Showing 27001 words to 30000 words out of 31845 words
Chapter 10 - Masarautarmu Book 2 Hausa Novels By Takori Kabara
Kuyangi da bayin Fulani duk sun sunkuyar da kai ko motsi sun kasa, sai yanzu suka fahimci
dawa aka daurawa Yarima aure, jikin su yayi matukar sanyi musamman Fanna, hawaye ta
soma na tausayin Sa'ade don bata cancanci aure na rashin kwanciyar hankali irin wannan ba ko
shekaru ashirin bata yi ba.
Saida Ya Gumsu ta tabbatar ta gayawa Bilkisu maganganun da har ta mutu bazata manta ba,
in kuma tana da zuciya to zata karbi 'yar ta daga auren Yarima sannan ta bar falon, duk wannan
bai isheta ba ta so ne Bilkisu ta fito tayi mata dukan da Askirama zai kasa ganeta.
Ita kuwa Sa'ade tana daki a kwance, tun shigowar Ya Gumsu data soma dukan kofar Fulani
ta taka aguje ta shige toilet ta rufe kanta, a zaton ta Ya Gumsu ta samu tabin hankali ne, so
yawancin duk abubuwan da take fada bata ji su ba kasancewar kofar sound proof ce.
Bayan fitar Ya Gumsu data ji shirun yayi yawa sai ta fito, a guje ta nufi kofar Fulani tana kuka
tana rokon ta ta bude. Kome Fulani tayi tunani? Sai kawai ta taso ta bude kofar.
Halin da Sa'ade ta ganta a ciki ya matukar tada hankalinta, fuskarta ta kumbura tayi jazur
idanun ta sun yi luhu-luhu. Sa'ade ta fada jikin Fulani ta wani irin rungumeta tana tambayarta
"dukan ki ta yi? Is she lunatic?"
Duk da halin da Fulani ke ciki sai da Sa'ade ta sanyata murmushi. Ta ja ta suka shige ciki
bayan tasa mukulli ta rufe kofar. Suka zauna a tare a gefen gadon ta.
"Ba duka na tayi ba, zagi na dai kawai tayi saboda an aurawa dan ta 'ya ta".
Innocently Sa'ade tace "to ke ina ruwanki don an yiwa dan ta aure? Ko ke kika ce ayi masa?"
Fulani tayi murmushi ta murza tausasan hannun Sa'ade cikin nata sannan tace.
"Laifi na gareta shine ni na haifi 'yar da Askirama ya aurawa dan nata, bayan wannan bani da
hannu a ciki".
Sa'ade ta yamutse fuska tace "ban gane ba? Zarah ta isa aure ne?"
Kwatakwata ta manta itama 'yar Fulani ce tsabar rudun da kalaman Fulani suka jefa ta".
"Zarah kadai na haifa? Kafun in samu Zarah wa na fara samu?"
Sa'ade ta luluka a duniyar a tunani, ita lallai so take ta canko wa Fulani ta haifa wanda ya isa
aure amma tunanin ta ya kasa bata, domin bata ga marabarta da Zarah ba.
Murmushi Fulani ta sake yi sannan ta rungume Sa'ade, "ki yi hakuri Sa'adatu kin ji? Mun yi
miki laifi daga ni har Askirama, ya nemi alfarmar in bashi ke ya aurawa Yarima nikuma kinsan
bazan iya juya masa baya ba. Tunda daga ni har ke zamansa muke yi cikin gidannan mu abin
ikon sa ne, sannan in da halarci ko mahaukaci Askirama ya kawo yace ki aura daga ni har ke
mun isa mu ce a'ah? Balle dan cikin sa mafi soyuwa a gareshi?"
Sa'ade sauraron ta take absent-mindedly tana hada daya da biyu domin ya bata ma'ana.
Aure.... ita da Yarima......Yarima wanne? YARIMA! Yarima!! Yarima!!! Shikadai ne mai wannan
sunan duk masarautar Askira.
"Don Allah Fulani ki fiddani duhun da kalamanki suka sanya ni.." ta fada cikin karkarwar jiki
data murya. Ta kama hannuwan Fulani biyu ta rike tamau a cikin nata.
Fulani ta ga wannan shine lokaci mafi dacewa da zata gayawa Sa'adatu komai, tunda bakin
alkalami ya riga ya bushe. Tiryan- tiryan ta gaya mata mafarkin da Askirama yayi akan ta da
yadda ya roketa ta bashi aurenta....da kuma auren da aka daura dazu....."Shine fa Ya Gumsu ta
zo tana wannan jidalin". Ita dai Fulani ta san Sa'ade na sauraron ta amma bata san lokacin da
ta fado jikin ta yarab! Cikin hali na unconsciousness......kamar suma, kamar fita hayyaci, cikin
biyun bata san wanne Sa'aden ta ke ciki ba. Sai ta rungumeta tana kuka abin tausayi ta rasa
wane irin taimako ya kamata ta bata....
MASARAUTARMU!
Ba ta taba jin tausayin Saade da soyayyarta ba irin yau, yau din da ta tabbatar sun kusa
rabuwa, rabuwa ba ta aje a dawo ba, aah rabuwa irin ta kowacce diya mace da iyayenta idan
munzalin aure ya riske ta. Fulani ta rasa taimakon da za ta bai wa Saade da ke kwance a jikinta
numfashinta na shirin barin gangar jikinta. Ta san Saade za ta razana in ta ji zancen nan,
amma ba ta zaci har haka ba. Abin da ba ta sani ba shi ne, Saade ta san sirrin Yarima, ta san
na matarsa Aisha-Sultana, tana kyamar dabiunsu na sabon Allah fiye da yadda ba a zato.
Hakan kuma bai hana ta ganin wani irin girman Yareema Sageer ba, da kimarsa cikin idanunta,
saboda iyakar kyautatawa a zamanta tare da su Yareemah ya yi mata.
Amma kalmar AURE a tsakaninsu, ai is underestimated. Wani abu ne da hankalinta da
tunaninta ba zai dauka ba. Kullum kallon kanta ta ke yarinya karama tamkar Zarah. A aura mata
Uncle Yareema ta kai shi ina? Matarshi ta sha giya ta yi mata shegen duka ko kuwa za ta iya
manta kalmar zina' da Sultana ta ce yana yi? Duk da ba ta gama sanin mene ne ainihin maanar
kalmar zina ba, amma ta fahimci wani abu ne mummuna, abin kyamata a addini da alada, kuma
da shi za ta ke kallon Uncle Yareema in har ba ta samu tabbacin ya tuba ya bi Allah ba daga
bakinsa.
Ba ta taba kawo wa ranta aure a nan kusa ba, karatu ta ke so, shi ne kuma burinta, sannan
tana matukar jin dadin abunta, yau da ba Askirama ne da kansa ya yi mata wannan yankan
kaunar ba, cewa za ta yi ba ya kaunarta don ba shi ya haife ta ba.
Amma ta sani, ta kuma amince kaunar da Mai Askira ke mata daga Allah ne. ba zai taba yin
wani abu da niyyar cutar da ita ba, amma har abada zuciyarta ba za ta yi amanna da auren
Uncle Yareema ba. Kamar yadda ba za ta iya karbarsa a matsayin miji ba. Ba gara mata auren
Saidu ba in ma auren ya zama dole? Shi ne tsaran aurenta. Fulani robar ruwan faro ta dauka ta yi ta shafa mata a fuska, wuya zuwa kirjinta. Ba ta fasa
ba sai da ta ji Saade ta saki nannauyar ajiyar zuciya. Ta kara langwabewa a kafadar Fulani ba
ta kara dagowa ba. Duk suka yi shiru cikin wannan yanayin, kowanne da abin da yake sakawa
a zuciyarsa. Zuwa can Saade ta yi magana a hankali.
Ni bana son Uncle Yareema Fulani, kamar yadda Mamanshi ba ta sonki. Ki ba wa
Maimartaba hakuri, ba zan iya ba.
Ta soma wani irin kuka a hankali mai girgiza zuciyar mai sauraro, balle kuma zuciyar UWA!
Sosai kukan na Saade yake motsa zuciyarta. Ta shafa kwantaccen gashin kan Saade da
hannun damanta ta ce.
Saadatu, me zan yi in faranta miki? Ki fadi ko mene ne, amma ban da cewa ba za ki yi auren
nan ba. Bakin alkalami ya riga ya bushe. Laifi kan laifi mun yi miki ni da Askirama, ina rokonki ki
dubi Allah da darajar da Allah ya bai wa iyaye a kan yayansu, ki dubi karamcin mai Askira gare
ki ki yi hakuri ki yi hakuri ki yi hakuri ki bar wa Allah komai. Saade ta ce, Ta ya ya zan zauna da shi mahaifiyarshi ba ta sonki? Ni ma bana sonshi,
matarsa ba ta sona. Komai na rayuwarsu daban yake da tawa. Fulani yadda ake shan ruwa a
firji haka ake shan giya a gidan nan kuma kuma Ta kasa cewa ZINA don sai ta ji kalmar ta yi
gundumemiya a bakinta ta alakanta ta da Uncle Yareema, saboda cikar kamalarsa da cikar
zatinsa kadai yana hanawa ka alakanta shi da kowanne irin aibi
Kin taba jin kishiya ta so kishiya ne Saade? Don haka ki cire wa kanki damuwar wai Gumsu
ba ta sona. Yanzu matsayin uwar miji ta ke a gare ki, ki yi duk iya yadda za ki iya wajen
kyautata mata. Sauran lamarin sai ki bar wa Allah.
“But I dont love him Fulani, ina da saurayi na dan ajinmu da na ke so, sunansa Saidu
Ki san abin da za ki dinga fada, don ke matar aure ce yanzu. Mace kuma addini bai bata
damar ta so kowa ba ko da kuwa da fatar baki ne sai mijin aurenta. Ki gaya min me ki ke so in yi
miki in faranta miki ki saki ranki ki manta da komai? Ki sa a ranki babu wani bambanci tsakanin
rayuwarki ta da da ta yanzu. As if normally makaranta za ki koma ki ci gaba da karatu, ni kuma
zan tsaya in ga cewa Yareema bai hada ki gida daya da Aisha-Sultana ba, kin san yana jin
maganata. Sannan zan roke shi ya daga miki kafa har ki kare karatu, in ba zai iya hakan ba ya
kara mata ta uku.
Saade kamar ta fashe da kuka saboda ita yanzu ko sunan Yareema ba ta son ji. Ya shigo
rayuwarta unexpectedly ya rusa ta. Duk burinta na yin karatu mai zurfi ba a yi shawara da ita ba
an kakaba mata aurensa. Yariman da ta tabbata yana neman mata.
Laifin me ta yi wa Fulani da Askirama da zasu rasa wanda zasu aura mata sai Yarima
Sageer?
Ta mike za ta bar dakin idon ta fal hawaye Fulani ta sake riko ta tana murmushi.
Ba ki gaya min me zan yi miki ba a matsayin gift dina na aurenki.
Saade ta ce, Fulani ni me ye nawa a ciki da har sai an ba ni gift? Ai ba'a nemi yardata ba
kafin a daura don haka bana bukatar kowanne gift din ki
Fulani ta danne dariyarta duk wani tension da ta ke ciki shirmen Saade ya sa ya tafi, ta ce,
matsayinki na babbar kanwar ango.
Saade ta kyabe baki ta ce, Yana da kannensa su Humaira yan gayu, ni in kina so ki faranta
min kawai ki sa a kai ni Tsanyawa in ga Hanne da Innarta, Baba Saleh da Inna Laure.
Ta yi ficewarta zuwa nata dakin, ta bar Fulani cikin tunani.
Hakika ta yi kuskure da ba ta kara kai Saade Tsanyawa ba, wajen bayin Allahn da suka sada
ta da ita. Da kuma matar babanta, duk da Saade ta ce ba zaman dadi suka yi ba, amma dai ai
ta rike ta komai lalacewar riko a lokacin da ita ta yasar da ita. Ta kudire a ranta za ta faranta wa
Saade da wannan kuma za ta nemo mata wan mahaifinta Kyari da yarsa Rahima kawarta duk
da ba ta da tabbacin da gaske Rahima yar Kyari ce ko ko kamanni ne kawai da suna ya zo
daya.
A take ta kira Askirama a waya kasancewar ba girkinta ba ne. Ta gaya masa tunanin da ta yi,
ya ce shi kuma ba zai kai Saade gidan Yarima ba sai ya nemo Babagana Kyari, sai ya aika an
dauko Baba Saleh da iyalinsa don ya tabbatar wa Ya Gumsu cewa, Saade da asalinta. Ba don
ya sassauta kiyayyarta ga auren ko ga Saade ba, sai don ya cika farin cikin Bilkisu da yarta. A koina Mai Askira yana da mutane, daga bayanin unguwar da Kyari ya zauna a Damaturu
daga bakin Fulani ya bi ya dinga tracing labarin Babagana Kyari. Mutanen unguwar suka
tabbatar masa Kyari da iyalinsa sun dade da barin Damaturu zuwa garin Maiduguri inda
Babagana Kyari ke kasuwancinsa na fata, har gidansa na Maiduguri sai da aka binciko, inda
makwabtansa suka tabbatar da cewa Kyari da iyalinsa suna kasar Italy kwata-kwata inda yake
sanaar kai fatu.
Mai Askira bai gushe da ci gaba da tracing Kyari ba har sai da wani abokinsa ya bada lambar
wayarsa ta kasar Italy, kuma a daren shi da fulani suka yi zaman kiran Kyari Babagana inda
suka yi magana a handsfree baki da baki shi da Bilkisu.
Ta cikin wayar Kyari yake kuka da ya ji mutuwar dan uwansa Hashimu, ya ce Ba yadda ban
yi da shi ba ya dawo gida ya ki, wai tunda kin guje shi ba shi ba Damaturu. Na ce ya ba ni yar in
rika, Hashimu ya ce mai raba shi da yarki sai mutuwa. Ashe kuwa ita din ce za ta raba su, daga
baya na bi bayansa har Kano inda ku ka zauna ban tadda shi ba, aka ce bayan kun rabu ya
koma wani kauye da yarshi, kauyen da har yau nake bincike Allah bai ba ni ikon sani ba.
Ina fatan yar tawa tana lafiya, kuma ya ya sunanta?
Fulani ta gaya masa sunanta Saadatu, sannan cikin jin kunya ta ce, Mai Askira ya daura
mata aure jiya, da Dan wajensa Yareema Sageer.
Askirama ya karbi maganar da cewa, Ka yi hakuri na yi maka shisshigi, ya kamata a ce ni na
fara nemo ka kafin daurin auren hikimar hakan ba ta zo min ba har sai da Fulani ta ankarar da
ni. Ka yi hakuri, ka yi hakuri, na yi gaggawa ga sadakinta nan na damka wa Bilkisu na
warawaran danyar gwal guda shida. Alhaji Kyari Babagana ya yi murmushi, ya ce, Its a pleasure meeting you your Royal
Highness the Emir of Askira. A yi min alfarmar kara sati daya kafin a yi bikin yata Saadatu, don
ni da uwarta da yan uwanta mu samu halarta.
Da sauri Askirama ya ce, An yi wannan alfarmar, na sanya har sati biyu biki da tarewa, don
bikin da ban yi a auren Yarima na farko ba shi zan yi a yanzu, tunda yanzu ne na san Yarima ya
yi aure irin wanda hankalina ya kwanta da shi, kuma na yarda da shi. Matarshi ta farko daga
Asia ya kawo ta. Sun dade suna tsara abubuwa na yadda bikin Saadatu da Yarima Sageer zai kasance kafin
su yi sallama.
Maimartaba ya dubi Fulani tana hamma, ya ce, me ya hada ki da Gumsun gari? An gaya min
wasu maganganu marasa dadi wadanda ban yi zato daga gare ku ba.
Fulani ta tabbatar ba wanda zai kawo wannan gulmar sai Fulani Hibbani uwar tsugudidi, Allah
kadai ya san iya abin da ta gaya masa. Ta yi kwafa sannan ta ce, Ni da idanuna ban ga Ya
Gumsu ba, kusan watanni shidda kenan. Amma na ji an ce ta zo nemana ina barci. Bayan
wannan ban san wani ba kuma. Maimartaba ya jinjina kai, amma bai ce komai ba. Ya san Bilkisu ba za ta yi masa karya ba,
amma maganganun da Hibbani ta gaya masa sun tayar masa da hankali. Cewa ta yi, Ya
Gumsu da Bilkisu sun yi dambe a gaban bayinsu da kuyangi. Bai yi wa Gumsu maganar ba don
tun artabunsu akan maganar auren rabonta da sake tako kafarta turakarsa. Yanzu abin da ya sa a gaba shi ne, ta yadda zai fuskanci Yarima da maganar, ya hana
Awaisu gaya masa, ya ce shi da bakinsa zai gaya masa ta hanyar da za ya fahimta.
Yarima bai san wainar da ake toyawa ba, domin bayan rabuwarsu da Awaisu a ranar
Maiduguri ya tafi, akwai wani project da yake rubutawa zai yi bincike a UNIMAID, wanda zai
dauke shi har tsayin kwanaki uku. Bincike ne da yake bukatar nutsuwa (applied research) a
fanninsa don haka ya kashe wayarsa. A daren ranar aka yi ta tura masa text na taya murna da fatan alkhairi ba tare da ya sani ba,
don duk wayoyinsa ya kashe su. Ya tattara hankalinsa kan abin da yake yi, yana gidan saukar
baki na jamiar Maiduguri.
Awaisu ne kadai ya san inda yake. Kwanansa biyu kawai sai ga Awaisu. Har masaukinsa ya
je, Yarima zaune cikin tattausar kujerar leather ta falon masaukinsa yana kurbar lemun Don
Simon a cikin tambulan, ya dubi Awaisu wanda bakinsa ke ta motsi yana yan mutsu-mutsu
wadanda Yarima ya riga ya gama gane su. Akwai abin da ke faruwa wanda ba ya son gaya
masa idan yana irin wannan mutsu-mutsun.
“You better be comfortable, wannan mutsu-mutsun naka da magana
Dariya Awaisu ya yi ya ce, Me ya samu wayoyinka na kasa samunka? Shi ya sa fa na zo da
kaina.
Tunda na zo ban kunna su ba, ina da muhimmin project a gabana, amma dama yanzu zan
dan kunna in ji lafiyar Saadatu. Tunda muka zo ba mu kara haduwa ba, kuma ni nan da kwana
uku zan koma Abuja, ina so in ji yaushe za ta koma sai in dawo in dauke ta.
Awaisu ya tsura masa ido yana son karantar wani abu game da shi a kan Saaden, bai fahimci
komai ba, ban da seriousness irin