Showing 33001 words to 36000 words out of 36679 words
Chapter 12 - Rana Daya Book 2 By Halima Abdullahi k Mashi
yana duba suman. Zumbur! Ya
mike tare da daga wayar ya ce, "Nafisa!"
Hamida ta ce,"Ni ce, ta ce kazo* Ya ce,
"To gani nan zuwa.Ya kalli Salma
"Ya aka yi?"
Tace,
"Yaya dama assignment ne za a nuna mini."
Ya kalli Aliya,
"Duba mata don Allah, bari in je gurin Nafisa in ji
Aliya tayi'yar dariyar yake tace
"Sai ka dawo, don Allah ka ce ina yi mata sannu.
Yana fita Aliya ta kalli Salma kallon sama da kasa irin kallon wulakanci da raini, ta ce "Aka yi
sati da Lahadi duk ba ki tuna da assignment ba sai yanzun da ki ka ganshi a nan dakin? To bari
in ja miki kunne, duk ranar da yake dakina na haramta miki zuwa.
Salma ta ce, "Anty don Allah kiyi hakuri, ina ta tunanin yanda zan ma Yaya magana ne,
" Aliya ta fizgi takardar tana dubawa. Salma ta ce
" Anty bari ki ga yanda aka ce….
Aliya ta katseta da cewa,
"Da Allah ni yi min shiru, ke ce za ki nuna min, tun kafin a haifi uwar me alli Balbela take da
farinta."
Salma ta ce,
"Me ki ka ce?" Aliya ta ce,
"Tun kina^yar mitsitsiyarki ni ke zuwa boko, kuma muke rubuta maths.
Salma ta ce, "Yi hakuri."
." Don ta lura Aliyar tayi maganar cikin fushi ne. bata koya mata ba, saidai ta rubuta ta bata tare
da cewa gashi nan ni bani da lokacin yi miki wani nune-nune.
Salma taje daki tana dubawa cikin kokwanto,tana tunanin gaskiya da kyar in haka ne, amma
zata je da shi Makaranta ta nuna ma Salma Dankasa
Shatima ya shigo,
"Ina Salman?" Ta ce,
"Nayi mata ta wuce, yarinyar nan Allah Yasa dai tayi karatu, naga dan abin da ta kasa
ganewa,ga takardarta duk ziro
Ya ce,
"To don Allah ki ke taimaka mata, sai a
hankali.Aliya ta ce,
"Har Lesson na ce zan ke yi mata." Ya ce, "To ai ko na gode. Yanzu ina zan samu zogala?" Ta
ce, "Wake so?" Yace"Nafisa.Ce.
Tace
"Gashi dare ya yi. Amma ka tambayi
Maigadi, in za'a samu danye sai a dafa mata yanzun ayi mata kwado.
Ya ce,
"Haka ne.
Maigadi ya ce, "Can makotan suna da shi
Sai gashi an samu, nan da nan Aliya ta zage ta dafa, ta cE
"Sai kuma in da za a samu kuli-kuli
Nan ma Maigadin aka sake tuntuba. Shi ya bazu cikin unguwa sai kusan sha daya saura ya
dawo. Kura-Kura aka samo. Aliya dai aka zage aka daka, ta kwadanta mata. Nan ya dauka ya
kai mata. Tasa a gaba kuwa tayi ta ci, cikin ikon Allah kuma sai gashi bata yi amai ba,
Salma tana zuwa Makaranta, ta nuna ma Salma Dankasa, Salma ta ce
"Wa ya yi miki?"
Tace *Matar Yayana
Salma ta ce,
"To ba daidai bane.
Ta dauko littafinta ta nuna mata.
*Kin ga nIfa.
* Salma mamaki ya cikata, amma ta share tace "Bari ta sake kwalewa sai tayi kafin Malaminsu
ya iso."
Amna cikin bacci taji karar wayar Shatima. Ta kalle shi yana ta bacci, da alamu yau ya gaji
sosai,don sun je Abuja ne sai ma goma ya shigo gidan.
Ta kai hannu ta shafa fuskarshi,
"Honey ana kiran wayarka tun dazu." Ya bude ido da kyar, taCe
"Ka gaji ko?" Ya ce,
"Na gaji sosai."
Yana daukar wayar daidai lokacin kiran ya tsinke.
Yana dubawa yaga sau tara ana kira. "Nafisa!"
ya furta da karfi tare da mikewa tamkar bai taba bacci ba. Amna ta dube shi, "Wai ina za ka?"
Yace,
"Nafisa, ina zaton jikin ne."
Amna ta sakko itama bata yi mishi magana ba,illa dai taje ta murda makullin kofa ta cire key din
tare da fadin, "Ba za ka fita ba. Na gaji da irin wannan abun, don ciki bai fi ciki ba.
Saboda salo bata tashi kiranka sai ranar da ka ke dakina? Sau biyu tana yi min haka, ba zan
bari tayi na uku ba, tunda naga abin nata yana neman ya zarme.
Shatima ya ce, "Haba Honey, kin san fa cikinta ba irin naki ba ne.
Ta ce, cikin mamaki,
"Au!
Dama akwai wani ciki na musamman ne wanda kayi mata shi ni baka yi min ba?" Ya ce "Ba
haka nake nufi ba, nata cikin me yawan laulayi ne. Don Shatima ya kira. Hamida ta ce,
"Tun dazun yake kira." Aliya ta ce "Bar shi kar ki daga har sai ya fito, in yana dakin wannan 'yar
gwal din ba ya iya fitowa, yanzu dubi jikin baiwar Allahn nan amma ya wofintar da ita.Hamida ta
ce
"Allah nima abin ya bani haushi,
na kira shi ya fi sau ishirin amma bai ko daga ba
Da ya daga ya ce min yana zuwa shine fa shiru Aliya ta ce,
"Sai ga shi ya kira ni wai inzo
Hamida ta cE
"Ai mun gode, Allah ya saka dabalkairi. Ai har Mamanmu na fada mata irin taimakon da ki ke
mana.Aliya ta ce,
"Ai yi wa kai ne.
" Sai da aka kira sallar Asubahi sannan ta koma dakinta.
Shi ko Shatima zama ya yi a kan durowar gefen gado, yana ta kiran layin Aliya, ita kuma ta baro
ta can dakinta domin da ta Nafisa ya yi ta kira yana tambayar Hamida ko Aliya tazo? Tana fada
masa cewa bata z0 ba.
Bayan yayì sallah ya ce "To yanzun sai ki bude ni in dubo ta ko?"
Ta Ce
'"Ai ba yanzun ka ke zuwa ba.
Ya cE
"To yanzun kuma zamu iya samun matsala tunda gari ya waye
Ta ce,
"Mu samu mana, dama nasan ba zaka kula dani ba kaje ka rabo ni da gidanmu ina can cikin
tattali
kaje ka dauko ni."
Ya ce, "Kin raina kulawar da nake ba ki? To kifada min abin da ki ke son in ke miki don ki
tabbatar da ina kula da ke
" Ya fada ranshi a bace.
Ta ce
"Ga shi ka kwana zaune kana dakina
zuciyarka na gurin wata."
Ta ce, "Yiwa kai ne dai,kuma bana fata kema wata rana in haka ta faru zaki ji dadì in ta hana ni
fitowa in wofintar da ke?"
Ta ce"Ni dai ba zan bude ba, dama ka shiga wanka in ba haka ba zaka yi lattin zuwa office."
Ganin da gaske ba za ta bude ba, ya bi shawarar ta ya shiga wanka. Kan ya fito ta bude sai ya
fita zuwa dakinsa ya hau shiri.
Bai ko kalli karin da Ladi Mai aiki ta hada mishi ba, ya nufi fita. Kofar a damke take, ya waigo ta
fito tana tsaye a falon. Ta ce,
"Ga abin karinka.
" Ya girgiza kai, "Bana jin yunwa.
Ta ce,
'"Ai ko ba za ka dakin wata ka karya ba.
Ta soma hada mishi shayi, Har gurin Kofar ta
Zota bashi. Ya amsa tare da fadin "In da ace za ki ke hada min ko shayin ne a duk ranar da nike
dakin ki da na yi tasa miki albarka Ya kai
Karshen maganar tare da kurbar shayin
Da sauri ya watso shi domin suga ya ji har
cikin kwakwalwar kanshi. Ya mika mata shayin
"Ga abin ki, bude ni." Ta kalli agogo, duk abinka sai shida ta cika,
Ya ce,
"Amna har yanzun ina mamakin ki sosai, ashe kin iya mugunta har haka?"
' Ta ce,
Na daina bari ana raina min wayo."
Ya jingina da bango,
"Shidar dai saura minti hudu.
Ta ce,Inma minti daya ne sai ya cika."
Ya samu Nafisa a yan da take, ya kira Likita ya ce zai kawo ta asibiti don fa jikinta ya yi laushi
Likitan yace
"Ko ka kawo ta babu abin da zamu ¡ya mata da ya wuce wannan ruwan. Amma zan
fita zuwa asibiti, ka fito bakin titi in same ka sai
muje in ga.jikin.Haka kuwa Shatima ya fita ya yi jiran kusan
minti biyar kafin Likitan ya iso. Shi kanshi Likitan
ya tausaya ma Nafisa, ya ba da wata allura ta
tsaida amai, ya ce ayi mata a gani. Amma ciki irin
wannan Kila sai ta kai wata biyar zata samu dan Salma tana ta jiran Shatima har takwas ta gota
Ta fito taje dakin Aliya nemanshi. Aliya ta ce an fada miki nan yake?"Salma ta ce,
"Ni wallahi yanzun bana tuna in da yake."
Ta ce,
"Yana dakin Amna.
" Har zata wuce sai
taga sun fito da Likita. Ta rusuna ta gaida su,sannan ta ce.
"Yaya mun yi latti.Ya kalli agogon
hannunsa. "Haka ne, ya ba ki tafi ba? Nafisa ce ba lafiya ban san lokaci ya tafi haka ba.
Ta ce,
"Anty ba lafiya, bari in dubata.
Sun gaisa da Hamida, sannan tayi wa Nafisar sannu.
Ranar latti taje Makaranta, sai da ya roka aka bude
mata don har sun ce ta koma.
**
Wata ranar Litinin misalin Rarfe biyu da minti bakwai. Salma ta sauka daga kan Mashin a bakin
Gate din gidansu. Ta ba mai mashin kudin sai taga bakuwar mota zata shiga gidan.
Maigadi yazo yana tambayar Direban gurin wa suka z0? Salma ta kalli Direban, kamar ta taba
ganinshi a wani guri. Sun yi kama da Shatima kadan.
Taji lokacin daga bayan motar an ce,
"Uwar Maigidan ce
Gaban Salma ya fadi, domin ko a
ina taji muryar Hajiyar Shatima ba za ta manta ba.
[8/19, 18:44] Ummi Tandamaí ½í¸‡: _________
*í ¼í¿šï¸�RANA DAYA BOOK 2í ¼í¿šï¸�*
CHAPTER 16 Karshen book 2
*BY HALIMA ABDALLAHI K/ MASHI*
Ta nufi cikin gidan gaba daya jiki a sanyaye,ta kasa bude kofarta,tabi motar da kallo har lokacin
da taga motar ta tsaya daga cikin jerin motocin Amna da Shatima.
Ta bude kofarta ta shige,kasa cire kayan jikin ta tayi na makarantar haka kuma ta kasa dora
girki,sai da tayi ta maza ta kunna risho ta dora tafasasshen nama.
Lokacin da su Hajiya suka shiga gurin Nafisa tana wanka,Hameeda tayiwa Mama da Hajiya
oyoyo Aliya ta leko taga bakin Nafisa ne Dan haka sai ta yafa mayafi taje ta nufi wajen Nafisa
da sigar duba jiki,tana shiga taga su Hajiya gabanta saida ya fadi tasan Hajiya ba kalar wasa
bace, amma duk da haka saita cije ta zube ta kwashi gaisuwa a gabansu tana gaishe su yanda
kasan zatayi masu sujada saboda girmamawa,Hameeda ne ta ajiye masu ruwa da lemu Aliya
tace" Ya jikin Nafisa yau dai jiki da sauki? Hameeda tace "to gata nan ciki tana wanka".
Cikin kissa tace "Masha Allah naji dadi sosai,tasha magungunan ta kuwa?".
"Kinsan kuwa sai kinzo take sha,domin nidai nayi nayi da ita takisha"
Aliya tace "to bari ta fito inna lallasheta nasan zatasha haka za'ayi tayi hakuri da ita bansan inda
zan samu tsakin nan bane bare ayimata abinda takeso amma ga rama can maigadi ya siyo
mana".
Duk zubar da takeyi su Hajiya suna jin ta kuma sun yaba da maganganun ta musamman ma
mahaifiyar Nafisa dan ance me da Wawa,Mama tace "Allah sarki kina dawainiya da Yarinyar
nan Kullum Hameeda tana fadaman duk abinda ke faruwa har dare kina zuwa ki dubata."
Hajiya tace "haka akeso aishi zaman aure dama zaman tare haka akeson babba ya kasance,ita
Yar'uwar takufa?
Aliya tace"Amna tana gurinta itama da sauki domin bacci takeyi,bari dai induba ta inaga yanzu
ta tashi,Mama tace"Allah sarki kina dawainiya da wannan kiyi dawainiya da wancan kiyi da
wannan Allah ya yi maki albarka.
Aliya ta amsa da"ameen" ta fita cikin jin dadi ta nufi shashin Amna domin dai burin ta kawai ta
shiga ne gurin kowa taga yadda yake,hakan ne zai bata damar kunna wutar da take bukata a
wannan gida,ta samu Amna a zaune tana kallon T.v mai aikin ta kuma tana bare mata kwai a
gefe akan filet.
Tace "sannu da hutawa"
Kallo daya Amna tayi mata,sannan tace"yauwa sannunta" ta maida kanta gurin T.v.
Aliya tace "Hajiyan Shatima ne tazo tana dakin Nafisa tana bukatar ki,tace inzo inkira ki."
Amna tace "Ina zuwa"
Aliya ta juya ta fice.
Tsaki kawai Amna taja banda Hajiya ce babu abinda zaisa taje wani dakin wata daga cikin
su,dan kawai ta nunamana cewa tafison yar'uwarsu ne kowaye Nafisa tafi Oho.....
Aliya na fita dakin Salma ta nufa ta sameta a jingine tayi jajjage.
Tace "to gasu Hajiyar Shatima can kije ki gaidasu Maman Shatima ne,Salma ta danyi rau rau da
ido cike da tsoro,tace "Aunty tsoro nikeji"
"Tsoron wa.?"
Salma tace Hajiya wallahi,Aliya ta"sai kace wata mayya,ta haifa maki miji gashi nan yanata
kashe maki uban kudi amma kice wai kinajin tsoron ta".
Salma tace "ba haka bane Aunty,ta taba man fada kuma ni ina tsoron fadanta.
Aliya tayi murmushin mugunta a ranta tace yanzu ma wani fadan zan sake ja maki,ta dubi
Salma tace to wuce kije ki gaisheta," Salma tace to bari in canza kaya in cire na makarantar
nan.
"Ta ya mutsa fuska jin cewa Salma zata samu canza kaya,inta cire kayan nan ai shikenan zata
rage mata sauki ma har ta samu tseguntawa Hajiya irin kudin da ke kashewa Salma wadda abin
ke damunta Kullum, Salma ta dauki dan mayafin jallabiyar ta tayafa tunda daga kanta babu dan
kwali ta fito cikin fargaba ta nufi shashen Nafisa.
Aliya ta shiga dakin ta dama ranar itace da Shatima kuma ta shirya mashi farfesun kaza yana
wuta batama gama ba,sannan tayi dafadukan cos-cos da hanta,nan ta jerowa su Hajiya a katon
tire ta shigo dakin Nafisa ta samu Salma tana rabe rabe a gefe ta kasa karasawa ciki,harda
tsawar ta tace "muje mana kin wani rabe gefe guda."
Hajiya tace"wacece?" Aliya cikin sigar son tura kiyayyar Salma ga surukar tasu tace "Salma ce
uwar shanshanci".
Hajiya ta gimtse fuska harma da Amna da Maman Nafisa da suke zaune, Salma ta tsugunna a
gabansu kana kallon ta kasan a firgice take,Aliya ta dire tiren a gabansu nan kamshi ya daki
cikin su,ta kalli Hameeda "kawo filet da cukula mana kisa".
Salma cikin raunin murya tace sannunku da zuwa Hajiya,Mama ne kadai ta amsa "yauwa sannu
Yarinyar nan".
Ta kalli Nafisa wacce ke zaune saman kujera tace sannu Aunty ya jikin? Itama fuskar ta a daure
tace "jiki da sauki" ta yunkura zata mike Hajiya tace koma ki zauna"
Salma ta zaro ido tare da zama cikin tsananin faduwar gaba,ta tuno alwashin da Hajiya tayi sai
tazo har kaduna tasa ankoreta,hawaye suka soma zubo mata...
Muryar Hajiya ne ya katseta daga tunanin da takeyi "iyayen kine sukazo daga Zaria suka saki
makaranta?". Cikin in inah Salma tace a'ah.
Aliya tace "Ina sukaga halin sata a makaranta sunaji da abinda zasuci" Salma ta kalli Aliya a
tunanin ta wannan maganar ta Aliya kamar tayine domin kareta a gurin Hajiya sai kawai taji
Hajiya tace
"Badai shi Shatima ne yasata ba?"
Nafisa ta tabe baki "shiyasa ta mana Hajiya makaranta me shegen tsada"
Aliya tace "tsada ai ba kadan ba ma tsadar,kusan dubu dari harda doriya"
Amna ta kalli Aliya domin jin bakon lamari ita bata shiga harkar kowa batasan ma me akeyi a
gidan ba.
Hajiy tace "Eyyeh!"
Aliya tace "to ai kudin shiga makarantar nan dubu saba'in da biyar ne banda kudin motar
dawowar ta da Kullum sai ya bada dari biyar ga kudin namanta da komai da yake badawa dubu
daya,"Aliya takai karshen maganar tanajin dadin tasamu abinda takeso.
Hajiya ta kalli Salma cike da tsana tace hakane kudin makarantar dubu saba'in da biyar?
Salma cikin rawar jiki tace "yanzu sun cike tamanin".
Hajiya ta mike da sauri tana fadin "lallai kam sun cike tamanin wato ke yakeyiwa aiki kenan
kullum rana ta Allah dubu daya da dari biyar a wata nawa zai kama? Jama'a kuyi mani lissafi?
Da sauri Amna tace dubu arba'in da biyar kenan zai kama duk wata"
Nafisa tace "Kan uba!! Muna zaune?"
Hajiya tace "to aikoni dana haifeshi idan ya yi man haka nasan ya kai daa"
Maman Nafisa tace "to shime yakaishi wannan batan basira? Wai rokon Allah da goge"
Hajiya ta soma kiran layinshi ya daga tace "Ina gidanka Allah yasa ka kusa tashi" yace "insha
Allahu nan da awa daya zan dawo" tace "saika iso" keda wayene? "Nida Mamanku ne
Mustapha ne ya kawomu".
Salma wacce sautin kukanta ya fara fitowa tace "don Allah Hajiya kuyi hakuri....."jifar da Hajiya
tayi matane da karamin filon kan kujera ya hanata karasa maganar ta.
Hajiya tacigaba da cewa "banason jin komai daga gareki Yar gidan masu asiri kawai,ai tundaga
lokacin da yaron nan ya zoman tamkar zaiyi hauka akan wannan kazamiyar Yarinyar nasan
aikin asirine.
Ta kalli Maman su Nafisa ki tunafa be taba kwanciya a asibiti akan wata ba sai silar wannan
Yarinyar dan nace bazai aureta ba ranar ya tashi a sankare idanuwa a kakkafe mukai asibiti"
Duk matan nan suka kalli Salma cikin mamaki musamman ma Amna wadda take da matukar
tsoron asiri.
Nafisa tace "wai dama ciwon nan nashi yanada nasaba da itane?"
Hajiya tace "inkinje gaba ma saiki fada daga nan abinda nayi mashi ya yi yawa kawai sai nasa
ayiman tambaya wajen malamai can ne suka fadaman wai uwar tane tasa akayi masa asiri da
sunan Shatima kuma an hada da naman