Showing 1 words to 3000 words out of 23776 words

Chapter 1 - Biyu Babu Book 3 By Fatima Tijjani Ahmad

10 Aug 2026

293

BIYU BABU-3
Fatima Tijjani Ahma




“Abdullahi idona”.
Ya ce, “Me ya sami idon naki?”
Na ce, “Ya buɗe”.
Ya juyo ya ce, “Mai?”
Na ce, “Ya buɗu”.
Taka burkin da ya yi ni aina sai da abin ya ba ni tsoro, a tsakiyar titi ya taka birkin, Allah ya sa
ba mota a bayanmu, ya ce.
“Fatima me ki ka ce?”
Na ce, “Idona ya buɗe”.
Ya ce, “To me ye a jikina?”
Na ce, “Abdullahi shadda ka sa baƙa”.
Yana jin haka sai ya sauka gefen hanya ya yi fakin sosai, zuba min ido ya yi ya kasa magana.
Ni kuwa abin da ya ke fita daga bakina bai wuce gaisuwa ga baban Fatima kakan Hassan da
Usaini shugabannin samarin gidan aljanna.
Salati na ke sake yi wa ɗan Amina goyon Halima, sahibin Abubakar. Mun jima
### SHAFI NA 6
**BIYU BABU-3** **Fatima Tijjani Ahmad**
ba wanda ya yi wa wani magana, sai zuwa can ya ce.
“Bari mu koma gida”.
Na ce, “To”.
Tunda muka taho ba wanda ya yi wa wani magana, kowa a cikinmu yana zance da zuciyarsa
ne. Ba mu iso gida ba sai da daddare magriba, kasancewar da ma ba da wuri muka fita ba, sai
la’asar ga shi kuma mu dawo mun tarar da cunkoso a kusa da ashibitin Malam Aminu Kano.
Ji na ke kamar na yi tsuntsuwa na tashi sama na zo gida. Muna ƙarasawa ƙofar gida sai ga
Babana da maƙocinsa a tsaye a ƙofar gida suna magana.
Ai tun kafin na fito na dinga ƙwala masa kira, kafin Abdullahi ya tsaya tuni na buɗe ƙofar mota
na fito. Hankalin Babana ya yi matuƙar tashi yadda ba kwa zayo, domin baro maƙocin namu ya
yi ya nufo gurina da sauri.
Ina zuwa na rungume shi yana tambayata, mene ne? Amma na kasa magana sai kuka, sai da
Abdullahi ya ƙaraso ya ce.
### SHAFI NA 7
**BIYU BABU-3** **Fatima Tijjani Ahmad**
“Baba idon fa ya buɗe”.
Sannan Baban ya ɗago fuskata, ya ce.
“Fatima ido ya buɗe?”
Na yi dariya na ce.
“Baba yau alkawarin Allah ya cika, idona ya buɗe ina ganinka, ga shi shadda fara ka sa”.
Ya ce, “Fatima, na yi wa Allah godiya, mu je cikin gida”.

Kafin na shiga gida Abdullahi ne ya fara shiga don haka kafin me ’yan gidan sun yo waje.
Ai nan da nan sai gidanmu ya fara cika da mutane, maƙota suka yo waje sun ji hayaniya, sai dai
duk wanda ya tambayi me ya faru? Idan aka ba shi labarin idona ya buɗe sai ka ga ya nufo
gidanmu domin ya gani wa idonsa ga kuma taya ni murma ni da iyayena, da kuma ’yan uwana.
Yau gidanmu fa abin sai wanda ya gani, domin ni kaina abin har ya soma ba ni mamaki, da ma
haka mutane suka damu da halin da na ke ciki, lallai ɗan Adam mai masoya da kuma maƙiya a
duniya.
### SHAFI NA 8
**BIYU BABU-3** **Fatima Tijjani Ahmad**
’Yan uwa kuwa akwai waɗanda suka zo tun a daren suka gan ni suka taya ni murna saboda
suna ganin su bari zuwa safiya ya yi nisa.
Abdullahi dan ƙanin mahaifina ne sai dai shi tuni Allah ya amshi mahaifinsa, yanzu haka yana
zaune da mahaifiyarsa dda kuma ’yan uwansa a cikin unguwar Sani Mainagge.
Tun a daren babana ya kira wayar Nazir, amma bai same shi ba. Ya kira ya kai sau shiɗa, don
haka sai ya kira mahaifinsa wato Malam ya sanar da shi, malam ya ji daɗi sosai, ya kuma faɗa
wa Babana yana nan zuwa gobe insha Allahu.
Amma kuma Babana ya manta da cewa ya gaya masa bai samu Nazir a waya ba.
Ranar kasa barci na yi saboda farin cikin ganin yau idona ya buɗe, ga shi ina kallon kowa, kai
al’amarin Allah sai kallo.
Shi kuwa gogan nawa ashe yau an tashi da hare-hare a cikin garin Kaduna, sune suka dinga
raba ma’aikata ga shi kuma sun shiga cikin duk hankalinsu a tashe, don daukacin
### SHAFI NA 9
**BIYU BABU-3** **Fatima Tijjani Ahmad**
gama mitin ɗin ma a cikin bariki ya kwana bai dawo gida ba.
Nazir bai tashi duba wayarsa ba waddda ya sa a silent, sai bayan ya yi sallar asuba ya shirya
cikin kaki zai fita kiran da ya gani na mahaifina shi ya ɗaga masa hankali.
Yana kuma dubawa ya ga kira har da asuba na kira shi, ya shiga damuwa ya koma ya zauna,
ya shiga laluben layin babanmu, shiru a kashe haka nawa ma, saboda yawan kiran wayar da
mutane suka dinga yi cajin ya sauka.
Shi ma Baban bai san ba shi da cajin ba, sai da wani ƙaninsa ya shigo ya ce yana ta kiransa
wayarsa a kashe, sannan ya ce a kunna inji. Ana kunnawa ni ma na samu na sa tawa wayar a
caji.
Nazir ya jima bai same ni ba, sannan ya sa wayar a cikin aljihu ya fita, kun san aikin soja ba
kamar sauran ayyuka ba ne bare yau zai yi gwangwani, ma’ana ya ƙi zuwa gurin aikin ya fake
da wani abu ba.
### SHAFI NA 10
**BIYU BABU-3** **Fatima Tijjani Ahmad**
Ni kaima ban ji daɗi ba, wallahi na so ace yau tare da shi za mu wuni, amma ina, Nazir ya yi min
nisa na kasa samunsa a waya.
Cikin ƙanƙanin lokaci yanzu mutane ne suke soma ɗaukar harami, yanzu mutane ne suke
shigowa, shi kansa Babana fasa fita ya yi saboda mutane, da kuma waya da ake yi masa ana
taya shi murna.
Da yamma sai ga Malam ya shigo, ko da na ba na sami Nazir ba ji ban ji daɗi ba, ni fa Nazir na
ke so na gani.

Mun gaisa da Malam ya min addu’a bayan taya ni murna da ya yi.
Bayan sallar magriba ina zaune a kan darduma an kawo min abinci amma na kasa cin abincin
sai kawai na kuma gwada kiran wayarsa. Ta shiga sai da ta kusa katsewa ya ɗauka, na ce.
“Haba Nazir...”
### SHAFI NA 11
**BIYU BABU-3** **Fatima Tijjani Ahmad**
Ya ce, “Ki yi haƙuri, yau ni kaina ba ni da lafiya saboda na ga kiranki na ga na Baba amma na
kasa samunku, har na fita gurin aiki ne shi ya sa, kuma ban ga kiran ba sai da asuba,
kasancewar jiya garin namu ba daɗi”.
“Baba, ka yi haƙuri wallahi jiya ina sun gaisa Nazir ya ce.
Neman layin wayata ya dinga yi amma shiru ɗaga bisani ya kira mahaifina. Bayan Sai na kashe
wayata.
Na ce, “Idona ya buɗe”.
Ya ce, “A’a sai kin faɗa”.
“Ka san me?”
Na ɗan jima sannan na ce.
“Ki yi min magana”.
Na yi shiru.
Ya ce, “Me?”
Na ce, “Bayan an riga ka gani?”
Kiyihakuri kin ji ko sai na zo?”
Ya ce, “Ki yi haƙuri yau ni kaina ba ni da lafiya saboda na ga kiranki na ga na Baba amma na
kasa samunku, har na fita gurin aiki ne shi ya sa, kuma ban ga kiran ba sai da asuba,
kasancewar jiya garin namu ba daɗi”.
Ya kuma ba shi haƙuri sosai, Baba ya ce.
“Ba komai Nazir, Allah ya rufa mana asiri, Allah ya ba mu zaman lafiya, ku kuma
### SHAFI NA 12
**BIYU BABU-3** **Fatima Tijjani Ahmad**
da ku ka sai da ranku wajen kare al’umma da kuma dukiyoyinsu, Allah ya kare ku. Nazir duk
sanda za ka fita gurin aiki ɗan da na ke so da kai shine ka saka a cikin ranka ƙaunar saboda
Allah ba wai don abin da za ka samu ba ko kuma don a kiraka soja ba”.
Nazir ya ji daɗin nasihar da mahaifina ya yi masa, don haka ya ke ta faman yi wa Baban godiya.
Zuwa can babana ya fahinci bai san abin da ya faru ba sai ya ce da shi.
“Kun yi magana da ita kuwa?”
Da saurinsa ya ce, “Ta kira ni, amma wayar ta katse kuma na kasa samunta kamar ma wayar a
kashe ta ke”.
Babana ya yi dariya ya ce.
“Nazir idonta ya buɗe jiya da yamma”.
Ai ko sai ji Baban ya yi yana faɗin.
“Idon wa fa?”
Ya ce, “Idon matarka Nazir”.
“Allahu akbar, Allah sarkin sarakuna, sarkin da barci bai siffantu da shi ba, sarkin da ya ke son
baynsa”.
### SHAFI NA 13

**BIYU BABU-3** **Fatima Tijjani Ahmad**
Ai kawai sai Baban ya ji Nazir na faɗin.
“Subbuhun Kuddusun rabbil mala’ikatu warhu”.
Sujjada ya faɗi ƙasa ya yi wa Ubangijin da ya haɗa shi da Fatima, ya kuma ɗora masa sonta
duk da irin ruguntsumin da aka shiga, yau ga farin ciki a ƙan farin ciki, yau ga lafiya ta samu ga
Fatima, ga kuma mahaifinta ya ba shi Fatima dole ya yi gaisuwa ga Sarkin da ya yi masa haka
domin shirin ba na mutum ba ne. Shi kuwa Babana da ya ji shirun ta yi yawa a cikin waya, sai ya katse wayar.
A lokacin da Nazir ya faɗi yana sujjada ga sarki Allah a kusa da shi akwai ogansa tare muka yi
waya haka kuma suna tare suka yi magana da Babana, suna tare ya faɗi sujjada duk a kan
idonsa.
Bayan Nazir ya ɗago kansa sai kuma ya ga ya ɗaga hannu sama yana ta faman addu’a, Nazir
ya jima a cikin a cikin faɗar Ubangiji bai fito ba.
### SHAFI NA 14
**BIYU BABU-3** **Fatima Tijjani Ahmad**
Bayan ya fito kuma sai fuskarsa ta cika da farin ciki. Samuel ya dubi nazir ya ce.
“Me ya faru haka?”
Ya yi dariya gami da mikewa alamar girmamawa a gare shi, ya ce.
“Ba komai”.
Ya ce, “Da ma fa ni matsala ta ku musulmi ƙarya, ga shi ka yi abubuwa a gabana waɗanda suke
nuna cewa akwai abin farin ciki a tare da kai, amma na tambaye ka ka ce ba komai, kuma ga
shi ka yi sallah duk da cewa lokacin da kuke yinta bai zo ba”.
Nazir ya ɗan yi jim sai kuma ya sake duban Samuel da har yanzu ya ke kallonsa, ya ce.
“Oga matata ce ta samu matsala ta ido har jamani mun je amma idonta bai buɗe ba, shi ne
yanzu aka yi min waya ake idonta ya buɗe shi ya sa na ga ba wanda zan iya yi wa godiya sai
Allah domin shi ne Ya Isa ya yi duk abin da ya ke so a lokacin da ya so, kuma ba wanda zai ce
da shi me ya sa? Yau na kashe kuɗi da yawa amma ba wanda ya samu ya gano matsalar gara ma a
### SHAFI NA 15
**BIYU BABU-3** **Fatima Tijjani Ahmad**
jamani ɗin wani likita ya ce mu dawo gida, kuma ka ƙara taba mata idonta zai buɗe, kuma ga
shi sarkin da ya isa ya buɗe mata idonta. Ka ga kuwa dole na gode masa”.
Samuel ya dubi Nazir ya ce.
“To yanzu da ka yi sallah ba ka yi wanka ba, wanda ku ke yi idan za ku yi sallah ba?”
Nazir ya ce, “Ai wannan da ka ga na yi ba sai da alwala ba, a’a haka ma idan ka yi ta Allah zai
amshe ka, kuma zai ji daɗin abin da ka yi. Ka ga yanzu naa samu lada mai yawa, domin da
wani ji za ka yi ya danno ashar”.
Samuel ya sake duban Nazir, duba mai nuna damuwa, ya ce.
“Ina sha’awar addininku, amma kuma dokokinku sun yi min tsauri”.
Nazir ya dube shi, ya ce.
“Me ye abin tsauri cikin addininmu? Ni kuwa a ganna addininmu ya fi kowane addini sauƙi, ga
kuma samun nutsuwa a rayuwa”.
Ya ce, “Abin da na ke ganin ba zan iya ba shi ne yawan yin wanka idan mutum zai yi
### SHAFI NA 16

**BIYU BABU-3** **Fatima Tijjani Ahmad**
sallah, ga shi ma sallah sai ka iya karatu, gaskiya abin da wuya fa”.
Nazir ya ce, “Yanzu idan za ka ci abinci da hannunka kana wankewa?”
Ya ce, “Sosai ma”.
Ya ce, “Idan ka wanke ya ka ke ji a jikinka?”
Ya ce, “Ina jin daɗi har zuciyata, domin na san hannun yana da kyau, kuma ba zan ci abincin
ina jin tsoron ko wani abu zai same ni ba”.
Ya ce, “To yanzu ban da abinka ai addininmu yana koyan tsafta ne domin duk sanda ka zo yin
alwala sai ka wanke hannu, to za ka ga datti yana fita daga hannun naka, idan ka wanke
hancinka? To duk sanda ka taɓa wani abu da shar’armu ta hana kuma kai ba ka sani ba, ko
kuma ka yi alwala sai ka wanke wannan zunubin, ke nan zunubi ta nan ake kankare maka su. Ita kuwa sallah idan kana yinta ai zama ba ta barinka ka dinga aikata saɓo, da ka yi hufin
aikatawa sai zuciyarka ta tuna Allah.
### SHAFI NA 17
**BIYU BABU-3** **Fatima Tijjani Ahmad**
Shi kuwa azumi kuma kuna yi sai dai yana da bambanci da namu da naku, naku kuna yin kwara
arba’in, namu kuwa kwara talatin ne, ko ashirin da tara kuma mu idan aka sha ruwa muna cin
abinci har sai lokacin da alfijir ya fito.
To me ye abin ƙi a cikin addininmu Samuel? Ko aure da Ya ce ka ajiye matar a cikin gida ka
kyautata mata ka kula da yaranka shi ne abin gudu a cikin addininmu, ko ƙakyautata wa
iyayenka da maƙotanka? Samuel me ye abin dugu a ciki?”.
Allaah mai iko, mai fidda matacce daga mai rai, ya kuma fidda mai rai daga matacce, Nazir bai
bar gurin ba sai da Samuel ya amshi addinin gaskiya, addinin da ya gasgata Annabi Isah dan
Maryama ne a matsayinsa na Annabin Allah, mahaifiyarsa kuma Siddik.
Ya karɓi musulunci ahanun Nazir, kuma Nazir ɗin ya ɗaukar masa alkawarin shi zai dinga nuna
masa yadda addininmu ya ke da kuma yadda zai dinga kuwala yana yinsa.
### SHAFI NA 18
**BIYU BABU-3** **Fatima Tijjani Ahmad**
Nazir bai sami sukunin kirana a waya ba sai da ya koma gida da dare, har na soma bacci na ji
kiran wayarsa.
Bayan mun gaisa na yi ƙoƙarin don me zai yi min haka na kira shi na fada masa ido ya buɗe
amma shi ne ban kuma jinsa ba, ga shi kuma idon ya gaji da kallon hanya har ya soma zubda
hawaye saboda rashin ganinsa, na ƙara da faɗin.
“Ko dai...”
Ya yi saurin katse ni.
“Fatima ki yi haƙuri, wallahi dole ce za ta hana ni zuwa na ganki amma gobe da safe zan biyo
jirgi na zo na ga idona sai na dawo, kin san garin namu ba daɗi”.
Na ce, “To ba komai, ka san ba ka laifi a gurina, duk yadda aka yi daidai ne, ba wani abu na san
ba ka wasa da lamurana, don haka ba ka laifi, na gode”.
Mun jima muna hira kafin ya kwanta saboda da safe da wuri ya ke fita, wani lokacin ma a wajen
aikin ya ke kwana kasancewar yanzu abin ya kuma kamari a
### SHAFI NA 19
**BIYU BABU-3** **Fatima Tijjani Ahmad**
cikin garin Kaduna, kodayake har ma nu nan Kano haka abin ya ke.

Da gari ya waye da safe ina tashi bandaki na shiga na yi wanka, na yi kwalliya cikin shadda riga
da siket, na zauna ina yin azkar domin yau ban samu na ji da asuba ba.
Na kusa gamawa na ji shigowarsa cikin gidanmu ko da na duba agogo sai na ga ƙarfe bakwai
da rabi na safiya, sai na miƙe domin na maida littafin da na ke karantawa.
Ina mikewa sai ga shi ya shigo, tsayawa ya yi yana dubana kamar bai taɓa ganina ba. Ni na
datse shirun da ke tsakaninmu, na ce.
“Sannu da zuwa Yallabai”.
Bai yi magana ba, na kuma cewa.
“Barka da zuwa”.
Sannan ya cire hular da ke kansa, matsowa ya yi yana zuwa dab da ni ya ɗora hannunsa a
fuskata ya ce.
“Fatima?”
Na amsa, “Na’am, Naziru”.
Sai ji na yi ya rungume ni a jikinsa.
Sai ji na yi ya rungume ni a jikinsa Sai ji na yi ya ya mun gode da ƙyar na ɓamɓare jikina daga
nasa. Ya zuba min ido
### SHAFI NA 20
**BIYU BABU-3** **Fatima Tijjani Ahmad**
yana ta murmushi, ya min kyau sosai domin yana cikin kakinsa na soja, kuma ya min kyau na
ce.
“Amma fa yau ka fi kullum kyau Nazir”.
Shi dai bai yi magana ba sai dai kallona ya ke yi kawai, a lokacin Babana ya shigo da sallama,
sannan Nazir ya amsa gami da juyawa yana kuma yi wa Babanmu fara’a.
“Sannu Baba”.
“Yauwa Nazir, ya aiki, ya kuma garin naku?”
Ya ce, “Wallahi Baba abin sai addu’a, idan murna mun danne su sai kuma ka ji sun ɓillo ta wani
gurin. Wallahi baba sai dai a dage da addu’a shi ne abin da ya kamata, amma daiakwai matsala
sosai wallahi”.
Bayan sun gama suna hira sai Babana ya fita ya bar mu a cikin ɗakina muna ta faman hira don
ma ina janye jikina da shi amma shi bai i ba ya makale a jikina ba.
Misalin ƙarfe goma na safiya ya ce zai tafi domin yanzu yana bakin aiki ne. Ya ɗan
### SHAFI NA 21
**BIYU BABU-3** **Fatima Tijjani Ahmad**
nemi afuwa ne a gurin Samuel wanda ya zama Sulaiman, ya zo ya gan ni.
Da zai tafi ya rike hannuna.
“Amarya ba a kya laifi ko kin kashe ɗan masu gida”.
Na ce, “A’a ba zan ma kashe ba”.
Ya ce, “To Fatima zan koma, inyaso sai na turo Malam domin ya zo a tsaida ranar ɗaurin aure”.
Wayarsa ya ba ni ya cire layinsa ya sa na turo Malam domin ya zo a tsaida ranar ɗaurin aure”.
Na rako shi har ƙofar gida inda ya shiga mota duk da cewaba motarsa ba ce, motar hajja ce da
ya ɗauko daga Malam Aminu airport. Mun rabu ba don rai ya so ba sai don ba yadda za mu yi.
Bayan ya koma ya kira Umar abokinsa

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login
google.com, pub-9213700357025247, DIRECT, f08c47fec0942fa0