Showing 24001 words to 27000 words out of 36679 words
Chapter 9 - Rana Daya Book 2 By Halima Abdullahi k Mashi
ba fa karamin
Soja ba ne. Ai ko da na hada ta da matar nan, kin san Allah yanzu baya wannan yawon, kuma duk hakkinsu
da ke wuyanshi yanzun yana saukewa, har da mota ya sai mata yanzu.”
Nafisa cikin fara’a ta ce, “Ai ko zan ansa.”
Anty ta ce “Amma fa suna da tsada, Allah Yasa
dai kina da kudi.” Nafisa ta tabe baki, “Ina zan ga
kudi? Kin san Allah sisi bai bani ba, ban san suba”
Ta ce, “Zan biya miki wannan, gaba na san za ki zo da kudinki.” Nafisa ta ce, “Nawa ne kudin?”
Tayi dariya tare da fadin “Kyaji in lokaci ya yi.’ Nafisa taji duk kuncin da ke ranta ya kau, sannan
taji tana jin yunwa, dama dai burinta ta zama ‘yar gaba-gaba a gurinsa.
Daidai wannan lokacin Salma ta fito gurin Maigadi zata bashi sako. Tana jin kunyar aiken
dattijon wanda tasan zai haifi mijinta ma bare ita. Ta risina.
“Baba dama sako ne zan baka.” Ya ce,
“Alhajin ya fada min. Ta mika mishi dubu daya, “Kubewa danya ni ke so da kuma nama.” Ya ce,
“Kubewa ta nawa?” Salma ta dan yi shiru, bata san ta nawa zata isheta ba, don haka sai ta ce
bari in tambayo Anty.”
Ta samu Aliya tana kallo, ta ce “Anty kubewar nawa zata ishe mu ni da Yaya?’ Aliya ta ce, “Ta
dari daya ma kacal ta isa, yau kuma tuwo za ki yi?”
Ta ce, “Ya ce yana son cin tuwo ne in yi
mishi.” Aliya ta ce, “Lallai kuwa, sai ki dage kiyi
shi me kyau yanda zai ci.’ Salma cike da wauta ta
ce, “Hala ya fada miki bai taba cin abincina ba?”
Aliya ta ce, “Ya fada min wai ba ki iya girki ba.” Ta fada cike da son tura ma Salma haushi.
Salma ta saki dariyar wauta. “Ai yau zan bashi mamaki, zan yi tuwon da zai yi santi.
Aliya ta taba baki, a ranta ta ce, “Wannan sokuwa ce, to sai ya ci tuwon in gani.” Ta ce, “In
ko haka kike so sai ki sa kifi, kubewa danya tafi dadi da kifi.”
Salma ta ce, “Haba?” Aliya ta ce, “Allah kuwa.” Salma ta ce, “Dama na gaji da cin nama. Kullum
sai na sa kilo daya a dan abincina, kuma baya ci.” Aliya ta ce, “Ai gashi nan kin soma kyau.”
Salma ta ce, “To bari in je in sa ya siyo min da kifin.” Aliya ta saki dariya bayan tafiyar Salma ta
ce, “Shashasha. In ni ce ke bani da da, bakina ni kadai kullum a bani dubu daya ta kilon nama
ai tarawa zan.
Bai zama dole in ci ma nama kullum ba. Amma ba zan fada mata ba tayi ta dirkar namanta. Ta
ba Maigadi kudi, ya siyo mata kifi da kuɓewa.
Da ya dawo sai ya kawo mata kifi busasshe da kubewa, ya kuma bata canjin dari uku. Ya ce, ta
ce kayi na mota Baba. Ya ce, “Eh har ma na sai goro na ashirin in nayi canji zan ba ki.” Ta sake
daukar Naira dari ta ce, “gashi Baba ka kara, wancan ma ka bar shi.”
Ya ce “To na gode.” Ya amsa. Har zata wuce ya ce, “Hajiya za ki ga na siyo miki kifi busasshe,
Maigidan naku ba ya son danye. Domin waccan satin , Hajiya din nan ta karshe.”
“Bani in sai mata.” Sai Alhaji ya ce, “Kada tayi abinci da danyen kifi don ba ya so.
Salma ta ce, “To’na gode Baba.” Ta wuce ciki ta koma aikinta. Ta nutsu sosai ta zauna a gaban
girkinta, ta gama ta kwashe a bakar leda guda biyu ta sa a kula.
Sai ta saka sauran ta kai wa Maigadi, don kullum ita ce kadai ke kai mishi abinci, sannan ta
dumama abincin ta na jiya ta taci.
Da yamma tayi wankan ta tasa leshinta na akwati, don sabbin kayan ta ke ta mirtsika tunda ba
a sako mata kayanta na gida ba, dama sun tsufa.
Sai da yayi Ishsha ya shigo gidan don yaje yayi aski. Yana shigowa ya wuce wanka. Da
jallabiya ya zo ya zauna zaman cin tuwo, tana budewa ta juye a plate. Ya ce, “Iye! Lallai yau zan
ci tuwo.”
Ta ce, “Naga kullum nama shi ne nasa maka kifi.” Cikin sauri ya ce, “Kifi?” Ta ce, “Bushasshe ne
fa.” Ya ce, “Amma miyar bata yi karni ba dai ko?” Ta ce, “Har citta nasa don kada tayi karni.” Ta
bude jikinta a sanyaye.
“Ci kaji kuma.” Ya shaki kamshin, bai ji karni ba, don haka ya ce “To ba ni cokali.” Shi kanshi ya
ji mamakin tuwon da ya ci. Tare suka ci da Salma har da suka rage ya ce tayi masa dumame da
safe
Ta ce, “Dama kana cin dumame?” Ya ce, “Ni da dumame nasan dadin tuwo ma, gidan Kaka in
na kwana lokacin ina dan makaranta Kaka take yi min, sai ta ce dumamen gata, tasa min man
shanu har da yaji.”
Salma tayi ta dariya “Nima ina son manshanu. Ya ce, “To zai siyo muku.” Ta ce, “Ka ce zamu yi
maganar zuwanmu Zariya.” Ya ce, “Bari in kira Auwal ya kai ma Inna ku gaisa, shi kenan?”
Ta ce, “Allah Sarki, ka ce min zan je.” Ya ce”Ban ce haka ba fa, na ce ne in na dawo zamu yi
maganar. Ta ce, “To yaushe za ni?” Cikin shagwaba take yin maganar. Ya ce “Sai kin yi kiba
tukuna.” Ta ce, “Don Allah Yaya ina son ganin Yaya Hadiza ma.” Ya ce, “To ki bari sai kin kara
kyau. Ta ce, “Ya za ka gane na kara kyau?” Ya ce, “Ai ina kallonki kullum.” Ta ce, “Me na kara?” Yace
“Haske kadai ki ka kara, sai fatar ki da ta soma murjewa, Ta tashi ta dauko dari biyun ta ce,
“Gashi canjin ka na tuwon.” Ya ce “Har da canji?” Ta ce, “Eh.” Ya ce, “To ki aje min.” Ta ce, “To.”
Ta tashi taje ta aje.
Baccin Amna ya soma damun Shatima, domin yau da ya ke dakinta ma baccin take kwasa
babu alamun zasu yi wata hira, shi kuma yana da bukatarta.
Yayi ta tashinta da kyar ta tashi zaune tana zuga hamma. Ya ce, “Amna!” Ta dube shi idanu
lumshe, ta ce “Umm, don Allah Honey bacci nake ji.” Ya ce, “Amna, ki tashi don Allah.”
Ta kara cewa “Please, ka bar ni mana.” Ya ce, “Allah sai kin tashi.” Ya girgizata. Ta tashi,
“Honey kaina ciwo yake yi, in ban yi bacci ba.” Ya ce, “To kin ci abinci?” Ta ce, “Bana jin yunwa,
sai bacci.”
Ya ce, “Kai ki tashi muje asibiti.” Ta ce, “Ni
lafiyata lau, bacci ne kawai matsalata.” Ya bar ta
yazo ya gama duk abin da zai yi kafin ya kwanta.
Sannan yaje ya jata jikinshi ya kwantar suka ci
gaba da bacci.
Da kyar yasa ta tayi sallar Asubahi, don haka ya soma tunanin lallai babu lafiya. Ya kira Aliya a
waya da safen yana tambayarta me yake saka mace yawan bacci? Aliya ta ce, “Dalilai da
dama, ciki har da shigar ciki.”
Ta ce “Wacece?” Ya ce, “Amna ce, yanzun ya za ayi a gane?” Ta ce, “Gwajin fitsari, tayi a wani
abu ka kawo in gwada.”
Da yake ranar Asabar ce ba shi da aiki, bai ko fito gaida saura ba, yana dakin ya sata gaba
yana kallo “An ce tana da ciki.” Sha daya ta farka da yunwa, ya ce tayi wanka taji karfin jikinta.
Ya ce”Me za ta ci?” Kafin ta fito yasa me aikin ta tanadar mata. tana ci zuba mata ido yayi. Ta
ce, “In za ka ci muci mana.” Ya ce, “A’a ki ba babyna ya koshi.” Ta saki dariyar da ta sa ta ta
kusan kwarewa.
Ta cc, “In ji wa?” Ya ce, “In ji masu ilimin abin. Yanzun ma fitsari za ki bani in kai a gwada. Ta ce,
“Wa zai gwada?” Ya ce, “Aliya kin san Nurse ce. Ta ce, “Wace ce Aliya kuma?” Ya ce, “Ta dakin
farko.”
Ta tabe baki “Oh, dama a nan gidan take? Ya ce, “Eh.” Ta ce, “Cikin matanka?” Ya ce, “Eh.” Ta
girgiza kai “Ba wadda zan ba fitsarina, don ni ba tsararsu ba ce. Kuma bana dauke da wani ciki
domin lokacin al’adata bai yi ba bare in tabbatar. Abin da na sani bacci lafiya ce, ina rama
baccin da ban yi ba ne a baya lokacin ina Makaranta, da kuma lokacin biki.” Yayi murmushi, “Shi kenan muje asibiti.” Ta ce, “Wane irin asibiti, ba zan je ba.” Ya ce “Shi ke
nan.
Aliya tayi ta damuwa tana son jin me ake ciki da batun cikin Amna, ga na Nafisa. Koda ta kira
Shatima cewa taji shiru bai kawo fitsari ba. Ya ce, “Ashe babu komai ta bar shi kawai.”
Suna cikin hira ta gama cin abinci, sai taji zuciyarta na tashi. Ta ce, “Honey zuciya tana tashi,
naci abinci da yawa.” Ya ce, “To kin taba jin haka?”
Ta ce, “A’a sai a ‘yan kwanakin nan. Abin kamar wasa Amna ta shiga bandakinta tana sheka
amai. Nan fa Shatima ya ce sai sun je asibiti. Ita kuma ta dage ai taji daidai da ta yi amai din.
Yayi ta lallashinta amma ta ki. Ya kira Hajiayrshi ya kai mata kara. Nan take ta kira layin Amna,
cikin sigar lallashi ta ce, “Amna ta yarda taje a dubata.” Ta ce, “To Hajiya.” Ta dube shi, “Ka ci
albarkacin Hajiya.”
Sai da suka yi sallar Azahar sannan suka shirya zuwa asibiti, doguwar riga ta saka da dan
mayafinta, shi kuma yasha kananan kaya. Sun yi kyau abin su sosai
A kan idon Nafisa da Aliya suka wuce. Kowaccansu da abin da ta kisima a zuciyarta. Cikin gari
suka shiga, in da ya kaita wani asibitin kudi gwajin nan take kala biyu suka yi mata.
Cikin sati uku da kwanaki ya bayyana. A gaban Likitan Shatima ya rungume Amna. A nan ya
kira Hajiyarshi ya fesa mata. suna hanyar dawowa a mota Hajiyar ta kira shi.
Ta nuna matukar murnarta da samun cikin, kuma ta ba ta shawarwari matsayinta na uwa.
Amnar tayi godiya, suka yi sallama. Har suka kai gida Shatima na yiwa Amna sannu da zaran
sun hada ido.
Da ya tsaya da mota kuma bayan sun kawo gida, cikin shagwaɓa ta ce sai dai ya dauke ta. Ya
ce, “In kullum ki ke son in dauke ki wannan abu ne mai sauki.” Kafin ta ce da wasa take yi har ta
ji ta caraf a hannunshi ya yi sama da ita, yasa kafa ya rufe motar.
Bai dire ta ko’ina ba sai a kan gadonta. Ya kira Aliya a waya ya fesa mata. Tayi murna sosai a
wayar amma a can kasan zuciyarta takaici ne da damuwa.
Ranar yana dakin har bayan Isha’i, sai da suka yi sallah yaga ta dan ci wani abu sannan ya
lallabata tayi bacci, sannan ya fita bayan ya fada ma mai aikinta cewa ta kula da ita saboda
dare.
Dakin Nafisa ya nufa dama can yake, in san
ranshi ne yaje ya duba Salma don bata da wayar da
zai ji laifiyarta, amma baya son mitar Nafisa. Lokacin da ya shiga gurinta ba ta falo, dakin shi ya
shige don ya yi wanka, bai neme ta ba ne don yasan yanda suka rabu.
Haka ko ya shigo dubata a ranakun da ba ya dakinta gaisuwa ke hada su. To bai san irin tarbar
da zata yi masa ba yau. Ya fito daure da Tawul ya ganta cikin kwalliya ta aje masa goran ruwa
da kofi a gefen gado kamar yanda aka saba.
Ya kalle ta cikin murmushi, a ransa ya ce, “Yau da akwai abin arziki.” Ta miko masa kayan
baccinsa yasa, ya dube ta. “Turarenki yayi min kamshi sosai.” Ta fadada fara’arta. “Haba?” Ya
ce, “Sosai ma, za ki sammin?”
Ta ce, “A’a, za dai ka dinga shakar sa a jikina.” Yayi ‘yar dariya. “Hakan ma na gode.” Ta ce,
“Muje ka ci abinci ko? Kus-kus ne nayi maka da fa-dukan shi, yayi dadi.” Ya ce, “Lallai kuwa kin
ce yau in ci har in kasa tashi.” Suka yi dariya gaba daya.
[8/18, 17:54] Ummi Tandama: _____
*️RANA DAYA BOOK 2️*
CHAPTER 12
*BY HALIMA ABDULLAHI K/MASHI*
*Wannan littafin na kudi ne akan farashin 300,idan kuna bukata zaku turo kudin ku ta wannan
account number*
```ACT<<0700549935
Halima Abdullahi Access bank sai ku turo shidar biya ta wannan number 09028485925```
*Ko kuma katin Mtn ta wannan number 09068032427 Ga masu son Audio na littafin RANA
DAYA shima muna dashi cmplt ku turo kudin ku ta account number din da muka bada can
samako kuma katin Mtn ta wannan number 09068032427 idan baki shirya siya ba ki bari
sai kin shirya sai kiyi magana*
*Masu son tallata masu hajar su suyi magana ta wannan number 09068032427 zamuyi maku
cikin sauki*
Mun tsaya
Haka ko ya shigo dubata a ranakun da ba ya dakinta gaisuwa ke hada su. To bai san irin tarbar
da zata yi masa ba yau. Ya fito daure da Tawul ya ganta cikin kwalliya ta aje masa goran ruwa
da kofi a gefen gado kamar yanda aka saba.
Ya kalle ta cikin murmushi, a ransa ya ce, “Yau da akwai abin arziki.” Ta miko masa kayan
baccinsa yasa, ya dube ta. “Turarenki yayi min kamshi sosai.” Ta fadada fara’arta. “Haba?” Ya
ce, “Sosai ma, za ki sammin?”
Ta ce, “A’a, za dai ka dinga shakar sa a jikina.” Yayi ‘yar dariya. “Hakan ma na gode.” Ta ce,
“Muje ka ci abinci ko? Kus-kus ne nayi maka da fa-dukan shi, yayi dadi.” Ya ce, “Lallai kuwa kin
ce yau in ci har in kasa tashi.” Suka yi dariya gaba daya.
Bayan ya gama da abincin kuma ya jinjina mata. Nafisa ta sha mamaki a kwanciyarsu, yanda
ya tara da ita sau biyu a daran. Sannan da safe da yake Lahadi ce yana makale da ita sai gurin
tara sannan ya tashi ya yi wanka.
Tayi ta tabara wai ya gaji da ita ba za ta iya tashi ta shiga kicin ba. Ya ce “Zauna in shigar miki.”
Shi ne ya hada musu abin kari, tayi wanka, tayi kwalliya suka karya. Ya ce, “To bari ya je ya
duba lafiyar sauran Jama’ar gidan.
Nan ne ta ɓata rai, wai haka jiya ai ita bai zo ya duba ta ba, kuma ta fito taga ya dauki Amna.
Nan take ya dauke ta da yake Nafisa irin matan nan ne marasa kiba, sai dai tana da dan tsawo.
Amma sanfurin jikinta, sanfuri ne irin wanda zai yi wuya tayi kiba ko me zata ci.
Ya ce, “To dauka dai gashi na dauke ki ina zan kai ki? Ranta yayi dadi ta ce, “Ka kai ni dakina.”
Ya dire ta kan gado, a kunne ya rada mata wata magana da ta sata fashewa da dariya, tare da
saka kanta cikin filo. Yayi mata cakulkuli ya fita ya barta tana dariya.
Sha biyu ya gani lokacın da ya kalli agogon falon Amina. Lallai yau hira tayi dadi tsakanin shi da
Nafisa. Ya samu Amna zaune tsakiyar gado
tana waya da ‘yan gidansu. A yanayin maganarta ya gane cewa ‘yan gidansu sun sani, ta fada
musu kenan.
Ya zauna suyi da wannan, wannan ya kira. Bayan ta gama ta dubi Shatima, “Su Mom suna
gaida ka.” Ya ce, “Ina amsawa. Ya jikinki?” Ta ce, “Naji sauki.” Ya ce, “To kin yi karin kumallo?”
Ta ce, “Eh, su fa suka tashe ni da kiran waya. Yanzu kam dole in tashi in yi wanka in karya don
Direba yana hanya zai zo mu tafi.” Cikin mamaki ya ce, “Ina?” Ta ce, “Gida mana! Dad zai sa a duba ni na musamman. Shatima ya
ce, “Ba ki fada musu cewa an duba ki a nan ba?” Ta ce, “Na fada musu, ka san Dad baya son
wasa da lafiya.” Ta fadi tare da sauka ta nufi bayi.
Shatima yayi shiru kanshi a daure, lallai wata
sabuwar matsala kuma zata kunno kai a gidan shi.
Shi ne mijinta shi ya kamata a nemi izininsa kafin a fada mata, shi ne ya kamata ya fada mata
cewa Dad ya ce za ki je Kano a sake duba lafiyarki, amma sai gashi ita ce take bashi labari,
babu wani neman izini. Jiki babu karfi, ya shige zuwa gurin Aliya. Yanayin da ta ganshi taso taji
ko menene, amma ta
san ba zai fada ba. Haka Salma duk shirmenta sai da ta lura cewa yau din yana cikin damuwa.
Domin taga be tsokane ta ba. Ya dai miko mata kudin nama. Ta ce, “Me zata dafa?” Ya ce, “Tayi
abinda take so. Gaba daya sai ya ji gidan yayi masa kunci. Dakin Nafisa ya nufa ya dauki
makullin mota ya fita.
Shi kanshi bai san ina ya dosa ba don yana bukatar shawara. Titin da zai kai ka filin bajakoli
nan yasha kwana ya tsaya, saboda akwai karancin zirga-zirga a titin. Ya kifa kanshi a kan
sitiyarin motar.
Kamar minti daya ya dago, ya dauki waya ya shiga kiran layin Munnir. Babu jimawa Munnir ya
daga, tun daga gaisuwa Munnir ya fahimci akwai matsala. Ya ce, “Ya ya abokina, naji muryarka
wata
kala?” Ya ce, “Akwai matsala.” Ya karanto mishi
komai. Munnir ya ce, “Tabdi! To ai tun da wuri
zaka yi maganin wannan matsalar ba sai ka bari
tayi girman da zaka kasa magance ta ba.”
Shatima ya ce. “Ta ya ya? Ni bana son ne a ce daga aure dududu ko wata biyu ba mu cike ba
amma na soma kuno da matsala.”
Munnir ya ce, “Kai da ka ke da basira ma, kayi kokari sosai fa, da harka tara mata guda hudu
zuwa yanzun babu wata matsala ko wani korafi.
Mace daya