Showing 3001 words to 6000 words out of 31845 words

Chapter 2 - Masarautarmu Book 2 Hausa Novels By Takori Kabara

cikin al'umma.

He's genius a halayya da dabi'a, superb a rayuwar auratayya, splendid a tafiyar da matar
sa.... Ko don ta cigaba da rayuwa da Yareema zata cigaba da zama cikin rigar addinin sa mai
wahala, amma ba don ya dadata da kasa ba.

Watanni ukku Yareema ba ya komai sai neman aiki ta yanar gizo ba da sanin maimartaba ba,
sai amarci da mai jan kunnen sa, Fulani Bilkisu ta zama uwar dakin Sultana ita ke kula da komai
da ya shafe ta don Ya Gumsu ko gaisheta tayi bata amsawa, haka Ya Maira bata taba takowa
gidan ta ba sai Humaira da Naja'atu, mazan kam suna zuwa sosai wajen Yareema musamman
Ashgar wanda ya maida gidan wajen hirar sa sabida yadda Yarima ke jan sa a jiki, don yana
tsananin tausaya masa, kuma yana samun sauki sosai daga rehabilitation din da Yarima yasa
shi ya samu a kasar Amsterdam.

Ayyuka har biyu Yareema ya samu a lokaci daya, NTNU (Nigerian Turkish Nile University)
dake Abuja sun bashi aikin koyarwa (lecturing) kamar yadda ya zaba a tsangayar (Pure and
Applied Chemistry), haka OAU (Obafemi Awolawo University, Ile-Ife) suma sun dauke shi da
gaggawa, tun kafin dawowar sa ya yanke shawarar komawa academia wani professsion da
'ya'yan sarauta basu fiya karba ba. Kamar yadda komai nasa yake daban da na sauran mutane,
haka tunanin sa ma ya ke. Ba ya danganta kansa da sarauta ko kadan kamar yadda mahaifin
sa ke so, a ganin sa tana hana 'yanci, sannan takura ce. Gashi shikuma mutum ne mai tsananin
son rayuwar da babu takura, kuma babu matsantawa a cikin ta.
Mutum ne mai (tsinkaye) da tsantseni a cikin dukkan mu'amalolin rayuwar sa, mai son dogaro
da kai, mai zafin nema, mai zafin nama, sannan mai nasara a kan duk abinda yasa a gaba. Bar
shi dai da son matan sa (his only shortcoming) abinda zamu iya kira nature a jikin maza jinin
sarauta, wanda zamu iya cewa tun bayan auren nan wata irin nutsuwa ta saukarwa Yareema
Sageer Askira; Mata suka rage burge shi banda matarsa Aisha-Sultana. Haka ya zauna yana
deleting numbobin mata kala-kala yare daban daban dake kan wayar sa, ya na fadawa kansa
da kansa; yadda ya bar Amsterdam gabadaya, haka ya baro ta tareda dukkan matan da ya
baro cikin ta.

Kasuwancin automobile din sa ma ya maido shi gida Nigeria ya dora Awaisu akan komai.
Yanzu kuma da ya dawo sai ya hada da biyu daga cikin kannen sa wadanda suke gab da
kammala karatun digiri akan kasuwanci, Suhail dan wajen Ya Kirjinoma da Ahmad kanin sa a
dakin su. An kai ruwa rana kafin Maimartaba ya yarjewa Yarima komawa Abuja da iyalin sa, don a
tunanin sa da farko ya dawo Askira kenan don har ya fara shirin yi masa nadin sarautar
Chiroma, amma sai Yarima ya zo da batun samun aikin sa da NTNU yana rokon Maimartaba
alfarmar ya bar shi ya tafi, sai da Fulani Bilkisu ta sa baki sannan maimartaba ya amince don
baya iya hanata kowacce alfarma ta nema, kuma Yarima ya zama dan gidan ta yanzu tun
lokacin da Maimartaba ya damka mata amanar Sultana. Ya bar shi ya tafi da alkawarin duk
bayan wata uku a gida zasu yi hutun kowanne karshen zangon karatu na jami'a.
Ranar wata Lahadi Yarima Sagir da maidakinsa Aisha-Sultana suka tattara suka koma Birnin
tarayyah. Humaira da Naja'atu da sauran kannen sa maza ne suka yi masu rakiya, basu dawo
ba sai da suka taya su suka shirya gidan su tsaf wanda Jami'ar NTNU ta baiwa Yareema Sagir
cikin jerin gidajen malaman Jami'ar. Jami'ar NTNU mallakar Turkawa ce (Turkish University) da suka bude a kasar Nigeria, suna
biyan malamansu sosai a matsayin ta na (private international university) ko kusa ba daya take
da jami'o'in Arewacin Nigeria ba wajen biyan malamai.

Haka gidajen malaman jami'ar dole tsarin su ya burge ka. Flat ne hawa daya mara girma
sosai, dakuna ciki hudu, kitchen da bandaki a kowanne dakin barci, tafkeken falo da bangaren
cin abinci (dining) sannan akwai garden daga bayan kowanne gida, daga gaban gidajen kuma
balcony ne domin shan iska da yamma, akwai rumfar gargajiya (hut) a cikin gate din kowanne
gida wadda aka zuba kujerun roba da gadon shan iska na Turkawa, gabadaya ginin daga na
jami'ar har na gidajen malaman an dauko tsarinsa da sample dinsa daga Istanbul ne, duka
gidajen iri daya ne sun kai guda 100 a cikin jami'ar.
Su Humaira suka dawo gida suna ta santin gidan Yayan su Yarima (Dr. Sagir Yusuf Askira)
sunan da Jami'ar ta mayar masa, da alwashin zuwa hutu duk sanda suka samu hutu domin ba
laifi Aisha - Sultana tana da kirki ga kowa nasa, daga auren zuwa yanzu ta saba da daukacin
kannen Yarima na sauran dakunan matan sarki, banda 'yan dakin Ya Gumsu. Tun bata fahimta
ba sabida rashin jin yaren hausa dana kanuri har zuwa yanzu ta fahimci Ya Gumsu bata yi
na'am da ita a matsayin surukarta ba. Da suka je mata sallama ma zasu taho abuja ko kallon ta
bata yi ba, haka tace da Yarima cikin fushi "tattara wannan danyen naman ku bar min sassa tun
ranka bai baci ba".
Ba wai ta ji me Ya Gumsu ta ce bane amma ta fahimci ba maganar arziki bace duk da Yarima
bai nuna komai akan kyakkyawar fuskarsa a lokacin da ta yi maganar ba, baya ga cewa da yayi
da ita ta tashi su koma gida dare yayi.
Satin su guda itama ta fara neman aiki da (Insurance Brokers) kasancewar tattalin arziki ta
karanta, Yarima ya samar masu kuku da mai gyaran gida duka kabilu, ba'a jima ba kuwa suka
dauke ta, sai ya zamo daga shi har ita ba mazaunin gida, a lokacin ne Yarima yayi wani aboki
dan kasar Turkey wanda yana cikin masu ruwa da tsaki na jami'ar sunan sa Dr. Ziyad, zasu yi
shekaru daya kuma a tsangaya daya suke koyarwa. Tun haduwar Sageer da Dr. Ziyad
abubuwa suka kara canzawa Yarima, domin Dr. Ziyad fitinanne ne na karshe kuma shi ba shi da
mata, gidan sa babu nisa da gidan Yarima don haka lokuta da dama suna tare, suyi yawo cikin
gari ko su debo 'yammata gidan Dr. Ziyad,
A haka suke rayuwar shi da Sultana kowa yana sha'anin gaban sa, don so suna son juna har
gobe amma rashin albarkar uwa ya hana auren gamsar da kowannen su ba tareda sun san
hakan ba.
Itama tunda ta waye da rayuwar Abuja shikenan ta koma harkokin ta na baya, bata kara tuna
wani abu wai shi musuluncin data karba ba, shaye-shaye take na fitar hankali, data gane inda
ake sayar da giya a Abuja kuwa shikenan kakarta ta yanke saka. Ta san halin Yarima akan
'giya' don haka bata taba gigin shigowa da ita gidan ba, kullum ta taso aiki sai ta tsaya a Bar ta
sha mai isar ta, ta yo guzurin kayan mayen ta kala-kala sannan zata dawo gida, tana riga shi
dawowa sau tari domin Dr. Sagir yafi fixing laccar yamma ga daliban sa, tana shigowa kai tsaye
dakin barcin ta take nufa ta zube a kasa ko a gado tayi ta barci, har sai ya dawo ya tasheta da
kan sa ya ce ta yi sallah.
Wannan itace kalar rayuwar Yarima da matarsa Aisha Sultana a birnin tarayyah, Abuja.
Rayuwar da kowanne ya zabawa kansa. A haka lokaci ya cigaba da mikawa. Abinda Yarima bai
sani ba tun dawowarsu Abuja da sati daya, Aisha-Sultana ta je an juya mata mahaifa.
*****

BAYAN SHEKARA BIYU!

Yau ne daliban El-Kanemi College of Islamic Theology suka kammala rubuta final paper din
su ta barin makarantar sakandire wato SSCE wadda ta kasance darasin addinin muslunci
(islamic studies). Farin cikin dake zukatan su ba zai bayyanu ba, fuskar Sa'adatu Hashim tafi ta
kowa yalwar far'a, ta yi dakacen wannan rana inama da Rahima Kyari! Sun yi hotuna na tarihi
kala-kala da kawayen ta da abokan arziki da suka yi zaman aminci tare. Babban farin cikin
SA'ADE shine Alanguburo yayi mata alkawarin karatu a jami'ar Turkawa dake Najeriya
(Nigerian Turkish Nile University) muddin ta fiddo da 9 credits, kuma daga yadda ta rubuta
kowacce paper tana da kyakkyawan zato akan kokarin ta.
Humaira ta gama makaranta shekaru biyu baya, yanzu haka tana jami'ar Maiduguri. Da suka
iso gida yau ta yi abinda bata taba yi ba a tsayin rayuwar ta (without minding the consequence);
a guje ta shiga sassan su tana kwalawa Fulani kira, Fulani bata san hawa ba bata san sauka ba
tana tsaye tana yi wa little Zarah fada taji anyi wuf! Da ita an kankameta a tsakar dakin. Dama
ga ta babu kiba ko kadan. Saura kadan ta sha kasa "I have finally graduated Fulani, i've really
-really made it!".
Kokarin banbare Sa'ade take daga jikin ta kada wani ya shigo ya gansu a haka, yayin da
Little Zarah ke ta kyalkyala dariya cike da murnan ganin Sa'aden, ta tafi itama ta rungume su,
Sa'ade ta saki Fulani da ke ta banbamin fadan so take ta karya ta? Ta russuna ta dauki Zarah
tana rada mata cikin kunnen ta "na taho miki da choculates mai dadi" Zarah ta ce "bazamu san
wa Fulani ba tunda tana yi miki fada" a haka suka shige dakin Sa'aden wanda Fanna ta gyare
tsaf. Ta sanya turaren wuta irin nasu. Don tana da masaniyar yau ne graduation din Sa'adatun.

Sa'adatu Hashim dalibar El-Kenemi, doguwa ce sosai, mai kirar jiki na bare-barin usli,
wadanda suka hadu da shuwa suka haifeta, suka bata colour din fata mai kyau da daukar ido.
Doguwa sambaleliya tamkar kirar matan Saliyon, a yanzu ne take cikin shekaru goma sha
takwas komai nata ya kai ya kawo, cikakkiyar budurwa mai wani irin class na daukar hankali. Duka wadannan Fulani Bilkisu ta nazarce su ne a lokacin da Sa'ade ta dauki Zarah suka bata
baya zuwa dakin Sa'aden, ta bisu da kallo cike da kauna tana jin wata irin soyayyarsu su a
zuciyar ta, a yanzu kam ta saduda, ta tabbata ta kuma haqqaqe tana son 'yar ta, kwatankwacin
ko ma fiyecda yadda ta ke son Fatima-Zarah. Ta koma cikin hamshakiyar kujerar falon ta ta zauna, ta lumshe idon ta a hankali, yayin da
tunanin shekaru goma sha tara a baya na yadda ta samu 'yar, ya soma rewinding filla-filla a
cikin kanta.....
****

SHEKARU GOMA SHA TARA A BAYA!
Mu 'yan kabilar "Baggara" ne wadanda aka fi sani da "Shuwa-Arabs", asalin mu makiyaya ne
masu yawo da dabbobin su a kasashen Africa, mun fito daga kasar Chadi wadda take daga
yammacin Ifriqiyyah, yawanci zaki samu yan kabilar Baggara sun watsu a kasashe irin Sudan,
Cameroon, Niger, Chad, Nigeria, da kuma Central African Republic. Baggara musulmi ne na haqiqa masu rikon addini tun karni na goma sha uku, harshen mu
shine "Chadian Arabic" wanda muke yin shi da shuwa-dialect, Allah ya zubawa Baggara
kyawun surah na kirar jiki data fuska, da wata irin kalar fata mai sheki da kyau, wanda ya samo
asali daga cakuduwar su da larabawan Sudan. Mahaifina Malam Soumana ya baro kasar Chadi tare da mahaifiyata a lokacin tana da cikina
tare da 'yan uwan su Baggara zuwa Nigeria inda suka yada zango a yankin Borno, daga baya
suka koma Damaturu bayan an haifeni da shekaru hudu, inda mahaifina yake sana'ar kiwo,
shanu yake kiwo da tumaki ya sayar a karshen kowacce shekara ya sayi wasu ya sake sabon
kiwo. Mahaifiyata Roumana tunda ta haife ni bata sake haihuwa ba, inada shekaru biyar Allah
yayi mata rasuwa.
Babana shi ya cigaba da raino na, yasa ni a makarantar firamare, daga baya jarin kiwon nasa
duk ya balbalce, wani abokin sa ya yaudare shi ya saye su da zummar washegari zai kawo
masa kudin gabadaya, cikin dare ya bar Damaturu da dabbobin gabadaya, wanda hakan yayi
silar talaucewar mahaifi na, muka koma rayuwa cikin kaka-ni-kayi, abinda zamu ci kansa ba
kullum muke samu ba, mahaifina ya koma yin dako a kasuwa duk don mu samu abinci baya ko
zancen aure don tsoron matan borno wadanda ba kabilar sa ba. A haka na rayu hannun
mahaifina cikin kwanciyar hankali don talaucin mu bai hana mana kwanciyar hankali ba, duk
wata buga-buga da dan adam zai yi don ya samu abinci mahaifi na yayi ta har na gama
makarantar firamare, inada shekaru goma sha uku watarana mahaifina ya zo da dabbobi masu
yawa, ya dinga yi musu turke yana daure su daya bayan daya, na tambayeshi inda ya samo su
sai ya ce ya karbe su ne yayiwa wani kiwon su zai dinga bashi ladan kiwo duk karshen wata.
Sabida zai yi tafiya Kano ci-rani bashi da wanda zai dinga kula masa da su.
Watarana muka wayi gari dabbobinnan babu ko daya, an biyo dare an sace su.
Mahaifina ya shiga tsananin tashin hankali, domin mai dabbobi ya kusa zuwa gida, duk
bayan wata uku yake zuwa, sabida tashin hankali mahaifina har kwanciya yayi ciwo don bai san
bayanin da zai yiwa mai dabbobi ba.
Bansan yaya suka kare ba, illa a wani dare mahaifina yana kuka ya gayamin gobe zai daura
min aure, bashi da abinda zai biya mai dabbobi, shikuma ya ce sai ya biya shi, ko ya bashi aure
na madadin dabbobin sa.
Na rasa a wane yanayi na karbi wannan zance na mahaifina. "Auren biyan bashi" zai yi dani,
sai kace ni din ba mutum bace mai darajah. Ban taba yiwa mahaifina musu ba amma wannan
karon na ce a'ah, bazan auri mutumin da ban sani ba ban taba gani ba, sannan kuma tafiya zai

yi dani can wajen ci-ranin sa ya rabani da mahaifina wanda shi kadai nake da shi a duniya.
Amma rashin yardar tawa bata kara komai ba, washegari mahaifina ya daura min aure.
Bayan gama daurin auren yana kokarin shiga gida ya fadi, faduwar da ta zamo numfashin sa na
karshe.
Kwana uku da rasuwar mahaifina makota sun tayani zaman makoki, kowa ya tausaya mun,
na zama abun tausayi, hankalina ba ya kara tashi sai na tuna auren da mahaifina ya daura min.
Na tsani auren na tsani mai dabbobin tunda bashi da zuciyar musulunci da ba zai iya yafewa
mahaifina asarar data same shi ba, zai ce ayi masa biyan bashi dani sabida rashin sanin
darajar dan adam.
Washegari sai ga mata uku sun zo wai sun zo tafiya da ni, daya tace sunan ta Yagana matar
Yayan mijin nawa ce, sai matan abokinsa guda biyu. Ina kuka ina komai haka suka fidda ni
daga gidan mu ko wanka babu, a gidan Yayan sa Malam Kyari aka bamu daki wai zuwa sati mai
zuwa zamu wuce Kano inda yake ci-ranin sa. Ban ga mijin ba sai da daddare. Ya manyanta sosai, ga shi bakikkirin ga rashin kyawun gani,
ni duk ba wannan ne damuwata ba yadda zan zauna daki daya da shi. Ga dakin ciki daya falle
daya. Ya cire babbar rigar sa ya rataye ya jawo ledar da ya shigo da ita yana ta far'a yace
"Amarya Bilkisu taho ki ci, ki kwantar da hankalin ki ni mai kaunar ki ne, na dade ina son ki,
kuma na gayawa Babanki yace shi bazai aurawa kowa ke ba sabida baki da kowa a kasar nan,
burin sa shine ku koma Chadi cikin dangin ku.
Nayi duk iya kokari na ba abinda ban bashi ba amma ya ki karba. Sabida haka ne na bashi
ajiyar dabbobi na kuma biyo dare na kwashe abina don in samu hanyar mallakar ki. Gashi
dabara ta tayi min amfani, saidai ban ji dadi ba da ya rasu ban nemi gafarar sa ba. Na so bayan
auren mu in gaya masa cewa ni na kwashe dabbobin". Na daga rinannun idanuna ina kallon mutumin nan da wata irin tsana...tsanar da ban taba
yiwa wani dan adam a duniya ba, kawai sai na sa kuka mai cin rai. Ya kawo hannu wai zai
lallashe ni na kai masa mahangurbar data sa dole ya ja da baya. Ya sake kokarin kamo ni na
buga tsalle na bar dakin da gudu. A ranar a dakin Yagana na kwana. A gabadaya kwana bakwai din da aka ce zamu yi a garin Damaturu ban kara yarda na shiga
wancan dakin ba, nasiha da lallashin duniya matar Kyari ta yi da shi kanshi Yaya Kyarin, amma
bana ce musu komai sai kuka. Tunanin makomar rayuwata nake da ba uwa, ba uba, babu dangi
sannan bansan asali na ba, abinda na sani kawai shine daga Western Chad muke. Bayan
wannan bansan komai akan iyayena da asalin su ba.
Sannan ga auren wannan azzalumin mutumin! Yo azzalumi mana! Wanda ya sanya
mahaifina cikin kaka-ni-kayi don biyan bukatar zuciyar sa. Ya raba mu, rabuwa ta har abada.
Don na tabbatar

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login