Showing 30001 words to 33000 words out of 34483 words
Chapter 11 - Abu Naka Book 3 Complete Hafsat C Sodangi
ki zage shi a gabanmu bane, ki faxi abin da ya kawo ki in ji tun ranki bai
vaci ba”.
Kanta a sunkuye ta ce, “Aikinshi zai sake”.
Kawu Gixe ya qara tunzura, ya ce, “To in zai sake aikinshi ina ruwanki, da can ke kika samar
mishi wannan xin da yake yi?”
Abu ta kalleta a hankali ta tambaye ta cewa, “Wani garin zai koma bakya so?”
Ta gane dai ba a gane maganar ba, don haka ta gyara da cewa, “Ba aiki ba, tiyata”.
Gaba xaya aka xauki salati.
“Tiyata?”
Abu ta yi tambayar da qarfi. Ta kama baki ta riqe tana kallonshi cikin mamaki.
Saddiqa ta ci gaba da bayani kanta a sunkuye.
“Aikinshi na farko tilastani ya yi na yarda ya kuma hanani faxa muku, da aka ce ciwo ya dawo
ya ce zai koma na ce a’a, a haqura har muka yi rikici da shi, na ce to kar ya sake yi min
maganar. Ban ankara ba sai kawai na jishi a asibiti wai ana aikin, yanzu kuma sun sake cewa
wai ya fara dawowa ya zo yana gaya min zai sake komawa, duk da na ce a’a, na san ba zai
fasa ba. Shi yasa na yi hanzarin dawowa gabanku don ban san ranar da zai tafi ba”.
“Kina da gaskiya, Mus’abu ya ci a guje shi”.
Tana maganar tana kuka.
“Wata tiyatar za ka sake komawa bayan duk hatsarin da aka tsallake? Ana yiwa Ubangiji qarfi
ne?”
Kawu Gixe ne ya jero mishi tambayoyin yana mai tsare shi da idanuwa.
Kan Mus’ab a sunkuye ya shiga bayani cikin ladabi don ya samu goyon baya. Abu ta katse
shi ta hanyar faxin.
“Kai tafi can, Saddiqa ba za ta sake binka ba ka je can ayi ta yi maka tiyata ana maimaitawa
kai kaxai, za ta zauna kusa da iyayenku ta samu nutsuwa, ta gaji da ganin fitina, ta gaji da
fitinarka. Kai fitinannen mutum ne, a ce mutum bai san haquri ba”.
Ta soma kuka, kuka kuwa mai tsanani da ya yi dalilin da ta fita ta bar gidan ta tafi nata.
Tsawon lokaci xakin shiru babu wanda ya sake cewa wani abu. Kawu Gixe ya kawar da
shirun ta hanyar yin magana a hankali, kuma cikin nutsuwa.
“Ina fata wannan maganar da ta yi na kana shirin komawa wani tiyatar ya zama qarya ta yi
maka ba gaskiya ta faxa ba”.
Shiru ya yi bai iya cewa komai ba, duk da ya san Kawu Gixen shi yake sauraro. Gajiya da
shirun Kawun ya yi ya ci gaba da maganar da ya katse.
“Kar in sake jin ka tayar da maganar tiyata a gidanka balle har aje ga sake yanka maka wani
wuri a jikinka, ya isa haka. Abu guda xaya da zai hanani haramta maka komawa asibiti shine,
neman magani halal ne, amma ban yarda ya kai ga yanka jiki ba. Muma a nan zamu yi iya
namu in mun ji mai magani na halal zamu karvar muku, muna yi muku addu’a zamu qara, in
mun sadu da mutanen da alherinsu ya bayyana zamu roqesu su taimaka mana da addu’a.
Mai bayarwar Ubangiji ne, shi kuma in ya yi nufin samun, to kun ne kawai fayakunu. Shi
kenan sai ka ga an samu. Ku dai ku dimanci istigifari, ku kuma haxa da haquri. Ke Saddiqa ki je
wurin uwarki ki yi mata sallama ku je wajen Inna ku yi mata sallama ku ba ta haquri, don ta tafi
hankalinta a tashe”.
Ta ce mishi, “To Baba”.
Ta tashi ta fita ta barshi yana ci gaba da yiwa Mus’ab nasiha kan muhimmancin haquri da
miqa wuya ga Ubangiji.
Ya ce, “To Kawu”.
Mus’ab ya shigo falon Gwaggonshi cikin ladabi, ya koma kan shimfixa can gefe ya zauna
cikin nutsuwa, qafafuwanshi a harxe ya shiga ba ta haquri.
“Ku yi haquri Inna ba zan sake ba, dama ni wai burina in dai ga Aisha ta haifar muku xa ne ko
da guda xaya ne da zai rinqa zuwa yana yi muku zarya a tsakar xakin nan ne kuna ganin shi, to
ga shi ta zo ta haxani daku har Kawu Gixe da su Abu duk sun mara mata baya a kan wai basu
yarda in sake zuwa tiyatar ba. Shi kenan ni kuma ba zan haifar muku kowa ba kenan?” Ya sunkuyar da kanshi qasa, hawayen da suka taru a gefen idonshi suka xiga.
Gwaggo Habiba ta yi kamar ba ta gani ba saboda kawar da kanta da ta yi, cikin nutsuwa sai
ta ce mishi, “Tashin hankalin dake cikin tiyatar ya yi yawa, ka bar gidanka ya zauna lafiya tunda
ita matarka ba tayar maka da hankali take yi ba, kai ma sai ka yi haquri. Ai ana addu’a ba kuma
za a daina ba, al’amarin kuma duk na Ubangiji ne”. Ya ce, “To Inna”.
Cikin zuciyarshi daxi ya kama shi, godiya yake ta yiwa Ubangiji da ya nuna mishi daidaituwar
al’amuranshi da iyayenshi, musamman ma mahaifiyarshi.
“Ke Saddiqa tashi mana baki ji mijinki ya shigo bane?”
Ta ce, “Qyale shi kawai Gwaggo, ya riga ya vata min rai ba wani binshi zan yi ba”.
Ta ce, “A’a, a’a, bana son rashin haquri, ina ce an riga anyi mishi faxa ya kuma ce ba zai sake
ba?”
Mus’ab ya xan gyara a hankali ya ce, “Nima fa tana vata min rai Inna ina dai yin shiru ne
kawai, saboda ni xin babba ne kar a ce bani da haquri”.
“Me take maka?”
Gwaggo Habiba ta buqaci sani.
“Tana takura min ne Inna”.
Saddiqa ta yi maza ta tashi ta zauna tana kallon shi, ya qi kallon ta balle ya ga kallon da take
yi mishin.
A hankali cikin nutsuwa ya ci gaba da yiwa Innarshi bayani.
“Magana da baki ne kawai ba ta yi Inna, amma kullum aiyukanta na nuna matsuwarta ne kan
son haihuwa, kullum a cikin sayayyar kayan jarirai take, babu halin mu fita mu dawo ba ta sani
na sayi kayan jarirai ba wai sun ba ta sha’awa. Sannan ina yi mana qoqarin jariran mu samu ko
da guda xaya ne ta zo ta kawo qarata an hanani. To ku gaya mata Inna ta fita hanyata da irin
wannan sayayyar, kar kuma in sake dawowa gida in samu tana karkaxe kayan, in na yi magana
ta ce wai qura suka yi”.
Daga shi har Saddiqan tausayinsu ne ya qara mamaye zuciyar Gwaggo Habiba, sai dai ba ta
bari sun gane ba.
Ta ce, “Ke Saddiqa in kun je gida ki yi kyauta da kayan jariran nan da kika tara mishi a gida,
ina dalilin su? Kayan sha’awa yana qarewa ne? In haihuwar ta zo kece mai sayen riga? To bana
so”.
A hankali ta ce mata, “To Gwaggo”.
Ta sake kallon Mus’ab ta ce, “Ku dage a kan yin addu’a, in ka ga har ka samu dagewa kan
roqon Ubangiji kan wata buqata taka, to qila ya yi nufin biya maka buqata ne, don haka kar ku
gaji da addu’a, in za ku kwanta kuma ku rinqa karanta (Suratul Maryam) bayan addu’o’inku na
kwanciya sau uku in har da rabon to zamu sadu da biyan buqata”. Ya ce mata, “To Inna”.
Suka yi mata sallama suka nufi gidan Abu, daga can suka nufi gidansu inda za su kwana
washe gari suyi sammakon tafiya Ajakuta.
SHEKARU GOMA DA AUREN SU MUS’AB
Mus’ab yana zaune a falonshi yana rubuce-rubuce, ya isa ya yi qiba ya yi jajur saboda
wadataccen kwanciyar hankalin da ya samu shi da matarshi, a yanzu sun daina zancen
haihuwa da damuwa kan al’amarinta, iyaka dai kullum a cikin addu’a suke, suna kuma ta shan
magani na asibitin da na Hausa, saboda kullum iyayensu a cikin aiken magungunan suke. Tun
ma ba Gwaggo Habiba ba, in da duk aka ce mata ga mai magani za ta je ta karvo ta kuma aike
musu.
Saddiqa ta shigo falon cikin kwalliya da qamshi mai daxi, kana ganinta za ka tabbatar eh, ta
dace da zama matar Mus’ab.
Can gefe ta je ta zauna tana cin kilishinta, a hankali ya xago ido, ya ce, “Haba Aisha wannan
wane irin rowa n? Kin yi min rowar qamshimki to kilishin ma ba za ki yi min ta yi ba?”
Ta yi murmushi ta ce, “Kilishi kai ka ce bai maka daxi ba”.
Ya ce, “To na ji ke fa?”
Ta taso daga inda take ta zo gare shi, ya ware hannayenshi duka biyu ta shiga cikinsu ya
mayar ya rufe, tsawon lokaci suna wasanninsu kafin ya gaji ya miqe tsaye xauke da ita a
hannunshi ya nufi xakin kwanciyarshi, tare da faxin muje daga ciki zan fi ganin fasalin kwalliyar
taki. Gabanta ya faxi, sai dai kuma ta yi maza ta shanye. Yana daga kwance yana kallon ta bayan ya kammala abin da zai yi.
“Kina da matsala amma kin qi ki yarda a tsakanin duk lokacin da na kusanceki sai na gane
dauriya kawai kike yi kina haquri dani, amma na tambaye ki kin ce ba haka bane”.
Ta yi murmushi ta ce, “Me ka gani?”
Ya harare ta bai tanka ba.
Ta sake wani murmushin ta ce, “Ni bani da matsala”.
“To ai shi kenan tunda abin da kika ga ya fi miki kenan. To maganar tafiyar fa?”
Cikin nutsuwa ta ce mishi, “A’a, Yaya ba bana son binka bane, amma ina so Gwaggona ta zo
ta yi min baqunta, shekaru goma ne fa tunda ta aurar dani amma ba ta tava sanin xakina ba, in
ma kunya ne ya hanata zuwa xakina, to yanzu kam ai na girma na isa a zo min baqunta”.
Ya jawota jikinshi ya qanqame, ya ce, “To in surukinta take kunya fa?”
Ta ce, “Eh, ai shi yasa nake so in yi amfani da lokacin tafiyar taka sai ta zo mu sake a gidan,
tunda ta san baka nan”.
“In dai tafi kenan in barki”.
Ta ce, “Eh, ina maka fatan alheri”.
Kwana biyu bayan nan Gwaggo Habiba ta iso gidan don yiwa Saddiqa baqunta kamar yanda
ta nema a dalilin tafiyar Mus’ab xin zuwa qasar Bulgeria kan wani aiki da aka tura shi, inda zai
je ya yi watanni uku.
Saddiqa sai kaiwa da kawowa take yi tana tarairayar Gwaggonta wacce ta mayar tamkar
wata jaririya saboda tattali da kulawa, ta sake kewayeta da nau’o’in abin sha bayan ta kwashe
na cin. Ta dawo ta zauna kusa da ita suna hira.
“Iko sai Ubangiji, gaba xaya mijinki ya canza Saddiqa, xan kwana biyun da na yi tare daku a
gidan nan kafin ya tafi sai na ga gaba xaya ya zama kamar ba shi ba, na ce hala shi yasa kema
kika sauya. Rabon da ki yi kyau irin wannan tun farkon zuwanku gida”.
Saddiqa ta yi murmushin jin daxin yabon da aka yiwa mijinta, ta ce, “Don ma bani da lafiya
Gwaggo”.
Da sauri Gwaggo ta tambaye ta cewa, “Baki da lafiya me ya same ki?”
Ta xan yi shiru ta rasa ta inda za ta soma maganar.
Gwaggo ta kalleta ta ce, “Ni kuwa ai ba wacce za ki voyewa al’amarinki bane in dai ba kina
nema ki canza bane”.
Da sauri ta ce, “A’a, Gwaggo ba haka bane, wani abu ne ya same ni babu halin Yaya ya
tavani sai cikina ya qulle ya yi ta faman ciwo, in yi ta murqususu ina wahala, sai da qyar zan
samu ya sakeni bayan na yi gumi na yi kashirvan. Ko jiya da daddare Gwaggo ba rashin kunya
zan yi miki ba, na yi haquri da shi ne kawai don na san wayewar garin yau xin nan tafiya zai yi”. Jikin Gwaggo a sanyaye ta ce mata, “To amma ba ki gaya mishi ba?”
A hankali cikin nutsuwa ta ce mata, “Shima ya gane don ya gane ina fargabar ya tavani, na
dai qi yarda ne kawai sanda ya yi min maganar”.
“To me yasa kika qi yarda Saddiqa? Matsala irin wannan ai ba za ki yi shiru ba”.
Cikin nutsuwa ta ce mata, “Gani na yi mun samu nutsuwa bai cika ma yin maganar asibiti ba
in ba dubiya muka je ba, maganin da kuke aiko mishi kawai yake sha. In na ce mishi bani da
lafiya sai kuma ya ta da hankali ya ce shine yasa min ciwon.
Sannan kinga wani qullutun dake nan gefen marata Gwaggo ba ki ji ciwon da yake yi min ba,
duk abin da nake yi qarfin hali ne kawai, in na nuna mishi wannan ai ban san tashin hankalin da
zai yi ba”.
Gwaggo tasa hannu tana tava gefen marar tata, abin da ta jin ya yi mummunar faxar mata da
gaba.
“Gareka muke bauta ya Ubangiji, gareka kuma muke neman taimako”.
Kalmomin da take ta furtawa kenan. Cikin nutsuwa ta kalli Saddiqa ta ce, “Wannan ai ba abin
voyewa bane, kar ki sake yin haka, yanda duk kika kai da gudun tashin hankalinshi ai dole ya
san damuwarki, in kika voye mishi wa za ki gayawa? Shirya mu tafi asibiti yanzu”.
“To ko zamu bari sai gobe Gwaggo tunda yamma ta yi?”
Gwaggon ta kalleta, ta ce, “Ke shirya mu tafi za ki yi ta zama da ciwo ne? In ta kama mu
kwana a can ba sai mu kwana ba”.
Dr. Usman ya gama duba Saddiqa, ya kalleta cikin nutsuwa ya ce mata, “Sauka ki zauna a
can”. Ya nufi wajen zamanshi ya zauna Gwaggo tana binshi da kallo.
“Ciki ne!”
“Na’am”.
Kamar cikin firgita Gwaggon ta faxi hakan. Hankalinshi a kwance ya sake faxin, “Ciki ne ya
fita ne daga cikin mahaifa yana so ya kawo matsala, in ba wanke shi aka yi ya fita gaba xaya ba
za ta samu lafiya ba”.
Gwaggo ta soma kuka, “Wankewa ya fita likita bayan duk wannan wahala da aka yi?”
Ya ce, “Eh, to ina ganin kamar ya fi sauqi tunda an samu lafiya ai za a sake samun wani, in
kuma kin fi so a gyara mishi zama sai a gyara. Sai dai za ta yi ta wahala don za ta yi ta zama
cikin dokoki”.
Ta ce, “Eh, gara a gyara”.
Gwaggo tana zaune kan kujera tana jiran a fito da Saddiqa daga xakin da ake yi mata gyaran
cikinta, cikin zuciyarta kuwa kiran sunayen Ubangiji take yi tana qara yi mishi tasbihi.
Sun dawo gida Saddiqa tana kwance saboda umarnin likita na kar ta yi wani aiki ko kuma
motsi mai qarfi na tsawon sati biyu. Gwaggo ce take kai wa da kawowa a cikin gidan, sai ji da
Saddiqan take yi kamar ta lasheta don farin ciki.
Kusan kullum raba dare take yi tana roqon Ubangiji ya tabbatar da wannan ciki ya zaunar da
shi lafiya, ya tsare mai xauke da shi daga duk wata wahala. In kuma lokacin haihuwar ta zo
yasa a samu haihuwar cikin sauqi, abin da za a haifan kuma yasa ya zama mai albarka.
Sati uku Gwaggo Habiba ta yi maimakon biyu da ta zo da niyyar yi, tana komawa gida kuma
Abu ta taho da niyyar zama, ba za ta koma ba har sai Saddiqan ta haihu ta yi mata jego.
Ran nan da asuba misalin qarfe huxu da rabi na asuba Mus’ab ya bugo mata waya.
“Wash! Yaya daga bacci fa ka tasheni”.
“Ai gara in tasheki Aisha don ki qara sanin nima ba wani baccin nake yi ba, ba ki san irin
haushin da nake ji ba da na yarda na baroki a gida, na riga na saba a tattaleni sai in rinqa jin na
takura da yawa, ga shi kwanakin sun qi gudu balle in samu in yi in dawo in same ki”.
Ta yi murmushi ta ce, “Ka yi a hankali Yaya kar ka damu kanka da son sai ka yi sauri,
magana guda xaya