Showing 24001 words to 27000 words out of 31845 words

Chapter 9 - Masarautarmu Book 2 Hausa Novels By Takori Kabara

kafin su koma hutun nan da suka zo sai da igiyar aure a tsakanin
su.
Sa'ade ta lura a wunin ranar bakidaya Fulani ta zama sukuku! Bata umh bata umh umh.
Abinci wannan a wunin yau bata ci shi ba kuma tace ba azumi take ba. Ta lura tunda ta dawo
daga turakar maigidanta take cikin wannan halin, to ko ita da Mai Askira ne suka samu sabani?
Saidai hakan mawuyaci ne don bata taba ganin ma'aurata masu fahimtar juna kamar su ba. Sai itama ta shiga damuwa, damuwar uwarka ai yana nufin taka damuwar. Damuwar Fulani
shine bata san ta ina zata farawa Sa'ade zancen aure ba, she's too young and innocent, auren
ma kuma da Yarima Sageer, wanda ta riga ta gama sanin sirrin su shi da matar sa, ta kuma
dauke shi matsayin guardian dinta. Sama da komai bata taba tunanin yiwa Sa'ade aure nan
kusa ba, ta so sai ta gama karatun ta, to kana naka Allah na nasa kuma nasan shine gaskiya.
Sa'ade sai zarya take tsakanin dakin ta dana Fulani very disturbed, ko Fulani zata kira ta tace
zo kiji damuwata, amma Fulani ko kallon ta ta kasa yi, ji take kamar ta yi ba daidai ba ta kuma yi
mata laifi data karba mata zancen aure bada sanin ta ba. Ba jimawa jikin ta ya dau dumi, data
tuno me ake yi a gidan Yarima Sageer "Zina da Shan giya". Ba ga matar ba ba ga mijin ba

kowanne shegen kansa ne, ta dauki innocent 'yar ta ta kai musu, matar ta sha giya ta rotsa
mata kai, ko mijin yayo zinarsa ya goga mata cuta?
Amma kuma wanene Yarima? Dan Askirama mafi soyuwa a gare shi. Askiraman da ya
maida Sa'aden mutum a lokacin da ita ta kasa karbar ta. Wannan damuwa a take ta kwantar da
Fulani Bilkisu, amma sai ta mike tana rangaji ta sawa kofar ta mukulli kada Sa'ade ko Fanna su
zo su dameta. ****
Ya Gumsu na tareda mai Askira a washegari, itace tayi turaka kuma itace zata wuni tare da
shi a wunin yau da baya fita fada, duk ranar Jumaah daga ya dawo masallaci sallahr jumaah
baya kara fita, yana zama ne ya ribaci yammacin da ibada musamman karatun Suratul-Kahfi da
suratul Mulk, Yaasin da Waqi'ah. Sannan yana karanta Suratul Nouh kafa 41 a kowanne
yammacin Juma'ah.
Tana hada masa shayi a cikin kofi (mug) ya dubeta da murmushi. Ya ce "Gumsun Askira,
Uwargidan mai Askira....inada wani kyakkyawan albishir dauke a bakin nan nawa". Ya Gumsu
ta karkace ta gyara zama bisa tattausar dardumar da maimartaba ke zaune har da tattara
dukkan nutsuwar ta ta bashi, a zaton ta albishir zai mata da tafiyar su wata kasar su huta. Amma abinda mai Askira ya fada bata taba jin abinda ya girgiza zuciyarta da rayuwarta
bakidaya irin sa ba. Ya jirkita kwanyarta, ya gusar da annurin fuskarta nan take ya mayeshi da
wani mummunan bacin rai da Askirama ko wani mahaluki bai taba gani a kan fuskarta ba.
"Kwanaki uku masu zuwa zan daura auren Yarima da Sa'adatu!"
Amma Ya Gumsu sai ran ta ya bata gara ta tambayeshi don ya tantance mata wace
Sa'adatun yake nufi? Don haka ta hadiye komai cikin laluma ta tambayeshi.
"Allah ya taimaki Giwan Askira, ko zan iya sanin wacece Sa'adatun?"
"'Yar ku Sa'adatu wadda yake riko a gidan sa ta wajen Fulani Bilkisu......".
Ai bai karasa ba sai ganin Ya Gumsu yayi tsaye a kansa, idanun ta a warwaje tana huci, yau
da ba shi ne sarkin Askira ba, da ba shine uban 'ya'yan ta ba, furfurarsa ko wannan himilin
rawanin nasa bai hanawa ta kwashe shi da mari.
"Idan wasa kuke..... Allah ya taimake ku ku bari, bana son irin wannan wasan....." cikin
mamaki Askirama ke kallon ta baki a bude, ya dauka wannan karon farin ciki zata yi da zabin da
yayiwa Yarima, shi da take fushin ya auri mai jajayen kunnuwa mara addini, ga wadda suka san
asalin ta suka san addinin ta suka bata tarbiyya cikin gidan amma tana neman kawo masa
zancen banza.
"Ni ne nake miki wasan? Zaki ga wasa kuwa ganin idon ki".
Mikewa yayi zai bar wajen Ya Gumsu ta sha gabansa idanunta tamkar an gumbuda musu
barkono "Allah ya taimake ka ashe kuwa zaka bani takardar saki na.......kafin ranar da zaka
aurawa Da na aure da tsintacciyar magen da har yau bamu san asalin ta ba, da 'yar data fito
daga hannun makiyiyata don su hada kai su cuce ni su ga baya na nida zuri'ata a
gidannan.....na tabbata ita ta kitsa maka wannan sharrin to insha Allahu a kanta zai kare!
Ba dai Yarima ba! Ba irin tsiya irin talauci ba, irin da babu cikakken asali don ni ban yarda ma
BAGGARA ne su ba sun fi kama da bororon daji......".
Mai Askira ya hadiye tsananin bacin ransa bai nuna ba ko a fuska, babu wata mace data taba
yi masa irin wannan tsaurin idon a rayuwar sa....amma Gumsun Askira zata ci albarka da
yawa....albarkar 'ya'yan ta...albarkar kasancewar ta uwar 'ya'yan sa. Da albarkacin

kasancewarta UWA ga duk wani mahaluki dake cikin Askira.
Kawai sai ya zagayeta zai wuce, bai taba sa'in sa da kowa ba, tsakanin sa da kowa dake
karkashin sa biyayya ne ana so ko ba'a so. Shiyasa ba karamin yaki yayi da zuciyar sa yau
akan Ya Gumsu ba, sabida babu saki a tarihin sarautar su, babu kaskanci ga uwar iyali.
Ya Gumsu bata daddara ba ta sake jawo Alkyabbar sa..."wallahi sai ka bani amsar inda kuka
samo yarinyar nan....ba tun yanzu ba nasan watarana sai ta zame min jidali, na san sai an
kakabawa 'ya'yana, yadda naga uwarta ta ci buri a kanta, dama dalilin kawota gidan kenan don
ta samu ta auri dan sarki.....kamar yadda ta samu tsuntsu daga sama gasashshe....to ai ba ni
kadai na haifi maza ba......don haka in har inada hakki akan Yarima na haihuwa da shayarwa to
ban yarda ba ban amince ba.....".
Mai Askira yayi murmushi yace "sai kace dan wani na arziki ne da kike tada haqarqari akan
sa ke mai da! Dan da tun yana karamin sa ya san dadin zina......girma da aure da martabar
gidan su bata sa ya daina ya kama kansa ba. Zan rufa masa asiri da 'yar mutunci don ta
taimaka mana ya kintsu shine kike wannan zubar da kimar? Gumsu ina jiye miki ranar jin kunyar
ki.....ranar da duniya zata san dan da kike tinkahon dashi har yanzu bai bar zina ba, matar sa
shan giya take, rayuwa suke kamar ta dabbobi, musuluncin nasu duka ba maraba.....gara ita
nata babu tushe amma wanda bai ji tsoron Ubangiji ba kuma girman aure bai hana shi yin zina
ba ba abun tutiya da shi a matsayin Da bane....

A da, na sanya kwanaki uku auren Yarima da Sa'adatu, don in samu inyi gayyata, to na fasa
yanzu, nida Waziri zamu daura auren yau Juma'ah bayan sakkowa masallaci. Don in nuna miki
ni ke da iko daku daga ke har dan naki. Gara ke na baki hakkin ki na uwa na sanar miki...
shikuwa saidai ya ji labari......". Yana gama fadin haka yasa kai ya fice fadar da bai yi niyyar fita yau ba.
Waziri sai ganin maimartaba yayi yana shigowa fada a matukar fusace, shikadai yake iya
gane fushin mai Askira. Kyawun fuskarsa da kamalarsa kan boye fushin sa a yawancin lokuta.
Yana zama fadawa suka yi kirari suka kuma basu wuri, don sun lura ya shigo fada ne kawai
sabida Wazirin sa Ibrahim.
"Ka fadawa 'King-makers' akwai daurin auren Yarima bayan sakkowa daga masallaci yau".
Waziri yayi kabbara a fili, don ya dade yana jiran ranar da Askirama zai zo masa da zancen
karin auren Yarima, yana daga wasu daga cikin labaran halin da rayuwar auren Yarima ke ciki
daga abakin Awaisu, hatta zancen cire mahaifa da Aisha -Sultana ta yi ya sani, bai gayawa mai
Askira bane don ya san in rashin jikoki ya ishe shi da kan shi zai magantu. "Amma Allah ya taimakeka baka ganin gara a hada masa guda uku a wanke su rana daya a
kai masa? Hakan taimako ne babba gare shi a bisa nazari na na halin da yake ciki, kamar guda
daya ta yi masa kadan".
Askirama yayi murmushi ya dubi Waziri Ibrahim, "wannan daya ce tamkar da goma! Kuma
itace maganin matsalolin Yarima insha Allahu. Tun farko ita naso ya aura ya kawo min zancen
baturiyar nan, idan har ta fito daga cikin Bilkisu ina tabbatar maka karamar Bilkisu ce.....da ace
Bilkisu na fara aure a rayuwata babu macen da zan kara aure". Waziri Ibrahim bai san sanda yayi dariya ba, yau mai Askira ya saki layi sabida soyayyar
Fulani Bilkisu, ya manta ko da wa yake magana....
A take ya dau waya ya fara aiwatar da umarnin sarki.

Kafin karfe 2 na rana duk wani da ya kwana ya tashi a garin Askira mace ko namiji ya samu
gayyatar daurin auren Yarima Sageer da Sa'adatu, banda Sa'aden da uwarta dake kule
kowacce a dakin ta zuciya babu dadi, ita Sa'ade halin da ta ga Fulani a ciki ne ya hanata
kwanciyar hankali, tun jiya data shige daki ta rufe bata kara fitowa ba, sannnan daga ita har
Fanna da Zarah tace bata bukatar ganin kowa. Abinci ma tace bata bukata tanada cake da
friuts a firjin gefen gadon ta.
Duk tunanin Sa'ade yafi bata matsala suka samu tsakanin ta da Askirama.
Wajejen karfe daya Fanna ta shigo ta samu Sa'ade dake kwance a gado tun safe, waya take
da Sa'id yana gaya mata yadda garin Abuja ya zame masa boring saboda rashin ta, maimakon
tayi dariya ta bashi amsa cikin raha yadda suka saba sai tace "Sa'id, ina cikin damuwa,
mamana ta shige daki ta kulle tun jiya tace kada wani daga cikinmu ya je inda take" Sa'id yace
"manya kanyi irin wannan a lokacin da suke so su kebe don su samu suyi tunani ko neman
mafita kan wani mhimmin al'amari da ya shafe su, so karki damu tunda kinsan lafiyar ta kalau,
ita da kanta in ta samu saukin al'amuranta zata neme ku......." Fanna ta ce "ranki ya
dade....ranki ya dade!" Ta cire wayar daga kunnen ta ta dubi Fanna, Fanna ta ce "lokacin sallah
ya yi, ga kuma abincin ki". Sa'ade ta yamutsa fuska ta ce "maida abincin nan" "me yasa bazaki
ci ba?" Inji Fanna cikin damuwa, uwa ta ki ci, 'yar ma tun safe ta ki cin komai duk sun sa ta a
damuwa....Lokacin yayi daidai da bugawar dakikar agogo karfe biyu da rabi na rana, ya tafi tare
da bugun zuciyar SA'ADE.... ba tareda ta sani ba, ta zama karkashin igiyoyin Yareema Sageer
har guda uku.
"An daura auren Yarima Sageer Yusuf Askira da Sa'adatu Hashim Askira akan sadaki
lakadan ba ajalan ba.....". Abinda Fanna ta ji kenan data sako kafarta a kitchen don dawo da
kayan abincin da Sa'ade ta ki ci, amma bata yarda tasu Sa'adatun bace don wani abu
makamancin wannan bai taba zuwa mata a rai ba, Yarima mijin baturiya wacece zata yi gigin
shiga gidan sa? Ai sai mai tsautsayi, matar da aka ce har kwalba take dagawa. Don haka ta
tausayawa koma wacece wannan Sa'adatun da aka aurawa Yarima. Don daula zata samu zata
shigeta iya shiga....amma tabbas ta hadu da gamon ta.
Abinda Fanna ke ta fada a ranta kenan tana cigaba da ayyukan ta a kicin.

Yarima yana dakin Awaisu na gidan Waziri a wannan lokacin, shima Awaisun ya zo
sakamakon kiran gaggawa da Waziri yayi masa. Ya kuma gaya masa ko me kenan amma yace
kada ya bari Yarima ya sani har sai an gama daurin aure, mai martaba zai gaya masa da kansa.
Awaisu, kamar zai suma don dadi da farin cikin jin wadda aka zabawa Yarima, once or twice,
Yarima ya taba yi masa maganar Sa'ade, yace ta iya girki sannan ga ta da hankali. Daga
wannan bai kara cewa komai akan ta ba. Ya tabbata ko baya son ta zai karbeta tunda har yana
yabon ta, sannan uwarta mutuniyar sa ce (Fulani Bilkisu). Bazai bada mata kasa a ido ya ce
baya son 'yar data fito daga hannun ta ba. Yarinyar kawai yake tausayawa zama da Sultana
amma zai nemi Yarima da ya raba musu gida don a zauna lafiya.
Shi dai Yarima ya ga Awaisu sai shiri yake cikin farar shadda excelcior, yana yi yana bin waka
a radio da alama cikin nishadi yake, ya ce Asiya tana jirana a cikin gida don haka na sallameka
inada daurin aure a fada inna gama da ita". Yarima ya kulu da wannan kora da Awaisu yayi
masa yace "ni kake kora? Daurin auren wa?" ALLAH ya taimaki Yarima wane ni in kore ku!
Amma don Allah ka kara gaba ko in bar maka mukullin dakin in ka gama hirar ka rufe, inada

daurin aure muhimmi". Daga haka ya sanya hularsa da takalmi ya fesa turare, ya dubi Yarima
yana murmushi ganin kallon takaicin da yake masa.... dariya yayi a rans yace ka kuma zama
namiji malam, a da muna maza ne tunda mai jan kunne kake aure, yanzu ne zaka san ka yi
aure da matan usli da suka amsa sunan mata.... Yayi ficewar sa ya barshi kwance a gadon sa da baki sake, yana mamakin Awaisu ne yau
yayi masa wannan wulakancin? Daurin auren da zai je ya fi shi Sageer muhimmanci???
****

Bayan daurin aure aka zarce da bushe-bushen algaita da kalankuwa, masu goge da masu
ganguna kowa na baje kolin nasa. Gabadaya garin ya rude da hayaniya anata labarin Yarima
ne aka daurawa aure da 'yar da kishiyar mahaifiyar sa ke riko, wasu na fadin 'yar ta ce data yi
shegen ta kafin tayi aure (wa'iyazu billah) Allah ka kare harshenmu daga fadin gaibu, da abinda
bamu da tabbas a kan shi.
Wannan zance ya kai kunnen Ya Gumsu ta hanyar 'yan kanzagin ta da 'yan hana ruwa gudu,
cewa ashe Sa'aden 'yar Bilkisu ce data yi shegenta kafin tayi aure aka kuma biyota da ita har
gidan auren ta.
Saura kadan Ya Gumsu ta haukace, ga Askirama yana fada bazai shigo ba sai bayan isha
balle taje ta huce akansa.
Me ya dace ta yi? Ban da ta je su yi wacce zasu yi itada Fulani Bilkisu? Shegiya a cikin
iyalinta! Ai gara mata mara addinin!
Yau babu ko mayafi haka ta ratsa ta tafi unguwar Fulani Bilkisu, ta wuce bayin ta da hadimai
fuuuuuu! Ko gaisuwar da suke mata bata karba ba.... yau ko ita ko Bilkisu, koda hakan shine
zaiyi sanadin igiyar aurenta.
Fanna na kokarin fitowa da tsintsiya a hannun ta Ya Gumsu tayi ciki da ita, saura kadan ta
fadi, sai wara ido take tana neman Fulani amma bata ganta ba, ta daga murya kamar zata
tsaga gidan tace.
"Bilkisu! Fito wajen ki na zo!" Wannan kira har cikin kwanyar Fulani Bilkisu, gabanta ya fadi
ta dafe kirjin ta, Ya Gumsu ta soma dukan kofar dakin ta tun karfin ta, tana cewa "Da na ya fi
karfin auren SHEGIYA kurwar mu kurr. Yadda kika lashe mai Askira shine kika kawo shegiya ta
lashe Yarima? Wallahi sai bayan raina wannan auren zai tabbata...." dukan kofar take kamar
zata ballata. Bilkisu jikin ta sai rawa yake hawaye na zubo mata, tana so ta fito ta fuskanci
Gumsu ta fada mata 'yar ta ba shegiya bace da ubanta kuma itama bada son ranta bane amma
ta san halin Ya Gumsu, zata tara mata mutanene aka, ta wulakantata gaban bayin ta, su taru su
zubar da mutuncin mai Askira don ta tabbata Gumsu dambe take so su yi ba wani abu ba, ta
samu hanyar lalata maganar auren, to ko za'a lalata zancen auren nan ba daga gareta ba, da
Gumsu ta san halin da ta ke ciki akan auren da ta tausaya mata, itama bata so, ko kadan bata
so. Saidai ta zabi farin cikin Askirama akan nata da na Sa'ade.
Don haka ta daure ta cije bata fito ba, ta bar Ya Gumsu ita kadai tana ta zage-zage, bakaken
maganganu ba irin wadanda bata fada akan Bilkisu ba, har da cewa da ganin ta dama an ga
tsohuwar karuwa ta zo ta hargitsa musu miji bakidaya ya daina ganin kowa da gashi sai ita, duk
wannan bai isheta ba ta zo ta hada auren masifa da bala'i a cikin zuri'arta, to ko zata yi yawo
tsirara sai Yarima ya sakar mata 'yar ta.

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login