Showing 18001 words to 21000 words out of 31845 words

Chapter 7 - Masarautarmu Book 2 Hausa Novels By Takori Kabara

Ta bata lokaci kafin ta fito cikin shigar atampa hiterget, suka tafi zuwa Nizamiye Hospital inda
suke da file.
Da tana da yadda zata hana zuwa asibitinnan da ta yi, amma yadda ta ga fuskar Yarima ta
san babu wani excuse da zai karba, fargabar dake ranta kadai ta isheta don bata taba zaton
watarana Yarima zai taba sha'awar haihuwa ba. Ita kuma duk son da take masa bata shirya
haihuwa da bakar fata ba, ta aure shi ne domin ya dinga satisfying soyayyar da take masa ba
don su tara 'ya 'ya ba.
A gaban sa likita ya duba ta, tayi fuska kamar bata san abinda ta aikata ba, ya kuma
tabbatarwa Yarima Sageer babu mahaifa ma a jikin matar sa, an cire ta gabadaya.
Yarima ya daga kai yana kallon Sultana wadda ta sunkuyar da kai, girar idon sa har wani irin
tattarewa take yi sabida bacin rai, har suka zo gida bai iya ya ce mata komai ba.
Suna shigowa gida kowa ya nufi dakin sa rai a bace. Har zai wuce daki yayi tozali da abincin
da Sa'ade ta shirya masa akan dining, ya kuma jiyo kamar jan majina irin na kuka da

sheshsheka daga dakin nata. Sai ya ji bazai iya wucewa ba tareda ya dubata ba, haka yau
bacin rai bazai bar shi ya iya cin abincin ta ba.
Knocking yayi mata har sau biyu, daga ciki ta amsa cikin dusashshiyar muryar data ci kuka.
"Waye anan?"
"Sunana Sagir"
Murmushi tayi sabida yadda ya fadi sunan cikin lallashi? Ta taso ta bude kofar, tareda dan ja
da baya don ta bashi damar shigowa.
Cikin idanunta ya kalla, wadanda suka kada zuwa brown, "kukan me kike yi?" Akwai alamun
hankalin sa ya tashi da ganin halin da take ciki, ai kamar jira take ya tambaya sai ta idasa
rushewa da kuka.
Da kyar Yarima ya samu tayi shiru, sannan ta rufe ido ta gaya masa ta fadi kwas din
Physiology shine dalilin kukan ta.
Ajiyar zuciya ta kwacewa Yarima, ya dauka wani abu ne terrible. Kai Sa'adatu 'yar maman ta.
"Do you have issue with some of your courses baki taba gaya mun ba?" "Ai Fulani ce ta ce kada
mu dinga hira" dariya ta kama shi sabida wautar ta data fito fili a yayin maganar. Ya tako zuwa
gaban ta, gab da ita ya tsaya duk invictus ya mamaye ta. She can feels him breathing softly....
"gaya min abinda yasa Fulani ta ce kada mu dinga hira" gabadaya ta daburce ta kuma ga
wautar kanta data fada masa hakan. Sannan bai bada space a tsakanin su wanda zata yi masa
musu ba.
Da sauri ta ja baya, amma sai taji bayan ta ya hadu da kofar dakin "umh...umh nima ban sani
ba Uncle Sageer" "ni na sani, in kin amince in gaya miki....." da sauri Sa'ade ta girgiza kai "don
Allah kada ka gaya min ni ba son sani nake ba" ta fada, her voice trembling. Kai gabadaya
tsokar zuciyar ta ma rawa take sabida closeness din dake tsakanin su da kamshin Paco
Rabbanne da yake hargitsa ta.
A hankali ya ja da baya yana murmushi yace "ki ce ma Fulani, ai mutum baya cutar da
abinda yake so ya zama nasa gabadaya. Ta bar ki kiyi hira da Yayanki. Fi-amanallah, har zuwa
lokacin da zai dau ajiyar da ya bata".
Bata gane zaurancen sa ba amma ta ce "toh" da sauri don ta samu ya bar ta haka, tayi jinyar
sababbin abubuwan da ke ziyartar ta, a zuciya, ruhi da gangar jiki gabadaya.
"Gobe zamu fara karatu ni da ke, physiology will never fail you again. Na bar ki lafiya".
Har ya fita bata san meyasa ta kasa dauke ido akan sa ba, al'amuran sa na yau masu ban
mamaki ne data kasa gane inda yasa gaba.
A hankali tabi lafiyar gadon ta, ta lumshe ido tana tariyo maganganun Yarima Sageer daya
bayan daya. In wani yace mata yana magana haka zata karyata. To me ya canza shi haka? Me
ya kawo canjin? Sai dai kuma ga mamakin ta ta kasa kiran Fulani ta gaya mata abinda yace din
duk da bata iya boye mata komai. Amma wannan karon sai ta ji ta kasa. Kamar tana jin
kunya.... Kamar yadda barci ma ya gagare ta. Sai scenes din Uncle Yareema ke mata gifcin
gizon makauniya.
****

Washegari da safe basu hadu ba, kowa ya kama gaban sa, cikin daren an tafka rigima
tsakanin Yarima da maidakin sa Aisha-Sultana, yace tunda ta yaudareshi ta cire mahaifarta ba
da sanin sa ba tasa a ranta ta bashi lasisin auren wadda zata haifa masa 'ya'ya.
Sultana ta dauki kalaman nasa a matsayin abinda ake kira 'shifcin gizo', watakila ya fada ne
out of frustration na ta cire mahaifa, amma in ma mafarki yake na zai hada ta da wata diya
mace a duniya su yi sharing din sa ya dade bai farka ba. Lokuta da dama in a buge take bata
mayar masa da magana, tana bin shi da ido ne kawai. Wadanda basa ko buduwa sosai. To yau
ma hakan ta bishi da rinannun idanun ta har ya shige turakar sa.
Zaune take akan irin kujerun sumintin nan na cikin makaranta karkashin wata bishiyar lemon
tsami mai duhun ganyayyaki, fitowarta kenan daga lacca ta zauna tana kara nazarin abinda tayi
jotting cikin littafinta. Sallama ta ji a kanta da wata lallausar murya kamar ba ta namiji ba, da
sauri ta dago ta kalli wanda ke tsaye a kanta, kallo daya tayi masa ta gane shi, coursemate
dinta ne amma bata san sunan shi ba. Ta amsa sallamar sa tare da maida kanta kan littafin ta,
yaron ya cika kyau kamar aljani, da ganin sa ruwa biyu ne ko kuma bafillace. Cikin lallausar
turancin sa ya ce "Ma'am, ki taimaka min da laccar da kika rubuta inyi photocopying, i missed
alot from it" Sa'ade ta zumburo baki "bana bada aron littafi na" murmushi yayi ba tareda ya ji
haushin abinda tace ba, kawai sai ya sa hannu ya dau littafin daga cinyarta ya juya ya soma
tafiya.
Sa'ade ta mike da sauri ta bi bayan shi tana fadin "Malam...malam" "sunana Mr. Sa'id ba
malam ba" "to ni ina ruwa na da sunan ka? Ka bani littafi na" yayi kamar bai ji ta ba, ya nufi wani
shago da suke photocopying, Sa'ade bata yi kasa a gwiwa ba wajen binsa tana ta mita "haka
kawai sai ka daukar mun abu ba izni babu yardata? Don baka san wanene Yayana a jami'ar
nan ba wallahi sai na sa an baka carry-over" bai san sanda dariya ta kubuce masa ba data fiddo
fararen hakoransa, yarinyar akwai wauta kamar diyar fari ga magana cikin shagwaba.
Ya hadiye dariyarsa ya mika wa mai hoton takarda littafin ya fada masa yayi masa photocopy
sannan ya juyo ya dubeta da wani irin kallo. "A'a spill-over zaki sa a bani ba carry-over ba.
Sa'adatu Hashim I loved to be your friend" zaro ido tayi na mamakin inda ya san sunan ta, sai ta
tuna a jikin littafin ya gani, ta kyabe baki tace. "Allah ya sawake in yi abota da namiji, matan ma sun ishe ni kallo ne balle kai sungumemen
kato?" Yayi dariya yace "ko sai na yi kamun kafa da Yayanki mai jami'a?" Wani kallo tayi masa
na sannu sarkin tsautsayi, sannan ta juya tana cewa.
"In ka so ka kwada littafin ka cinye na bar maka".
Ta kama hanyar komawa hall.
Tana zama laccara na shigowa suka fara karatu, sai ga wanda ya kira kansa Mr. Sa'idu ya zo
ya zauna a gefenta, a hankali ya ajiye mata littafin ta yana murmushi, a ranta tace sai shegen
murmushi kamar gonar auduga, jan aji da class sai Uncle Yariman Askira, kafin yayi murmushi
ma za'a dade. Amma shi wannan sai faman murmushi yake kamar mace. Wata zuciyar tace

Sa'ade! Me kike cewa? Da sauri ta ce "ba abinda nace kenan ba, nufi na Uncle Yarima yafi
kowa jan aji a duniya" ta kara ankara da kalar tunanin da take yi tayi saurin toshe bakin ta tare
da dafe kanta tana fadin "Yaa Ilaahy! Na tuba ya Allah!" Bata san cewa a fili ta fada ba.
Kowa a ajin sai da ya juyo ya dube ta, kasancewar an yi tsit ne ana sauraron malamin. Tayi
maza ta sunkuyar da kanta tana fadin meke damu na ne? Ni Sa'aden Tsanyawa? Ba komai
bane sai tunanin Yarima Sageer Yusuf Askira. Wanda ya dusar da hasken sauran maza daga
idanun ta, ya dasa wani dan kankanin tsiro a zuciyarta daga lokacin da bazata iya tantancewa
ba.
Sa'id bai bar Sa'ade ba, tun daga ranar ya like mata, inda duk tasa kafa cikin NTNU nan yake
mayar da tasa. Ba da sanin ta ba ma ya bi bayansu a mota itada Salis bayan sun tashi karatun
ranar ya ga gidansu cikin quaters ne, nan ya tabbatar 'yar wani babban Dr. Din ce kamar yadda
tayi masa barazana. Kodayake ta ce Yayanta. Tun tana basar da shi amma yawan hakurin sa
da yawan murmushin sa yasa dole ta soma kula shi suke harkar karatun su tare. Dama tana
neman abokin karatu kuma ajin nasu maza sunfi yawa, tsirarun matan dake ajin kabilu ne.
Tun ranar da Yarima yace zai fara koya mata karatu kuma tafiya ta kama shi zuwa Lagos
(Lagos State University) zai halarci annual conference. Basu kara haduwa ba sai yau da ya
dawo, kuma Uche ma ya dawo daga Osun, tayi masa ta'aziyar mahaifiyar sa ta shige dakin ta a
ranta tana fadin "shikenan na huta da girkau, wahalar da ba'a ce min an gode". Uche yana tsaye yana girki ta shigo kitchen din, ruwa take so ta sha, na firjin dakin ta duk sun
kare. Ta bude firij din kitchen din tana fadin "Uche what are you cooking for your Oga?" Uche ya
ce "Basmati Rice and salad nake yi masa, ban sani ba ko zai so" tace "kada kasa spices din
can da kake using, kayi amfani da rosemary, coriander da oregano, basu da karfi, he really likes
their aroma". Uche yayi godiya da gyaran data yi masa.
Ta bude firji babu ruwan gora sai wasu manyan kwalabe, an cire takardun jiki babu rubutun
komai, Uche ya bata baya yana yankan albasa bai lura da abinda take ba, ta dauka tana juyawa
a hannun ta sannan ta bincire murfin zata kai bakin ta. Sai ji tayi an yi wurgi da kwalbar daga
hannun ta, ita kanta saura kadan ta fadi sabida yadda Yarima ya angije hannun ta da karfi. Kwalbar ta fashe, ruwan ciki ya malala a kasa, wani ruwa mai wani irin tsami da hamami,
Yarima bai tsaya ba ya finciki hannun ta suka bar kitchen din yana ce da Uche ya gyara wurin
ya fitarda duka whisky daga firinjin ya zuba a bola.
Bai tsaya da ita koina ba sai a falo ya jefata jikin Aisha-Sultana, wadda ke zaune tana danna
ipad din ta. Ta dago a fusace sai idon ta cikin na Yarima, yadda ta ga idanun sa kamar na
mayunwacin zaki ya kada mata 'ya'yan hanji. Muryarsa har sarkewa take ya ce "Sultana! Ban
hanaki shigomin da giya gida ba? Ko kin san saura kadan yarinyar nan ta sha giyar ki? Me kike
so in cewa iyayenta da ace ta sha da suka damka min amanar ta? Kuma har a firinjin kichin
sabida kin raina ni?"
Sultana tayi mici-mici da brownish idanunta, "cewa nake mun yi da kai sai ka daina shiga
gidan Ziyad yin zina nima zan daina shan beer?"
Da sauri Yarima ya nunawa Sa'ade hanya yace ta bace a wurin kafin ya kifta idon sa. Ai kuwa
kafin ya kifta din ta kai kofar dakin ta tana jin karar marin da ya kaiwa Sultana. Ta dafe kunci ta
ce "you slapped me?" Bai tsaya a wurin ba ya danna kai dakin ta ya watso su duk daga firinjin
ta, ya kwalawa Uche wani mahaukacin kira, ya fito da gudu daga kitchen yana amsawa, ya
nuna masa dakin Sultana yace ya kwashe whisky ya je ya zubar gabadaya.

Yau Sa'ade ta ga tashin hankali don har dare ya tsala tana jiyo fadan Yarima da matar sa har
tissue tasa ta toshe kunnuwan ta tana kuka, marin da ya yiwa Sultana ya daga mata hankali ba
kadan ba, ita bata san giya bace kuma ba sha zata yi ba sunsunawa zata yi taji menene? Sai
Allah ya kawo shi. Tana so ta kira Fulani ta gaya mata ta tuna abinda Fulani ta gaya mata
wancan karon cewa maimartaba ya ji wayar su, har yace zai dau mataki akan Yarima. Ina ga in
ya ji ana shan giya kamar ruwa a gidan sa? Wa'iyazu billah.
Ko isashshen barci bata samu ba yau, don haka washegari ko karin kumallo bata tsaya yi ba
ta riga kowa ficewa a gidan ko Salis bata jira ba, duk nisan dake tsakanin gidan su da cikin
makaranta ta gwammace ta taka a kasa data kara ganin fuskar Yarima mai zuwa yin zina ko
matarsa mai shan giya kamar yadda suke cewa. Sa'idu ya ganta duk a birkice, ya bata wuri ta zauna, "hi friendy, me ya sameki haka?" Kawai
sai ta saka kuka tace "don Allah ka san inda ake shiga motar Askira?" Ya ce "ni ko sunan garin
ban taba ji ba" ta sake rushewa da kuka, yayi-yayi ta gaya masa abinda aka yi mata ta ki, har
malamin su ya shigo suka fara darasi, dole ta tsagaita da kukan ta bashi hankalin ta, don inda
abinda ta ki jini a duniya to carryover ne.
Da wuri suka gama lacca yau, tace da Sa'idu gida zata koma, da in sun gama lacca da wuri
maimakon su tafi gida lab suke zuwa suyi research da ya shafi karatun su, yace ina direban ta
tace ba shi ya kawo ta ba da kafarta ta taho, kuma ta baro wayarta gida balle ta kira shi ta gaya
masa inda take. Sa'idu yace "do me a favour to drop you at home, tunda naji kina zancen zuwa
Askira bazan barki ki tafi ke kadai ba".
Ya dage da nacin sai ya kaita, ta san Sa'idu zuwa yanzu yaron kirki ne mai kokari da son
taimakon ta, don haka ta amince ta shiga motar sa kirar civic suka karasa gida.
Sa'idu na yin parking daidai Yarima ya zura mukulli jikin motar sa zai bude, yayi mugun
hadewa cikin danyar shaddah ruwan madara samfurin excelcior (London). Wadda ta sha aiki
da zare ruwan kasa irin na sarauta. Gilashin idonsa ya zare a hankali don tabbatar da Sa'ade ce
yake gani a motar wani ko wacece? Fasa bude motar yayi ya kafa musu manyan lumsassun
idon sa har Sa'idu ya kashe motar Sa'ade ta bude ta fito tana masa godiya. Sa'idu ya so ya fito
ya gaida Yayan Sa'ade amma yadda yaga fuskarsa kamar hadarin da ya nausa yayi gabas dole
ya kama kansa, ya ja motar sa da gudu ya bar harabar gidan don kwarjinin Yarima da haibar sa
da cikar kamalar sa kadai ya tabbatar masa ba karamin mutum bane, kada yaje ya gane shi ma
wani abu ya samu karatun sa, duk da ya so ya fito ya gaisheshi ya gaya masa taimaka mata
kawai yayi shi dan ajin su ne, amma ina! Tsoro ya hana shi. Makarantar ma bai koma ba ya
gudu gidan su a unguwar Maitama.
Ta gaban sa Sa'ade ta zo ta wuce amma ga mamakin sa ko kallon sa bata yi ba ta wuce ciki.
Mamaki ya kusan kayar da shi, bin bayan ta yayi cikin takunsa na kasaita. Tana saka kafa a
dakinta ta turo kofar yasa hannu ya dafe kofar.
Sai ta sakar masa, ta juya ciki ta na kokarin sauke jakar dake goye a bayan ta wadda ta
lamushe dukkan komatsanta harda laptop.
Muryar Yarima har tsakar kanta, babu alamun wasa ko kadan a tattare da shi. Zata iya
rantsewa bata taba jin sa yayi magana da irin wannan muryar ba. So furious, angry and
jeolous.....!
"Sa'adatu who is this boy?"
Bata san yaya aka yi ba, bata san wa ya kitsa mata ba, kawai sai ta samu bakin ta da cewa

"saurayi na ne" bayan ita kanta bata gama sanin ma'anar kalmar saurayin ba. Kawai ta san ta
tsani Uncle Yarima ne yanzu, tunda dukan matar sa yake yi, in ta sha giya ai shi ya bata dama.
Idanunsa sun rikide sun juye zuwa wani yanayi da bazata iya fassarawa ba. "Look into my
eyes...and tell me he's your boy friend" kokarin ja da baya take. Data rasa mafita, ga zuciyarta
na wani irin azalzala da mixed feelings; haushi, tsana, da zazzafar soyayyah duka a lokaci
daya, kawai sai ta saka kuka.
"Ni dai a

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login