya kallah yasan gaskiya,kuma da bata
tabbatar da hakan ba da bata bada shaida ba".wasu hawayen ne suka kawo idon Halima ta
kasa cewa komai kafin Amma taci gaba da cewa"a lokacin ne Abba ya kira Daddynki yana
sanar masa da baƙin ganin da yayi"haka Daddynki ya kwasa ya tafi gidan amma ba abunda ya
canza dan Abba yayi matuƙar fushi a nan ne yake faɗin ya rabu da Aliyu har abada kuma ya
ciresa daga cikin ƴaƴansa ko da mutuwa yayi kada Aliyu yazo kan gawarsa kuma duk abunda
yasan ya masa toya tattaro ya dawo masa dashi".ko kaɗan Daddy be nuna beji daɗi ba dan
shima ya yarda ɗari bisa ɗari Aliyu ya aikata hakan saboda lura da shaidu da kuma yarda
Hajiya Maryam ta bada shaida da kanta akan ɗanta,shima cikin fushi ya yayiwa Aliyu faɗa da
wulaƙanci sosai ya kuma yi ala wadai da irin halin da Aliyu ya canza kuma a nan ne ya yarda
Aliyu ya shiga ƙungiyar Asiri,shima yace bashi ba Aliyu kuma bazai yafe masa ran ɗansa daya
salwantar ba,a takaice dai haka suka kori Aliyu da matarsa Rumana wacce take cikin halin
ciwo,Allah kadai yasan yarda suka rayu bayan shekaru kuma akaji labarin Rumana ta samu ciki
kuma a lokacin Aliyu yana zaune da Dattiya tsohon mai gadin da Hajiya Jamila tasa aka kora
,yanzu kuma bazan iya ce maki ga in da Dattiya yake ba,a wata majiyar wai Hajiya Jamila ta tari
Aliyu ta faɗa masa lallai yayi hankali da kansa wannan duk yana daga cikin sakamakon marin
daya yi mata ne kuma ya jira abunda zai faru na gaba,bayan ta dawo ne kuma Abba ya saketa
duk wani asirin data masa ya warware,.a lokacin Daddynki yaso ya ganta yaji meya haɗa su
amma sam Abba ya hana yace ba amfani kawai ya barta shi bazai iya ci gaba da zama da ita
bane,wannan takaicin sakin yasa ranar da Rumana ta haihu ko tashi daga in da take bata yi ba
Hajiya Jamila ta shigo ta kasheta har lahira ga yaro jariri kuma,a nan ne kuma Aliyu ya kamu da
ciwon zuciya mai tsanani saboda tsaban rikicewan da yayi ,daga wannan lokacin kuma babu
wanda ya kuma jin labarin Hajiya Jamila har gobe kam,amma kuma Aliyu yana da ƙudirun
nemanta a ko wanne yanayi ko da hakan zai zama abu na ƙarshe da zai aikata a rayuwarsa,mu
kuma tun daga wannan lokacin alaƙar mu taja baya zan iya ce maki rabon dana ga wani cikinsu
harna manta,Ammi kinji iya abunda na sani a rayuwar Aliyu,sanin gaskiyar wannan al-amari
kuma sai Allah sai kuma wanda yayi fatanmu dai Allah ya bayyana gaskiya kowa ya gane
matsayarsa".kuka sosai Halima ta fashe dashi gaba ɗaya ta gama rikicewa,idanuwanta sunyi
jajir tace"Amma har raina ban yarda Yaya Aliyu zai iya haka ba,duk iya halinsa na fahimci yana
da kirki ga addini sai dai ban musa shaye-shayen da yake ba shima wannan kuma na ɗauka
duk ƙunci ne yasa ya faɗa wannan harkar amma ki yarda yana da zuciya mai kyau".murmushin
da yafi kuka ciwo Amma tayi tace"nasan waye Aliyu ,kuma Aliyu a da babban malami ne yana
da matuƙar ilimi na boko dana addini,fatanmu dai muyita yi masa addu'a har Allah ya bayyanar
da gaskiya".kasa cewa komai Halima tayi ta miƙe ta fito tana share hawayen dake kuma zubo
mata.tsayawa Faruq yayi yana ɓata fuska yana kallon yarda idonta ya canza launi alamun taci
kuka sosai,langwaɓar da kai yayi yace"meyasa kike son wahalar da kanki haka?,dan Allah kiji
tausayinmu Ammina,ki sani kece farin cikinmu a gidan nan,kuma kinsan yawan ɓacin ranki
abunda zai iya janyowa".murmushin ƙarfin hali tayi tana cewa"na daina Yayana".murmushinsa
mai kyau yayi kafin ya jata suka zauna yana mata fira har yaga taɗan sake tana dariya kafin ya
tafi ya barta..
Ɗuƙe take ta rasa abunda ke mata daɗi yau kimanin kwana biyar kenan bata saka Abu bilal a
ido ba bare kuma taji daga garesa kusan kullun sai ta shiga gidan Aunty Aysha amma bata
ganinsa kuma kota tambayeta itama sai tace kwana biyu bata ganshi ba.miƙewa tayi tana jan
Hijab ɗinta ta leƙo parlo ganin babu kowa yasa ta fita da sauri a gate kam babu wanda ya tareta
ta fice daga gidan,gidan Aunty Aysha ta shiga da sauri ta ƙarasa ciki tana kallon motar Abu bilal
a parking lot ,har tuntuɓe takeyi wurin saurin ta shiga,cak ta tsaya tana ƙare masa kallo wanda
shi ɗinma ita yake kallo kamar yau ya soma ganinta,gani tayi yayi rama sosai da alama yana
cikin damuwa.ƙasa tayi da kanta,sai lokacin shima ɗauke idonsa daga kallonta ya wuce kan
chair ya zauna beko kulata ba,cikin parlon ta dawo daidai gabansa ta tsaya cikin rawar murya
hawaye na kawowa idonta tace"Yaya ina ka tafi na daina ganinka?".banxa yayi mata ko kallonta
beyi ba bare kuma tasa ran zai bata ansa,zama tayi a gabansa tana tanƙwashe ƙafafunta
tace"dan Allah ka gaya mun Yaya".wani irin ɗaure fuska yayi kamar an saukar masa da mutuwa
yace"i'm not your Yaya".wani irin haushi ya kama Khadija da shigowanta parlon kenan ta kalli
Halima tace"malama tashi muje gida dallah"ko kallonta Halima batayi ba saima saurin miƙewa
da tayi ganin Abu bilal yabi hanyar fita cikin ɗaga sauti tace"i know who you are".cak ya tsaya
tare da lumshe idanuwansa da suka fara sauya launi ya juyo yana kallon Halima yace"then
what?,everything you hear about me just believe it babu wanda bani nayi ba,duka ba zargi bane
sai kuma me kike so ki sani bayan wannan?".wani irin kuka mai cin rai Halima ta saki da
matuƙar ƙarfi ya runtse idonsa danji yayi sautin kukanta har cikin ƙwaƙwawalwar kansa ya rasa
wanne irin yanayi ne yake ji a kanta a lokutan nan,cikin muryar kuka tace"wallahi bazan taɓa
yarda ba,tabbas akwai wani abu a ƙasa ba zaka taɓa aikata irin haka ba".wani tsaki yaja afin ya
tureta daga gabansa ya wuce abunsa.a nan wurin ta duƙe tana sakin wani kukan da gudu Bilal
ya iso wurinta ya duƙa tare da tallabar fuskarta yace"Aunty,ki daina kukan bana so,ki daina
zance wa Abba ya daina maki faɗa ina sanki kinji,duk wanda nake so Abbana yana sanshi
".sosai ta riƙe Bilal a jikinta amma ta kasa cewa komai bare ta tsaida hawayen idonta,hannu
yasa yana goge mata hawayen fuskarta yana nuna mata alamun tayi dariya,murmushi ta ƙirƙira
tana ƙoƙarin miƙewa.Khadija kam ta cika tayi faful a wurin ƙiris take jira ta fashe,jan hannun
Halima tayi fuuu suka fice Bilal na binsu da kallo.ta baya Abu bilal ya hango fitarsu wani iska
mai zafi ya furzar ya kuma duƙar da kansa yana sauraron bugun zuciyarsa.har cikin bedroom
Khadija taja Halima kafin ta sakar mata hannu tace"watau bakiji kashedin Daddy ba
kenan?,Halima me kika gani ga Ɗan daba da kika maƙale masa har kina zubar da girmanki da
hawayenki a gabansa?,meye ya shiga kanki ne?".wani kallo take bin Khadija dashi kafin
tace"kada ki sake ce masa Ɗan daba,nace bana so,ko daban yake yi aike be maki ba".sakin
baki Khadija tayi tana kallonta kafin tace"koma me zakice karesa da kikeyi be isa yasa a daina
masa wannan kallon ba tunda ya aikata,kuma ki sani bazan taɓa baki goyon bayan kiso Sudais
ba har abada".tsuka Halima taja kafin tace"dama ban roƙa ba"ta ƙare maganar tana buɗe ƙofa
ta fice daga ɗakin bin bayanta Khadija tayi a daidai ƙofa suka ci karo da Lamis,wani irin faɗuwa
gaban Halima yayi ta koma da baya tanayin ƙasa da kai.
ALLAH KA GAFARTAWA IYAYENMU KAYI MANA KYAKYAWAN ƘARSHE
2152592149 Maryam Ismail UBA bank 300nairah, VIP 500,shaidar biya da Kuma masu son
tura kati(300) ta wannan layin 07033636337.
[11/13, 23:34] Jordan: 17
Dedicated this page to Balkis Adam Bello
Khadija kam da wani irin kallo tabi Lamis mai wuyar fassaruwa,murmushi yayi yana cewa"sarkin
ɓoyo yau kin fito kenan".cewar Lamis,kasa cewa komai Halima tayi kafin Khadija tace"ai
kwanan nan Yaya sauyi kala-kala ma ka ganshi".harara Halima ta bita dashi kafin tayi ƙasa da
kai tace"ina yini Yaya Lamis",da lafiya lau ya ansa yace"muje kuga wani abu".be jira cewarsu ba
yayi gaba suka bisa baya a chair ya zauna yana ɗauko wani ƙaramin box ya miƙawa Halima
sannan ya ciro agogo mai kyau ya miƙawa Khadija yace"ga naki ƙawarmu,bansan zamu haɗu
ba aeda kema an maki naki na daban"murmushi kawai tayi tace"na gode kwarai Yaya hakanma
ae yayi".baki Halima ta turo kafin tace"thanks".kallonta kawai yayi kafin ya janye kallonsa daga
gareta.miƙewa Khadija tayi tace"muje ki rakani tau".murguɗa baki Halima tayi yace"wallahi baza
ni ba".sakin baki Khadija tayi,murmushi kawai Lamis yayi yace"muje na ajiyeki ƙawarmu".dariya
tayi tana cewa"kinga na samu rakiyan da yafi naki".gwalo kawai tayi mata ta wuce ɗakinta,a
haka suka fita a motar Lamis,tunda suka tafi babu mai cewa komai can Lamis yayi breaking
silent ɗin da yace"Khadijatau ya kike da ƙawar taki?",ɗan murmushi tayi tace"Yaya ina
lafiya,Halima sarkin rigima ma tana lafiya".kansa ya shafa yana cewa"bari ta jiki nikan in ce
bansan anyi bama".dariyan itama tayi tana faɗin "tuba nake" a haka har suka ƙarasa gidan su
Khadija,10k ya bata amma da ƙyar ya samu ta ƙarɓa sannan ya juya ya tafi abunsa....shiru yake
yana shafa kansa yayinda idanuwansa suke lumshe a hankali ya ware su wanda harsun canza
launi ,iska ya furzar yana cewa"wai me yake damuna yanzu?",ina so na ganta".ya faɗa yana
miƙewa tsaye key ɗin motarsa ya ɗauka yana fita yayinda zuciyarsa ke masifar azazzalarta da
masifan son Halima tabbas yasan son Halima ya shammaceshi yayi masa mugun kamu shi
kansa bazai iya faɗin taya hakan ya faru ba,burinsa kawai ya kasance da ita,duk wani motsin da
zaiyi sai ta faɗo masa a rai,ɗaura kansa yayi akan sitiyari cikin sanyin murya yace"sonki yana
azabtar da ni Halimana".tuno rigimarta yayi lokaci ɗaya ya saki ƙayataccen murmushi ya kuma
dannawa motan shi key ya nufi unguwar su Halima.a waje yayi parking daidai ƙofar gidan Aunty
Aysha kafin ya fito zai shiga gidan kamar kullun sanye yake da wando jeans ash colour sai
t-shirt black colour mai dogon hannu sosai yayi matuƙar kyau sai fitar da sihirtaccen ƙamshi
yake yi ga tsadaddiyan agogon gucci ɗaure a tsintsiyar hannunsa,cover's black ne a ƙafarsa sai
sheƙi sukeyi ,a hankali ya tura ƙofar gidan Aunty Aysha ya shiga sai da yaje ƙofan parlo sannan
yayi sallama da gudu Khalifa ya rugo ya rungumesa yana cewa"oyoyo Uncle".ɗaga yaron yayi
sama yana shafa kansa kafin yace"ina Bilal?".ɗan shiru yayi kafin yace"yaje gano aunty Halima
,kuma Umma bata sani ba yace kada na gaya".lumshe idanuwansa yayi lokaci ɗaya yaji
zuciyarasa ta buga da ƙarfi ga wani irin tsinkewan zuciya lokaci ɗaya,dafe kansa yayi da yaji ya
matuƙar sara mashi yayi saurin sauke Khalifa ya juya zai fito da sauri,riƙesa Aunty Ayaha tayi
tace"Sudais lafiya kuwa?" shiru yayi kafin yace"Bilal,zan kira sa".be jira cewarta ba ya fice da
sauri,hijab ta saka itama ta bi bayansa dan kwata kwata bata yarda da yanayinsa ba tasan dole
akwai abunda ke damunsa.zaune Halima take akan bene sai jujjuya kai takeyi tana jin ansa
kuwwar ihun da kuma maganar da ake gaya mata,Bilal kam yana ta tsaye gabanta yana riƙe da
hannunta yana jijigawa yana cewa"Aunty ki buɗe idonki don Allah,nifa ke nazo gani ko Umma
bata sani ba"ya karashe maganar kamar zaiyi kuka.a hankali ta soma buɗe dara-daran
idanuwanta da suka kaɗa sukayi jajir kamar gauta lokaci ɗaya suka juye,zumbur ta miƙe tana
rufe kunnanta da ƙarfi ga wani irin rikitaccen ihun data saki,raɗau haka Abu bilal yaji dodon
kunnansa ya ɗaukar masa ihun Halima wani irin bugawa ƙirjinsa ya kuma yi ya tura gate ɗin
gidan da sauri ya shigo ,Daddy,Amma da fitowarsu kenan dan jin ihun Halima yasa