Showing 15001 words to 18000 words out of 34483 words
Chapter 6 - Abu Naka Book 3 Complete Hafsat C Sodangi
ya san babu wani labari da zai fi wannan daxin bayarwa a wurin Abu.
Ya xan yi shiru kaxan cikin wani tunanin, zuciyar tashi ce dai take sake tuna mishi da irin
wunin da ya yi tare da Saddiqa bayan tafiyar Abu a ranar cikin kuka da takura mai yawa, wanda
ya yi dalilin da ko aiki bai samu damar zuwa ba.
Son shi ne ba ta yi yasa take waxannan abubuwan ko kuwa? Ya yi maza ya kawar da
wannan tunanin saboda dalilai guda biyu. Na farko mu’amalarshi da ita a farko, yanda ta
bijirewa auren Sadisu ta nemi a barta kawai ta yi mata yanda ita da kanta ta gayawa
Gwaggonta ita xin shi take so, da yanda ita da kanta ba tare da ya nemi ta yi mishi hakan ba ta
voyewa Abu halin da suke ciki a lokacin da ta zo gidan.
Waxannan dalilai guda biyu sune suka qarfafa zuciyarshi ya xan ji sanyi, ya kuma qarfafa
zuciyar tashi a kan himmatuwa wajen ganin ya shawo kan lamarin nashi.
Hadari ya taso tare da iska mai tsanani, wanda ya yi dalilin da liman ya bayar da umarnin
haxa jam’in magariba da isha’i a masallacin.
Ya shigo gida daidai ruwan saman yana saukowa, zuciyarshi ta yi mishi daxi saboda sanin da
ya yi Saddiqa matsoraciya ce. Wurinta ya fara isa bayan ya gama rurrufe qofofin gidan.
“Kin yi sallah kuwa?”
Ta amsa mishi da eh. Ya wuce ta yana tunanin irin takurar da ya ga ta yi, ina ma dai NEPA su
xauke wutar lantarkin. Yana yin wannan tunanin ya miqa hannu kan mitar gidan ya kashe wutar,
duu ya bayyana a ko’ina. Ya wuce ya nufi wurinshi.
Bai daxe da shiga wurin nashi ba ya ji motsin Saddiqa a cikin falon nashi.
“Waye aa nan?”
Ya yi tambayar don ya gane maganar ne ba ta son yi. A hankali ta ce mishi, “Nice”.
“Kina son wani abu ne?”
Ta xan yi shiru kafin ta daure ta ce mishi, “Wuta aka xauke ni kuma bana son duhu “.
Cikin nutsuwa ya ce mata, “Eh, Aisha duhu ai ba shi da daxi”.
“Ko za ka sa a kunna Jean?”
Ya ce, “To, sai dai ruwan ya yi yawa bai kamata in fitar da shi a cikin ruwan ba, saboda kuna
Jean ai kinga babba ne mu xan bari mu gani ko ruwan zai yi sauqi”.
Ta yi shiru.
“Ko kina tsoro ne?”
Ta ce mishi, “Eh”.
Ya yi kamar ya ce ta shigo wurinshi sai ya fasa, ya fito ya zo inda take ya kama hannunta ya
ce, “Muje in rakaki wurinki”.
Da hikima da lallami ta yarda suka hau gadonta tare suka kwanta, shima kuma ya yi haquri
ya kawar da kai daga gareta, don ya fi son shiryawarsu maimakon kara tsoratata. Sai da aka
kira sallar asuba ya miqe zai yi alwala ya mai da wutar gidan.
Har wajen qarfe taran safiya ba ta sake ganin ya shigo wurinta ba, ba ta ga yana shirin tafiya
aiki ba. Kalmomin Abu suka faxo mata, kullum ki gaishe shi, kullum ki yi mishi abinci mai daxi,
kullum ki gyara mishi shimfixa.
Don haka ta miqe ta nufi wurin nashi da nufin zuwa ta gaishe shi. A hankali ta tura qofar
xakinshi tare da yin sallama, saboda ganin ba ta ganshi a falon ba.
Ya amsa yana daga kwance a gadonshi, ta kai gwiwowinta qasa a yanayin girmamawa ta ce
mishi, “Ina kwana Yaya?” Ya amsa “Lafiya lau Aisha, ya ya gidan ya kwana?”
Ta ce mishi, “Lafiya, me kake so ayi maka na abin karyawa?”
A hankali ya ce mata, “Huta kawai Aisha”.
Ta xan kalle shi ta ce, “Ba ka da lafiya ne?”
Ya zuba mata ido yana kallon ta tare da tambayar ta, “Me kika gani?”
Cikin nutsuwa ta ce, “Na ganka a kwance bayan yau xin akwai aiki, kuma na ce me kake so
in yi maka ka ce in huta”.
Bai kawar da kanshi daga gare ta ba ya ce mata, “Bana cikin yanayin da zan ji daxin zuwa
aikin yau, saboda na xan takura, in kuma abin da nake so za ki yi min ki zo kusa dani mana ki
rage min damuwa ta”.
Ta xan yi shiru kanta a sunkuye, a hankali sai ya ce mata, “Sai na ji kamar Abu ta yi ta yi miki
magana a kan kar ki yi wasa da auren ki, na xauka ni da ke zamu yiwa nasihohin da ta yi mana
biyayya Aisha”.
Ba ta kalle shi ba balle ta yi mishi wata magana, sai dai hawayenta da suka soma zuba. Ya
shure abin rufar nashi ya zo ya kama hannunta ya shigar da ita xakin.
“Zo muje ki gaya min abin da ke saki yawan kuka. Nisa da gida da kika yi? Kina son ganin
Gwaggonki ko?”
Ta yi maza ta gyaxa kai nuna alamar, “Eh”.
Yasa hannu ya share mata hawayen.
“Ai na sani, na san kina ganin Gwaggonki nima kuma ba zan hanaki ko in qi kai ki wurinta ki
ganta ba, illa iyaka dai kawai zan bari sai kin kwantar da hankalinki mun zauna lafiya tukunna,
ko yau xin nan kika yarda muka fara zama lafiya, to ni kuma a shirye nake mu daidaita lokacin
da zan kai ki ga Gwaggon naki”. Da irin waxannan kalaman na dabara ne da yawan nuna na fiki daxewa a duniya Mus’ab ya
samu ya shawo kanta cikin ruwan sanyi, ta yarda ta miqa mishi al’amarinta ya samu ya yi yanda
yake so da ita, ta kuma jurewa hakan.
Wunin ran nan ko qofar gidanshi bai buxe ba sai da ya yi nufin tafiya sallar juma’a, ana
idarwa kuma ya dawo gida. Haka washe gari asabar da kuma lahadi yana gida yana
hutawarshi.
“To Yaya yaushe zamu je wajen Gwaggo?”
Sai ya yi maza ya soma lissafi.
“To bari ko kwana talatin da tafiya Abu ta yi don kar a ganmu yanzu ayi zaton ko babu lafiya”.
Ta ce mishi, “To”.
Kwanaki talatin xin suna cika ya xauke ta ya nufi qasar Italy in da ya je ya yi hutun aikinshi na
kusan watanni biyu, tafiyarshi ta farko tun bayan dawowarshi daga can inda yaje ya sadu da
aminai, abokai da kuma tsofaffin malamanshi da aminanshi.
A lokacin da suka dawo gida kuwa tunanin Saddiqa da tattalinta bai wuce na me za ta yi ko
ya ya za ta yi ta kyautatawa mijinta ba.
Watanni biyar sun cika bayan kawo Saddiqa da Abu ta yi har lokacin bai ce ga ranar zuwa
gida ba, tamkar ya mance alqawarin da ya yiwa Abu na ba zai bari ta rinqa jin marmarinshi ba
ta ganshi ba.
Ita ma Saddiqa mafi yawancin lokaci ta kan tuna Gwaggon nata ne, ta ce kai Yaya yaushe ne
za ka samu lokacin da zamu je gida ne? Ina fa marmarin ganin Gwaggona”.
Ya yi tsaki ya ce, “Ai ayyuka ne bari dai mu gani daga nan zuwa qarshen watan nan. In ta ce
to. To sai kuma wani jiqon in ta sake tunawa. Daga shi har ita sun zama tamkar basu ba, ko
Liman da Mus’ab xin ya tasata a gaba ya kaita gaishe shi mamakin ganinta ya yi, ya cewa,
Mus’ab xin yi qoqari ka kai wa iyayenku ita su ganta don su sanya maka albarka. Ya ce, “To
malam”.
Suna zaune a falonshi suna hira, sun gama karyawa Mus’ab ya kalle ta ya ce, “Ki gama
aikinki da wuri ki shirya in anyi sallar magariba zamu je mu ga Dr. Usman”.
To kawai ta ce saboda ya yi maganar ya fi a qirga, yau xin dai ya zartar da hukuncin tafiyar
ne kawai.
Da daddare Mus’ab da Saddiqa suna zaune gaban likita, Mus’ab ya gama yi mishi bayanin
abin da ke tafe dasu. Gwaje-gwaje sosai ya yi musu, ya kuma umarcesu dasu kawo mishi wasu
abubuwa na jikinsu.
Bayan sunyi hakan ne ya xibar musu kwanaki uku ya ce su dawo don su ji sakamakon gwajin
nasu.
Sun dawo suna zaune gaban likitan wanda yake kallon takardun dake gabanshi cikin nazari
kafin ya xan xago ya kalli Saddiqa ya ce mata, “Ko za ki xan jiramu a waje?”
Mus’ab ya harzuqa da jin maganar tashi ya ce, “Matata ce fa, me za ka gaya min da ba za a
faxa a gabanta ba?”
Saddiqa ta miqe tsaye ta ce, “Babu komai Yay bari in je in jiraka a mota, in ka gama kawai sai
ka sameni a can mu tafi”.
Ya bita da kallo har sai da ta fita ta ja musu qofar kafin ya dawo da kallon shi wurin likita.
“Me kake so ka gaya min likita wanda yasa ka korar min mata?”
Likita ya ya kalle shi cikin nutsuwa ya ce, “Ba korarta na yi ba, bana yi maka sha’awar tashin
hankali ne da ita, na san a yanda ka renita ta zama haka ba za ka so komai tsakaninka da ita
ba illa zaman lafiya da kwanciyar hankali”.
Gaban Mus’ab ya yi mummunan faxuwa, cikin sanyin jiki ya tambaye shi “Me ya faru likita?”
Ya tsare shi da ido yana kallon shi tare da sauraron abin da zai gaya mishi.
“Barasa da sigari sun riga sun yiwa kayan cikinka lahani, haka nan ka daxe kana xauke da
ciwon sanyi da ake samu wurin matan da basu tsaya wuri xaya ba, saboda baka kula ka xauki
matakin da ya dace a kanta ba har ta yi maka illa, ka kuma san ita wannan cutar tana cikin
cututtukan dake hana maza haihuwa, don tana toshe jijiyar dake fitar da qwai zuwa mahaifar
mace.
To ga kuma wancan matsalar da na ce maka barasa da sigari sunyi maka, ban da wannan ita
ma matarka mun same ta da ciwon, sai dai bai riga ya yi mata qarfi sosai ba, na kuma san zai
yiwu a wurin ka ta samu”.
Mus’ab ya ji tamkar a sama yake saboda tashin hankali, gaba xaya kunnuwanshi suka daina
jin komai in ban da kalaman da likita ya furta mishi sune kawai suke ta nanata kansu.
“Ka yi haquri Mus’ab kar ka xauki abin da tsanani sosai, akwai magungunan da zamu baka in
ba suyi ba mu canza wasu, kai dai kar ka bari matarka ta san abin da kake ciki ba wani tabbas
ne dasu ba. Kar ka kalli wannan xawainiyar da ka yi a kanta ka mai da ita matar zamani ta bijire
maka ba komai bane, musamman ma da yake abin ya shafi haihuwa. Don haka in ta matsa tana so ta san abin da ake ciki ni zan iya ba da result xin da zai nuna
matsalar a wurinta yake, don dai ka samu zaman lafiya a gidanka. A nan asibiti kuma ba za ta
samu mai gaya mata komai ba”.
Mus’ab ya miqe tsaye tare da faxin “Na gode likita”. Ya fita ba tare da ya saurari rakiyar da
likitan yake yi mishi ba.
Saddiqa tana zaune a qasa gaban Mus’ab, kuka take yi. Ya buxe ido a hankali cikin nutsuwa
ya ce mata, “Yanzu nan baki yarda da abin da na gaya miki ba cewar ni lafiyata qalau bani da
wata damuwa ba”.
“Ya ya zan yi in yarda bayan ba haka na saba ganinka ba, ni idan na yi maka laifi ne baka
son gaya min to ka yafe min”.
Ya miqe zaune a kan kujerar ya ce,”Haba Aisha, ni kuwa a rayuwata me za ki yi min ya vata
min rai?”
“To mene ne? Tun daga ranar da muka je asibiti gaba xaya ka canza ka sauya, ka zama wani
irin, in bani na yi maka laifi ba waye?”
“To bari mu yi sallah kin ji ana kira, jeki ki yi alwala ki yi taki sallar kafin in dawo daga
masallaci”.
Bai jira amsarta ba ya miqe ya fita, bai dawo gidan ba ko da aka yi sallar ya yi zamanshi a
waje yana hira tare da jama’ar unguwa.
Saddiqa tana kwance a xakinta saboda ta dena zuwa xakin Mus’ab, shi da kanshi ne kuma
ya nuna mata bai son zuwan nata, don haka ta yi qoqari ta kame kanta.
Me ya samu Yaya Mus’ab? Ta yiwa kanta tambayar. Tsawon lokaci tana tunani wani abu ne
ya same shi bai son gaya mata, ko kuwa dai haka kawai yake fito mata da waxannan halayen
da ba ta tava sanin yana dasu ba.
Ta yankewa kanta shawarar zuwa ta same shi ko barci yake yi ta tashe shi in yaso su yita ta
qare, ta gaji da kauce-kaucen da yake yi mata.
Ta jawo zaninta ta xaura kan rigar baccin dake jikinta ta nufi xakin nashi, tun daga falonshi ta
soma shaqo warin sigari, gabanta ya faxi, kar dai Yaya Mus’ab ke shan sigari a wannan tsohon
daren?
Ta kutsa ta shiga cikin xakin nashi ba tare da ta yi mishi sallama ba, yana zaune a bakin
gadonshi da karan sigarinshi a hannu, gefe guda kuma kwalbar barasarshi ce ‘whisky’.
Saddiqa ta zube gabanshi cikin kuka mai tsanani, nan take ya sureta da sauri ya yi waje da
ita ya nufi falonta ya shimfixeta a kan doguwar kujerarta.
“Ba na ce ki dena zuwa wurina ba ki gaya min ba?”
Ta ba tanka mishi ba kukanta kawai take yi, ba ta dena ba har ya bar wurin ta ya koma nashi,
saboda zai yi shirin sallar asuba.
Kafin ya dawo har ta gama yin shirinta, yana shigowa ya kalle ta cikin nutsuwa ya tambaye
ta, “Wannan jakar fa?”
Ba ta kalle shi ba ta ce mishi “Gida zan tafi”.
“Gida ina?”
Ya yi tambayar cikin wani irin yanayi.
Ta ce, “Misau”.
“Na yi miki wani abu ne?”
Ta ce, “A’a”.
“Ban miki komai ba amma kike so ki tafi ki barni, don kin ganni a cikin damuwa kina so ki qara
min ita?”
Ba ta kalle shi ba ta ce, “Ai ban santa ba balle ka ce ita ce za ta koreni”.
“Ko baki santa ba ai kin san ina da ita”.
Ta yi maza ta ce, “Kai kaxai ta shafa bana kuma so in jita”.
Ta miqa hannu ta soma jan jakarta za ta fita ya yi maza ya kamo ta ya riqe.
“Kar ki tafi ki barni Aisha, in kin barni da wa kike so in zauna?”
Ta ce, “Da halayenka”.
Ya qi sakinta.
“Me na yi miki Aisha kike nema ki qara min damuwa bayan wacce nake ciki, ban son ganinki
cikin tashin hankali ne yasa ban gaya miki ita ba, Aisha ba wai ina voye miki ita bane, ki yi
haquri ban gaya miki ita bane saboda ni na jawo komai sai nake ganin ya kamata ne ni kaxai in
yi ta damuwar ba in watsa ta zama damuwar kowa da kowa ba. Duk da hakan kuma ban samu kwanciyar hankali ba saboda na riga na cuci kaina na kuma
cuce ki ta hanyar sanya miki cutar da baki san hawa ba baki san sauka ba, ko Innata bana jin
za ta yafe min abin da na yi mata, tunda dai ke ce ‘yarta guda xaya da ta bari a duniya”.
“Kai Yaya Mus’ab wacce irin magana kake yi haka?”
“Na cuci rayuwata Aisha, na cuci rayuwata, na cuci rayuwata”.
Saddiqa ta soma kuka sosai saboda kalaman nashi. A hankali cikin nutsuwa ta gama
sauraron bayanin da yake yi mata.
“Shine dalilin da yasa ka koma shaye-shayenka ka sha barasa ka sha sigari? Wato duuk ma
abin da zai faru ya faru? Wacce irin rayuwa ce wannan? Yanzu ko abinci me daxi ne aka ce ya
cutar da lafiyarka ba za ka fita hanyarshi ba balle savo?
Ka yi savo an jarrabeka sai kuma ka ce to tuban da ka yi ma ka fasa? Wataqila har neman
matan ma ka koma”.
Ya yi maza