Showing 36001 words to 36679 words out of 36679 words
Chapter 13 - Rana Daya Book 2 By Halima Abdullahi k Mashi
bakar akuya da yawun bakinta da ruwan hawayenta
aka bashi yaci,daf da bikin nan fa har gida sai da ya siya masu da sauri Salma ta dago tana
fadin "wallahi Hajiya ba siya mana ya yi ba hayace,"Hayar.....
Hajiya ce ta sake jifarta da wayarta dake hannun ta "karya zanyi maki kenan dan ubanki?"
Aliya cikin sauri ta dauki wayar tare da fadin haba Hajiya wayarki kar tayi lahani mana.
Hameeda wacce tausayin Salma ya kamata haka kawai taji ba gaskiya bane abinda Hajiya take
fada ba,dan haka ta saci wayar Nafisa tayi cikin daki ta fada bandaki domin yin abinda ya dace.
Aliya ta kalli Hajiya kiyi hakuri bari in zuba maku abinci.
Sakawa Maman ku dan ni bazanci abincin nan ba sai anyita ta kare yau din nan.
Nafisa tace"gwara ayita ta kare domin kada kowa ta yadda kiri kiri hmm"
Aliya tace "aikuwa bayin kansa bane bakiji abinda akace bane"
Amna wadda ta yadda da zancen nan dari bisa dari ta kalli Salma cikin tsana indai tana gidan
nan kam nidai bazan zauna ba dan a gaskiya banason asirce asircen nan da akeyi.
Hameeda ta kira sau uku kafin ya daga tace Yaya don Allah kazo gida yanzun nan ga Salma
nan an tsareta su Hajiya ne"
Gaban Shatima ya fadi ya manta da tsanar da Hajiya tayiwa Salma, yace "nagode Hameeda
ganinan zuwa."
Lokacin tashinshi beyi ba haka dole ya tashi yaje gida da gaggawa domin kashe waccen wutar
wadda shedan ya rura a cikin sa ya dauki uzuri gaggawa ya fita bema san irin gudun da yakeyi
ba kawai saidai ya ganshi a layinsu,yana parking lokacin Mustapha ya fito daga falon Aliya.
Shatima ya nufi gurinshi "inasu Hajiya?" Mustapha yace suna falon Nafisa.
Shatima yace "to bari inje mu gaisa" Mustapha ya biyoshi domin ya gama cin abincinshine.tun
daga baranda yakejin muryoyinsu daya bayan daya.
Hajiya tana fadin"ba bakin dan akuya ba ko bakin dan jakane kukayi asiri dashi yau sai kin bar
gidan nan".
Cikin kuka Amna take fadin"yanzu zan kira Dadyna nima yazo ya daukeni dan bazaiyiwu in
zauna ba,Ina tsoron asiri".
Nafisa take fadin" jiya nan fa saida nayi mafarki da ita gaskiya bazan iya tuno meya faru a
mafarkin ba amma tabbas ita na gani,ni kaina idan tana gidan nan to wallahi Mama saidai mu
tafi daku yau din nan."
Mustapha ne yafara shiga hakanne ya hana Aliya magana taso tayi magana dan ta hangoshine
a tsaye.
Cikin tashin hankalin ya shigo cikin dakin gaba daya suka maida kallon su gareshi sannan
kowacce ta shiga nanata abinda zata nanata, kowacce ta nanata abinda ta fada.
Hajiya tace "duk kuyi shiru yanzun dai kai kazo ka zaba koni dana haifeka ko kuma iyalanka ko
kuma wannan Yarinyar ita kadai? Ta nuna Salma wacce take durkushe tana cikin firgici da
matsanancin tashin hankali,itama kallon shi takeyi cike da tsananin bukatar taimakon
shi,idanuntane suka nuna shi kadai take bukata,shine taimako na karshe da takesa rai zaiyi
wani abu akan wannan halin da take ciki.
Hajiya ta katseshi da fadin "Zan la'anceka!!!..." Zan la'anceka!!! In ka sake kallon ta,kuma na
baka nan da minti daya rak ka yanke hukunci..........
*Alhamdulillah anan muka kawo karshen littafi na biyu,a yanzu kuma labarin zai fara, akwai
cakwakiya fah,anan kuma muka kawo karshen free pages idan kina bukatar 3&4 din littafin
RANA DAYA ki turo kudin ki 300 ta wannan account number diní ½í±‡í ¼í¿»*
```ACT<<0700549935
Halima Abdullahi Access bank sai ku turo shidar biya ta wannan number 09028485925```
*Ko kuma katin Mtn ta wannan number 09068032427 Ga masu son Audio na littafin RANA
DAYA shima muna dashi cmplt ku turo kudin ku ta account number din da muka bada can
samaí ½í±†í ¼í¿»í ½í±†í ¼í¿»ko kuma katin Mtn ta wannan number 09068032427 idan baki shirya siya ba ki bari
sai kin shirya sai kiyi magana*
*Masu son tallata masu hajar su suyi magana ta wannan number 09068032427 zamuyi maku
cikin sauki*