Showing 3001 words to 6000 words out of 23697 words

Chapter 2 - Dangina Book Compelet Secret Pen

01 Sep 2026

271

mata ta fara rabamusu saida ta karar dasu tas sannan ta juyo ta
kalleshi tai tsaki ta nufi bakin titi aikuwa hakan yayi daidai da zuwan me nafef ta shiga saida ta
kusa isa gida ta tsaya a wani dan karamin provision ta siyi kayan ciye ciye ta mishi trnf ta
wayarta sanan ta nufi gida tana zuwa ta ajiye Ammi kayan ta nufi dakinta .


Gaba daya tanajin haushin kanta meyasa ta bishi suka fita ai wanan kaman taci amanar julabib
ne shin idan ranar alƙiyama ta hadu a julabib mezata ce masa shin ta lalata qljannar daya bata
,ce masa zqtayi tayi aure akan nasa me hakan yake nufi wayyo Allah wlh ko duniya zata
tsaneta bazata auri Abdulmallik ba haka ta wuni kuka gaba daya tana cikin damuwar da babu
mai fahimtarta babu wanda zai fahimci halin da take ci


Nifa fans tambayoyina sunfi nqku

Shin meyasa Ammi ta dage akan auren nan duk da yarta bataso

Shin wani abune Abdulmallik yayiwa hafsat data tsaneshi

Shin waye julabib

Shin waye yayanta kuma yana ina

Shin abunda zuwaira takeson hadawa bazai dameta ba kuma kundaiji furcin hafsat

Shin wace Nanna kuma waye danta

Ku biyoni akwai sarkakiya me yawa wanda ni kadai nasan yazan warwareta .

Share pls
*DANGINA*
*[AKA RABANI DASU]*

STORY &WRITEN


BY

ADAMA UMAR
SECRET PEN


07081940768



LOVE AND ROMANTIC STORY

DA SUNAN ALLAH MAI RAHMA MAI JINKAI


3️⃣



PAGE THREE

Yauma kaman kullum suna cikin break a daining abunda zai baku shaawa shine harda Nanna
ake cin abincin( wata xuciyata tana faɗamin wannan nannar tana da wani matsayi a wannan
family),saida kowa ya gama cin abinci Ammi ta kalli nanna batayi magana ba nanna ta fara
tattara kwanuka kallon Hafsat Ammi tayi ta ce
Wato Hafsat bazaki cire wannan damuwar a ranki bako kina dqi ganin halin da muke ciki idan
kikace bazaki auri Abdulmallik ba kinsan wanine zaizo neman aurenki kuma idan suka nemi yan
uwanmu mezqn labarta musu don haka kiyi hakuri da wannan lamari ai auren nan

Waishin Ammi ina yan uwanmu suke ina yan uwan mahaifinmu shidan nasan ya rasu amma ina
iyayensa ina yayyensa ina kawunensa ina baffanunsa washin kema Ammi ina naki yan uwan
suka shiga,meyasa bazqki gabatar damu a garesu ba karki manta mun fuskanci kalubalem
rayuwa kala kala tun muna yara akan gorin asali sannan yanzu ma akan rashin asali zaki aura
mun Abdulmallik umma kodai ta hanyar banzw kika samemune

Tass taji saukar mari a kuncinta wanda hakan ya tilasta mata da yin shiru tanakallon Ammi sa
hawaye ya wanke mata fuska ,kallon Hafsat Ammo tayi ta ce

Idan kika sake tambayata asalina kona mahafinku wlh ban yafe mikiba

Shiru tayi taji duniyar da take ciki ba nata ba ne domin furucin Ammi ya doketa dukar da kanta
tayi tana rushe da kuka Ammi kuwa dakinta ta nufa ta dinga kuka kaman ranta zai fita Nanna ce
ta shigo dakin jikinta a sanyaye domin taji duj hirar da tawanzu a tsakaninsu kusa da Ammi ta
shigo ta fara rarrashinta kafun ammi ta ɗago kanta ta ce
Dama haka alhakin iyaye yake Nanna nasani ko istigifari bazanyiba Alhakin iyayen mune yake
bibiyarmu tundaga kan abunda ya faru da Hafsat nafara gane haka gashi yanzu yara sunzo
kuna tambayata ina yan uwanmu da wani baki zan musu bayani taya zan musu bayanin abunda
muka aikata nida mahaifinsu ,shin wani hali zasu shiga idan sukaji asalinsu wayyo Allah nanna
wlh da rayuwarmu tanada remote dana sarrafa na.maida komai bai faruba

Hawayen dake zuba a fuskar nanna ta share ta ce

Hakane hjy kisani kowa da kalar kaddararsa ki sani wannan itace kaddararki keda alhaji
marigayi ,kuyi neman gafarar Allah zai yafe muku sannan tunda kinga yara sunason sani su
suwaye ayi hakuri a waiwayi gida domin gudun gori

Haka ta dinga rarrashin Ammi kafun ta fito ta nufi dakin Hafsat ,kqman yadda tayi tinani tana
zaune tana rike da hoton julabib tanata kuka karban hoton tayi ta ce

Haba Hafsat yanzu akan wannan magana shine zaki famewa kanki wani ciwon da warke a
zuciyqrki

Rungume nanna tayi ta ce

Meyasa Ammi ta dage akan saian auri Abdulmallik wlh banasonsa nafiso in zauna banyi aureba
ta hakane zan nunawa julabib soyayya ,wlh idan nai aure kaman naci amanarsa ce


Ba haka bane Hafsat ki sani shi kanshi julabib Allah ne ya bamushi amma ya dauke abunsa kiyi
addua Allah yasa son da kikewa julabib yadawo kan Abdulmallik shikenan zaki samu saukin
rayuwa

Shin Nanna bakisan abunda ya shiga tsakanina da Abdulmallik bane

Na sani nasan komai bana bukatar karin bayani kidauka kaman wannan abun bai faruba ,ki
dauka kaman baayi komaiba,ki daukeshi mijin ƙawarki kawai ki aureshi kije kicigaba da ibadar
aurenki ,ki manta da julabib ki manta da wani an halicceshi waishi julabib ki manta kunyi zaman
mata da miji
Haba Nanna kina mahaifiyar julabib kike cewa in manta dashi

Kwarai ki manta dashi duk da cewa nina haifeshi amma nace ki mqnta dashi ,akullum idan na
kalli julabib nakan tina mahaifinsa amma gashi Allah a daukesa ,nashiga kunci sosai amma da
karfin addua Allah yasamun dangana don haka kema ki miƙa alamuranki gurin ubangiji

Hawayenta ta share tayi shiru tana tina rayuwarta da julabib

Flash back
Kwance take akan kirjinsa hannunsa daya akan cikinta ya kalleta ya ce

Baby yanzu zuwa dan lokaci zaki haifa mana baby ko ,wow waya hangoni da baby a hannuna

Juyowa tayi ta shafa gemunsa ta ce

Wlh my bibi koni ina burin Allah ya kaini wannan lokaci kafun Allah ya dau raina

Haba mesa kike fadar haka ai bakisan waye gawar fariba

Hakane bansan waye na farko ba amm da zaa bani zabi zan bada raina ka rayu kaida baby na
nasan zaka kula da Ammina da Nannanmu ga baby na amma ni katafi ka barni bakin cikin
missing ɗinka ma ya isheni nima na bika

Ah yanzu don na mutu kina nufin kema zaki bini ,gaskiya bakimun adalciba abunda nakeso
dake ko bayan raina ki saki ranki kiyi aure kicigaba da walwala ,kiyiwa mijinki biyya kaman
yadda kikemun koma fiye da abunda kikemun

Hawayene suka wanke mata fuska ta ce

Pls my bibi mubar magannan nan don wlh bana tinanin koda halinda zan shiga matikar na
rasaka

Rungumeta yayi yana share mat hawaye ,haka kawai yakeji bazai rayuwa me tsawo tare sa
Hafsat ba ...

Dafata Nanna tayi tai firfigit Ta dawo hayyacinta ta fashe da kuka hakan ya tabbatarwa da
Nanna halin tinanin nata ta shiga ,haka taita rarrashinta har bacci me nauyi ya dauketa Nanna
ta fita ta jawo mata kofar .


Haka ta ta shi jiki babu kwari gaba data.ta rasa ya zatayi ta rushe maganar aurenta DA
abdulmalik haka Ammi taita rarrashinta akan ta amince da maganar auren ,amma gaba daya
batajin zata iyq auren Abdulmallik ,yau ma kaman kullum yasha wanka yazo gidan ya tura baba
me gadi ya kirata babu jimawa ya dawo akan tana zuwa ,ammice ta nufi dqkinta ta shaida mata
ana sallama da ita haka ta fito da hijab ta nufi hanyar waje Ammi ce ta kira sunanta ta juyo ta ce

Waike Hafsat haka zakina zuwa babu ruwan sha

Shiru tayi kafun tai murmushi ta nufi kitchen ,glass cup me kyau ta dauko ta bule bold ta
dumbuli barkwano ta zuba a cup din kafun ta nufi friedge tana zuwa ta zuba exotic a cikin glass
cup din ta fita girgiza kai ammi tai ta ce

Hafsat bazakiyi hankali ba

Tana zuwa yaata baza baki yana gyara zaman hularsa baijira ta masa tayiba ya karba ya ce

Godiyq nqke da alama dai na fara samun shiga tunda har tarbata musamman nake samu

bata kulashi ba don tasan neman magana yake ,kallonta yayi ya ce

Anwuni lafiya kawarmu

Bata kulashiba yayi murmushi yana kai kofin bakinsa da sauri yq furzar jin wani zafin barkwano
ya ratsa bakinsa da makokoronsa kallonta yayi yqga kaman batasan yanayi ba ya ce

Hafsat mena miki haka ,ashe tsanat da kikemun harta kai haka

Kwarqi tafi hakama kuma ta ninka shi sau dubu sabain ,wlh Abdulmallik idan ka aurenitamkar
ka auri tashin hankali ne gidanka da rashin zaman lafiya ,kai bari in fada maka zan iya kasheka
kuma in kashe kaina duk akan wannan lamari

Tabbas Hafsat da na dauka abun naki kaman wasane amma tunda maganar ksa ta shigo ciki ai
lamari ya baci don haka kiyi hakuri idan kika aureni zakiyi farin ciki marar misaltuwa ,zan maye
miki gurbin julabib kai harma na fishi

Wani tsawa ta daka masa ta ce

Karka sake fadan wannan kalma baa halicci wani namiji da zanso sama da julabib ba sannan
baa halicci wanda zausoni sama dashiba ,na yarda an haifeni ne da son julabib bq koya nayiba
,kasani babu wata fuska da natsansna gani sama da taka babu wani gunjin sauti dana tsana
sama da muryarka babu wata mummunan halitta da banason gani sama da kai don haka ka
tattara kabar mana gidan mu tunda gidan bana hadin cinya bane ko

Murmushi yayi ko daya maganganunta basu shigesaba shdai abunda ya sani zata gama bakine
daga baya ta dawo soyayyarsa don haka zai iya kokarinsa yaga ya kafa tutarsa a cikin zuciyarta
ganin yanda ranta ya baci yasa ya shiga motarsa mai gadi ya bude masa ya bar gidan .

Cikin kuka ta koma cikin gida domin ta tina da abun kaunarta julabib .

Tunda ya koma gida gaba daya jikinsa a mace ita kanta zuwaira ta lura da hakan shiyasa ta ke
tambayarsa

Waini dear meya faru ne meke damunka

Kallonta yayi ya ce gaskuya bazan boye miki.ba na janye raga maganar auren Hafsat

What ka janye kuma .......



Share pls
*DANGINA*
*[AKA RABANI DASU]*



STORY &WRITEN


BY

ADAMA UMAR
SECRET PEN


07081940768



LOVE AND ROMANTIC STORY

DA SUNAN ALLAH MAI RAHMA MAI JINKAI


4️⃣



PAGE THREE

Eh Tabbas na janye domin na gaji da fuskantar walakancin dq takemun nibama walakanciba ki
sani duk abunda tamun zan shanye amma bazan juri tana kiran sunan wancan banzan a gaba
na ba kuma koda munyi aure saita kira sunansa don ta bakanta mun rai nikuma wbunda bazan
jura ba kenqn
Haba honey damq na fada maka dole zaka fuskanci matsalloli kala kala karfa ka manta da
babban laifin da kayiwa Hafsat kaine sanadiyar rabatada danta sannan kaine sanadiyar rabata
da mijinta haba ko wannan laifin ta kalleka dashi ai bazata yafema cikin saukiba nidan abunda
nakeso dakai shine dole ka zamabmai juriya a soyayya ,dole ka jure koma meye sanna kai
kokari ka mallaketa ai duk wani qbu da takeyi saboda taga yanzu baa karkashib ikonka take ba
amma kana aurenta kagama da wannqn babin

Shiru yayi yana nazarin maganarta tabbas a zancenta akwai kamshin gaskiya amma taya zan
fara tunkarar Hafsat da maganar aure haka yayi ta sakawa da warwarewa saukar muryarta a
kunnensa ne yasa ya juyo yana sauraron abunda take fada


Nasan tinanin da kake taya zata yadda a fara maganar aurenku ko ,to ba ita zamu tinkara ba
Ammi itace makaminmu da ita zamuyi amfani wajen cin nasarar wannan.yakin

Haka taita nuna masa matakan nasara a aurensu har shimq yq yarda suj warware akan zataje
ta samu Ammi idan ba matslaa manya su shiga lamarin .

Kaman yadda tayi alkawari hakan ta kasance zqune suke ita da ammi tana shaida mata sakon
da Abdulmallik ya turota akan a bashi dama ya turo wakilansa su nema masa auren Hafsat
,Ammi tayi farincikin jin hakqn babu musu ta amince da suturo zuwa anjima zataje ta samu
liman suyi magana ,sannan zuwaira ta karisa dakin Hafsat ,kwance ta sameta tanata sakawa da
warwara domin taji duk abunda su ammi suka fada kenan yanzu idan tayi sanya haka zaa aura
mata wanda bataso anya bazata shiga duniya ba kuwa kowama ya huta to ya ammi zatayi idan
ta shiga duniya.wata zuciyar ta tambayeta saikuma wata ta bata amsa da yazatayi kuma ai
itama haka tayiwa iyayenta tana cikin wqnan zancen ne zuwaira ta shigo dakin bata kalleta ba
balleta mata sannu da zuwa kusa da ita ta zauna ta ce

Haba haba.Hafsat bazaki rungumi kaddara ba ,zaki zauna kiyita zama cikin kunci haba sai kace
akanki akw fara meyasa kike hakane

Dallah rufemun baki munafukq ai nasani duk wannan alamari ke kike daɗa taazzarashi wato
zaa kawo kudin aurena ko to sai ayi auren mugani wlh ko gawata baa ganiba balle akai cikin
gidansa

Subhanallah anya kina cikin hayyacinki kuwa kike irin wannan kalamai ,anya kinsan meyake
futowa daga bakinki ,aure fa akace zaa miki ba wani abu ba kiamince da Abdulmallik zakiji
dadin zama dashi wlh bashida matsala ko kadan matsalarsa daya kuma ke kanki kinsan ya

daina to meya rage dan Allah ina rokonki da ki amince ki yarda

Bangajrta tayi ta fita a dakin ta nufi bangaren Nanna domin ita ta gaji da jin abunda take fada
mata

Kaman yadda aka shirya Ammi ta kira aminan mijinta guda biyu ta sanar musu idan babu
abunda zasuyi gobe zaazo neman auren hafsat dukkansu sunji dadi sunsawa abun albarka .

Washe gari

Da musalin karfe 6:09 na yamma Ta dawo daga makaranta cikin gajiya.ga shegen yunwa dake
ibarta har wani jiri takeji ,gaba daya tayi nadamsr zuwa makaranta don babu abunda ta gane
tsabar damuwa ,shigowa falon tayi ta ajiye hakarta tana kallon Ammita ce

ammi sannu da gida

Yauwa sannu yadai karatunne ya dawo daie haka

Eh wlh ammi gaba daya karatun ya bamu wahala

Ok kije gacab abincinki maza ki dauka

Tashi tayi taje ta dauki abincin ta dawo falo har yawunta tsinkewa yake tsabar yunwa ,kusa da
ammi ta zauna ta fara cin abincin kallonta qmmi tayi ta ce

Yauwa Hafsat dazu DA hantsi magabatan yaron nan sunzo neman aurenki kuma anbasu.har
ansa muku lokaci nan da 2 weeks ga sadakinki ma ankawo

Abincin da takecineya shiga kofofin hancintq aikuwa nan take tari ya sarketa ta fara ba
gaggautawa ruwa ammi tabata sannan tarin ya tsagaita gaba daya idonta sun fito waje tsabar
wahala kallon Ammi tayi ta kalli kudin ta ce

Ammi wani karya naji kunnuwa na sunamun kaman an kawo kudin aurena naji kince kuma da
Abdulmallik

Kwarai ka kuwa kuma auren babu jimawa domin kuba yara bane kuma kunsan juna tunba
yauba

Haba.Ammi wannan wani irin tozarcine ,saikace wata kaza zaku daukeni kubada aurena kuma
nanda sati biyu saikace auren tattabaru gashi yayana baya gari zanyi aure gaskiya ammi bazan
yarda ba

No na kira yayanki shima yana hanya nan da sati daya

Why Ammi meyasa zqki yanke hukunci batare da neman izinina ba kinsan yanzu ni nake da
daman nemaw kaina miji fa

Eh kwarai na sani kuma na zaba miki ,wlh Hafsat idan baki maida hankalinki ki nitsu waje
dayaba zakiga yadda zamuyi nida ke


Tunda Ammi tai mata maganar aure taji abincin ya fita a akanta cikinta ya toshe ko yunwarma
bataji,tashi tayi ta nufi dakinta tai kuka son ronta tana cikin kukw kaman wacce aka mintsina ta
firgita ta tashi dauko daya daga cikin akwatunan ta ta fara zuba kaya a ciki saida ta shirya tsaf
sannan ta ajiye a cikin drower ta dauko babbar jakarta ta zuba wayoyinta da system da charger
saida ta gama hada komai nata ta nufi bandaki tai wanka ta dauro alwala ta fito ta tayar da
sallah ,bata tashi akan dardumanba saida ta gabatar da isha sannan ta koma kan gado tana
saka tana warwara wata zuciyqrta tana shaida mata abunda take shirinyi ba abu me kyqu bane
amma batada mafitar da yawuce haka da tayarda a mata auren dole ya lalata rayuwarta har
abada domin matikar aka mata auren nan shi zaikaita har cikin wutan jahannama domin bazata
bawa mijin hakkinsa ba kuma bazata masa biyayya ba gwanda kawai tayi iya kokarinta kar ayi
auren don matikan akayi auren nan to an lalata mata rayuwa tana cikin wannan tinani taji anyi
knowking izinin shigowa ta bayar tana share hawayenta ,Nannace ta shigo tai murmushi irin
nasu na manya domin taga hawayen da take gogewa kusa da ita ta zauna tana dafa kafadarta
ta ce

Hafsat shin amminki ta sanardake maganar aurenki da akasa nanda kwanaki jalilan

Wani murmushi ta kakalo tayi ta ce

Eh nanna ta fadamun

To wani hukunci kika yanke

Tinanin da nake kenan har yanzu ban yake hukunci ba shawara nakeyi da zuciyata

Kisani ba koda yaushe zuciya take baka shawara mai kyauba ,a wasu lokutan takan baka
marasa kyau don haka inaso kiyi shawara da kwakwalwarki bada zuciyarki ba

Hakane Nanna nagode

Shikenan yanzu qbunda nakeso ki tashi kiyi istihara saiki kwanta Dafatan Allah ya nuna miki
aurenki dashi alkhairine ko kuma akasin haka

Shikenan Nanna in sha Allah zanyu kokarin yin hakan

Mikewa tayi ta nufi bandakin dake cikin dakin

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login
google.com, pub-9213700357025247, DIRECT, f08c47fec0942fa0