Showing 3001 words to 6000 words out of 22520 words
Chapter 2 - Abu Bilal Book Compelet Maryam Majidadi
gidan Aunty
ko?".gyaÉ—a masa kai yayi.sannan yaci gaba da cewa "to Abu Bilal na gode"ya faÉ—a tare da
rungume Abban nasa,shima rungumesa yayi yana jin zuciyarsa na zafi a haka ya cireshi daga
jikinshi ya sakashi mota ya rufe,har motar ta ɓace Bilal na ɗaga masa hannu.juyawa kawai yayi
ya koma cikin gidan,kai tsaye bedroom ya shige ya faÉ—a saman bed tare da rumtse idanuwansa
abubuwa da yawa suna dawo masa a kai.
ALLAH KA GAFARTAWA IYAYENMU KAYI MANA KYAKYAWAN ƘARSHE.
VOTE
COMMENTS
SHARE
[11/13, 23:34] Jordan: í ¼í½‡í ¼í½‡í ¼í½‡í ¼í½‡í ¼í½‡í ¼í½‡
*ABU BILAL!!!*
í ¼í½‡í ¼í½‡í ¼í½‡í ¼í½‡í ¼í½‡í ¼í½‡
```By``` ```Maryam``` ```ismail``` ````Majidadi```
*_______________________
______________*
*í ¼í¼ˆí ¼í·°AINUWA í ¼í·¼RITER'Sâœ�í ¼í¿¼*
*í ¼í·¦SSOCIATIONí ¾í´�í ¼í¿»*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
FREE PAGES
PAGE 3
Ko kaÉ—an a daren Abu bilal kasa runtsawa yayi gaba É—aya tunaninsa da komai nasa ya gama
birkicewa,ganin abun bamai ƙarewa bane yasa ya tashi ya ɗauro alwala ya soma sallah,wannan
yana É—aya daga cikin nagartan halayansa duk tsanani be manta da sallah ba da kuma azumin
alhamis da litinin ,haka zalika yaransa ko me sukeyi basa bari lokacin sallah ya wuce su.sai
bayan yayi sallahn asuba ya samu bacci mai nauyi ya É—auke shi akan sallayar.Tun sassafe
Karima ta fito tsakar gidan ta soma share-share(Karima Æ´ar mama uwani ce).bayan ta gama ta
tattaro wanke wanke tana wanke wa,kamar yarda ta saba duk kullun tana gamawa ta É—aurawa
Mama uwani girkin wainan da takeyi na siyarsa,a hankali gidan ya soma tara mutane masu
siyan waina,hayaniyarsu ce ta tashi Abu bilal daga bacci wanda dama shi duk irin nauyin baccin
da yakeyi motsi kaÉ—an kan iya tashin shi,wani siririn tsaki ya saki saboda ya tsani wannan sa'an
ta Mama Uwani babu abunda suka rasa amma ko kaɗan ta kasa haƙura da wannan
sana'ar,zura jallabiya yayi ya fito fuskarnan murtuke sai ɗacin rai yakeyi saurin duƙar da kai
Karima tayi ganin irin mugun kallon da yake jefarta dashi,da sauri ta miƙe tayi baya,ji kakeyi
gidan yayi tsit gaba É—aya masu siyan wainan sunyi shiru a tunaninsu yabar gidan tun da sukaga
su Jagwado basa ƙofar gida.wiƙi wiƙi da ido Datti yayi sana baya baya yana faman boye rigar
dake jikinshi dan rigar Abu bilal É—ince an mashi shanya jiya ya É—auke yace"Allah ya soni dama
Uwani tace in ɗauka in gwada muga ko zaiyi mun kyau,banni dai ban taɓa satar maka kaya
ba,ah tau Allah na tuba me akayi akayi wani kayan Sude can bare shi Sude É—in".wani irin
mugun kallo Abu bilal ya jefesa dashi kafin ya halbar da ƙatuwar robar da Karima ta gama zuba
ruwa ciki,tuni su Jagwado suka shigo a guje suka kora masu siyan waina,ƙafa yasa ya halbar
da ƙullun wainan.da sauri Mama uwani ta miƙe tace"Amma Dattiya kaji tsoron Allah ni nasan
kama ɗauki kayanshi bare nace kasa ko xai maka kyau?".ganin da gaske Abu Bilal ƴan ɓannar
yake ji sai ɓarin kaya yake yi yasa ta dauke roban kuɗinta tayi ɗaki a guje tana danna
kuba.Karime dake rakuɓe ya dakawa tsawar da yasa ta soma sakin ƙara da ƙarfin gaske
tace"Yaya Aliyu na tuba wallahi bazan sake fita nayi dare ba".wani kyakyawan mari ya sakar
mata wanda yayi sanadiyar dauke jinta da ganinta na mintoci kafin da ƙyar ta fizgo baki da niyar
yin ihu ,suman tsaye tayi lokacin da Rambo(karen Abu bilal)yayo kanta yana sinsinanta,a guje
Jagwado yazo ya shiga tsakaninsu ya riƙe Rambo yace"Allah ya huci zuciyar mai gida,hakan
bazata sake faruwa ba insha Allahu".da kausashiyar murya ya kalleta yace"kin san sauran
ai".ya wuce ɗaki yana hararar Dattiya dake laɓe bakin kofa yana niyar sakin fitsari a
wando.yana shiga É—akin towel ya É—auka ya wuce toilet yin wanka.minti 40 yayi ya gama
shiryawa tsab cikin ƙananan kaya kamar kullun yau kam harda p-cap ya murza a kansa sai
tashin masifar ƙamshi yakeyi duka kayan jikinsa dark blue ne dama Abu bilal ba daga baya ba
wurin saka takalmi sau ciki,sosai ya fito ɗan gaye dashi yana kuma ɗaukar hankali.jin ƙamshin
turarensa ya fara tunkaro waje yasa Karima yin saurin É—auraye robar dake hannunta tayi saurin
lafewa bayan kitchen tana raba idanu,wani irin taji lokacin da taga ya fito,ƙura masa ido tayi
kamar zata zazzago idanuwanta.tsaye yayi bakin É—akinshi babu kowa a tsakar gidan kuma ta
gyara ko ina tsab.ƙwafa yayi yace"zan kwakwale idanuwanki masu kama dana mayu".da sauri
Karima tayi saurin yin ƙasa da kanta tana jin kamar zuciyarta zata fasa ƙirjinta ta fito dan
masifar tsoro,tasan ko be ganta ba yana gane idanuwa a kansa,kai tsaye waje ya fita in da ya
iske yaransa a wurin miƙewa sukayi suna musabaha dashi kafin ya zauna kan kujera tare dayin
É—aya kan É—aya ya kuma lumshe idanuwansa.Aguje Halima ta fito tana saka Ahlari a jakar dake
rataye a kafaɗanta saurin riƙeta Amma tayi tace"Little ae baki makara ba bare kuma kiyi mani
wayau ki fita baki karya ba".wani irin kwaɓe fuska tayi kamar zata saki kuka tace "wallahi Amma
basan karin nan nake ba,ki barni dan Allah".zaro ido Hajiya Mama tayi tace"haba Sadiya babbar
budurwa Tahfeez fa zakije ina amfanin fita baki ci abinci ba,yanzu tau bara na haÉ—a maki a
lunch box".kyawawan idanuwanta ta lumshe kafin ta waresu tace"to Mama".cike da tsananin
soyayyah Faruq ya kalleta yace"Æ´an mata yau ni zan ajiyeki a school gaskiya".raurau tayi da ido
kafin ta zagaya da sauri wurin Daddy ta saƙalo hannuwanta akan wuyanshi ta kwantar da kanta
a kafaÉ—anshi cikin turo baki tace"Daddyna ka gaya masa ni nafi son zuwa Tahfeez a
ƙafa,ƙwaɗayin ladan nake yi".murmushi Daddy yayi ya shafo kan ƴar tasa yace"dandai kince
lada Ammina amma ko ni basan fitanki a ƙafa nake yi ba,kinsan yanzu duniyan ta lalace".juya
idanuwa tayi kamar mai tunanin wani abu can tace"to Daddy kuyi mani addu'a zanje lafiya na
dawo lafiya da yardar Allah".murmushi Hajiya Mama tayi tace"insha Allah kuwa,zoki wuce kada
kiyi latti kinji".karɓar box ɗin tayi cike da ladabi ta dan durƙusa tace"na gode Mamana"kafin ta
wuce tace"sai anjimanku kafin in dawo yau ayimun abun daÉ—i".ta fita tana kwashe hijabinta
sama tana gyara riƙon box ɗinta.sake baki Amma tayi tace"naga ranar da Sadiya zata
girma,kwatakwata yarinyar can bata da wayau sai shirme,kuji yarda ta fita tana yaye hijabi,duk
ta wani sakalce a gari".murmushi Daddy yayi yace"ni dai a barmun Ammina tayi abunda take
so,komai lokaci ne insha Allah zata daina data ƙara girma".cikin natsuwa take tafiya tana kallon
littafin dake hannunta tana gyara haddanta,hankalinta kwance tana tafiya harta ƙaraso ƙofar
gidan su Khadija,a daidai soron gidan ta samu Khadija tsaye da alamu fitowarta kenan itama da
shiga irin ta Sadiya,washe baki Halima tayi tace"to ki fito muje dan ni nan ba tsayawa zanyi
ba".murmushi Khadija tayi tace"a lallai yau dan an fito da wuri ba ae dole kice haka,ni wuce
muje".a haka suka jero suna tafiya.yauma Halima ce side din da su Abu bilal suke zaune.ganin
unguwar ƙwalam ba kowa yasa Khadija zaro ido shaf ta manta da yaune lahadin ƙarshen wata
kuma yaune yaran Abu bilal ke gyara unguwa kuma babu wanda ya isa ya fito bare ya biyo ta
hanyan.tsayawa sukayi da sauri ganin su Jagwado sun tsaya a gabansu,ras ras haka gaban
Khadija ya bada sauti yayin da Halima kam ko a jikinta dan tsab ta gane Jagwado shine wanda
ya watsa mata ruwan kwata a jiki.littafin dake hannunta ta rufe ta kwashe Hijab dinta ta saka
littafin a jakka,cikin rawar baki Khadija tace"dan Allah kuyi haƙuri wallahi na manta shiyasa na
janyota muka biyo ta nan hanyar"gaba ɗayansu juyowa sukayi suna ƙarewa Halima kallo wanda
ko kaɗan bata san me sukeyi ba gaba ɗaya ta zuba kyawawan idanuwan ta ƙure Abu bilal da
ido ko kiftawa bata yi.idanuwansa a lumshe kamar ko yaushe cikin kausasshiyar murya
yace"bar kallona"ko kaɗan taƙi dainawa saima lumshe ido da tayi lokacin da raji daddaɗar
sautin muryarsa ta sauka a dodon kunnenta.wata uwar tsawa Jagwado ya daka mata wacce
tasa ta juyo da azabar ƙarfi cikin hassala itama tace"dallah malam kabar mun tsawa tun da kai
ba uban.."kasa ƙarasa maganar tayi ganin Abu bilal tsaye a gabanta yana jefarta da mugun
fusataccen kallo.har ƙasa Khadija ta duƙa tace"Abu bilal dan girman Allah kayi haƙuri baƙuwace
anan,insha Allah ba zata sake kallonka ba ko yiwa yaranka rashin kunya"cikin sauri Khadija ta
janyo Hijab ɗin Halima tace"ki basu haƙuri".sakin baki Halima tayi kafin tace"tabɗi,wallahi bazan
bashi ba,ko ba shine ba jiya ya watsa mun ruwan kwa.."saurin saka hannu tayi ta rufe bakinta ta
kuma fashe da kuka saboda É—allin da Abu bilal yayi mata a baki fuska É—aure yace"uwar rashin
kunya".ƙasa tayi da kai tana rusa ihu tare da bubbuga ƙafafuwanta tanayin baya baya tana
cewa"Allah sai na gayawa Daddy,dama kaima mugune irin wancan"ta ƙare maganar tana nuna
Jagwado da hannu.wani uban haushi ne ya turnuƙe zuciyar Abu bilal cikin cool voice yace"bara
na maki duka sai ki kawo kaka ba Daddy ba".wani irin zaro ido tayi zuciyarta na bugawa da ƙarfi
ta yarda box din hannunta ta fasa wata gigitacciyar ƙara wanda sai da Abu bilal ya rufe
kunnuwansa ya kuma rumtse ido da ƙarfi,sannan Halima ta sheƙa a guje har tana ture
shi.ƙwafa yayi yana kallon gudun da takeyi wanda taƙi biyu xaiyi ya kamata ya juyo yacewa
Khadija"bar nan".har ƙyarmar jiki takeyi ta miƙe zata bar wurin a tsawace Jagwado yace"your
box".kwashe box É—in tayi itama ta runtuma a guje tana godewa Allah daya sa basu faÉ—a tarkon
Abu bilal ba.a hanya ta samu Sadiya,tana ganinta ta ƙalƙale da dariya harda riƙe ciki .wani uban
harara Khadija ta jefa mata tace"kici gaba tabbas wata rana bazaki dara ba in dai akan Abu bilal
ne,dan baki san waye shi ba shiyasa sakarcinki yake sawa kike neman cutar da rayuwarki a
banza,ina mai tabbatar maki kuma Mugun da kika kirashi tabbas zai maki aikin mugunta".wani
irin lumshe ido Halima tayi tace"wow nice name Abu bilal"sai kuma ta saki ƙayataccen
murmushi.tsaki Khadija taja ta wuce warta cikin islamiyya har lokacin gabanta be daina dakan
ukku ukku ba.
ALLAH KA GAFARTAWA IYAYENMU KAYI MANA KYAKYAWAN ƘARSHE.
VOTE
COMMENTS
SHARE
[11/13, 23:34] Jordan: í ¼í½‡í ¼í½‡í ¼í½‡í ¼í½‡í ¼í½‡í ¼í½‡
*ABU BILAL!!!*
í ¼í½‡í ¼í½‡í ¼í½‡í ¼í½‡í ¼í½‡í ¼í½‡
```By``` ```Maryam``` ```ismail``` ````Majidadi```
*_______________________
______________*
*í ¼í¼ˆí ¼í·°AINUWA í ¼í·¼RITER'Sâœ�í ¼í¿¼*
*í ¼í·¦SSOCIATIONí ¾í´�í ¼í¿»*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
FREE PAGES
PAGE 7
```Start``` ```patronizing``` ```ABU BILAL``` luvly ```fans
Ta hanyar wannan account din 2152592149 Maryam Ismail UBA bank 300nairah, VIP
500,shaidar biya da Kuma masu son tura kati(300) ta wannan layin 07033636337.
Lumshe ido Halimatu tayi kamar mai bacci sai kuma ta ware idanuwanta akan fuskar Khadija
tace"ni bance maki am in luv with him ba,just dai i want to be with him that's all".Dafe kai
Khadija tayi tace"lallai kam kice tashin hankali na dunfaromu kuwa,wannan mutumin kina tunani
yana da feelings akan wani abu wai soyayyah?,to bari kiji Abu bilal besan meye tausayi ko
soyayyah ba,a duk duniyar nan ina ga yaronsa da yayarsa kawai yake tausayi yake kuma
É—agawa,ina tunanin idan kika fahimci waye Abu bilal kece mace ta farko da zaki fara nisanta
kanki dashi".wani irin faÉ—uwa gaban Halimatu yayi sai kawai ta share tace"ashema yana da
feelings tunda har yana iya aure ya haifi yaro".ƙwafa Khadija tayi tace"ina dai faɗa maki idan ma
son shi kika fara to kiyi gaggawan cirewa dan a duniya babu wanda ya tsana sama da mutun
yace yana son shi".fari da ido Halima tayi tace"what ever".suna a haka Faruq yayi ƙwanƙwasa
ƙofan jin tace"yes come in "yasa yace"Faruq ne".dariya khadija tayi tace"eh Yaya ka shigo".tura
ƙofan ɗakin yayi ya shiga bakinsa da sallama kai tsaye gaban Sadiya ya duƙa yace"Ammina
sannu,how is your body"ƙasa tayi da kanta tace"Alhmdllh".kallonta yayi kafin yace"ina kike jin
pain ".lumshe ido tayi tace"no where,dama fever ne".gyaɗa kai yayi kafin ya miƙa mata Drugs
É—in hannunshi yace"kisha yanzu and at the night kuma".a hankali ta furta thank u.murmushi yayi
kafin ya juyo yace"Khadija ya gida da Ummi?".sakin baki tayi tana dariya tace"haba Yaya Faruq
ni da ka manta ko ina existing ma a room É—in nan,saboda Æ´ar rigima ba lafiya".murmushi ya saki
yace"ba haka bane,kinsan dai Ammin tawa uwar raki ce ae".murmushin itama tayi tace"haka ne
kam,su Ummi suna lafiya,ai kwana biyu baka leƙa ba".shafa kansa yayi zuwa gemunsa
yace"when i'm less busy zan shigo na gaishe ta"daga haka ya miƙe ya fita yana janyo masu
ƙofan.nannauyar ajiyar zuciya Khadija ta sauke tace"ke ga namiji daya ansa sunansa namiji mai
nagarta amma ki wani maƙalewa wani".cikin rashin fahimtar in da zancen nata ya dosa
tace"who's that".harara Khadija ta zabga mata tace "zaki cemun baki san Yaya Faruq yana
sonki bane?".a bazata tambayar yazo mata ta wani ƙwalalo ido tace"haba mana is just your
imagination he's my Yaya fa,mu duka Amma ne fa ta rainemu".Dariya zancenta yaso bawa
Khadija tace"ai naga dukanku ita ta haifesu kuma babu aure a tsakaninku"."kinga Khadija i can
never imagine dating Yaya Faruq,please let's call up the chapter".Halima ta faÉ—a.
Shiru Khadija tayi bata kuma cewa komai ba ta miƙe tsaye tana cewa"malama tashi ki raka
ni".miƙewa Halima tayi tana janyo long hijab ɗinta mai hannu ta saka tace "muje".a jere suka fito
a babban parlo suka samu Daddy da Amma suna kallon news.Har ƙasa Khadija ta duƙa ta
gaishe da Daddy shima cikin sakin fuska ya ansa yana saka mata albarka 10k ya bata yace ta
gaishe da su Ummi.langwaɓar da kai Halima tayi tace"let me escort her".jinjina kai Daddy yayi
yace"a kula da hanya".da to suka ansa kafin tayiwa Amma sallama ta fito,a jere suka fita daga
gidan.har sun soma tafiya daidai ƙofar gidan Aunty Aysha Halima taci burki tare da kallon
Khadija tace"ki rakani nan mana,2days ban shiga wurin Aunty Aysha ba".kallonta Khadija tayi
tace"amma baxamu daɗe ba gaskiya bana son magriba yamun a hanya".ta ƙare maganar suna
tura ƙofan gate ɗin gidan.da gate man suka fara gaisawa da yake yasan Halima ya barsu suka
wuce ciki,babu lefi shima gidan yana da girma ,suka tura main entarance na main parlo bakinsu
ɗauke da sallama.tsaye yake ya juya baya yana zuba ruwa a mug,sanye yake da ƙananan kaya
kamar kullun yayi sagging trouser É—insa har kana iya hango farin boxer É—in dake jikinsa,duk
yarda sukeyin sallaman hakan besa ya juyo ba sai da Aunty Aysha ta fito daga kitchen tace"kai
dai Aliyu naga ranar da zaka bar wannan mishkilancin naka ace sallama ma anayi ba zaka iya
buÉ—e baki ka ansa ba".juyowa yayi yana kafeta da ido bece komai ba nan idonsa ya safka akan
Halima da yake janyo hijab É—inta daga jikin door,murmushi Aunty Aysha ta saki tace"haba
Halima ai nayi fushi gaskiya,yaushe rabonki da gidan nan saboda Allah,ko jiya kina tahfeez na
leƙa na gaishe dasu Amma".da fara'arta itama ta ƙaraso cikin parlon tana cewa"wallahi Aunty
school ne baya bari".ta ƙarashe maganan suna zama karab idanuwanta suka sarƙe cikin na
Abu bilal wanda yake kai Mug É—in ruwan sanyi bakinsa wata uwar harara ya afka mata ,da sauri
tayi ƙasa da kanta tana cewa"Aunty ina su Nahnah?".juyawa tayi tace "ae kinsan da yake mun
ƙara yawa gidan na tabbata Bilal da Khalifa sun janye mun ƴar auta suna baya ana hawa
keke".Sai lokacin Khadija taga Abu bilal zaro ido tayi tana addu'ar Allah yasa kada Halima ta
ganshi.miƙewa Aunty Aysha tayi tace"bara a kawo maku ruwa".ruwa da lemu ta ɗauro a
ƙaramin tray ta kawo masu tare dasu Bilal dake biye da ita.da gudu Bilal yazo ya faɗa jikin
Halima yace"la Aunty ni kika zo nema a gidan mu?,kinga Abbana taso muje ki gaishe shi".ya
ƙare maganar yana jan hannun Halima dake kallon fuskarshi da murmushi sai a lokacin ne taga
tsantsar kamar Bilal da Abu Bilal."ka santa ne"Aunty Aysha ta tambaya.Nahnah dake lafe jikin
Halima tace"eh Momy ita ce Auntyn da yake baki labari ta tahfeez".juyowa tayi tana kallon Abu
Bilal tace"Aliyu yauga Auntyn Bilal ka gani sai ku gaisa".wani irin haÉ—e fuska yayi yana kallon
Aunty Aysha data tsare shi da ido.cikin ƙasa da kai Halima tace"ina wuni".tana kuma maimaita
sunan Aliyu a ranta.yana tafiya yace"lafiya" .yayi hanyar waje wani irin haushi ya turnuƙe
zuciyar Khadija kawai tace"to zamu wuce"."da wuri haka kuma".Aunty Aysha ta faɗa.miƙewa
Halima tayi tace"dama rakiya zan mata na biyo,insha Allah zan shigo ai".itama Aunty Ayshan
miƙewa tayi tana jan hannun Bilal daya maƙalewa Halima tana cewa"to Allah ya kaimu,sai kin
shigo".da ƙyar ta janye Bilal daga wurinta sannan suka fita Khadija sai masifa takeyi dan khadija
badai faÉ—a ba.banza Halima ta mata har suka rabu kafin ta dawo gida zuciyarta cike da
tambayoyi iri iri.�angaren Hajiya Mama kam duƙe suke a gaban wani ƙaton mutumi baƙi ƙirin
dashi sai mazurai yake yi cikin murya marar daÉ—in saurara yace"me kike so ayiwa
yarinyar?".nisawa Hajiya Mama tayi tace"boka ina so a turawa yarinyar baƙaƙen aljannun da
zasu hanata zama lafiya,wanda zasu rikita mata rayuwa wani lokacin ma ayi tunanin mayyah ce
ko kuma ta haukace,so nakeyi idan suka tashi a kamota can dawa,kuma duk wanda ya
kusanceta da sunan so ko tausayinta to ya mutu ya zama kuma ace ita ake tunanin tana
kisan".jinjina kai Bokan yayi yace" zaki biya million 1,aikinki an gama da batun shi yanzu haka
suna niyyar shiga jikinta,sai dai duk ƙarshen wata xaki basu jinin baƙaƙen dabbobi wannan
dalilin ne zaisa duk tsanani su kasance tare da ita".wata irin murmushi ya suɓucewa Hajiya
Mama tana jin damuwanta yazo ƙarshe ta buɗe jakkarta ta kwaso kuɗin ta jibgesu gaban Bokan
sannan ta tashi suka bar kan dutsen ita da Hajiya talatu.daidai Halima zata shiga gida taji wani
irin masifar sanyi na ratsa duka sassan jikinta ga tsigar jikinta data mimmiƙe gaba ɗaya,lokaci
É—aya kuma taji ta daina jin sanyi .gate É—in gidansu ta buÉ—e ta shige.
ALLAH KA GAFARTAWA IYAYENMU KAYI MANA KYAKYAWAN ƘARSHE
VOTE
COMMETS
SHARE
DAN ALLAH IDAN KIN KARANTA KIMUN SHARING..
[11/13, 23:34] Jordan: í ¼í½‡í ¼í½‡í ¼í½‡í ¼í½‡í ¼í½‡í ¼í½‡