Showing 21001 words to 24000 words out of 31845 words

Chapter 8 - Masarautarmu Book 2 Hausa Novels By Takori Kabara

maida ni Askira, wallahi na gama zaman gidan ku"
Yarima ya ja da baya sabida da karfi ta fasa kukan. "Da mu kayi miki mene?" Ya fada yana
hararar ta, in wani yaji irin kukan da ta fasa tsammani zai yi wani abun yayi mata. Ba ta ce
komai ba sai cigaba da kukanta. Da zata iya da ta ce dashi sabida dukkanku fasikai ne marasa
tsoron Allah. Amma ta san ko giyar wake tasha bazata iya dubar tsabar idon Dr. Sageer ta gaya
masa haka ba. Apart from all these she respects him so much.
Yana da wata irin kima a idanun ta da bata san yaushe ta samu matsugunni a zuciyarta ba.
Tafi danganta hakan da kulawar sa da kyautatawar sa gareta.
Yarima ya dubeta a fusace, ya rasa yanayin da yake ciki yau, amma ya tabbata bai taba
ganin abinda ya bata masa rai a duniya irin Sa'adatu da saurayin ta a mota ba, yaga yadda
hawaye ke gudu akan kundukukinta kai ka ce wani mugun abin aka yi mata. Ya nunata da dan
yatsa ba tare da ya bari hawayen da take zubarwa sun yi tasiri akan sa ba "Yau ta zama rana ta karshe da zai kuma tako min gida, ba shi kadai ba kowanne rubabben
saurayin ki ma, in ba haka ba in gayawa Fulani da maimartaba su cireki a makarantar su yi miki
aure tunda hakan kike so".
Sa'ade ta zaro ido abin dariya abin tausayi "Uncle Yarima wasa nake ba saurayi na bane ba,
wallahi, dan ajin mu ne" ya juya ya fice bai saurareta ba, damuwar duniya Sa'adatu ta shigeta,
ba abinda take tsoro, taki jini take kuma gudu a rayuwar ta irin AURE!
Saida yayi kwana uku bai kara kula ta ba, bai kara nemanta ba, he's really suffering a ruhi da
zuciyar sa akan ganin Sa'ade da saurayi akan dalilin da bai sani ba. A haka su Sa'ade suka fara
jarrabawar karshen zango babu shiri ko kankani tsakanin ta da Yayan nata Yarima.
Ranar da sukayi takardar karshe ta kira Fulani ta gaya mata, Fulani ta gayawa maimartaba,
shikuma ya kira Yarima yace yasa direba ya kawo Sa'ade gida tayi hutu. Yarima yace dama
shima zai shigo Askiran jibi, zai taho da ita da kansa.
Sa'adatu na kwance a gadon ta tana karanta mujallar turanci ta 'Thrills and Boom' taji
knocking a kofar ta. Ta gyara kwanciyarta da dankwalin ta daya cire sannan tace "yes". Yarima
ya sanyo kai a dakin, t/shirt ce a jikin sa fara kal an rubuta Marks&Spencer da bakin rubutu, sai
bakin wandon jeans mai kauri. Hararar ta Yarima yayi sannan ya jingina da kofar, a hankali ya
ce.
"Sabida na hanaki kula samari, shine kika daina gaishe ni ko?"
Sa'ade ta sunkuyar da kanta bata ce komai ba, amma sosai taji kunya, wai wa yace ma
Uncle Yarima Sa'idu saurayin ta ne? Bata cika son magana tayi tsayi a tsakanin su ba, karatun
ma da yace zai koya mata bayan dawowarsa daga tafiyar da yayi saida ta san yadda tayi ta
kaucewa hakan ta roki Sa'idu ya koya mata lokacin jarrabawar kwas din, yana da effect mai
karfi kanta wanda shi bai sani ba itama bata sani ba, abinda ta sani kawai shine bata son
mu'amala mai zurfi a tsakanin su.
"Ki shirya gobe da asubah zamu kama hanyar Askira, maimartaba yace a kai ki kiyi hutu"

bata san lokacin da ta dago zaune ba tana ta faman blushing, bai tsaya kallon ta ba yasa kai ya
fita.
Tun a daren ta hada duk abinda take bukatar tafiya da shi. Baccin ta ma ragagge ne sabida
doki. Tayi kewar Fulani da Zarah.....Shi kansa Askirama ta yi kewarsa.
Washegari data yi sallahr asubah bata koma barci ba, wanka tayi, tayi ssaukar shiga ta bakar
abaya mai santsi da adon stones sosai a jikin ta. Bata shafa komai a fuskarta ba sai wet-lips ta
kuma fesa sassanyan turare. Ta zauna bakin gadonta da trolley dinta a gaba tana jiran Yarima.
Bai fito ba sai wajen karfe shidda na safe, kallo daya tayi masa da ya murda kofar dakin ya
shigo bayan tayi masa izni, taji bazata iya jure kallon ba, kwayar idanunta ta zamo mai rauni
sabida yau ya fito Prince dinsa.
Ta taba ganin maimartaba da irin kayan jikin sa, yakan saka kayan in zai zauna cikin iyalinsa,
kaya ne kufta da wando na sarautar Askira wadanda basu cika nauyi ba. Amma kuma sun sha
aikin zare na silver da hula zanna bukar a kansa. Kasancewar kusan kullum cikin shigar suit
take ganin sa yau sai ya zamo mata wani daban, classique and elegant kai kace Askirama ne
ya zama yaro.
"Lets go!"
Inji Yarima, ganin ta sunkuyar da kai bata ce komai ba, bayan a badini kirjinta ne ke wani irin
harbawa da sabbabin emotions da bata san daga ina suke fitowa daga karkashin zuciyarta ba.
Hannu yasa ya ja trolley dinta. Ya fita ta bishi a baya bayan ta dau handbag dinta tana
mamaki a cikin ranta; Yarima ya dau kayanta da kansa. Sai taji har tsigar jikin ta na tashi da
wani irin feelings mai sanyi a zuciyar ta. Hakan kuma bai janye bakin fentin data ke kallon shi
dashi ba. A falo suka ci karo da Aisha - Sultana, kayan barci ne a jikin ta, ta tsaya jingine da kofar dakin
ta tana kallon su, ta gabanta Yarima ya wuce dauke da jakar Sa'ade, Sa'aden na gaisheta da
safiya, wata harara ta zabga mata ba tareda ta amsa ba. "Mun tafi Askira Aunty, sai na dawo"
jin bata amsa mata ba ta wuce ta, ta tadda Yarima a mota, Salis ne ya ja su. Ta dauka a motar
zasu tafi har Askira amma sai ta gansu a filin jirgin saman Abuja.
For the first time Sa'ade a jirgi, in ka gansu itada Yarima tsammani zakayi sababbin couples
ne sabon aure duk da babu hira a tsakanin su. A cikin jirgin Azman ne mai zuwa Maiduguri a
first-class seats, ga kujerar ta ga ta Yarima, Lokacin da waitress ta kawo abin motsa baki kasa
cin komai tayi sabida uneasiness din da take ciki na zama a gefen Yarima. Ga kamshin Paco
Rabbanne dinsa dake kara hargitsa ta. Shikuwa yayi amfani da wannan damar wajen kare mata
kallo, kallon da bai taba yi mata ba, har ya zarta ka'idar muslunci domin kallo ne na kurullah. A
zuciyar sa ba abinda bai fada ba, wanda daga shi sai Ubangijinsa suka sani, a zahirin sa kamar
ba ita yake kallo ba.
Bai fi minti goma ya rage suyi landing ba Sa'adatu ta soma jin amai na taso mata sakamakon
wani Igbo da ya gifta ta gabanta yana warin qashi irin na maza, ai kuwa tana yunkurawa domin
ta tashi sai amai ya kelayo a jikin Yarima Sageer, basu da yawa a first class seats din don haka
hankalin sauran mutanen ya dawo gare su, Sa'ade ta hau zazzare ido cike da tsoro bakin ta na
rawa tana son furta ban hakuri kalaman sun ki fitowa. Amma ga mamakin ta ko a fuska bai
nuna kyama ba, wani irin kallo yayi mata yace "sai kin goge min shi tas!"
Tayi narai-narai da ido kamar zata yi kuka don damuwar abinda tayi masa "...don Allah kayi
hakuri Uncle Yarima....ban yi da sani ba" a ginshire ya ce "na ce kin yi da sani ne?" "To kayi

hakuri don Allah bazan iya goge maka ba" suna wannan jayayyar sai ga waitress tazo don ta
gyara wajen tana ta yiwa Sa'ade sannu don a zaton ta ciki gareta.
Kasancewar kayan rubi biyu ne ta saman kamar jabba take mara nauyi akwai jamfa daga ciki
yasa ya cire ta saman. Sa'ade tayi maza ta dauko turarenta a jakarta ta mika masa. Karba yayi
yana jujjuya shi a hannun sa 'sapphire' itama Fulani ce ta bata, a tunanin ta zai bukaci turare
tunda tayi masa kayan karni. "Me zan yi da turaren mata?"
"Ka fesa saboda karni"
Ta fada kamar zata saki kuka don damuwa, ta rasa da bakin da zata bashi hakuri. Mika mata
turarenta yayi yana dubanta ta kasan ido yace a hankali "idan matata taji kamshin turaren ki a
jiki na what do you expect?" Sa'ade ta runtse ido tace "ni fa ban bayar da wata manufa ba, don
ya kashe smell din aman ne" "idan kuma ni son smell din aman nake fa?" Kallon sa tayi da
budaddun idanuwa.... mamakin ta ya bayyana karara cikin idanun ta
Ba jimawa jirgin su yayi landing a Maiduguri.
Motocin ASKIRA EMIRATE har guda biyar manya da kanana suka zo tafiya dasu, da fadawa
da dogarai cikin uniform din su na bayin masarautar. Mota guda suka yi amfani amma da yake
babba ce sosai kirar (4matic) mai kujeru takwas ba kujera daya suka zauna ba, Sa'ade na daga
kujerar baya Yarima na owner side. Suka dauki hanya. Ji take kamar tayi fiffike ta ganta a dakin
mahaifiyar ta. Har suka zo Askira barci take wanda a jirgi takuruwar zama kusa da Yarima bai
barta ta yi ba.
Ana bude musu motar ta fice da azama bata jira fitowar Yarima ba, wanda tun shigowar su
Askira taga kamar komai nasa ya canza, simplicity din da annurin ya tafi, ya juye ya rikide ya
zama cikakken Prince din sa.
Da gudu ta karasa unguwar Fulani Bilkisu ko jakarta bata dauko ba sai biyota aka yi da ita.
Da Zarah ta fara tozali, suka ruga da gudu suka makalkale juna. Zarah na tambayar me ta taho
mata dashi daga Abuja? Tace "everything, sweetheart". Fulani ta fito daga shigifarta cikin wata
irin kyakkyawar shiga ta alfarma, ta tsaya daga bakin kofa tana kallon su da murmushi, kamshin
ta ne yasa Sa'ade ta lura da ita, ta ajiye Zarah ta kwasa da gudu ta rungume Fulani, kawai
kuma sai ta fara hawaye.
Fulani tace "yau nake ganin sakarci, me aka yi na kuka? Ko suna miki wani abu ne?" Ta
girgiza kai "babu komai, kukan farin cikin sake ganin ki nake yi, watanni shidda ba kwana
shidda ba". Fulani ta hau tureta daga jikin ta jin takun ana shigowa, Fanna ce ta taho dauke da
abinci a makeken tray ta ajiye a dining. Tana murmushi tace da Fulani "Allah ya taimakeki yau
tare na hada muku abinci da uwar daki na, don Allah ku ci tare" Sa'ade ta sa dariya cikin dadi
tana kallon uwartata. Fulani ta gimtse fuska tace "Fanna yaushe na koma abokiyar wasan ki?"
Fanna tayi nara-narai da ido tana murmushi tace "Allah ya ja da ranki Alfarma ce muke nema,
wata shidda cif bamu ganki ba".
Babu wanda ya gayawa Fanna Sa'ade 'yar Fulani ce ta cikin ta amma ta dade da fahimtar
hakan. Yadda aka yi ta samu 'yar ne bata sani ba.
Tana gama fadin hakan ta juya ta fita, Sa'ade tayi wata irin super ta dane jikin Fulani saura
kadan ta kada ita, Zarah sai dariya take yi. A haka suka ci abincin cike da begen juna su uku.
Tana gamawa tayi wanka ta sauya kayan jikin ta zuwa marasa nauyi ta dauko waya ta kira
Sa'id. Yace "Sa'adatu, yaya kwana biyu kuma ya hutu? Ina fatan kina bitar Physiology textbook

dinnan?" Sa'ade tace "ni yanzu ina garin mu bana Abuja ka kyale ni in huta da wani karatu, ina
tare da uwata rabin raina" Sa'id yayi murmushi yace "sai na zo Askira kawo gaisuwar neman iri"
Sa'ade tayi tsaki tace "Allah ya sawwake inyi saurayi da classmate dina, wani dan yaro da kai,
ni dinnan da kake gani matar manya ce inji Fanna" dariya sosai Sa'id yayi, ya ce "me yafi ka
auri yaro sabon jini kamar ka? Ya sa ka dariya kaima ka saka shi? In yaga dama ya goyaki ya yi
ta zagaye gida dake?" Sai ganin Fulani tayi tsaye a kanta. Ba karamin firgita tayi ba ganin
expression na fuskarta. Tayi maza ta kashe wayar ba tareda ta yiwa Sa'idu sallama ba.
Tana zazzare ido na rashin gaskiya.
"Keda wa kike waya?"
Fulani ta tambaya fuskarta babu annuri.
A tsorace tace "dan ajin mu ne kawai"
Fulani ta juya bata ce komai ba. Saidai kwarai ta so ta magantu din, but she don't want to be
too strict har Sa'ade ta koyi boye mata sirrikan ta. Saida ta kai bakin kofa sannan tace mata ta
tafi wajen Askirama kada ta nemeta.....
****












Rami ne mai tsananin zurfi, wanda har baya iya hango karshen sa sabida zurfin sa, ya leka ciki
sabida ya ji kamar muryar Yarima yana kuka yana neman taimako. Bai ga ta inda ta bullo ba
kawai ya ganta ne a bakin ramin, tana rike da igiya mai tsayi, tana zuwa bakin ramin ta jefa
masa igiyar tace "Kama ka fito da iznin Ubangiji". Bai ga fuskarta ba sabida ta sunkuya ne akan ramin, gashin kanta ya sakko ya rufe fuskar
tata gabadaya, saida tayi magana sannan ya shaida muryar ta.
Ba jimawa ya ga ta kama igiyar nan tana janyo wanda ke ciki har ta fiddo shi tsaf, yana fitowa
suka rungume juna suna hawaye. A lokacin ne ya samu damar ganin fuskokin su gabadaya;
Sa'adatu ce da dan lelen sa YARIMA SAGEER.
Tamkar an warware masa dukkan baccin da ke kansa ya farka firgigit misalin karfe biyu na
sulusin dare, lokaci ne da aka tabbatar mafarki yana iya zama reality. To ko me wannan
mafarkin da yayi yake nufi? Sa'adatu as saviour of Sageer? Ba don babu kyau bayyana mafarki
ga wani ba, da ya nemi Limamin Askira ya gaya masa mafarkin da yayi. Duk da haka a nasa
hankalin, ya fahimci tamkar wani hannun ka mai sanda ne Ubangiji yayi masa, mai nufin akwai
wani babban al'amari tsakanin Sageer da Sa'adatu kamar yadda ya so hakan ta kasance a
baya.

Bai san sanda ya sa hannu ya soma tashin Fulani Bilkisu wadda ke barci sadidan a gefen sa.
Ta tashi tana yamutsa fuska tana mutstsikar ido. Ya ce "Bilkisu bude idon ki ki dube ni". A
yanayin da Askirama yayi maganar cikin rauni yasa ta dole watstsakewa.
"Lafiya Askirama? Lafiya gatan mara gata? Lafiya giwan ASKIRA?"
Ta fada cikin tausasa murya, mai Askira ya kama hannayenta duka biyu ya rike cikin nasa.
"Alfarma nake nema wajen ki irin wadda ban taba nema ba...... ki bani Sa'adatu in aurawa
Yarima a gobe".
Fulani Bilkisu ta ji maganar ne tamkar saukar aradu a kunnen ta, kwakwalwarta ta kasa
digesting maganar yadda ya kamata sabida wani abu ne da bata tsammani ba a rayuwar ta.
Bata kin Yarima don tamkar dan cikin ta ta dauke shi. To amma neman matan da ake cewa
yana yi fa tun bai san kansa ba har girman sa har ita Sa'adatun ma ta shaida da bakin ta? Shin
Sa'ade ta cancanci hada rayuwa da wayayyen mutum irin Yarima? Ina Sa'aden ta ina hada kishi
da Aisha-Sultana?
Don haka Fulani ta rasa amsar da zata baiwa mijinta mai Askira, sai bin shi da ido, a zaton ta
makuwa yayi cikin barcin sa. Amma da ya girgiza kafadun ta ya sake maimaitawa sai ta
tabbatarwa kanta mai Askira yana nufin abinda yake fada ne.
"Kin amince ko Bilkisu? Hankalina bazai kara kwanciya ba batare da na tabbatar da sunnah
tsakanin Sageer da Sa'adatu ba, jikina na bani itace zata zamo maganin dukkan matsalolin sa,
don ban taba yin mafarkin da bai zama gaskiya ba".
Ya kwashe mafarkin da yayi duka yanzun nan ya fada mata.
Fulani Bilkisu ta rasa abinda zata ce, she's mute for some minutes, tana mai tariyo tarin
alkhairin Sarki Yusufu ga Sa'ade tun zuwanta Askira, shin bazata manta da komi ba ta bisu da
addu'a ta zama mai rama khairan da khairan?
Ta lumshe idon ta cikin na Askirama, wanda ke tabbatar masa da ta karbi alfarmar sa, bata
da abin cewa. Itada Sa'adatu duka abin ikon sa ne sai abinda ya hukunta a gare su.
****

Koda ta koma dakin ta a washegari bata ce da Sa'adatu komai ba, cikin dimuwa da zullumi
take, sabida Mai Askira ya ce

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login