Showing 6001 words to 9000 words out of 34483 words
Chapter 3 - Abu Naka Book 3 Complete Hafsat C Sodangi
kar ki tuba, in kika yi haka ai baki zama cikakkiyar ‘yar iska ba”.
Saddiqa ta gaji da leqen abin da ke faruwa ta koma gadonta ta hau ta zauna cikin rawar jiki
da tsananin tsorata da abin da ke shirin faruwa da hannun Jennifer.
Ban da duk wani mugun halinshi da Gwaggo ta sani bai da tausayi ko na anini. Ta faxi hakan
cikin zuciyarta.
A waje Mus’ab ya tari mai tasi ya jefa Jennifer a ciki ya miqawa mai tasin jakarta a hannunshi,
ya ce, “Ku tafi ta gaya maka inda za ka kaita, in kun je ka xebi ladan aikin ka a ciki”.
Ya juya ya koma cikin gidanshi inda ya bar Saddiqa.
“Kukan me kike yi Aisha?”
Ya miqa hannu zai tava ta, ta yi maza ta maqure a jikin bango.
“Kar ka tava ni”.
Ta yi mishi kashedi.
“Bana son ganinka kusa dani tsoro kake bani, duk abin da Gwaggo ta gaya min game da kai
haka abin yake, sa’a ma ka ci ba ta san rashin tausayinka ba da ta qara tsanarka.
Na sha jin tana cewa, halinka guda xaya da ta sani shine kai xin mai tausayi ne, ba ta sani ba
shima tausayin ka daina shi. Abin da ya fi komai bani mamaki cikin lamarin shine, wai Gwaggo
ce ta haifeka”.
Mus’ab ya miqe tsaye ya nufi toilet xin dake xakin ya barta tana kuka. Ruwan wanka ya haxa
mata ya fito ya kalle ta a nutse qwarai ya ce mata.
“Shiga ki yi wanka tunda kin ce bakya so in rinqa tava ki zan kiyaye al’amarinki qwarai
matuqa kika kiyaye nawa, ni wani irin mutum ne da na fi so inda hali in baiwa kowa haqqinshi,
ina girmama mace, in kuma ji tausayinta har in yi mata adalci.
Amma kuma bana iya yiwa wacce ba ta san darajarta kanta ba, ko kuma wacce ta nemi
shige iyaka”.
Ya juya zai fita tare da faxin, “Amma kin san in har na je na dawo baki yi ba zan yi miki”.
Ta yunqura ta tashi ta shiga toilet xin da nufin yin wankan, shi kuma ya fita waje ya kira qarti
da za su tsabtace falon Saddiqa daga qazantar da ya samu na fitsarin da Jennifer ta yi ta
sakewa a dalilin wahala da kuma barasar da ta zube.
Saddiqa tana zaune kan kujerar gaban madubi tamkar mai shirin yin kwalliya, sai dai
zuciyarta kawai take sauraro. Ko me yasa Kawu Gixe xaukan aurenta ya baiwa Yaya Mus’ab?
Anya kuwa Kawu Gixe yana sonta ma kuwa?
Ta zurfafa cikin tunani. Wani abin da Kawu Gixe ya tava yi mata da zai sa ta yarda eh, lallai
yana yi mata so irin wanda uba ke yiwa ‘yar da ya haifa.
Shigowar da Mus’ab ya yi ya katse ta. Ya zauna a gefen gadon cikin wata lallausan jallabiya,
ga qamshinshi mai daxi yana tashi, da alama shima wankan ya yi.
Tiren abinci da ‘ya’yan itace ya ajiye a gabanta.
“Fara da wannan kafin ki ci kazar”.
Yana maganar ba tare da ya kalle ta ba, bai kuma fasa yanka mata kazar ba duk da zafinta,
haka nan yanayin fuskarshi bai sauya ba da alamar har lokacin ranshi a vace yake.
“Kar ki sake yunqurin gudu ki ce za ki tafi gida ke kaxai, ni kaina zan iya mayar dake gida
gaban Gwaggonki tunda har yanzu kuna ganin bani aurenki da Kawu Gixe ya yi kuskure ne. To
na ji na yarda, tunda ita Gwaggon nine wanda ba ta so, to na ji na yarda, tunda abin haka ne na
ji na yarda zan kai ki gaban Gwaggon in baku zavi…..” Kan ya qarasa ta katse shi ta hanyar hankaxa tiren abincin ya kife a qasa, ta yi maza ta miqe
tsaye cikin kuka. Shima ya miqe yana kallon ta tare da mamakin abin da ya yi wanda ya jawo
hakan.
“Bana so, ina jin kunyarka ina kuma girmamaka, ka barni in ci gaba da hakan. Muna magana
da kai kana sa sunan Gwaggo a ciki, ita ce za ka kai ni gabanta ka bamu zavin auren ka? Ka
bani ni da kai mana, ko kuma don ka ga an baka ni ba da yardar ta ba sai kuma ya zama…..”
Ta qara tsananta kukan da take yi.
“Ki yi haquri Aisha, ki yi haquri na yi kuskure da na ambaci sunanta, to amma me yasa da za
a kawo ki ba za ta yi miki irin nasihar da take yiwa sauran ba? Sai ta ce in kinga ba daidai ba ki
gudu, ba za ta qarfafeki a kan ki tsaya ki taimakeni in gyara halina da take ganin a kanshi ne
take qina ba?” Saddiqa ta galla mishi harara karo na farko da hakan ya tava faruwa a tsakaninsu.
“Nice ma zan taimakeka ka gyara halayenka? Lallai kam”.
Ya xan yi murmushi kaxan karo na farko shima tun bayan da ya neme ta ya rasa a gidan.
“To shi kenan na ji in ba za ki taimake ni gyara halina ba, ai kuma bai kamata ki yi dalilin da
mu’amala tsakanina da Gwaggon taki zai qara lalacewa ba ko?
Kin tava tunanin inda kin yi nasarar isa gabanta ke kaxai da sunan gudu abin da zai biyo
bayan hakan tsakanina da ita? Ke bakya sha’awar kyakkyawar mu’amala ta shiga tsakanina da
ita? Ai har da kwaxayin hakan ya qara sani dagewa a kan auren ki Aisha, don na san tana sonki
za ta yi mu’amala mai qarfi da gidana, ko ba don ni ba saboda ke. Kina tsammanin ina jin daxin abin da ke tsakanina da ita ne? Ita ta haife ni fa, nine namiji
guda xaya da take da shi, don me ba za ki gyara tsakanina da ita ba sai ki nemi ya qara
lalacewa?”
Jikin Saddiqa ya xan yi sanyi, lura da hakan ya sa shi qara yi mata magana.
“Kawu Gixe da ya bani ke ba kuskure ya yi ba Aisha, ya san ina sonki ne, ya san ba zan iya
zaluntarki ba, ya san zan yi miki adalci, ya san babu wani wanda ya fini cancantar aurenki ko da
kuwa a ya ya halayen nawa suke, domin nine nake zaune ni da Innata mu biyu sai aka same ki
kika shigo cikinmu. Muna ta murna muna ta ina muka saka dake, muna ta sonki muna renonki cikin kulawa da
tausayawa, duk da yawan kukan ki da yawan rikicinki, raina kan vaci in na ga yanda Inna ke
wuni hidima da xawainiya, da daddare kuma ki hanata barci da yawan kukan ki, ta yi ta fama
dake, ta yi jijjiga tana girgiza ki har sai asuba ta yi kafin ki yi barci, lokacin nan kuma ba lokacin
barci bane a wurinta, za ta kwantar dake ne kawai ta miqe ta shiga wasu sabgogin.
Ran nan raina ya vaci haushinki ya yi matuqar kamani na fito na zo na sameta na ce Mama
bani fitinanniyar yarinyar nan ki gani ki samu ki kwanta kema ki huta kamar kowa, zan je da ita
xakina in rarrasheta, in kuma kin fi so a goyata, to goya min ita a bayana ki xaure min ita ta
yanda zanin ba zai kwance ba. Sai na ga ta yi murmushi ta ce min, kar ka ji haushinta komai ta yi kar ta vata maka rai
yarinya ce ba ta da baki, bamu sani ba ko wani abu ke damun ta.
Kalamanta kan sanyani jin tausayinki, in zauna in yi ta taya ta rarrashinki ina tausayi, ina
ganin ba laifinki bane damuwa ce tasa kika hana min Innata bacci.
Gari in ya waye in yi maza in yi mata ayykan da zan iya taimakonta dasu, wanki,
wanke-wanke, shara, xiban ruwa duk babu abin da bana yi kafin in tafi makaranta, don ta xan
samu lokacin kwantawa ta huta da rana, dana……”
Qwan! Qwan! Qwan! Xim! Xim! Xim! Xum! Xum! Xum!!!
Bugun qofa ake yi babu qaqqautawa. Mus’ab da Saddiqa suka zubawa juna ido saboda jin
yanda ake bugun qofar. Gaba xaya suka kalli agogon dake xakin, tara saura kwata ne na dare.
“Iko sai Ubangiji, ko waye kuma yanzu?”
Mus’ab ya kalle ta jikinshi a sanyaye.
“Ki yi haquri Aisha bana nufin vata miki rai, ban kuma karvi aurenki don in saki ki yi baqin ciki
ba”.
Ya miqe ya nufi inda ake bugun qofar, a zuciyarshi yana tunanin to ko dai Jennifer ce ta turo
mishi ‘yan iska don su xaukar mata fansa kan abin da ya yi mata? Ubangiji dai yasa ba wata
fitinar ce ta sake biyo shi har gida ba.
Mus’ab ya isa qofar ya xan saurara kaxan don tantance muryar dake magana.
“Anya Baba basu tashi daga gidan nan ba kuwa?”
“Kai tafi can kai ma sakarai dukan qofar ne baka iya ba, kana yi kamar kana tsoro”
“Zan ji tsoro kai Baba in na tarwatsa gilasan gidan nan ya ya zan yi? Masu tsada ne fa”.
Ta ce, “A hau! Babu abin da za ayi maka ai jikokina ne a gidan suna nan a ciki babu wani
tashin da suka yi, sun hangame bakuna ne kawai sun kwanta suna bacci, ana bacci kamar na
mutuwa to ba a tunanin komai balle a rage dare a xan yi nafilfili”.
“Abu ce”.
Zuciyar Mus’ab ta gaya mishi.
“Me ya sake dawo da Abu yanzu?”
Ya tambayi kanshi cikin tsananin faxuwar gaba.
“Yanzu haka Inna ce ta turo ta”.
Ya juya ya koma wurin Saddiqa ba tare da ya buxe qofar ba, duk da su ma basu daina dukan
da suke yi mata ba.
“Aisha, Abu ce ta zo”.
“Abu?”
Ta yi tambayar a yanayi na tsananin mamaki tare da dirowa daga gadonta.
Mus’ab ya juya don komawa ya buxe musu qofar ta yi maza ta ce mishi, “Ka shigar da ita
wurinka kar ka kawo ta nan”.
Ya ce mata, “To”.
Mus’ab ya isa jikin qofar yasa hannu yana buxewa tare da tambayar, “Waxanne baqi ne haka
basa sallama sai dukan qofa?”
“Kai tafi can ka bani wuri, a ga qato kamar ka a ce wai shi ake bugawa qofa haka saboda
yana bacci bai farka ba, ai kuwa dai ya ji kunya”.
Ya yi murmushi ya ce, “Abu kenan, to ba a gidana nake ba?”
Ya shigar dasu qayataccen falonshi daga ita har direban.
“Sannunku da zuwa”.
Ya sake yi musu gaisuwar bayan sun samu wuri sun zauna, shima ya koma wata kujerar ya
zauna.
Saddiqa ta shigo falon cikin kwalliyar burgewa, ga shi ta yane jikinta da gyale sai qamshi take
yi.
“Wa ya vata miki rai a hanya Abu na ji kamar kina faxa?”
Abu ta harareta ta ce, “Yanzu idonku biyu ake ta buga qofar nan baku fito kun buxe ba?”
Ta yi murmushi ta ce, “Hirar amarci fa muke yi”.
Ta ajiye tiren da ta shigo da shi a gaban Abu ta koma ta sake shiryowa direban nashi ta ajiye
mishi, bayan ta gaishe shi ta koma kusa da Mus’ab ta zauna a gefen kujerarshi.
Mus’ab ya sallami direban da ya kawo Abu tare da alheri mai yawa, ya dawo ya sake zama
kusa da Abun yana taya ta matsa qafafuwanta da take yi.
“Ai kin wahala da yawa ne Abu, kwanan nan kika tafi kin sake dawowa, wannan tafiyar ai ta
yiwa jikinki tsanani. In ce ko dai lafiya?”
Abu ta ce, “Ina fa lafiya, fitinanniyar uwarku mana ta yi sanadin tasowata wai ita za ta zo ta
ga halin da na baro mata ‘yarta a ciki saboda hankalinta bai kwanta. Ko da yake dai nima nawa
hankalin ba kwanciyar ya yi ba, saboda yanayin da na barku a ciki”.
Ta basu labarin al’amuran duka. Saddiqa ta miqe ta nufi kicin tana cewa, “A’a, Abu ni bana
son haka, in za ku yi maganarku ku yi amma ban da Gwaggona a ciki, Gwaggo ce za ta turoki ki
zo ki ganan mata halin da nake ciki hankalinta bai kwanta ba, wa take yiwa haka a cikin
surukanta? In kin ji marmarin ganina kin zo kawai ki ce kin ji marmarin ganina, amma ba ki ce
Gwaggona ta turo ki ba”.
“Ka ji ta ko? Ka ji min ja’irar yarinya ko? Wani marmarin ganinki za a yi? Na sani da uwar taku
ta ce za ta zo in barta ta zo da kanta tunda baki ga abin arzikin da na yi ba”.
“Qyale ta Abu mu yi zancenmu”.
“Kun zauna lafiya ne?”
Ta yi tambayar cikin raxa wai kar Saddiqa ta ji.
Ya xan kalle ta a yanayi na murmushi ya ce, “Me kika gani yasa kika tambaya?”
Kan ta sake gaya mishi abin da ta ganin Saddiqa ta fito riqe da kwanon farfesu ta ajiye mata,
ta koma kusa da Mus’ab ta zauna.
“To kin ce Gwaggo ce ta turoki ki yi bincike in muna zaune lafiya mene ne? Ina ce dama don
kin san zamu zauna lafiyan ne yasa kika gudu kika barni?”
Mus’ab ya ce, “Rabu da ita Abu ba ta so ne in gaya miki gaskiya, sai dai abin da nake so ki
sani shine, ko na zauna lafiya da Aisha ko wane irin hali nake ciki ba zan sake daxewa ban zo
Misau ba, ba zan barki ki ji marmarin ganina baki ganni ba Abu, saboda na san kina sona”.
Ta ji daxin maganar tashi, nan take ta yi ta sa mishi albarka.
Sun yi hira gaba xayansu har suka kai lokacin da Aisha ta ce mata dare ya yi Abu muje in
rakaki ki yi wanka ki sha magani ki kwanta don ki huta gajiyarki”.
Ta ce mata, “To”.
Mus’ab yana zaune a falon cikin tunani za ta dawo ne ko za ta zauna a can, sai gata ta shigo.
Kwanukan dake wurin ta kwashe za ta fita dasu.
“Ke nake jira fa Aisha”.
Ba ta yi magana ba ta tafi ta dawo.
“To zo daga nan mana ya ya za ki zauna kuma a can?”
Ta ce, “A’a, nan xin ma ya yi”.
Ya qara gane don Abu ta yi abubuwan da ta yin duka.
“Ina ce nan za ki zo mu kwana?”
Cikin nutsuwa ta kalle shi ta ce, “Saboda me?”
“Saboda shine abin da ya dace ki yi, kema kin sani ko ba a gaya miki ba abubuwan da kike yi
min sun yi yawa, bai dace a ce kina yiwa mijinki haka ba”.
Ba ta kalle shi ba ta ce, “Ba ka ce za ka kaini gaban Gwaggona ka bamu zavi ba?”
Ya yi murmushi ya ce, “Wannan maganar ba ta wuce ba”.
Ya taso daga inda yake zaune ya zo wurinta yasa hannu ya sureta, ya ce, “Tunda kin riga kin
kawo kanki falon bari kawai in qarasa dake cikin xakin kawai”.
Ya zaunar da ita a kan gadon ya koma gefe ya zauna.
“Ina ce wannan maganar mun gama ta, kuma in bakya so in rinqa sa sunanta a cikin
maganarmu ke me yasa kike yi min abin da kika ga dama? Yanzu kina nufin inda kin san zan
kai qararki wurinta ta yi hukunci a tsakaninmu za ki rinqa yin irin waxannan abubuwan? Yanzu
su Bilki za su yi haka?” Shi da kanshi ya baiwa kanshi amsar “Ba za suyi ba, saboda sun san mazansu suna da….”
Bai qarasa ba ya yi murmushi saboda kallon da Saddiqan ta yi mishi, ya canza maganar tasu
da tambayar ta.
“Me kike ganin za ki yiwa Abu na karyawa da safe?”
Ta ce, “Da zai yiwu waina da miya ko funkaso”.
Ya yi maza ya ce, “To muje kicin xin mana in taya ki ki duba abubuwan”.
Qarfe xaya ta yi