Showing 27001 words to 30000 words out of 34483 words

Chapter 10 - Abu Naka Book 3 Complete Hafsat C Sodangi

da kafaxarshi”.
Gaba xaya aka amsa “Amin”.
Kalaman Abu ne wannan bayan ta amsa sannu da zuwa da gaisuwar da aka yi ta yi mata.
“To a nuna min inda zan yi sallah”.
Saddiqa ta wuce za ta nuna mata, ta tarar tuni har Kawu Gixe ya idar. Ta tsuguna a gefe tana
gaishe shi.
“Ya ya aka yi aka yi irin wannan aiki haka baku sanar da gida ba?”
Ba ta iya ce mishi komai ba in ban da kukan da take yi, saboda ta riga ta gama tsorata da
yanayin da aka fito da shi a ciki.
Har suka bar asibitin ran nan bai wani dawo cikin hayyacinshi ba, ita kam ta so a ce an barta
ta kwana a wurinshi Abu ce ta ce gara su tafi wai in sun zauna me za suyi mishi bayan ga
likitoci suna ta kaiwa da kawowa, ga kuma Kawu Gixe da Sani suma a nan za su kwana?
Sun dawo gida Saddiqa sai bin Abu da kallo take yi, zuciyarta tana raya mata duk halin da
Mus’ab ke ciki hankalinta a kwance yake, da kanta ta xebo abinci ta zauna ta ci ta xora da
‘ya’yan itace, ta yi wanka ta hau gado ta yi kwanciyar ta tana tambayar Saddiqa,. To don kin qi
ci kin qi sha sai me? Ina ce duk iya shegenku ne ya jawo hakan? Da kin hanashi ai da bai yi ba. Saddiqa ta zuba mata ido tana kallon ta cikin matsanancin takaici, ta ma rasa me za ta ce
mata.
Dare ya yi nisa sanda ta farka ta duba agogon wayarta uku da rabi ne na dare, ta shafa inda
Abu ke kwance ba ta nan, ta tashi ta tura qofar banxaki a hankali don ta gani, nan ma ba ta nan.
Ta fito falo ba ta ganta ba.
Har ta zuwa za ta koma xaki sai ta tura qofar xaya xakin, Abu tana ciki a zaune kan

sallaryarta hannayenta duka biyu a xage zuwa sama, kuka take yi hawaye sai gudu suke yi a
fuskarta.
“Ya Ubangiji, wannan yaro Mus’abu….”
Abin da kawai Saddiqa ta iya ji kenan. A hankali ta mai da qofar ta rufe ta nufi xaki ta je ta
kama tata harkar.
Suna idar da sallar asuba suka isa asibitin, har lokacin Mus’ab yana kwance a rigingine
kamar yanda suka barshi, bambancin kawai shine a yanzu yana furta kalmomi da wanda ke
kusa da shi yake iya ji.
“Cikina, cikina, a san min ruwa in sha”.
Saddiqa ta kalli mahaifinta ta ce, “Baba wai zai sha ruwa”.
Kawu Gixe bai kulata ba sai Sani ne ya yi mata bayani, “Sun ce kar a ba shi komai”.
Tausayin halin da yake ciki yasa Saddiqa ta soma zubar da hawaye. Da sauri Kawu Gixen ya
ce mata, “Ke, kar fa ki kawo mana iya shege a nan? Kuka? Ba ki san za a yi hakan bane da
kika ingizashi yaje ya yi? Wannan fitina da me ta yi kama? Dole ne sai kowa ya haihu?
Waxanda basu haihu ba basa rayuwa ne? Yanzu babu bayin Allah mutanen kirki da su basu
haihun ba?”
Abu ta tave baki ta ce, “Uhm! Nima dai abin da na ce mata kenan”.
Sani ya yi maza ya ce, “A’a, Kawu Aisha kuwa babu yanda ba ta yi da shi ba shi ya qi”.
Da sauri Kawu Gixe ya ce, “To me yasa ba ta faxa ba ta ja bakinta ta yi shiru?”
Cikin nutsuwa Sani ya ce, “Kawu ina ganin tuna an riga anyi sai ayi addu’a kawai ayi dace, ita
Aisha kam Kawu kowa ya ganta ai ya san ta shiga wani al’amari, tunda ai ko shekaran jiya
gidansu ba haka na ganta ba, daga jiya zuwa yau ne fa ta yi wannan zabgewar”.
Kwanan Mus’ab uku kafin ya dawo cikin hayyacinshi sosai ya san abin da yake ciki da
waxanda suke tare da shi.
Kowa sai murna yake, yana fara samun sauqi Abu ta yi xib! Ba ta ko kallon inda yake
kwance, ko ya yi qarfin hali ya yi mata magana ba ta wani kulawa balle ta amsa.
Saddiqa ta kalle shi ta ce, “To kai ka yi haquri mana ka yi shiru dole ne sai ka kula Abu?”
Abu ta galla musu harara dukansu biyun, ta ce, “To ni don ba a kulani ba sai me? Ni ai bake
ba ce ya dena kulani mana. Fitinannun mutane masu neman fitinar tsiya, ana zaune lafiya ku
tada mutane a tsaye”.
A hankali ya buxa baki ya ce, “Ki yi haquri Abu, Aisha ba ta da wani laifi nine na hanata gaya
muku, in ta bi umarnina kuma ai ba laifi ta yi ba”.
“To amma kai me yasa za ka yiwa kanka irin wannan abin, kai baka san haquri ba?”
Ya xan yi murmushi ya ce, “Zuciyata ce Abu ta qi ta yi min daxi, babu abin da take so irin ta
ga Aisha da ciki, ko ganin mace mai juna biyu na yi sai in ji inda a jikin Aisha yake da ya ya zan
ganta ta yi?”
Ta kawar da kai tare da tsaki ta wuce ta yi tafiyarta ta barsu su biyu. Ya miqa hannu ya yafito
Saddiqa ta matso kusa da shi, a hankali ya buxa baki ya ce mata.
“Ki yi haquri Aisha, mun sha wuya amma kwanan nan in muna raye da yardar Ubangiji
buqatarmu za ta biya, zan ganki kema kina tura cikinki kamar yanda nake ganinshi wurin matan
mutane”.
Saddiqa ta yi murmushi ta ce, “Amma dai kuwa kafin ayi hakan Yaya ai kuwa dai kam an sha
wuya”.

Ya ce, “Eh, amma ai babu komai Aisha, in dai har buqata ta biya to ai kuma duk wata wahala
tarihi ce”.
Ta ce, “Haka ne Yaya”.
An sallamo Mus’ab ya dawo gida a dal8ilin sauqin da ya smau. Kawu Gixe da Abu kuma sun
koma gida Misau.

SHEKARU BIYAR BAYAN YIWA MUS’AB TIYATA
Saddiqa da mijinta suna zaune lafiya cikin kwanciyar hankali da nunawa juna qauna mai
yawa, sai dai har yanzu matsalar gidan ba ta kau ba, buqata kuma ba ta biya ba, haihuwa da
ake neman ba ta samu ba.
Bayan tiyatar farko da aka yi mishi, Mus’ab ya sake komawa wata tiyatar nan ma ya tsira da
qyar, ita ma dai anyita ne a dalilin jijiya ta toshe, wato dai lalurar farkon ce ta sake dawowa. Har
yanzu kuwa babu wata alama da ta nuna an samu nasara, domin cikin shekaru bakwai xin
aurensu ba a tava ko da vari ne a gidan nashi ba, sai dai al’ada ta xuake, in anyi bincike a ce
wani ciwo ne yake neman tava mahaifa.
Suna cikin rumfa a harabar gidan bayan Mus’ab xin ya dawo daga gudun motsa jiki suna
tattaunawa. Ya miqa hannu ya xauki inibin da ya tarar tana ci a tiren silba yana taunawa a
hankali.
Saddiqa ta zuba mishi ido cikin nutsuwa saboda ta gane akwai abin da yake son gaya mata.
“Na ga kamar magana za ka yi?”
Ya xan yi murmushin qarfin hali tare da faxin, “Hankalinki nake so ki bani”.
Ta yi maza ta ce, “Dama a wurinka yake”.
Ya ce, “To, kin gane ko?”
Ta ce, “Uhm! Ina jinka”.
Ya yi ajiyar zuciya mai qarfi ya ce, “Yanzu ke Aisha kina ganin zamanmu haka a gidan babu
qaruwa ya yi dai-dai?”
Ta ce, “Kamar ya ya?”
Ya ce, “Babu haihuwa mana, ke kin ce ba ki yarda a ce za a sake yi min wani aikin ba, a
gabanki ne kuma likita ya tabbatar mana da cewar ciwon nan ya sake dawowa, amma in anyi
saurin cire shi ba zai zamo mai tsanani sosai ba. To ina ce gara kawai in je ayi aikin tun bai qara
yin qarfi ba?” Ta zuba mishi ido tana kallon shi a wani yanayi na rashin sanin abin yi, da qyar ta iya buxa
baki ta ce mishi, “Ashe maganar sake yin aikin nan bai qare ba?”
Ya gyara zama cikin sakin fuska ya ce, “Ba wai bai qare bane, so nake mu fahimci juna ni
dake Aisha, nima ba son aikin nan nake yi ba, to amma ya ya zan yi?”
Ta zuba mishi ido kamar ta yi magana, sai kuma ta fasa. Cikin nutsuwa ta ce mishi, “Ina
zuwa”. Da sauri ta miqe ta shiga gida tamkar mai xauko wani abu ta dawo.
Ya zauna nan wajen minti sha biyar bai ga ta dawo ba, ya miqe ya bi ta cikin gida su qarasa
maganar. Yana shiga falonta ya tarar da ‘yar guntuwar takarda ajiye a kan kujera.
Ga abin da ya gani a rubuce.

YAYA MUS’AB
Na dai lura babu abin da kake so irin ka ganni cikin tashin hankali da damuwa, ka ganni cikin

matsanancin hali. To na gaji ba kuma zan sake yarda ka sake jefani cikin wata fitinar ba, don
haka na tafi, daga yau na bar maka gidanka, zan koma gaban masu tausayina”.
Sai wata rana.
Mai qaunarka Aisha.

Mus’ab ya zubawa wasiqar ido cikin kixima, ya rasa me ya faru? Me ya yi da zafi haka har da
za a xauki irin wannan matakin? Tsawon lokaci yana tunani ya kasa ganowa.
To ko dai ta gaji da zama dani ne babu haihuwa? Tunda ta san matsalar tawa ce. Ya xauko
wayarshi ya danna lambobinta, ta xauka ya jita tana kuka, jikinshi ya yi sanyi maimakon vacin
rai zalla.
“Aisha me ya faru? Ki dawo mu yi magana”.
“Ka qyale ni kawai, ka barni kawai in huta na gaji, na gaji da ganin fitina gara in yi nesa da
ita”.
“Kina ina ne yanzu?”
Ta ce, “Ina kan hanyar tafiya gida, zn tafi Misau zan koma gaban iyayenmu”.
Ba ta jira wata magana daga gareshi ba ta yi maza ta kashe wayar tata. Ya zubawa wayar ido
yana kallonta tare da nanata faxin Misau. Cikin kixima.
Saddiqa tana zaune gaban Gwaggonta cikin gajiya da vacin rai, tunda ta isa take zaune
gabanta tana kuka, hankalin Gwaggo ya kai matuqa wajen tashi saboda kukan da take yi da
kuma halin da ta ga Saddiqan a ciki.
Abu ta iso saboda aiken da Gwaggo Habiban ta yi mata, ganin Saddiqa ya sata mummunar
faxuwar gaba, ta nemi wuri ta zauna cikin sanyin jiki tana tambayar ta.
“Lafiya? Me ya faru? Me ya kawo ki gida ke kaxai? In ma rikici kuka yi ai bai kamata ki biyo
doguwar hanyar nan ke kaxai ba, in kika yi haquri zai wuce kina xakinki. In abin ya yi tsanani da
za ta faxa ma sai a tashi babba ya je”
“Inna ai tunda aka kai mishi ita ba ta tava shiga wannan yanayin ba, in dai kuma ba
matsalarsu bane”.
Gwaggo Habiba tana faxin hakan ta kama kuka, duk da a gaban Abu take ta kasa haquri yau
kam ta voye damuwarta kan lalurar rashin haihuwar Mus’ab, xa guda xaya namiji da take da
shi. A baya ba ta tava tsammanin hankalinta zai koma gare shi har damuwarshi ta zama tata ba
irin yanda ta zama a yanzu, ta rasa dalili, xinbin jikokin dake gareta sun kasa sanyaya zuciyarta
ta yi sanyi kan rasa xa a gidanshi da aka yi.
“Me ya faru Saddiqa? Yi magana mana, ki gayawa uwarki damuwarki kinga kin sata tana
kuka. Yi mata bayani dan ta samu sauqin damuwarta”.
Cikin zuciyarta ita ma ta yi tunanin yarinyar nan wataqila ta gaji ne da lalurar Mus’abu tunda
ta riga ta san matsalar tashi ne. tausayin Mus’ab ya yi matuqar kama ta.
Cikin kukan ta ce, “Na gaji, fitinarshi ta isheni, don haka na bar mishi gidanshi yaje ya yi ta yin
abin da ya ga dama”.
Ta miqe taje ta hau gadon Gwaggonta ta yi kwanciyarta saboda kasancewar hutun sallah
take yi.
Gari ya waye sanda ta tashi ta je ta yi wanka da ruwan xumin da Gwaggonta ta kai mata, ta
fito ta zauna tana shafa.
Gwaggo ta kalleta cikin nutsuwa da kulawa ta ce mata, “Kin rame Saddiqa, tunda kika je

gidan mijinki ban tava ganin ki na kasa jin daxin ganin naki ba irin wannan karon, ku rinqa yiwa
rayuwa haquri, duk abin da kuka gani zai wuce wata rana har ayi ta bayar da labari”.
Ta ce mata, “To Gwaggo”.
Ta miqe ta xauko doguwar riga ta sanya ta rufe kanta da gyale, ba ta tsaya yin kwalliya ba
tasa kai za ta fita.
“To ina za ki ba ki karya ba?”
Ta ce, “Da na je na gai da Baba ya ce in na kintsa in je yana son magana dani, kuma na ga
shigar Abu ma wurin shi kar in tsare su”.
Ta ce mata, “To”.
An haxu a xakin Malam Abdullahi shi da Abu da Saddiqa, ta sake gai da shi cikin ladabi da
nuna girmamawa.
A hankali cikin nutsuwa ya tambaye ta.
“Me ya faru kika baro mijinki kika dawo gida ke kaxai Saddiqa?”
Cikin nutsuwa ta ce mishi, “Baba na gaji da zama da shi ne kawai”.
Gaban Malam Abdullahi ya yanke ya faxi, cikin zuciyarshi ya tabbatarwa kanshi rashin
haihuwar Mus’ab ne ya isheta, tausayin Mus’ab xin ya kama shi.
Sai dai kuma nan take sai ya ji zuciyarshi tana raya mishi zai tsaya ya ga an yiwa Saddiqa
adalci tunda dai ai ta yi haquri, bana shekaru bakwai ne da auren nasu, amma ba ta tava buxa
baki ta yi wata magana ba.
“Assalamu alaikum”.
Suka jiyo muryar Kawu Gixe yana sallama daga bakin zaure. Da sauri Gwaggo Habiba ta fito
daga wurinta don taran xan’uwan nata, sai dai ganin Mus’ab biye da shi ya sata kaucewa ta
koma zuciyarta ta yi mata qunci ganin yanda Mus’ab shima ya rame har ma gara ta Saddiqan
da tashi. “Kin tarasu ne a nan kina yi musu qarya suna sauraron ki? Za ki fita ki ba mutane wuri ne ko
kuwa?”
Da sauri Malam Abdullahi ya ce mishi, “A’a, ba fa irin wannan hukuncin a a zartar a
tsakaninsu ba, don tunda ta kawo maganar gabanmu, to gaskiya da gaskiya ne kawai zai yi
maganin al’amarin”.
Abu ta yi maza ta ce, “Gaskiya kenan, ke Saddiqa dawo ki zauna ki faxi abin da ya dameki
babu zare ido cikin lamarin balle a je ana tsorata wani”.
Ta koma ta sake zama can gefe a rakuve. Malam Abdullahi ya zuba ido yana kallon ta.
“Kin ce kin gaji da zama da shi me kike so ayi miki?”
Cikin nutsuwa ta ce, “So nake a rabamu”.
Gaban Mus’ab ya yi mummunan faxuwa, kanshi a sunkuye ya yi maza ya qara sunkuyarwa.
“A raba ku a kashe auren kike so?”
Ya yi mata tambayar idonshi yana kallon ta.
Ta ce, “A’a, Baba zama da shi wuri xaya ne kawai ba zan iya ba”.
Gaba xayaa kowa a xakin ya samu sauqi, tun ma ba Mus’ab da Abu ba.
“A barni in zauna a gida shi kuma yaje can ya yi zaman shi”.
“Ya yi miki wani mummunan abin kenan?”
Abu ce ta yi tambayar hankalinta a kwance saboda ta gane rikici tsakaninsu ne ya dawo da
Saddiqa gida ba rabuwar aure take so ba.

Ta ce, “Bai min komai ba na gaji da zama da shi ne kawai, saboda na gaji da halinshi na son
kai, bai san kowa ba sai kanshi, abin da ya ga dama yake yi, in ya tashi yi kuma baya tausayin
kowa, ba……..”
Kawu Gixe ya ce, “A’a, ya fa isa haka, ya isa, don sun xaure miki gindin ki yi magana ba yana
nufin za ki zaunar damu

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login
google.com, pub-9213700357025247, DIRECT, f08c47fec0942fa0