Showing 33001 words to 34483 words out of 34483 words

Chapter 12 - Abu Naka Book 3 Complete Hafsat C Sodangi

dai da zan yi maka ita ce, ka taho da goron albishir mai girma, don za ka
dawo ka samu abin da zai faranta maka rai irin farin cikin da baka tava yi ba a rayuwa”.
Ya yi dariya ya ce, “Kin mai da maganar wasa Aisha tunda kika faxi hakan, ni yanzu da wani
farin ciki da zan yi wanda ya kai na ranar da Kawu Gixe ya bani ke balle har ya fishi?”
Ta ce, “To ai shi kenn Yaya mu bar maganar kawai sai ka dawo”.
Ya ce, “To shi kenan sai na dawon”.
Cikin Saddiqa ya shiga wata na shida lokacin da aka soma shirye-shiryen dawowar Mus’ab.
Ran nan tun safe ya iso gidan a dalilin saukar asuba da ya yi, ga mamakinshi bai ga Saddiqa
wajen taren shi a airport ba, sun iso gida bai ganta a qofar gidan ba.
Ya shiga falo yana zaton ganinta, Abu ya gani. Cikin mamaki ya buxe baki ya ce, “Hajiya Abu
nake gani a gidan ko mafarki ne?”
Tana murmushi ta ce, “Ba mafarki kake yi ba nice”.
“Kar dai ki ce min kema zumuxin dawowar nawa ne ya saki yin wannan doguwar tafiyar don
ki tareni”.
Ta sake wani murmushin ta ce, “Zumuxin yi maka albishir da taryen abin alherin da ya
samemu ne ya kawoni Mus’abu, ni kam ai ba jiya ko yau na iso gidanka ba, watana biyu kenan.
Matar gidan ce kawai ba ta yarda a gaya maka ba”.
Kan Mus’ab ya xauke jin kalaman Abu, amma don ya sauwaqewa kanshi komai sai ya
tambaye ta.
“Ina Aishan take Abu?’
Ta nuna mishi xakinta, ta ce, “Ni na hanata tashi tarenka na ce ta jiraka nan inda take za ka

zo ka sameta saboda ta bi dokar da likita ya sanya mata”.
Gaban Mus’ab ya yi mummunan faxuwa, kar dai lalurar da ya bar Aisha tana vovvoye mishi
ce ta yi riqan da har likita yake doka a kai?
Da sauri ya faxa xakin nata, qamshi da ni’imar dake ciki bai hanashi kaxuwa da ganin da ya
yi mata a kwance ba.
“Me ya same ki Aisha?”
Ya yi tambayar a sanyaye. Ta saki lallausan murmushi tana daga kwancen ta ce, “Qaraso
mana Yaya, so nake in jika a jikina”.
Tana faxin hakan ta ware hannayenta nuna alamar shi take sauraro. Ya yi maza ya qarasa
gareta, nan take suka soma tumurmusar juna, sai dai basu je ko’ina ba ya ja ya tsaya yana
kallon ta cikin kixima.
“Mene ne wannan Aisha?”
Ya yi tambayar yana mai kallonta. Ta saki lallausan murmushi a hankali cikin yanayi na raxa
ta ce mishi, “Ciki ne, cikin da kake ta fatan ganinshi a gidanka ne yau kake ganinshi, shine
albishir xin da dama nake gaya maka na tanadar maka”.
Yasa hannu biyu ya qanqameta a jikinshi tamkar dai ba a cikin hayyacinshi yake qanqamar
ba saboda tsananinta.
“Haqiqa kin yi min albishir Aisha da abin da tuni na haqura da ganinshi a gidana, don haka
nima zan yi miki tukwuici da abin da ba ki tava tsammanin samun shi ba”.

SHEKARU GOMA BAYAN NAN
Mus’ab mai shekaru hamsin da huxu a duniya, yana zaune a hamshaqin gidanshi dake
unguwar G.R.A kan titin T/Valewa a cikin garin Bauchi.
Mus’ab ya ajiye aikinshi ya dawo gida shekaru biyu da suka wuce, ya kuma zavi zama kusa
da Kawu Gixe, don haka ya gina wani tafkeken gidan a Bauchi.
Ya yi hakan ne kuma don cika burin da yake da shi na ganin ya sadaukar da abin da ya saura
na rayuwar wajen ganin ya bayar da ingantacciyar tarbiya ga yaran da ya haifa, a ganin Mus’ab
tarbiya wata aba ce dake buqatar lokaci, haquri, juriya, tausayi, kulawa da kuma soyayya. Haka
nan aiki ne da ya hau kan iyaye duka biyu, wato uwa da uba. Yana zaune cikin hamshaqin falonshi da duk wani abin da ke ciki daga qasar Italy ya shigo da
shi, tare da ‘ya’yanshi guda uku, Maryam, Abdullahi da Muhammadu Gixaxo takwaran Kawu
Gixe.
Gaba xaya litattafansu suke nuna mishi lokacin da Saddiqa ta shigo cikin falon sanye da
doguwar riga xinkin senegal a jikinta, ta yi kyau sai sheqi take yi, ta nemi wuri ta zauna sannan
ta kalli yaran ta ce musu.
“Maza ku tashi ku tafi ga Malamin ku ya zo”.
‘Yan samarin biyu suka yi waje da gudu suna rige-rige, ya yin da ‘yar budurwar ta qara
lanqwashewa jikin mahaifinta tana tambayarshi.
“Baba ina ce nice mamanka?”
Ya yi maza ya amsa mata tare da zuba idanuwanshi a gareta, “Ke ce mamana Mama”.
Saddiqa ta sake kallon yarinyar wacce ta yi kamar ba ta jita ba, ta ce mata, “Kema tashi ki
bisu”.
Ta miqe tsaye ba don tana so ba sai don bin umarni, ta kama hanyar fita daga falon. Mus’ab

ya bita da kallo har sai da ta vace mishi daga gani.
Maryam ita ce yarinyar da Mus’ab ya xauki son duniya ya xora mata saboda dalilai masu
yawa, farko samunta da ya yi bayan ya xebe tsammani, na biyu takwarar Innarshi ce matar
Kawu Gixe wacce take mahaifiyar Saddiqa. Na uku tsananin kamanninta da mahaifiyarshi
Gwaggo Habiba, ko cikin ‘ya’yan da Gwaggon ta haifa ba a samu mai kama da ita haka ba. Sai
na huxu basirarta, yarinya ce mai kaifin basira, duk shagwavarta da sakarcinta sau xaya tak
malami yake faxar abu ta kama.
Ya dawo da kallon shi ga Saddiqa cikin nutsuwa ya ce mata, “Kin korar mun uwata ba ki
kyauta ba bayan ina jin xuminta”.
Ta matso kusa da shi cikin shagwava ta langave a jikinshi ta ce, “Tausa nake so Yaya jikina
ciwo yake yi min, Yaya ga shi kuma kasala ta dame ni”.
Hanni biyu ya saka ya rungumo ta a qirjinshi, ya sake miqa hannunshi na dama ya tallabo
qasan mararta cikin tausayawa da kulawa yake ce mata, “Haquri kawai za ki yi Aisha, ina ganin
matsalolin nan naki suna samuwa ne a dalilin za ki sake samo min wata Innar tawa”.
Saddiqa ta yi murmushi cikin shagwava ta ce, “Haba Yaya, ka rinqa samun Innar kenan? Ai
gara nima ka yi min kara ka sanya min sunan Gwaggona”.
Ya kalle ta cikin nutsuwar dake qara bayyanar da gaskiyar abin da yake faxi, ya ce mata,
“Aisha ke a gareni tamkar wata tauraruwa ce da kusurwowi biyar ke gareta, kusurwar farko tana
bayyana matsayinta, kusurwa ta biyu tana bayyana tausayinta, kusurwa ta uku tana bayyana
gargaxinta, kusurwa ta huxu ita ke bayyana soyayyarta. Sai ta cikon biyar xin ita ce mai
bayyanar da abotarta. Aisha gabana kan faxi in ji tamkar zan razana in na tuna a baya kin tava
qina, sai in ce to da za ki sake yin hakan a yanzu a wane hali zan samu kaina?”
Saddiqa ta yi murmushin farin ciki saboda gamsuwar da ta yi da matsayinta wurin mijinta. Ta
ce, “Ai a wannan lokacin ina cikin wauta ne Yaya, ban san mene ne so ba, ban fahimci yanda
soyayya take ba, ban gane soyayya ta asali ba. Zamana da kai ne ya fahaimtar dani na gane
soyayya ta asali, babu ganin girman laifi a cikinta sai yanda za a yi a yafe, babu maganar
sauraro a cikinta sai fahimta, babu rabuwa sai yanda za a yi a zauna tare har abada. Ni taka ce
Yaya Mus’ab, Innarka ce ta haifar maka ni, dama don kai ta haife ni kar gabanka ya sake
faxuwa a kaina, na kuma gode maka da ka yarda ka zaveni na zama nice tauraruwar
zuciyarka”.
Sai anjima.
Mu sadu a wani littafin cikin yardar Ubangiji.
Taku.
Hafsat Chindo Sodangi.

Alura:
Sabon littafin MATA DA KICIN XINSU littafi na biyu yana nan fitowa ba da daxewa ba, a
neme shi don samun qaruwa har da abincin masu lalurori.

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login
google.com, pub-9213700357025247, DIRECT, f08c47fec0942fa0