Showing 1 words to 3000 words out of 23697 words

Chapter 1 - Dangina Book Compelet Secret Pen

01 Sep 2026

266


DANGINA
*[AKA RABANI DASU]*



STORY &WRITEN


BY

ADAMA UMAR
SECRET PEN


07081940768



LOVE AND ROMANTIC STORY

DA SUNAN ALLAH MAI RAHMA MAI JINKAI


1️⃣

PAGE ONE

Zaune suke a falon kuna ganinsu kunsan suna tattauna abu mai mahimmanci ,yatsunra yana
sarke a cikin na yar uwarta ta sake kallonta ta ce

Dan.Allah Hafsat ki amince da buƙata ta dan Allah bamuda wata mafita da yawuce haka babu
abunda zamuyi mu goge lqifinmu a gareki saita wannan hanya pls ki taimaka

Kwarai Hafsat abunda zuwaira take faɗa miki gaskiya ne na roƙeki nima gani na durkushe akan
guiwowina dan Allah ki amince da buƙatar mu

Fisge hannunta tayi daga yatsun yar uwartata sannan ta dauki jakarta ta kallesu kawai ta fita a
gidan cikin hanzari sunanta suke kira amma ina ko juyowa batayi ba balle kuma ta sauraresu
,kallon zuwaira yayi ya ce

Mucigaba da jarrabawa insha Allah wataran zata amince kinsan sai mun mata uzuri yanzu tana
cikin wani hali ,harna rasa da wacce irin fuska zan kalli hafsat wlh ,amma mucigaba da

kokartawa insha Allah wataran zata amince

Hawayen dake zuba daga fuskarta ta goge ta ce

Haba hafsat kibani dama kibani dama mana mu goge babban tabon da muka miki ,ki amince
mu cireki a cikin kuncin da kike ciki da bakin ciki

Tafaɗa tana kqra rushewq da kuka

Rungumota jikinsa yayi yana ban baki .

A banagaren hafsat kuwa Allah ne kawai ya kaita gida lafiya tana zuwq tayi park na motarta
sannan ta fito ta nufi ciki gida ,tana shigowa ta hadu da amminta tana zaune tana karatuna
alquran ta zare glass ɗin idonta ta kalleta ta ce

Wai hafsa lafiyarki kuwa ,gaba ɗaya yanayinki ya sanja wai me yake damun kine


Kwanciya tayi a kafadun wannan dattijuwa kana ganinta kasan mahaifiyartace ta ce

Wlh ammi na rasa ya zanyi dq zuwaira gaba day tasani a gaba akan wannan kudiri na ta
nikuma nama rasa ta ina zan fara amincewa kai bazan ma faraba domin wlh ita da kanta zatayi
nadamar faruwar wannan kudiri nata

Ajiyar zuciya Ammi tayi ta ce

Gaskiya Hafsat bazan boye miki ba ,kinsan nidai mahaifiyar kice ,bazan baki shawarar da bata
gari ba ,a ganinq kuma a abunda ya dace ni kaina ina mai baki shawarar da ki amince da
bukatar zuwaira da mijinta wannan itace mafita a gareki

Zubur ta tashi daga kan kafaɗarta ta kalleta Ta fara magana

Haba Ammi kema haka zaki fada,yanzu kina daya daga cikin mutanen da zasu goyi bqyan
wannan lamari ,gaskiya Ammi tunda kince shawara ba umarni ba gaskiya bazan yadda da
wannan kudirin ba .

Tanq gamq faɗar haka tq tashi da hanzari ta haura sama ,Ammi tq maida glass ɗinta tq ce

Yaro yarone Allah ya ganar dake kamqn yadda ya nunqmun faidar hakan .


Yau tana da lecture around 8:00 shiyasa ta tashi ta shirya da wuri ko break batayi ba haka
tayiwq Ammi bankwana ta fita tana zuwa makaranta ta nufi hall taji ankira sunanta a hankali ta

juyo ta kalli me siran sunan ta ,dafe goshinta tayi ganin zuwairace ta kira sunanta ,agogon
hannu ta ta kalla taga batada lokqcin bqtawa aikuwa ta wuce ta shiga hall ɗin batare da ta tsaya
ba,wuri ta nema ta zauna tana jiran su gama lecture ta fito suyi magana don yau babu wanda
zai rabata da hafsat matikar bata amince da kudirinta ba ,To abangaren Hafsat ma haka gaba
daya tinani ta tsaya yi akan maganganun da ake mata ita gaba ɗaya kanta ya kulle kuma
kwakwalwarta ta toshe bata hango abunda ake faɗa ba ganin tinanin bqzai kaita ko inaba
shiyasa ta kwatsar da zancen ta maida hankali akan karatunta ,gqba daya lecture ta dau zafi
shiyasa gaba ɗaya a gajiye ta fito amma me tana fitowa tayi karo da zuwaira tana jiranta
kallonta takeyi kafun tai magana ta kariso inda take ta ce


Dan Allah Hafsat bazan gajiya ba bazan karaya ba sannan bazan haura ba matikar baki yadda
da kudirna ba ,mena miki meyasa cike tsanata kumq kike ƙyamata ,shin guduna kikeyi

Ohooo haba zuwqirq meya kawo maganar nan da zakice ina kyamqrki yaushe mukayi dake inq
gudunki kawai don naki amincewa da kudurinki shiyasa zaki yanke mun danyen hukunci haka
gaskiya kiyu hakuri ,karki manta yadda muka taso dake tamkar yan uwa kudubq irin shakuwa
da kaunar dake tsakaninmu kisani inaso ya daure harga yayanmu ,amma ki sani matikar
kudirinki ya cika zai iya zama sanadiyar tarwatsewar muamalarmu ,hakan zai dawo gaba mai
tsanani a tsakaninmu kuma harga yayanmu ,inqso ki bari Allah ya zaɓamun duk abunda ya
dace dani a rayuwata dan Allah karkiyiwa Alla shishigi

Shiru tayi gaba dayata rasa me zata faɗawa kawartata hakan yasa ta fashe da kuka ta ce

Da kinsan alkhairin da nake hangowa da baki faɗi wannan zantuttuka ba

Shin wani irin alkhairi kika hango wanda ni nakasa hangowa pls allow me to rest banason
damuwa

Bata jira me zatace ba ta nufi parking space tashiga motarta tayi gidq ,jiki a sanyaye zuwaira
tabar makarantar tana nazqrin shin taya zata fara bullowa da kawar tata ta amince da ita .

Tana zuwa gida bata tsaya bata lokaiba ta wuce daining domin wata azababbiyar yunwa da
take damunta serving ɗin kanta ta fara sanna tafara cin abincinta hannu baka hannu kwarya
,tana cin qbinci sai hoton lokqcin rayuwarta ta baya ya fara dawo mata ,tana tina yadda ta
kasance da walwala da nishaɗi da farin ciki amma yanzu ya zama tarihi ,ture abincij tayi domin
saitaji duk abincin ya ginsheta ,tashi tayi ta nufi dakinta ta ajiye hakarta ta kalli wayarta na ƙara
,dauka ta duba tsaki tayi ganin sunan my besty ya bayyana ɓaro ɓaro ,jifa da wayar tayi akan
gadon kafun ta fara rage kayan jikinta ta faɗa bandaki ,tana shiga ta tsaya kallon kanta a
madubi tana duba shin ta kara ƙiba kota rage shin tumbinta ya karu koya ragu wannan ta
kasance dabiarta ce saida ta gama karewa jikinta kallo sannan ta fara wankan ,tana gamawa ta
fito daure da alwala ta dauko wata doguwar riga ta zura ta tada Sallah ,tana tayar da sallah
saiga Ammi ta shigo da waya a hannunta ,kara wayar tayi a kunnenta ta ce

Ayyah zuwaira sallah take shiyasa bata ɗaga kiranki ba amma idan ta idar zan hadaku

Shikenan Ammin na gode

Saida ta idar da sallah sannan tai afduointa ta shafa tasawa kofarta kry ta kwanta a lafiyayyen
gadonta tana kulle idonta tana sauraron bugun xuviyarta da alama bacci takeso ya dauketa
,wayarta ce ta fara ruri da alamar neman agaji tsaki tayi kibata duba ba tasan wace me kira
shiyasa ta dauko wayartasata a silent ta maids kanta ta kwanta har bacci ya dauketa .
Ba ita ta farka ba sai misalin ƙarfe 3:00 na rana aikuwa a gurguje ta tashi tayi wanka Hafsat
kenan sarkin tsafta haka take kaman wata agwagwa.kullum cikin wanka take ,bata fitoba saida
ta dauro alwala sannan tafito ta shirya ta nufi falo ,tqna fita ta tarar da Ammi tadan mike kan
sofer maakaciyarsu nanna tana mata tausa karisowa tayi ta rungume Ammin ta ce
Kai ammi yau nasha wahala gaskiya shiyasa dana dawo ban nemiki ba

Na sani kuma naje dakinki a rufe nasan bacci kike abunda nakeso dake ki tashi ki dauko
mayafinki inaso ki kaini anguwa

Shikenan Ammi amma bazamu jirq mu gabatar da sallar laasar ba saimu fita

Shikenan bari inje indauro alwala saura minti 5

Tashi tayi ta nufi dakinta ,kallon.Nanna tayi.macece mai dan shekaru don a ƙalla zatakai
shekara 40 gashi tanada nitsuwa ga ilimi ita kanta tashi tayi taga Ammi da Nanna domin batai
aure bama me gadin gidan aka aura mata sannan ya rasu ya tafi ya barta da yaro daya tilo
dagananbata sake aure ba ko zancen aure Ammin tayi tayi harta gaji ,ajiyar zuciya tayi tace
Nanna dan akwai abunda nakeso in tambayeki kinga.dai ke babbace watakil kema ki hango
abunda na kasa hangowa

Jinjina kai tayi ta ce

Ina jinki hafsatu

Kaman yadda kika sani Zuwaira ƙawata tace kuma...

Kiran sallah ne ya katseta ta ce.

Kibari hjy nanna idan muka.dawo nida Ammi zanzo har dakinki inbaki labari bari inje inyi sallah

Shikenan to Allah ya dawo daku lafiya

Tafaɗa tana mikewa itama ta.nufi dakinta ,bayan sun idar da sallah kowacce ta fito da shirin fita
sannan suka shiga mota suka fita a gidan ,suna ciki tafiya Hafsat ta kalli Ammi ta ce

Ammi wai ina zamuje ne sai tafiya mukeyi

Murmushi ammi tayi ta ce

Gidan zuwaira.

Fuskarta babu alamar wasa ,hakqn yasa Hafsat tadan haɗe rai ta cigaba da.drinving,dede kofar
gidan taja tai parking Ammi ta kalleta ta ce

Me kike nufi kina nufin bazaki shiga ciki bane kome

Gaskiya Ammi ni bazani ba.kije ki kawa...

Bata karisaba.kawai taji saukar mari kan kuncinta ta dafe.ta juyo a mamakance tana kallon
Ammi.





Share pls
*DANGINA*
*[AKA RABANI DASU]*



STORY &WRITEN


BY

ADAMA UMAR
SECRET PEN


07081940768

LOVE AND ROMANTIC STORY

DA SUNAN ALLAH MAI RAHMA MAI JINKAI


2️⃣





PAGE TWO

tabbas Ammi tana.wasa da yara amma tanada zafi.kuma ga zuciya macece tsayayya akan
yayanta duk da ta.kasance ita ta rainesu amma hakan baisa tarbiyyarsu ta lalaceba ,batayi
magana ba ta buɗe marfin motar ta fita aikuwa Hafsat ta rufa mata baya domin taga babu
alamar wasa alamarin Ammi .
Zaune suke a falon dukkansu suna kan rug itq kuma Ammi tana kan kujera ta gyara glass ɗinta
ta fara magana kamar haka

Wato Abdulmallik komai ya faru mu daukeshi mu kaddarine daga Allah dan adam bazai taɓa
maka qbunda Allah bai maka ba ,mu sani komai ya faru a cikin duniyar nan dama alƙalami ya
rigada ya rubutashi don haka komai ya samemu karmuce wane ne ya mana ,Allah ne kawai
yake iya yin yadda yaso da bawa saidai wani ya zama sila ,wanda shima a sanadiyar wannan
silan zai gane ya shiga wata jarrabawa ce ,kusani dukkan mu musulmaine don haka bazamu
taaya ɓatawa kanmu lokaciba mu yafewa juna komai ya faru ya wuce har abada banason daya
daga cikinku ya kara kallon dan uwansa da abunda ya faru ,kuma naju dadin hukuncin da
zuwaira kika yanke hakan ya nuna kinada kaifin tinani don haka inaso dukkanmu mu taru.mu
rufawa juna asiri abun mun nan yazamana tuwona maina

Tunda ta fara magana Hafsat take hawaye tasan ba wani abu Ammi take ba.illa ta yarda ta
amince da Abdulmallik amma anya zata iya aurensa kuwa shin dawani ido zatana kallonsa
tabon daya mata bazai taɓa gogewa ba don haka bazai yiwu ma ta fara haɗa inuwar wre dashi
ba.,saida Ammi ta gama koro zance sannan suka mata godiya ta tisa hafsat a gaba suka nufi
hanyar gida ,a hanya take faɗa mata ta sani kozata rayu kozata mutu sai andaura aurenta da
Abdulmallik don haka idan zata saki ranta ma ta sake ta amince dashi kuma tana gama
makaramta zaayi aurensu nan da 6 month ,maganar ta doketa gaskiya me Ammi take nufi
,Ammu tana nufin zqta mata auren dole gaskuya bazwu yiwuba sannan zatai iya kokarinta na
ganin ta cusa tsanarta a zuciyar Abdulmallik da matarsa zuwaira.

Suna komawa gida ta nufi dakinta tasa kuka ra rufe ,kukq kawai take me cin bataso ta tin
rayuwarta ta baya amma y zame mata dole matikar zatana ganin Abdulmallik dole ta tina da

wannan banzar rayuwar tanq cikin haka saitaji wayarta tana ruri tana dubawa ta saki wani
kayataccen murmushi ta dauka wani kuka ne ya kubuce mata ta ce

My derling bro

Tq faɗa tanq fashewa da kuka ..

Rarrashinta yq fara domin ta saba mishi shagwaɓa duk lokacin da yakirata ,saida yasha aikin
rarrashi sannan ta hakurayake tambayarta me yake damunta kaman zata fada masa abunda
yake damunta saikuma tayi tinani zata iya tayar masa da hankali.shiyasa ta hakura ta boye
masa domin tasan kalar zuciyar yayanta zai iya daukqr mummunan mataki wanda zai kaita ga
shiga fushin ammi hira suka taba kadan sannan yakashe wayar ,sai taji sassauci aranta ba
kaman daba .

Suna zaune a falo suna dan taba hira duk da ba sosai Hafsat take responed ba gaba daya
kwakwalwarta ta cushe ta rasa taya zata bullowa wannan alamari kaman daga sama taji karar
shigowar sako wayarta tana zudewa taga zuwairq ce ta.mata sako kamat haka

Gaskiya.kawata naji dadi sosai kuma na gode miki da kika amince da auren Abdulmallik bansan
da wani baki zan miki godiya ba ki shitya yau.Abdulmallik zqizo kudan fita don ku kara fahimtar
juna

Tsaki tayi wanda ita kanta batasan.tayi tsakinba mamaki take da alajabin wai wacr irin zuciya ce
a kirjin kawar tata anya zuwaira tanada zuciya kuwa ,taya zata fara zaman kishi da zuwaira
tabbas tasan tanada kishi bazata.duba wai don zuwaira kawarta bace babu damuwarta yanzu
zqta.keta mata.rash in mutumci indqi akan abunda zuciyarta take sone amma qi batason
Abdulmallik shit as take gamin bazata taɓa yarda ya zamo mijinta ba.kaman yadda ya cusa
mata bakin ciki itama saita cusa masa koda kuwa zai mutu ne bazata taba.amincewa va ,haka
taita zancen zuci har Ammi ta lura.da condition ɗin da take ciki sunanta ta kira cikin sanyin
murya ta ce

Yanzu Hafsat bazaki cire damuwa a xuciyarki ba kenan kindinga ririta wannan maganar haba
meyasa kikeso kija da ikon Allah kisani komai ya faru dake kaddara ce ta ubangiji babu wanda
ya isa yayi miki abunda Allah bai miki ba don.haka ina mai. baki shawara ida zqku saki jiki ku
fahimci juna to kisaki idan kuma zaki tsaya lusaranci ga fili ga mai doki bazan sakr shiga
wannan maganar ba kinsan dai hukuncin da na yanke

Hawayen dake zuba a idonta ta share ta tashi ta nufi dakinta tai kuka saida ta koshi wani bacci
ya dauketa ,kqman daga sama taji ana knowking kaman bazata budeba kawai ta mike ta bude
Ammi ta gani tsaye tana binta da kallo ta ce

Kinsan kina da bako shine zakizo kihau bacci to maza ki tashi yana jiranki yanzu ki fito

Daga mata kai kawai tayi ta maida marfin kofan ta rufe ,dq badon fishin mahaifiya balai bane a
gareta da wlh bazata fita ba amma babu yadda zatayi dole ta bishi ,ba wani shiri tayiba ta fito
rike da mayafinta a hannunta ko sallama bata yiwa Ammiba ta fita a gidan ,yana jingine a jikin
motarsa yana waina makullin motar kallo daya tayi masa ta dauke kai tazo taja ta tsaya batayi
magana ,murmushi yayi ya ce

Barka da wannan lokaci hjy Hafsat ,kinfito lafiya duk cewa kin shanyani zaman jiranki amma
banga kin jima ba domin na jima ina kallon kifa domin inga takunki mai jan hanka

Hannu ta daga masa ta ce

Wlh Abdulmallik wlh dabadan Ammiba kayi kaɗan in fito wai don kazo saidai kazo ja gaji da
zuwa ka tafi ,kasani bana sonka kuma bazan taɓa sonka ba ,kaine namiji na fako dana tsana a
rayuwata ina mai baka shawar kaje ka samu Ammi kace ka fasa aurena karmuzo munayi
nadama nan gaba

Murmushi yayi ya ce

Shin bakisan kiyayya tana iya komawa soyayya ba kuma soyayya tana iya komawa kiyayya
,don haka a shirya nake domin na karbi kowanni irin hukunci daga gareki ,nasani Hafsat kowani
mataki kika dauka a kaina bazaki huceba domi nasan na kuntata miki na bakanta miki
gwargwadon iyaka amma ina neman yafiyarki kuma ina menan gafarrarki kiyi hakuri ki bani
dama in bayyana miki soyayya ,ki bani dama in goge tabon dana miki ,ki bani dama pls kibani
dama

Tsaki kawai tayi ba tare da tabashi amsa ba wannan Shi ake kira da ihu bayan hari wannan shi
ake cewa nade taburman kunya Allah ya hana ramar da gari zai wayeta kalli Abdulmallik a
matsayin mijinta da takalli wannan ranar gwanda ta mutu inyaso akai masa gawarta cikin
gidansa ,tana cikin wannan zancen zuci taji ya ce
to shikenan tunda yanzu haushina akeji shikenan yanzu kizo muje inkaiki shopping ,pls kibani
dama in kyautata miki koda sau dayane

Waye ni kasani bakada dukiyar da zaka sayeni da ita wlh ,badai ni kace kanason gani a
matsayin mataba to kashirya duj ranar da natare a gidanka to bakinciki kunci da takaici ka
shirya dasu keda kun kulla abota mai karfi ,don kaga tafiyata idan ka gama tsayuwa zaka iya
tafiya .
Tana bude kofar sukayi ido hudu da Ammi tana zaune ta zuba mata idon ka da kanta tayi ta
magana tace

Harkunje siyayyan ne

Shiru tayi ta fara inda inda tace

Zakije ku tafine kokuma sai nadauki mataki akanki

Batayi magana ba ta juya tana fita takallesa ya juya babu shiri ta shiga bayan motar ta zauna
kallonta yayi baiyi magana a yaja motar suka bar gidan ,wani babban mall ya kaita ya ce ta zabi
duk abunda takeso bata kulashiba ta shiga ta fara dauko kayayyaki komai hannunta ya dauka
akai saida ta dauka saida ta cikq basket guda biyu har suka euce kata sannan sukazo akayi bill
suna fita ta tara almajirai d

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login
google.com, pub-9213700357025247, DIRECT, f08c47fec0942fa0