Showing 1 words to 3000 words out of 22520 words
Chapter 1 - Abu Bilal Book Compelet Maryam Majidadi
[11/13, 23:34] Jordan: í ¼í½‡í ¼í½‡í ¼í½‡í ¼í½‡í ¼í½‡í ¼í½‡
*ABU BILAL!!!*
í ¼í½‡í ¼í½‡í ¼í½‡í ¼í½‡í ¼í½‡í ¼í½‡
```By``` ```Maryam``` ```ismail``` ````Majidadi```
*_______________________
______________*
*í ¼í¼ˆí ¼í·°AINUWA í ¼í·¼RITER'Sâœ�í ¼í¿¼*
*í ¼í·¦SSOCIATIONí ¾í´�í ¼í¿»*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
All thanks to Allah SWT for the privilege to start this book,special greetings to my siblings
,cousins and My lvly fans that have waited so long for Majidadi,and now am back da wani saban
salon,I know u will luv it,cos I am in luv with it too,ABU BILAL daban yake da saura.í ½í¸˜í ½í¸�í ½í¸€
FREE PAGES
PAGE 1
Tafiya takeyi da sassarfa ,idanuwanta dake sanye cikin farin medical glasses É—inta wanda yake
tamkar na gayu ya kuma ƙawata fuskarta takai dubanta ga tsadaddiyar Agogon dake ɗaure a
tsintsiyar hannunta,É—an zaro dara-daran kyawawan idanuwanta tayi tana kallon lokaci da alamu
ta makara sosai.kayan jikinta na kalla dan ganin irin saurin da takeyi sanye take cikin uniform
blue wando da hijab doguwa har ƙasa mai hannu sai farin ɗankwali wanda duk yarda ta
janyoshi be hana gashin kanta bayyana ba,wanda yake kwance lub a goshinta harya kusa
haɗewa da giranta,a kafaɗarta kuma irin jikkarnan ta goyo da mata ke yayine saƙale ta saka
hannu ɗaya ta bar ɗaya yana yawo a bayanta.Halimatu Doguwace daidai misali bata da ƙiba ko
kaɗan sai dai kuma jikinta ko ina a ciccike yake bata da irin farin nan sai dai tana da matuƙar
kyau komai nata kamar ita tayi kanta,Halimatu bazata wuce shekara sha bakwai ba.A daidai
bakin layin ta tsaya tace "washh Allah Khadija wallahi na gaji"ta ƙare maganar tana kallon
Khadija dake tsaye ta haÉ—e fuska.juyo idanuwa Khadija tayi tace"Malama idan zakizo mu wuce
kizo,haka kawai kin samu latti da wannan shiriritar taki".rausayar da kai Halima tayi tare da
shagwaɓe fuska ta wuce gaba kawai.bin bayanta Khadija tayi tana mita kamar zata ari baki.dafe
kai Halima tayi tace"billahil azeem kin dameni!!,zamu raba hanya yanzu ku...".kasa ƙarasa
maganar tayi tana kallon gefenta.zaune yake akan farar kujerar roba yayi É—aya kan É—aya duk da
yana zaune bazaisa ka kasa gane cewar shi dogo bane ba,yana da faffaɗan ƙirji,chocolate
colour ne,in da fuskarsa ke ɗauke da daradaran idanuwa ga gashin girarsa baƙi siɗik kamar
wanda yayi jagira,yana da dogon hanci mai ɗaukar hankali ga ƙaramin bakinsa dake ɗauke da
laɓɓa masu tudu sunyi kamar browni kamar lite pink.yana da matsakaicin gemu sai gashin baki
in da gefen fuskarsa ke da É—an siririn saje kaÉ—an har zuwa saitin kunnensa,gashin kansa
gwanin burgewa baƙi siɗik yasha aski sai ɗaukar ido yake yi.sanye yake da wando fari 3 quater
sai farar T-shirt ,idanuwansa a lumshe ga hannunsa É—aya ya É—aga yana shafa sumar kanshi
fuskarnan ɗaure babu alamar wasa a tattare da ita ABU BILAL kenan.wani irin ƙwalalo ido
Khadija tayi ganin yarda Halimatu ta saki baki tana ƙarewa ABU BILAL kallo,hakan kuma yayi
daidai daya soma buÉ—e lumsassun idanuwansa jin ido na yawo a jikinsa carab idanuwansa
suka faɗa cikin na Halima da azabar ƙarfi ta rumtse idanuwanta tana ja da baya yayin da
zuciyarta ta harba da masifar ƙarfi.wani irin fizga Khadija tayi mata suna barin wurin da sauri
wani irin kallo Khadija tayi mata da masifa tace"kinyi hauka ne?,meke damunki haka?,kina so ki
janyo mana bala'in da kab danginmu baxasu iya kare mu ba?,ni dai ki rufamun asiri yarda kike
zuwa unguwar nan lafiya toki koma gidanku lafiya kin daiga ta silata kike shigowa unguwar
nan".galala haka Halima kebin Khadija da kallo wanda ko kaÉ—an ta kasa fahimtar abunda take
cewa.har lokacin gabanta be daina faɗuwa ba da ƙyar ta haɗo magana can cikin maƙoshi
tace"waye shi?".Harara Khadija ta xabga mata tace"ban sani ba,kuma ni daga yau ki riƙa
wucewa islamiyyan kawai na sameki a can".siririn tsaki Halima ta saki tace"banxa masifaffiya
kawai"ta fizge hannunta tana shigewa cikin islamiyyan ,duka yinin ranar a haka Halimatu tayi shi
gaba É—aya bata fahimtar komai babu abunda ta koya a makarantar duk tayi kamar wata marar
lafiya,gaba É—aya Khadija na lura da ita amma haka ta share dan bata son tado maganar
ɗazu.tunda aka tashi islamiyyan bakin islamiyyan yake cike da ɗalibai da gudu yaron ya ƙaraso
gaban Halimatu ya janyo hannunta yace"Aunty dan Allah ki gyaramun"ya ƙare maganar yana
kallon takalmar ƙafarsa da zaren su ya warware,juyowa tayi tana kallon yaron kyakyawa dashi
yarone ɗan kimanin shekara biyar a duniya sosai uniform ɗin islamiyyar suka yi matuƙar
amsarshi ,murmushi ta sakar mashi ta shafa kanshi tare da duƙawa tace"to brother".ɗaure
masa igiyar takalmin tayi kafin yace"thank u".da murmushi a fuskarta tace"what's your
name?".hannu yasa ya shafi sumar kansa ya furta"BILAL ALIYU".kafin tayi magana taga
zaratan maza su biyu sun janye hannun Bilal daga jikinta a tsorace taja baya da sauri kamar
zata faɗi ganin su ya matuƙar tsoratata babu annuri ko kaɗan a tattare dasu.numfashi Khadija
ta mayar tare da ɗago Halima daga ɗuƙen da take cikin sanyin murya tace"Sadiya why all
this?,please na roƙeƙi karki janyo wani abun daba shi bane".a daddafe suka wuce gida,tunda
suka tunkaro in da tabar wannan mutumin na É—azu take kallon wurin kamar idanuwanta zasu
faɗo sai dai babu kowa a wurin,lokaci ɗaya taji ko kaɗan bata jin daɗin jikinta,haka a saɓule
sukayi sallama da Khadija ita kuma ta kama hanyar gida tana tafiya da tunanuka iri iri a ranta.a
matuƙar razane take bin jikinta da kallo wanda aka malale mata shi sharkab da ruwan kwata
duka jikinta ya ɓaci har a saman glasses ɗinta ji tayi ranta ya matuƙae ɓaci da azamar sauri ta
rufawa motar baya har in da sukayi parking ta tsaya tana ƙarewa Drivern motan kallo cike da
masifa tace"ka kallah yarda ka ɓata ni da ruwan ƙazanta,ko dabba kayiwa haka aika tsaya kaga
lafiyarta balle kuma mutun".a fusace ya ɓalle marfin motar ya fito yana binta da mugun kallo
yace"anje an ɓata zan zuba maki tafi a wurin nan wallahi".tuni idanuwan Sadiya sun sauya kala
a hassale tace"wallahi ko da wasa balle a gaske,duk wani abun da kake ji dashi to nawa yafi
ƙarfin naka,idan kuma kana ganin wasa toka gwada,wanda besan darajar Ɗan adam ba
kawai".sosai zuciyar Jagwado ta ɓaci dajin furucin yarinya ƙara a kansa hannu ya ɗaga zai kifa
mata mari,ganin Abu Bilal ya buɗe murfin mota ya fito a hankali cikin takun ƙasaita ya ɗaga
masa hannu sosai sautin muryarsa ya daki dodon kunnenta in da da ƙyar ya iya furta
"kiyi...haƙu...ri"ya ƙare maganar da nisa a tsakani ya juya ya shige gaban gidan da suke
tsaye.wani irin daskarewa a wurin Sadiya tayi tana bin wannan mutumi da kallo tuni taji duk
wani ɓacin ranta ya gushe a haka ta juya ta nufi hanyar unguwarsu da babu nisa sosai
tsakaninta da wannan...daidai ƙofar wani tanƙameman gate naga ta tsaya ,hannunta tasa tare
da tura ƙofar masu gadin dake wurin su biyu suka miƙe da sauri sanye da uniform suna mata
sannu da zuwa,fara'a faÉ—aÉ—e fuskarta tace"ina wuninku,nikam nace a daina tashi mun haka ku
É—in ai tamkar iyaye kuke a gareni".cike da jin daÉ—i da irin karramawa da dattako irin na Sadiya
suke mata fatan alkhairi.tana ta ansa addu'ar da suke mata kafin ta nufi main Entrance na
gidan.Sai lokacin na samu damar ƙarewa gidan kallo wani irin tanƙameman gida ne wanda zaka
iyakiransa gari guda tsayawa faɗin tsaruwar gidan ɓata lokaci ne dan ko rade's ɗin dake parking
lot abun kallo ne.ko ina ga masu aikin gidan nan sai shawagi sukeyi suna kuma yiwa Sadiya
sannu da zuwa tana ansawa murmushi faÉ—aÉ—e a fuskarta ,masha Allah shine abunda na faÉ—a
lokacin data shiga parlon aljannar duniya kenan babu wasu tarkace a parlon sai dai ya tsaru iya
tsaruwa daga cikinsa ne kuma ya rabu har ɓangarori ukku.ɓangaten dama naga ta shiga tun a
parlon ta soma kwaÉ—a sallama tare da kiran "Amma!,Ammana!!".wata farar dattijuwar mata ta
fito cikin shiga ta alfarma fuskarta É—auke da murmushi kallo É—aya zaka mata ka hango tsantsar
kamarta da Halimatus sadiya."Æ´ar albarka sannu da dawowa,ya akai na ga jikinki haka?"Amma
ta faɗa.cike da soyayyar mahaifiyar tata ta langwaɓar da kai gefe tace"Ammana ruwa ne aka
watsamun a hanya,amma yanzu zan gyara jikina "ta ƙare maganar tana tura ɗaya daga cikin
ƙofofi ukku dake parlon.da alama kuma nan ne bedroom ɗinta,ɗakin ya tsaru komai na cikinsa
royal blue ne ko ina ɗakin gyare yake tsab sai zuba ƙamshi yakeyi ,jakkar dake rataye kafaɗarta
ta ajiye a ma'ajinta sannan kai tsaye ta wuce toilet,uniform É—in ta soma cirewa sai da ta saka su
a injin wanki ta wanke tas har inner's É—in jikinta sannan ta sanyasu a wurin shanya dake toilet
ɗin,sannan ta ƙarasa ciki ta soma sakarwa kanta shawa.da ƙarfi ta runtse idonta ganin wannan
saurayin na É—azu yana mata gizau babu abunda take gani sai siffarsa da kuma kunnenta dake
tariyo mata dadaÉ—ar muryarsa,a daddafe ta samu tayi wankan ta fito É—aure da towel sai
ƙamshin daɗaɗan sabulan wankanta takeyi kai tsaye gaban mirror taje ta busar da yalwataccen
gashin kanta wanda yake baje har tsakiyar bayanta sannan ta shafa lotion da sauri sauri
,doguwar riga na kanti ta saka fara ƙal da ita ta feshe jikinta da turaruka masu daɗi sannan ta
janyo agogonta ta saka ta kuma saka glasses É—in idanuwanta taja veil É—inta black tayo waje.
ALLAH KA GAFARTAWA IYAYENMU KAYI MANA KYAKYAWAN ƘARSHE
VOTE
COMMENTS
SHARE FISABILLAH
[11/13, 23:34] Jordan: í ¼í½‡í ¼í½‡í ¼í½‡í ¼í½‡í ¼í½‡í ¼í½‡
*ABU BILAL!!!*
í ¼í½‡í ¼í½‡í ¼í½‡í ¼í½‡í ¼í½‡í ¼í½‡
```By``` ```Maryam``` ```ismail``` ````Majidadi```
*_______________________
______________*
*í ¼í¼ˆí ¼í·°AINUWA í ¼í·¼RITER'Sâœ�í ¼í¿¼*
*í ¼í·¦SSOCIATIONí ¾í´�í ¼í¿»*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
FREE PAGES
PAGE 2
kai tsaye parlo ta fito tana kallon wayar hammunta ƙirar samsung kusan cin karo sukayi da sauri
taja baya tana ƙarewa Faruq kallo tun daga sama har zuwa ga fuskarsa dake ɗauke da faffaɗan
murmushi,murmushin itama ta saki tace"Yaya Faruq yaushe ka dawo ne?".far yayi da idanuwa
yana buÉ—e hannayensa yace"lokacin da little Ammiena ta manta dani note(Faruq yaron yayar
Daddyn Sadiya ce wacce ta rasu,su biyu iyayensu suka haifa sanadin hakan Daddy ya sakawa
Æ´arsa Halimatus sadiya).murmushi tayi tace"ni dai ban manta da Yaya ba Allah".matsa masa
tayi ya wuce ciki wurin Amma yayin da Halimatu ta fito main parlo na gidan tana kallon Hajiya
mama dake hakimce akan chair hannunta ɗauke da remote tana canza tasha.duƙawa Sadiya
tayi tace"Mama barka da gida".sakin fuska Hajiya Mama tayi kamar ba ita bace ke ɓata rai
yanzu tace"a'a Æ´ar albarka an taso daga tahfeez É—in kenan?".GyaÉ—a kai Sadiya tayi alamar eh
tana É—ago kanta tana kallon Daddy da shigowarsa gidan kenan fuskarta É—auke da murmushi ta
ruga tana karɓar jikkar hannunshi tace"Daddyna barka da dawowa".shafa kanta yayi yana janta
a jikinshi cike da soyayyarta yace"lafiya qlau little,ya Tahfeez?".cikin sanyin murya tace
"Alhmdllh".wani irin tuƙuƙin baƙin ciki ne ya tokare zuciyar Hajiya Mama ganin Daddy ya janyo
Halimatu jikinsa ji tayi kamar zuciyarta tayi zallo ta hito saboda tsananin kishin ita bata taɓa
haihuwa a gidan ba,kuma Sadiya ita kaÉ—ai ce Æ´arsa duk duniya.a fili kuma sai ta saki murmushi
tace"Daddyn Sadiya barka da dawowa,ya aikin?".cike da murmushi yace"lafiya qlau Hajiyar
Halimatu ,ya fama da Æ´ar rigimar tawa?".nan ma dariyar tayi tace"ai kasan yau ana Tahfeez
rigiman da sauƙi yanzu dai ake shirin farata"dukansu dariya suka saka kafin ta karɓi jikkar
hannun Halimatu ita da Daddy suna wucewa babban part na cikin parlon.
�angaren Abu bilal kuwa yana shiga madaidaicin gidan nasu ya soma halbar da bucket ɗin
daya ci karo dashi a hanya,saurin miƙewa tsaye Mama tayi tana gyara kashin ɗaurin
ɗankwalinta tana ƙarewa Abu bilal kallo wanda ta taso ne da masifa taji uban waye ya halba
mata bokiti,wata dariya Datti ya saki yace"su Uwani masifa to ba ni É—in da kika raina bane,masu
gidan ne da kansu,sai naga kinyi shiru kamar ruwa ya ciki".ƙanƙance ido Mama Uwani tayi
tace"to ai ina da gaskiya tunda bakai ka sayar mun bucket É—in ba".ko kallonsu Abu bilal beyi ba
ya wuce zai shiga part É—insa da gudu Bilal ya rugo tare da rungume Abbansa daga baya.wani
irin lumshe idanuwa Sudeis yayi yana jin abun har cikin ransa yasan duk duniya yaron shi tilo
É—aya ke iya yi masa haka,fuskarsa kada ran kada han ya juyo tare da É—aga yaron sama ,dariya
sosai Bilal ya saki yana cewa Abbana"welcome".dawo dashi yayi akan ƙirjinsa tare da sunbatar
goshinsa yace"thank u".shiru yayi alamar yana son sake wata maganar,fahimtar hakan da Bilal
yayi duk da ƙananun shekarunsa yasan halin Abbansa tsab yasa yace"Tahfeez alhmdllh,nayi
karatu da yawa,Abba yau har Aunty nayi a scul"."amma nan nan ka shigo mu ka fara iskewa ko
sallamar bamu samu arziƙinta ba bare kuma gaisuwa,Allah na gani Aliyu halinka sai kai,haka
kawai kaita cutar mu".rufe ido da ƙarfi Sudeis yayi yana kuma taunar lips ɗinsa kamar zai huda
kafin ya juyo da runannnun idanuwansa yana watsawa Datti harara,ganin yana yin idanuwansa
yasa Mama uwani shigewa É—akinta da sauri tana kyarmar jiki.ba shiri Datti ya kwashi silifas
É—insa yana niyar yin waje kusan cin karo sukayi da Aunty Aysha wacce tasha ado na alfarma
daka ganta kasan hutu ya gama ratsata, kallo É—aya zaka mata kaga tsantsar kamarta da Sudeis
fuskarta ɗauke da murmushi ta ƙarasa shigowa tace"a'a ba kanta Kawu guduwa da silifas a
hannu?,da alama yau ka taɓo ɗan rigimar taka kenan?".wiƙi wiƙi yayi da ido yana washe baki
dan yasan yau kam yayi arziƙi bashi ba zuwa maula.ƙwafa yayi yace"kedai bari Aysha ,cutar
dani kawai Aliyu ya gama yi,Allah yasan ko kallon banza ban taɓa yi masa ba".sauke Bilal
Sudeis yayi bece komai ba ya wuce part ɗinsa yana ɓalle buttons na gaban rigarsa.ɗakine
madaidaici parlo ne É—auke da kujeru da kayan kallo komai na É—akin fari ne tas gyare yake tsab
sai zuba masifar ƙamshi yake yi,kai tsaye bedroom ya shiga nan ma ɗakine madaidaici ɗauke
da gado da wadrobe da miro komai tsab,toilet ya shiga ya cire wandon jeans na jikinshi ya
soma sakarwa kansa shawa ya ɗauki lokaci a toilet ɗin kafin ya fito ɗaure da towel a ƙugunsa
ga ƙarami yana goge kansa da shi,ƙarar wayarsa yasa ya fito parlo kallon Aunty Aysha yayi ya
É—auke kai ya kwashi tsaÉ—aÉ—É—un wayoyinsa ya koma bedroom.kallonsa tayi ta girgiza kai ta juyo
tana sauraran surutun da Bilal ke zuba mata tana murmushi tana ɓare masa chololate ɗin data
masa tsaraba.kai tsaye gaban mirrow yaje ya shafa lotion É—insa yayi ya feshe jikinshi da É—aÉ—É—an
turarensa masu masifar ƙamshi sannan ya buɗe wadrobe ɗinshi boxer ya ɗauko da singlet ya
saka sannan ya saka crexy trouser ya saka T-shirt blue colour,agogon gucci ya É—aura a
tsintsiyar hannunsa kafin ya tako a hankali zuwa parlon cikin É—aya daga cikin kujerun ya xauna
yana kallon Aunty Aysha ciki ciki yace"sannu".ko kaÉ—an batayi mamakin yarda yayi mata ba
tasan halinsa sarai nan ma yayi abun arziƙi daya ce mata sannu,juyowa tayi ta kallesa
tace"Sadauki Aliyu ni na rasa me wa'ancan tarkacen yaran keyi a ƙofar gidan nan,Aliyu kallo
É—aya xa'a maka ai maka kallon É—an daba É—an shaye-shaye wannan wacce irin rayuwe kake
yi?,ka koma gida Aliyu ka ƙi ,kabar zuwa aiki ni na rasa meye matsalanka,to ka sani yau nazo
É—aukan Bilal ne,baxan iya bari ya taso yana ganin mahaifinsa a cikin irin wannan bauÉ—aÉ—É—iyar
rayuwar ba".sosai maganar É—auke Bilal ya daki zuciyarsa duk tsawon maganar da takeyi sai
yanzu ya ɗago yana ƙare mata kallo.tabbatar masa tayi tace"yes,yau zan ɗauki Bilal ko kana so
ko baka so,ace yaro ko islamiyyah yaje wa'ancan ne zasu je ku É—auko shi?".lumshe ido yayi ya
rasa abun cewa da ƙyar ya iya haɗo kalaman"Aunty no..kada..ki"shiru yayi ya kasa ƙarasawa
yana jin bugun xuciyarsa na tsananta,shareshi tayi ta wuce bedroom É—insa akwati ta É—akko ta
soma saka kayan Bilal a ciki tas ta kwashe komai niƙi niƙi ta fito da akwatin parlo ,shikam Abu
bilal kasa cewa komai yayi illah kallonta da yakeyi,janyo hannun Bilal tayi tace"ka fito da
akwatin xanje mu gaisa da Mama Uwani sannan mu wuce.bata jira cewarsa ba ta wuce É—akin
Mama Uwani.da sallama a bakinta ta shiga É—akin ,ansa sallamar Mama uwani tayi tace"a'a
Aysha ce,sannu da zuwa".da yauwa Aunty Aysha ta ansa ta ƙarasa shiga tana janye da hannun
Bilal a saman tabarmar da Mama uwani ta shimfiÉ—a mata ta xauna bayan sun gaisa tace"Mama
nazo tafiya da Bilal ne".zaro ido Mama tayi tace kice mana yau gidan ba lafiya kawai muyi ta
kanmu,É—auke Bilal a gidan nan ai tamkar kafa wani tashin hankali ne".dariya sosai Aunty Aysha
ta saki tace"lallai yaukam akwai rigima ku ƙyalesa yayi ya gama"miƙewa tayi ta buɗe jakkarta ta
ibo kuÉ—i masu yawa taba Mama uwani tayi mata sallama,sosai tayi mata godiya sannan ta
rakota ƙofar ɗaki.tsaye Aunty Aysha ta hango Sudeis ya jingina bayansa a bango ya lumshe
idanuwansa ga hannuwansa rumgume a ƙirji.matsowa tayi kusa dashi tasa hannu ta janyoshi
tace"haba autan Mamy ka daina ɓata ranka,kaga ba nisa ne tsakanina da kai ba ko yaushe idan
kaso zaka iya zuwa kaga Bilal,kayi haƙuri zanyi hakan ne duk dan tarbiyarsa ta
gyaru".shagwaɓe fuska yayi tare da langwaɓar da kai kamar wani ƙaramin yaro shafa kansa
tayi tace"am sorry my lovely bro"..murmushi ya sakar mata wanda yayi matuƙar ƙawata
fuskarsa.sama ya É—aga Bilal yana shafa kansa suka fito waje,a nan suka samu Datti yana ta
kwashewa su Jagwado albarka san ranshi,miƙewa yayi da sauri yana gyara hular kanshi yana
matsowa kusa da Aunty Aysha,a lokacin har an saka akwatin Bilal a motar da tazo dashi.kuÉ—i
da yawa ta bawa Dattiya sannan tayi masa sallama kafin ma ta idasa maganarta yayi gaba
abunsa tunda ya kwashi kuɗi,zagayawa gefen motar yayi ya durƙusa ya kama hannuwan Bilal
yana kallonsa karo na farko da naga yayi magana mai tsayi yace"Allah yayi maka albarka,ka
kula da karatu sosai ,ka zauna wurin Aunty xanzo ko yaushe ina ganinka kaji".ido cikin ido Bilal
ke kallon Abbansa can yace"Abba zaka riƙa kawo mun chocolate ɗina a