Showing 27001 words to 30000 words out of 36679 words

Chapter 10 - Rana Daya Book 2 By Halima Abdullahi k Mashi

ma in ka aje in ba a yi sa’a ba kafin kuyi wata daya makota sun soma jin ku.”
Shatima ya ce, “Ai kaina ya kulle, basirar tawa duk ta toshe, ka riga ni aure dai, ka san kuma
yanda kowane Maigida yake takama da ikon gidansa.”
Munnir ya ce, “Haka ne.” Shatima ya ce, “To sai a ce an tauye maka wannan ikon.” Munnir ya
ce, “Abin da yafi kawai ka cije ka hana, ka ce ba ka bada izini ba, nasan dai za a dan samu
fushi da sauransu kayi lallashi daga baya. In ko ba haka kayi ba, tabbaci hakika matsalar ta
samu gindin zama. Shatima ya ce, “Haka ne, bari in koma gidan kawai da na fito ne nayi fushi a kan in sun tafi
suma wuce Kano don ni.” Munnir yayi dariya. “Ai ka tsaya a namijinka nawa.”
Shatima ya ce, “Har ina son in kira Hajiya itama in ji ta bakinta.” Munnir ya ce, “Kar ka sake kayi

wannan kuskuren, domin zaka yi da na sani a gaba. Bari in fada maka wata magana abokina,
duk rintsi kar ka sake ka sako iyayenka a cikin abin da ya shafi matsalar gidanka.
Na farko zaka jona raini tsakanin Mahaifiyarka
da matarka, domin ka san suma iyayenmu sai a hankali, basa so a ce kaza laifinmu ne, don
haka sai kaga sun dora mu kan shawarar da mu zamu fitamma zamu cutar da iyalanmu.
kuma kayi rashin sa’a a goyi bayan matar kai kuma kiri-kiri ka dinga cutuwa. Don haka kar ka
sake ka zama mai kai matsalar cikin gidanka ga Mabaifiyarka, shi ke haddasa irin rikicin nan na
tsakanin sirika da sarakuwa, wanda har yanzun an kasa cimna nasarar kawo karshen wannan
lamarin shekaru masu yawa. Kawei abokina ka zama wanda kullum iyalansa suke ganin girman darajar iyayensa. Su kuma
iyayenka kullum kana fada musu labari mai kyau, mai faranta rai daga iyalansa.
Kai ko wata ce cikinsu ta kai kararka gurin Mahaifiyarka, in kaje kar ka ce ita ce ta min kaza da
kaza, ka ce ayi hakuri zaka gyara.”
Shatima ya ce, “Amma dai na gode da wannan shawara, in Allah Ya yarda zan kiyaye. Shi yasa
a ka ce me shawara aikin sa baya baci, sai dai asirinsa ne a tone.” Suka sa dariya, sannan suka
yi bankwana kowa ya kashe waya.
Ya aje mota ya nufi dakin Amna. Tana zaune a kan Dining tana cin kwai da Tea. Ya kalleta, “Sai
yanzun ki ke karyawa?”
Gira ta daga masa alamun “Eh.” Ya ce “Me yasa? Ki daina wasa da abinci ba fa ke daya ba ce
yanzu.” Ta ce, “Na gama hada abin da ni ke bukata ne, kar ya zo ya yi tajirana, ban dauki kayan
sawa ko daya ba, don ina da kaya a gida a dakina. Ko lefena ma yana can…” Ya katse ta da
cewa, “Ina wai za ki je ne kina ta fadin kar ya zo ya yi ta jiranki.” Ta cc, “Sau nawa zan fada maka cewa Dad ya ce a zo a tafi da ni.” Ya ce, “Amma Dad din bai
fada min ba. Ya za ayi ki tafi ba tare da neman izinina ba
Cikin mamaki ta kalle shi ya wani hade rai. Ta ce, “Dad dina fa na ce, ko ba ka ji da kyau ba
ne?” Ya ce, “Naji ki sosai, amma tafiyarki kiran Dad din naki ikona ne ba ikonsa ba, don haka
bisa ikona babu in da za ki je, ki kira shi direban a waya ki ce masa ya juya.”
Ta mike a fusace, “Shatima kana son ka ce min za ka hada kanka da Dad dina? Shi ne fa ya
haife ni ya raine ni, ya sani Makarantu mafi tsada a in da muke, har waje ya kai ni a can ka
ganni ka ce,
kana sona. To don Allah ka dawo cikin hankalinka bana son mu samu matsala, don… ihun
murna da Summy ta shigo da shi, shi neya katse Amna daga zafafan maganganun da ta
tanada don fesar ma mijin nata. Ta rungume
kanwar tata, tare da nuna murnar ganinta. Sumayya ta kai hannu ta shafi cikin Amna tare da
fadin “Na riga Dad taba Baby.” Amna ta saki dariya tare da tambayar ko sun yi muhawara ne?
Sumayya ta ce “Ai ba su san na biyo dircba ba, domin Dad yacd babu wanda zai fara shafa
Baby.”saishi Amna cikin dariya ta kalli Shatima, wanda ya harde hannu yana kallonsu. Ta ce, “Honey dubi
son kudi irin na Summy. Bai ce komai ba, Sumayya ta dan risina “Ina yini Ya Shatima, ban
ganka ba fa.” Ya ce, “Ai ba za ki ganni ba, idonki ya rufe.” Suka yi ciki suka bar shi nan
tsaye.malala Kafın yayi wani tunani har sun fito, me aikinta dauke da dan karamin akwatinta. Sumayya da me
aikin suka yi gaba, bayan ta ce “Yaya har da kai zamu?” Ya ce “A ‘a ina da office Summy.” Ta

ce, “Yau Sunday.” Ya ce, “Gobe ni ke nufi
nima.” Amna ta kalle shi, “Honey sai mun yi
waya.” Ya ce, “Za ki tafi ba da izinina ba? Za ki tafi cikin fushin Allah da tsinuwar Mala’iku?”
Amna ta ce, “Ni ban gane zantukanka ba, in ka gama fushin zamu yi waya.” Ta fice abinta. Bai
fito ba har sai da ya daina jin sautin motarsu. Ya fito ya kulle dakin ya nufi dakin Nafisa.
Kan kujera yaje ya zauna ya zabga tagumi. Nafisa ta zo ta zauna kusa da shi, ta dafa shi.
“Lafiya kuwa?” Shatima ya ce, “Kanshi ke ciwo.” Ta ce, “Gashi babu magani a gidan ko za’a aiki
direba ne ya siyo?” Ya girgiza kai tare da lumshe
ido. “Gajiya ce da kai-kawo, in ya dan huta zai daina.” Ta rage TV sannan ta ce, “In baka guri
ko?”
Ya ce, “Ta zauna.” Ya janyo ta jikinshi suka yi shiru. Yana ta son ya danne bacin ranshi, yana
karanta ma ranshi cewa ga wasu matan nan yana da su, me zai sa ya damu kansa da bakin ciki
don ta tafi? Amma duk da haka ya kasa.
Ya mike zumbur! Nafisa ta bi shi da kallo. Ya nufi dakin shi, ya canza kayan jikinshi zuwa
shadda. Yasa hula da takalmi, yana saka turare Nafisa ta shigo. Ya ce, “Zariya zan je.” Ta ce,
Lafiya kuwa?” Ya ce, “Lafiya lau.” Ta ce “To sai ka dawo.”
Ya leka dakin Aliya, ya ca “Beri ya shiga Zariya ya dawo.” Ta ce. “Allah ya tsare hanya.” Ya isa
gun Salma. Tana jin ya ambaci Zariya ta daka tsalle ta ce, “Yaya in zo muje?” Sai ya ji wani
mugun bacin rai ya taso masa tamkar ita ce Amna.
Ya shigo rai bace “Ina za ki zo muje? Don na ce za ni Zariya za ki ce ki zo muje, ni sa’anki ne?
kin san me zan je yi ne? in ki ka kara yi min irin wannan sai na miki dukan tsiya!”
Salma ta tsorata iya tsorata, jikinta sai kar
karwa yake, tana mamakin dama haka Shatima ya
iya fada? Tsaki yaja sannan ya fita. Tayi ta kuka,
Tsonsa ya darsu a zuciyarta.
Kai tsaye gidan su Munnir ya nufa, don ya kira shi cewa ga shi nan zai shigo Zariya ina zai
same shi? Ya ce, Gida. A kofar gida suka tsaya don ya ce ba zai shiga ciki ba.
Ya ba Munnir labarin yanda aka yi da yaje gidan. Munnir ya ce, “To fa! Ai shi kenan tunda an
riga an yi.” Shatima ya ce, “Kar ka ji yanda raina ke baci, ni kaina ai zam fi so a ce suna kusa da
ni
ina ririta cikina. Amma nayi alwashi a zuciyata ba zan je ba har ta dawo.”
Munnir ya ce, “In kayi haka ba laifi ba ne, amma kar kayi. Ka kira waya kuma kaje. Ta yiwu su
basu da ilimin sanin mahimmancin aure, ko bambancin da ke tsakanin miji da kuma iyaye. A
hankali za ka ke nusar da ita, har ta gane. Kai
kuma ka kwantar da hankalinka, ka sani ma ko
cikin sauran wata na da cikin?”
Shatima ya ce, “Nayi ta kokarin in cire abin a raina, amma na kasa.” Haka dai Munnir yayi ta ba
shi shawara kafin suka rabu. Yaje ya gaida su Hajiya, take tambayarsa “Lafiya da yamma?” Ya
ce, “Lafiya lau, yaje gurin Munnir ne akwai abin da suka yi.”
Ta ce, “Ina mai jiki fa, laulayi da sauki?” Ya ce, “Ta ma tafi gida dazun.” Hajiya ta ce, “Gida
kuma?” Shatima ya ce, “Eh, ai za su dubata na musamman ne.
Hajiya tayi dariya, “Kadan da aikin masu hali, shima dan zai ga gata.” Shatima dai ya ce,
“Umm!” Ya mike yayi mata sallama.

A hanya yayi Magriba. Koda yazo yayi fakin ya jima cikin mota yana takaici kafin ya fito. Har
[8/19, 11:38] Ummi Tandama😇: *🏚️RANA DAYA BOOK 2🏚️*


CHAPTER 13



*BY HALIMA ABDULLAHI K/MASHI*

*Wannan littafin na kudi ne akan farashin 300,idan kuna bukata zaku turo kudin ku ta wannan
account number👇🏻*

```ACT<<0700549935
Halima Abdullahi Access bank sai ku turo shidar biya ta wannan number 09028485925```

*Ko kuma katin Mtn ta wannan number 09068032427 Ga masu son Audio na littafin RANA
DAYA shima muna dashi cmplt ku turo kudin ku ta account number din da muka bada can
sama👆🏻👆🏻ko kuma katin Mtn ta wannan number 09068032427 idan baki shirya siya ba ki bari
sai kin shirya sai kiyi magana*
*Masu son tallata masu hajar su suyi magana ta wannan number 09068032427 zamuyi maku
cikin sauki*


ya nafi dakim Nafisa sai ya tuna yau a gurin Salma yake. Ya juya ya nufi dakinta.

Tana kan Darduma a can kuryar dakinta, tunda

tayi sallah ta kasa tashi, ga faduwar gaba don

lokaci-lokaci sai ta dafa Kirji. Matuka ta tsorata da

fushin Shatima, har yana fadin zai mata duka!

Tana jiyo sallamar Shi tsoro da fargaba suka

hanata amsawa. Ya aje• hularshi a kan kujera ya

nufi kicin. Ya dauko goran ruwa guda daya, ya zauna.

Duk da babu sanyi da ya daga sai da ya sha fin rabi, sannan ya aje goran. Yayi ajiyar zuciya. Ya

dauki wayarsa ya kira Nafisa, tana dagawa ya ce ta kawo masa jakarsa nan dakin Salma.

Babu-gardama Nafisa ta dauko ta nufo dakin Salma. Da alamu wannan bacin ran na Shatima
ya saka matan nashi, shiga taitayinsu, musamman Salma.

Tayi sallama a Rofar dakin ya daga murya ya

Ce Shigo mana, kin coge kamar wadda za a cinye

ta." Ta shiga ta mika mishi tare da fadin "An lafiya?" Ba tare da ya kalleta ba ya ce, "Lafiya?"

Ta wurga, ido tana kallon falon Salma, cikin

mamaki duk da take ji a family ana cewa su Salma

matsiyata Ne bata yi tsammanin tsiyar har ta kai

haka ba.

Ta taba baki tare da fadin "Uhum!" Ya dago

daga kokarin da ya ke na ciro Laptop a Jaka ya ce,

"Ya ya?" Ta girgiza Kai tare da sake kallon dakin

ta ce, "Babu komai,

' Ya ce, "To kina iya tafiya.

Ya fahimci dakin take ma wanna yatsinan.

Salma da ke ciki tana jin su. Lokacin tana ta

shawara a kan ta fito ko kar ta fito? Jin fitar Nafisa

sai ta yi ta maza ta fito.

Cikin tafiya tamkar Wahainiya ta nufi kicin. Ta

dauko Tiren da ta jera kuloli guda biyu, daya farar

shinkafa daya miya. Sai dan karamin kwanon silba

da ta zuba naman yau farfesun shi tayi.

Ta bude dan kwandon da ta yanka ganyen latas

da kokumba, shima ta dora.Ta.zo ta dire tiren, kan ya zube ma saboda

yanda jikinta ke Bari ta sauke daga tiren ta jere, ta koma ta dauko cokali da plate, da goran
ruwa da kofi.

Ta dago da niyyar tambayarshi ta zuba.mishi, sai suka hada ido. Cikin sauri ta sadda kanta har
da dauke numfashinta. Domin ta zaci zai antaya mata mari ne.

Jin shiru ta sake dagowa. Muryarta na rawa taCe.

"Yaya in zuba maka?"Na koshi.

* Ya fada a daKile. Da gudu ta mike kuma a rikice zata yi daki, tamkar ya kwashe da dariya sai
ya dake yace.Ke" Kamar zata saki fitsari ta tsaya cak amma ta kasa waiwayowa.

Ya ce,

"Zo nan ki kwashe kayanki, ko nine zan kwashe miki?"

•Ganin rawar jikin tata zubar da abincin a kofar kicin, da rasa me zata yi sai ta fashe da kuka.
Yana kallonta yayi murmush: ya dauke kai Ta kwashe ta kai kicin, tazo ta haye gado ta
kudundune.

Lokacin ne Shatima ya samu dama har ya yi dariya sosai. Sai kuma ya ji zuciyarsa tayi masa
sauki. Ya yarda da batun Likitoci, da suka ce dariya tana rage damuwa.

Yana bude aiki zai fara, sai •yaga sakwanni a

Emel din sa. Tun karfe uku sakon ya shigo cikin akwatinsa, suna da meeting a Abuja karfe tara
na safe.

Yayi hamdala da yaga sakon yanzu, da sai da safen zai gani.

Dole Zai yi bukin din jirgin safe na karfe

takwas.Salma bata yi bacci sosai ba, tana jin Shatima

ya shigo har da gyara mata kwanciya. Tana jin shi yayi alwala ya tada nafila.

Da asubahi ta tashi tayi sallah, ta fito zuwa kicin. Kan sallaya taganshi yana karatun Alkur'ani,
irin dan Karamin nan.

Taje ta dafa ruwan zafi, sannan ta soma suyar

dankali kafin shida ta hada komai. Ta fito ta samu ya fito wanka yana cikin dakinta yana saka
kaya.

Tsam! Ya tsuke cikin suit bulu me duhu, rigar ciki bulu me haske. Tayi saurin dauke kanta

lokacin da taga zai waiwayo. Ya iso gurinta, tayi saurin tsugunnawa tana fadin, "Ina kwana?"

Ta dauke numfashinta jin bai amsa ba, kuma

bata yi zato ba sai taji an kama kafadunta an mikar da ita. Idanunta a lumshe hawaye suna
kwaranya.

Cikin taushin murya ya ce,

"Salma!" Ta bude

idanunta a hankali, sunyi jajir. Ya ce, '

"Wai kukan me ki ke yi haka?"

Cikin rawar murya ta ce,

"Ban san ranka zai baci ba, jiya wallahi da ba zan ce zan bi ka ba.

Ba zaton shi ta sulale Kasa kan gwiwarta.

"Ka yafe ni don Allah." Ya zauna a kan kujera. "Tashi

ba kiyi min laifi ba, jiya ne raina yana baci ba laifinki ba ne.

* Ya dauki hankicin shi da ke gefe

Ya share mata hawaye.

Ya ce,

"Tashi ki kawo min abin karin.

" Ta ce,

"Na kawo.

" Ta juya don hada mishi shayi. Yana

kallonta tun da ya hada shayi a gabanta, shi kenan kullum haka take hada mishi babu kuskure

Suga da yake irin ta kwali yake amfani da ita ta san adadin da yake so. Ta mika mishi, sannan
ta sa cokali me yatsu ta ciro

mishi yankan Biredi guda,uku, tasa a cikin plate,

sannan ta aje mishi kwai da dankali.

Ya ce,

"Sannu da Rokari, kina Koari sosai

Ta dube shi "Na gode.

" Cikin jin dadi ta nufi kicin

don kammala kayan da ta yi aiki da su. Yana goge baki da 'yar takardar share baki. Ya ce, "Zan
tafi Abuja.

Ta dan ware ido cikin mamaki ta ce,

*Kuma yaushe za ka dawo?"

Yace "Yau insha Allah

Ya nuna mata dubu daya a kan kujera, "Ga kudin namanki nan.

" Ta ce,

"To Allah Ya dawo da kai lafiya." Ya shafa kumatunta "Na gode.

Ya fita ta koma kicin ta ci gaba da aikinta. Ya sallami sauran ya fita. Maigadi ya ce,

"Alhaji yau motar babu lafiya ne?" Ya ce, "A'a zan hau Jirgi ne zuwa Abuja, yanzu zan dauki
motar haya ne.

YADDA ZAN FAHIMCI MUJINA

Na daya, na fahimci baya cin danyan kifi, na biyu ba ya son a shiga huruminsa in yana cikin
fushi, na uku yana son komai a gaskiya.

Tayi murmushi da ta karanta, a fili ta ce,

*Insha Allah sai na gama fahimtar halayensa.

* Ta tashi ta maida littafin. Ta dauki kudin nama ta fita zuwa gurin Maigadi, sai aka kwankwasa
Kofa

Yaje ya bude, cikin mamaki sai ta hango Yaya

Hadiza, cikin mura taje ta rungumeta. Ta dauki Amira don murna. Yaya Hadiza ta ce, "Duk cikin
murnar za ki dauki wannan Katuwar yarinyar"?"

Da gudu ta dawo ta ba Maigadi sako ta Koma.

Hadiza ta ce "Kin gan mu sai yau ko?" Salma taCe Wallahi kullum ina ta kewar Inna, ya ba kuzo
da ita ba?"

Tace

"Sai ta fita takaba sannan zata zo Suna ta hira, Hadiza tace

"Kin yi fari kin Kara dan Tsawo, amma ba kiba.

Salma ta Ce,kuma sai ina ganin kamar nayi Kiba." Ta ce, '

"Kin dai yi kyau, Kila Kibar sai nan gaba.

Ranar ta yini har yamma suna hira. Ta ba Salma shawarar yanda zata dinga adana kudi

maimakon cin kilon nama kullum. Ta ce, "Na dari uku ya ishe ki, sauran sai ki ke adanawa. Sai
ki ga kin tara kudin da za a gyara miki daki, duk abin da babu a sai miki kafin Allah ya ba ki ciki
ki haihu mutane su zo."

Salma tace

"Sai dai in tambaye shi in ya yarda, don bana son in yi masa rashin gaskiya, na kula ba ya son
haka.

Hadiza tace Ke amma sakarai ce ko? Ance miki maza suna son a rage musu kudin cefane ne?"'
Salma tayi shiru a ranta tace

*Don shawara na

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login
google.com, pub-9213700357025247, DIRECT, f08c47fec0942fa0